Showing 30001 words to 33000 words out of 82977 words
Chapter 11 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt
ciki kuwa har dashi dan haka yafara da kansa cikin kwarewa da wayewa ta masu ilmi,
"Am Ahmad Nasir..." Sannan ya nuna wani dake zaune agefensa na dama sit din gaba alamun shima ya gabatar da kansa, nan daya bayan daya kowa yafara mikewa yana fadar sunanshi,
Duk amadi ya kosa azo kan nadiya domin yana son yaji sunanta,iPhone dinshi ya kunna ya dora akan stand din da yake tsaye yafara kokarin lalubo lecture note din da ya shirya, yana dagowa sai ganin nadiya yayi kawai ta zauna nakusa da ita zai tashi nan ya dakatar dashi ya nunata da yatsa, yace,
"Sorry, ke meye sunanki?"
Sai da ta hade rai sannan tayi magana, "Nadiya mu'az.."
Yanda tayi maganar ahankali yasa baijiba kawai dai yaga lebenta ya motsa,
"Sorry.." Yasake fada yana kallonta,
"Nadiya mu'az" yan ajin suka maimaita da karfi nan ya jijjiga kai, haka daya bayan daya suka gama gabatar da kansu,
Course outline ya zayyano musu sannan ya dauki topic guda daya yafara yimusu bayani akai, komai nashi yana yine cikin nutsuwa babu hayaniya, dama kana ganinsa kaga mai cikar kamala domin yanada suffa ta mutanen kirki,
Kowa a ajin sai da amadi ya burgeshi domin turancin shi kadai abun burgewa ne irin yanda yake fitar da kalmomi,
Tsawon awa daya da rabi ya dauka acikin ajin sannan ya fita bayan ya amsa tambayoyin daliban,
Tunda yafita zuciyarsa take nuno masa hoton nadiya, har ga Allah shidai bai taba ganin wata halitta wadda ta dauki hankalinsa lokaci daya kamar nadiya ba, gaba daya ta tafi da tunaninsa wanda har yanzu bai gane abinda hakan yake nufiba,
Har yaje admin block ita kawai yake gani acikin idanuwansa, office din shugaban makarantar yaje sannan ya shiga wurin sauran lecturers din wadanda yakeda alaka dasu yan department din da yake suka gaggaisa ya fito,
Jikin motarshi ya tsaya ko zai sake ganin nadiya amma hakan bai faruba ganin babu alamunta gashi yanata tsaye a rana yasashi bude motarshi ya shiga, hakura yayi ya tafi amma kuma zuciyarsa cike take da hotunan nadiya wanda taketa tunato masa dasu, tun a lokacin yasan lallai maganar hajiya ta tabbata da tace masa kila acan zai samo matar...
Nadiya kuwa duk haushin amadi takeji saboda ya cika kallo gaba daya ya hanata sakewa ya takura mata da kallo dan haka take ganin dakyar idan zasu daidaita dashi,
Lokacin da yagama lecture ya fita ba karamin dadi tajiba saboda ita yanzu duk wani namiji mai kallonta baya burgeta saboda ta dawo daga rakiyar maza yaya kabeer ya shafawa sauran maza kashin kaji awurinta,
Sannan har yanzu yaya kamal cousin dinta bai hakura da itaba domin kusan koda yaushe yana yawan yimata waya ga turo katin waya da kudi da yake yimata,Wannan ya tabbatar mata da cewa yana nan akan bakansa har yanzu,
Tun daga ranar ita nadiya ta manta da batun wani amadi amma shi amadi fa? Wai..! Ai ranar da tunaninta yakoma Gida sannan shi duk a tuninsa budurwa ce bata taba aureba bare harda yara 2,kasa bacci yayi tunaninta ne kawai ke addabar zuciyarsa,
Kwana biyu da ganinta duk tunaninshi ya sauya, zuciyarsa ta kamu da kaunarta babu abinda idanuwansa keson gani sai ita, shi bai san ai haka so yakeba, daga ganinta sau daya sai kawai tunaninta ya hanashi sukuni?.
Yammacine mai cikeda dadi domin wata sanyayyiyar iskace kawai ke kadawa yayinda tsuntsaye keta faman shawagi a sararin samaniya, amadi yana kwance akan three sitter a falo sanye yakeda jar t shirt da bakin boxer ya kunna tv yana kallon kwallon kafa amma kuma sai tunanin nadiya yafara kwankwasa masa kofa dole tunaninsa ya rinjayi zuciyarsa yafada kogin tunanin nadiya, har hajiya ta shigo bai saniba domin yatafi duniyar tunani,
"Auta kosai za ayi maka ko alale?" Shiru taji yayi bai amsa,
"Autana.., autanah.."
Sai a lokacin yaji kiran da hajiya keyi masa,
"Autanah lafiya kuwa? Kodai yunwar ce.." Hajiya tafada tana murmushi domin azumi yakeyi duk litinin da alhamis baya wuceshi,
"Haba hajiya yunwa sai kace wani yaro.."
"Ato nasani, ai nazata yunwace ince ko bazaka iya kaiwa ba ka karya.."
Dariya yayi ya tashi zaune yana dafe da kansa, "cewa nayi alale za ayi maka ko kosai?"
"Hajiya ayi kosan kawai.." Juyawa hajiya tayi zuwa kitchen inda magajiya mai aiki take tana ta kiciniyar hadawa amadi kayan shan ruwa,
Bin hajiya yayi da kallo aransa yana jin cewa anya kuwa zai jure har kwana hudu batare da yaga wannan yarinyar nadiya ba saboda yau alhamis shikuma sai Monday sukeda lecture dinshi....
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[7/27, 8:21 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *MIJINA SIRRINA...!*๐น
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert and perfect writers_
_Ina kuke? Momcyn Anas, Boddo Alka, Hafsat mai sheriff, kunfi kowa son mijina sirrina shiyasa nabaku page 35 tukwici kyauta, Allah yabar zumunci.._
*35*
aishaummi.blogspot.com
*J*ingina yayi da jikin kujerar da yake zaune azuciyarsa kuma yana tunanin cewa gaskiya ya zama dole gobe yaje makarantarsu nadiya yaganta ko yasamu sassauci daga radadin da zuciyarsa keyi masa saboda ita.
Washe gari da safe yayiwa hajiya sallama yatafi bayan ya cab'a kyau cikin wata coffee colour din t shirt da bakin jeans, ba karamin kyau yayiba domin ya fito akamarsa sak,
Yana fita anty siyama na zuwa gidