Showing 39001 words to 42000 words out of 82977 words

Chapter 14 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt

27 Sep 2025

3171

Amira ita kuma tafara tattare kwanukan abincin da yaci.


Nadiya kam tana daki bata san abinda yake gudana ba amma jitake aranta amadi yama yi mugun raina mata hankali, daga ganin kanwarta sai yace ita yake so yanzu?

Tsaki taja tayi juyi, "koma menene shi yajiyo dai dama ni ba sonshi nake yiba.."

Shigowar Amira ne ya katse mata tunani, "su fadeel sunbi yaya Ahmad unguwa"

"Kuma meye nawa ni aciki?" Nadiya ta bata amsa cikin fada, fita Amira tayi daga cikin dakin, jin karar shigowar massage awayarta yasata dubawa,

_Wasafa nake yimiki babu wata shek'a da na sauya, so karki fara kishi da kanwarki dan naga har kishi ya bayyana acikin idonki karara,munje unguwa da twins dina nasan ke ko nace kizo ki rakamu ba zuwa zakiyi ba shiyasa banyi inviting dinki ba, sai mun dawo,1,4,3.._


Gyara kwanciyarta tayi tana hararar wayar kamar yana wurin, "ruwanka kuma"

Amadi wurin wasan yara ya nufa dasu fadeel, kowa yagansu zaiyi tsammanin cewar yaranshi ne gashi suma sun fara shakuwa dashi sosai,

Wasa suka rinka yi cikin farin ciki shikuma yana yimusu pics wani lokacin kuma ya shiga yayi musu tare, shi kansa bai san adadin yawan hotunan da yayi musu ba,

Sai da sukayi wasa mai isarsu suka gaji tikis suka fara kiran yunwa sannan ya daukesu zuwa wani restaurant dake gaba kadan da wajen wasan yaran,

Fito dasu yayi suka shiga ciki yayi musu order din abinci, amala da miyar ganye da kaza, shi yarinka basu abincin har suka koshi sannan yaci yabiya kudin abincin suka fito,

Maimakon yakaisu gida sai ya nufi supermarket dasu nan suka shiga ya lodo musu kayan dadi kala kala yafito yana rikeda fadeela daya hannun kuma ledar da ya iyo shopping ce fadeel kuma yana biye dasu,

Kamar a mafarki kabeer ya hango yaranshi wani rike dasu lokacin da yake packing acikin harabar supermarket din, duk da yadade rabonshi da yaran domin ba zuwa ganinsu yakeba amma ai bazai iya mantasu ba, cikin gaggawa ya fito daga cikin motarshi ya nufi wurinsu amadi,

Amadi yana kokarin bude motarshi kabeer ya isa wurin,

"Fadeel,fadeela...."

Kabeer ya kira sunan yaranshi yana karewa amadi kallo,

"Bawan Allah kai kuma waye da zaka dauko min yara ka kawosu nan wurin batare da izinina ba?" Kabeer yafada cikin gadara,

Kallonsa amadi yayi "banfa ganeka ba, waye kai please"

"Ohhh tambayata ma kake ko waye ni? Ok to nine mahaifin wadannan yaran kai kuma waye"

"Allah sarki, ni nine wanda yake shirin zama babansu ta hanyar auren mahaifiyarsu"

Ai take zuciyar kabeer ta tsananta bugu kishi ya bayyana a fuskarsa karara, haushin amadi ya kamashi musamman ma da yaganshi handsome babu alamun kauyanci ko shirme atare dashi,

"To bani yaya na inyaso kaje ka auri uwar tasu ita kadai amma yaya tunda nawane babu wanda zaiyi min gadara dasu"

Murmushi amadi yayi wanda ya bayyanar da beautiful point dinshi,

"Amma dai kasan ai ba kai kadai ka haifi yaran ba ko? Dan haka tunda bakai kadai ka haifesu ba to baka da iko dasu kai kadai, idan yaranka kakeso ka karba kaje gidansu nadiya ka karbesu acan, amma nidai yanzu bazan baka yaraba yanda nafito dasu sai na mayar dasu wurinda na daukosu.."

Kabeer najin haka yatada fada yana daga murya kamar wani zautacce,

"Wallahi sai kabani yarana saboda bakai ka haifa min suba, kai fadeel kuzo mu tafi nine ubanku ba wannan ba"

Zuwa yayi zai kama hannun yaran anan suka fashe da kuka suka kankame amadi suna makale kafada alamun bazasuje wurinsa ba abinda yayi mutukar sake daga hankalin kabeer,

Nan mutane suka fara taruwa kabeer sai fada yake yana zagin amadi kamar wani marar hankali, ko takansa amadi baibi yasaka su fadeel a mota yashiga yatashi motarsa yabar kabeer yana cewa,

"Wallahi yarana zan karbo, sai anbani yayana.."

Wannan shine mafarin nadamar kabeer saboda yahadu da yayanshi na cikinsa amma sunki zuwa wurinsa daga yakai hannu zai tabasu sai su saka kuka.

Nadiya na daki azaune bayan tayi wanka ta shirya tana kwalliya su fadeel suka shigo dagudu, fadeel ne mai kokarin dauko ledar siyayyar da amadi yayi musu,

"Momy kinga uncle ya siya mana, kuma mun hadu da wani a supermarket sunyi fada da uncle yace wai shine babanmu.."

Fadeela tafada tana zama akan cinyarta, sake tambayar fadeel tayi nan yafada mata kamar yadda fadeela ta fada,

Tashi tayi tafita waje wurin amadi, yana saman motarshi azaune,

Tsayawa tayi ajikin motar tana son ta tambayeshi abinda su fadeela suka fada mata amma takasa saboda basa doguwar magana dashi.

Zuwa can tadaure ta kalleshi tace,

"Naji su fadeel suna fada min wani zance"

"Name?" Ya tambayeta,

"Wai kun hadu da abbansu a supermarket"

Shiru yayi mata baiyi magana ba,

"Ya kayi shiru?"

"Ehhh"

Yace da ita yana kokarin dirowa daga saman motarsa,

"Dagaske ne mun hadu dashi may be ma kiganshi yazo anjima.."

Sai da taji kanta ya sara saboda ita yanzu bata son duk wani abu wanda zai hadata da yaya kabeer,

"Zanje in tafi amma wannan shine tafiyata ta karshe bazan sake dawowa gidanku ba har sai naji matsayina awurinki, dan haka nabaki dama ki zauna kiyi shawara da zuciyarki sannan ki yanke hukunci akan maganarmu, idan har zaki aure ni kifada min idan bazaki aure niba karki boye min ki sanar dani gaskiya, nabarki lafiya"

Bai jira amsar da zata bashi ba ya wuceta yaje ya bude motarsa ya zabureta yabar wurin.....




*Fatan Alkhairi ga k'awar kirki maryama qaumi...*



_Gaisuwa mai yawa ga masoyan littafin mijina sirrina, khairat dan dawaki,heedah, hajjaju chuchu, Nasma, kadija mai kano, Billy reality, mom amir,ummy aysha, meenah 4eva da duk wata masoyiyar MS.._






*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_




_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*




® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




Your birth day is the perfect day to say I care, because you will remeber me when u certainly make it a big affair, and when you do hold a party... I bet you will be the one who would care
to make ur special day a costly affair!!!!HBD MARYAM QAUMI.


_Fatan alkhairi ga masoyan Anty amadi, Hawwa mudi, baddo alka, salma luv and others.._








*44*


aishaummi.blogspot.com




*K*asa motsi nadiya tayi illah kawai kallo data rinka bin motar amadi dashi har ta daina hangoshi, gabanta ne taji ya tsinke yafara faduwa wanda bata san dalili ba,

Dakyar tayi ta maza taja kafarta tabar wurin ta nufi cikin gida, da amira tafara cin karo tana kokarin hada kayan wanke wanke, daf da zata wuce ta shiga daki taji maganar mama daga kofar kitchen tana yimata magana,

"Bakon naki yatafi?"

"Ehh mama yatafi.." Tafada jikinta asanyaye,

Kallonta mama tayi dakyau anan tagane cewar akwai abinda yake damunta dan haka tasake yimata magana,

"Nadiya ya kamata dai ki zauna kiyiwa kanki karatun ta nutsu domin wallahi ina jiye miki yin nadama aduk ranar da kika bari wannan yaron ya subuce miki, kiduba kiga irin dawainiyar da yake yi da yaranki, ko haka ai yasa ki saurareshi.."

Shiru tayi tana sauraren mama,itafa kowa yakasa gane matsalarta ne, ita gaba daya mazanne yanzu sun gama fita aranta, gani takeyi tunda yaya kabeer yayi mata wannan cin mutuncin to kowanne namiji ma hakan zaiyi mata,

"Kinji abinda nafada miki ko..?"

Muryar mama tadawo da ita cikin hayyacinta,

"Ehhh naji mama.." Tabawa mama amsa, juyawa Maman tayi ta nufi cikin kitchen tana cewa,

"Yawwa yadai fi miki"

Daki ta shiga nan tasamu su fadeel duk sun wargaza kayan siyayyar da amadi ya iyo musu suda su waleeda da husna,

Ko takansu bata biba ta nemi wuri ta zauna tana tunanin abinda zaije yazo nan gaba acikin rayuwarta, da ace su mama zasu barta to da ita da sake yin aure sai a lahira amma aduniya dai kam tagama,

Tadade tana tunani acikin ranta har na tsawon wani lokaci,shigowar Amira ce ta katse mata tunanin da takeyi,

"Anty nadiya wai ana sallama dake awaje.."

"Amira dan Allah ku kyaleni kaina ciwo yakeyi.."

Juyawa Amira tayi tafita,Amira bata jima da fitaba mama tashigo dakin,

"Haba nadiya ki leka mana kiga ko wanene inyaso sai kibashi hakuri tunda bakya jin dadi.."

Mikewa tayi ta fita batare da tayi magana ba,

Kamar acikin mafarki ta hangoshi tsaye yasha wani black space (no respect) kamar kada ta karasa wurin sai kuma taga cewar gara taje inyaso sai ayi wacce za ayi,

Yanda yasha kunu ya hade girar sama da kasa haka itama tasha kunun ta daure fuskarta tamau fiyeda yadda ya daure tasa,

"Lallai yaya kabeer dinnanma dan rainin wayone.." Tafada acikin zuciyarta gamida karasawa wurinda yake zuciyarta cikeda tsanarsa tareda jin haushinsa, ita sai yanzuma take nadamar kasancewarta matarsa ada,

Ko sallama bata yimasa ba ta tsaya tareda rike kugu,

"Naji ance ana sallama dani dama kaine? Idan Kaine to gani kayi kafadi abinda ya kawoka domin sauri nake.."

Mamakine ya kama kabeer ganin yanda nadiya ke faman kallonshi shekeke tana yimasa kallon hadirin kaji,

"Waye wanda naga yakai su fadeela supermarket...?" Yafada cikin kunar rai tareda gadarar cewar yaranshi ne,

Saida ta dan yimasa wani kallo mai taken ka rainawa kanka wayo sannan tace,

"Saurayina ne wanda zan aura, da magana ne?"

Wani takaici da haushine suka ziyarci kabeer lokaci guda,kallonta yayi ta cikin bakin glass dinshi,

"Saurayinki?"

"Kwarai kuwa domin ba bazawari bane saurayine sabo fil..."

Saurin dakatar da ita yayi, "ya isa haka, kina jina, kibude kunnenki dakyau kiji daga yau sai yau, kar wani wanda ya sake gigin daukar min yarana domin ba wani dan iska bane ya haifar minsu, nine na haifi abina.."

"Dakata yaya kabeer, kai har kana da bakin da zaka kira su fadeel da sunan yaranka? Yaran da kayi watsi da rayuwarsu ka banzantar dasu, yaran da harma sun manta da cewar kaine ubansu, tunda muka rabu dakai daidai da rana daya baka taba zuwa ka gansu ba bare ka dauki dawainiyarsu, kaga kuwa indai hakane to baka da bakin da zaka kirasu da 'yayanka..." Ta karashe maganar tana yin hucin bacin rai,

"Haka kikace? Nadiya ni kike fadawa haka? To tunda abin babu mutunci aciki wallahi sai kin bani yarana, zanzo zan tafi da yayana inyaso kije ki auri duk uban wanda zaki aura.."

"Wannan ne kuma baka isaba, sannan ni ba uban wani zan aura ba saurayi zan aura mai sona wanda babu abinda yasani na yaudara baima taba auren ba bare har ya zama uban wani.."

Tana gama fadin haka ta juya tafara tafiya batare data sake sauraron kabeer ba, in banda daci babu abinda makogaron kabeer yakeyi saboda yasan nadiya magana ta fada masa,sannan gashi zatayi aure zata auri wani wanda bashiba,

"To tunda kin zabi ayi rashin mutunci kisani wallahi sai na karbi yayana ko da karfin hukuma ne.."

Tana jinsa amma bata waiwayo ba saboda ita yanzu bata kaunar koda ganin fuskarsa ne, kanta kuwa in banda ciwo babu abinda yakeyi saboda tashin hankalin yaya kabeer,

"Ohh ni nadiya ko sai yaushe zan samu kwanciyar hankali?" Ta tambayi zuciyarta, ko mama bata fadawa cewar kabeer bane bare tafada mata yanda sukayi dashi ta shige daki ta kwanta.


Tana kwance adaki har lokacin sallar isha yayi, tana jin dawowar Abba amma bata iya fita taje tayi masa sannu da zuwa ba saboda ciwon da kanta keyi mata.

Abangaren amadi kuwa abinda yafadawa nadiya kawai yafada ne saboda yana son ta amince ta aureshi amma yasan bazai iya rabuwa da itaba koda kuwa zata cigaba da fada masa bata sonshi kamar yadda ta saba,

Karfe 5 da yan mintuna ya isa gida, lokacin da yayi packing din motarshi yana kokarin fitowa yaji ihun murnar su inteesar da hamid yaran anty siyama,

Fitowa yayi ya rike da hannunsu,

"Uncle amadi tun dazu munata jiranka kadawo ka kaimu..."

"Ohhhh hamid rigima kai kullum a zuwa yawo kake ne..?"

Falo suka shiga inda su hajiya ke zaune itada anty siyama suna kallon labarai,

Zama yayi acikin kujera sharaff alamun agajiye yake,

"Anty Amadi daga ina haka?" Anty siyama ta tambayeshi tana rikeda juice a hannunta,

"Anty daga zance nake.."

Murmushi tayi ta kurbi juice din dake hannunta,

"Kaima wasa kake, yaya zakayi da zee?"

"Nidai anty mubar wannan maganar, yanzu dai yaushe zanzo nakai su inteesar yawo..?"

"Haka dai kake koda yaushe baka son maganar aure, ban saniba ko haka zaka zauna babu aure, ai tun yanzu ya kamata kafara neman kaga idan lokacin yazo shikenan sai kawai atada maganar aure.."

"To anty" yafadi tareda mikewa kasancewar agajiye yake liss, dakinsa yawuce domin watsa ruwa amma kuma zuciyarshi sai tuno masa da rabin ransa takeyi wato nadiya,

Bayan yafito daga wankan ne yaji bazai iya yin komai ba har sai ya kirata yaji muryarta,

Tana tukunkune ciwon kai na azabtar da ita taji karar wayarta sharewa tayi taki dauka duk da cewar bata san wanene mai kiran ba,

Kasancewar yasan halinta na kin daukar waya idan bata gadamaba yasashi hakura bai sake kiraba ya ajiye wayar yafita zuwa falo wurinsu hajiya, kusa da hajiya ya zauna,

"Hajiya yau me kuka dafa ne?"

"Autana ai yau girkinka nayi maka daban, abinda kafi so nasa aka dafa maka..."

"My hajiya kince yau inji dadina kenan.."

Yafada yana murmushi tareda tashi ya nufi kan dining yana jin anty siyama tana cewa,

"Kaga dan gatan hajiya"

Murmushi yayi baice komai ba saboda idan da sabo to yasaba da tsokanar da anty siyama take yimasa.

Duk da cewar ya kira nadiya bata daga ba hakan bai hanashi sake kiranta ba da misalin karfe 9 nadare, amira ce ta dauki wayar saboda ita nadiyan tayi bacci, ai amira nafada masa nadiya bata da lafiya ya gigice ya rude,

"Yanzu tana ina?"

"Gata tana bacci.."

Katse wayar yayi yazauna abakin gadonshi duk sai yake jin jikinsa yana sauya masa, bai san wanne irin so yake yiwa nadiya ba, kasa aiwatar da komai yayi ya zauna shiru har na wani lokaci,

Ganin karfe 11 saura yasa yasake kiranta, lokacin ta farka tana dafe da kanta wanda yake yimata zazzafan ciwo....




*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA..!*🌹
_(Labarin k'auna)_




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


® *HASKE WRITERS ASSO* _(Home of expert & perfect writers)_




*Gaisuwa mai yawa ga HAJARA MAMI (Natty girl) ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike..*


_Fatan alkhairi ga Easha Bagwai & Dshanty..._




*45*



aishaummi.blogspot.com




*D*a k'yar ta iya daukar wayar tana mai runtse idanuwanta saboda zafin ciwo,

"Sannu nadiya... Ya jikin naki?" Yafada muryarsa asanyaye kamar shine bashida lafiyar,

"Da sauki.."

"Meke damunki?"

"Kainane yake ciwo"

"Kinsha magani?"

Duk ta kosa da wadannan maganganun da sukeyi saboda sarawar da kanta keyi mata,

"Uhmmm, kinsha magani?"

"Nasha.."

"Sannu, Allah yabaki lafiya"

"Amin"

Shiru kowannensu yayi shi yana tsoron kar ya cigaba da magana ya dameta ita kuma dama duk tagama kosawa da maganar da sukeyi, ahaka suka cigaba da zaman kurame har na tsawon minti ishirin sai can ya dan saki ajiyar zuciya yayi magana,

"Baby ko kinyi bacci ne?"

"Uhm, uhm.." Ta amsa masa,

"Kinci abinci ne?"

"Uhm" tasake bashi amsa, shirun suka sake yi,

Tana rike da kanta bata iya komawa bacci ba saboda baccin da tayi dazu har dare ya raba,

Yanda batayi bacci ba haka shima amadi baiyi baccinba sai dai idan ya danji shiru yace ko tayi bacci tace a'a ahaka suka zauna har wurin karfe 4 sai lokacin tasamu barci ya dauketa, jin yayi magana shiru bata amsaba ya tabbatar masa da tayi bacci sai lokacin shima yasamu ya dan kwanta kafin asuba ta karasa.


***


A fusace kabeer yabar gidansu nadiya yana driving yana tsaki gamida masifa shi kadai,

"Harni yarinyar nan zata cewa wai saurayi zata aura? To ta auri jariri ma karewar yarinta..."

Shi gaba daya maganganunta babu abinda ya bata masa rai kamar auren da yaji zatayi nan yaji tsohuwar soyayyarta ta motsa masa take sonta ya dawo sabo fil acikin zuciyarsa yaji yanzu babu wata wadda yake son kasancewa da ita a matsayin mata sama da nadiya,

Packing yayi agefen titi ya tsaya yafara tunanin abinda yake shirin faruwa dashi, abubuwa sun hadar masa goma da ishirin nafarko saki uku yayiwa nadiya gashi yanzu Allah yasake jarabtarsa da sonta akaro na biyu a lokacin da bashida wata dabara, ga zumuncin da yayi watsi da fatali dashi gamida watsi da yaranshi da yayi wanda harma sun manta dashi sannan yanzu kuma yana son kasancewa dasu,

Tsakaninsa da iyayensa babu alaka mai kyau tsawon shekaru suna fushi dashi sannan asabe mc kullum cikin zugashi take tana cewa ya rabu dasu basai yaje wurin da sukeba sannan zasu yi masa fushin ba, koda yaushe cikin bashi gurguwar shawara take, yanzu bashida kowa sai ita, duk tabi ta kanainayeshi ta dorashi akan hanya marar bullewa.


Kamar zaiyi kuka haka ya lallaba yaja motarsa ya nufi gida duk da cewa idan yaje babu abinda zai samu na farin ciki awurin asabe sai ko damuwa saboda bata da lokacinsa sai na kanta, bata da tsabta, babu komai atare da ita sai damuwa shi kansa akoda yaushe yana yiwa kansa ala wadarai saboda rabuwa da yayi da nadiya,

Mace mai tsabta da biyayya komai nasa tana tattali amma banda asabe,

Lokacin da ya kutsa kan motarsa cikin gidan da asabe yayi arba ta rako wasu kawayenta guda uku sai shewa sukeyi suna guda daga ita sai wata yar ficikar Riga kalar ta bacci, kullum aikin kenan yawo da kayan bacci wuni zatayi dasu ajikinta,

Ko kallonsu baiyi ba ya wuce packing space yaje ya faka motarsa ya fito yawuce ciki,

Cikin sauri tabi bayansa zuwa cikin falonta wanda yake cike da datti domin mai yimata aiki ta yi tafiya zuwa garinsu ita kuma bazatayi ba,

Akan kujera ya zauna cikeda damuwa, kusa dashi taje ta rabu tafara farfara idanuwa,

"Barka da zuwa, sannu da dawowa, nima kawayena na raka, su atika ne sukazo wai bikinta za ayi shine ta zo yimin maganar anko.."

"Yanzu me kikeso inyi miki?" Yafada akufule domin acikin haushi yake,

"50 thousands zaka bani.."

"To kibari sai naje na sato kamar yadda nasaba sai inbaki.."

Yafada cikin fada tareda mikewa, saurin shan gabansa tayi taci kwalar rigarsa....



***


Misalin karfe 8 nasafe amadi ya fito cikin wata blue din shadda,rigar iya gwiwarsa ta tsaya mai dogon hannu, kafarsa sanye da takalmi baki, sumar kanshi yake tajewa da cumb hajiya ko fitowa batayi ba tana daki sai mai aikinta ce ke cikin kitchen tana kiciniyar hada musu break,

Ruwan tea yasha kawai ya fita, bai zame ko inaba sai kasuwa,koda yajema mutane basu firfito ba sai kalilan abinda yakaishi yayi ya fito ya nufi rano,

Lokacin da ya isa garin ba afi karfe 10 nasafe ba, gidan daga amira sai mama sai nadiya amma gaba daya yaran an shiryasu sun tafi makaranta,

Nadiya tana kwance a falon mama akan doguwar kujera amira ta shigo rikeda wayar nadiya,

"Anty nadiya yaya Ahmad ne yake kiranki.."

"Mayena kenan.." Tafada acikin zuciyarta amma afili kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login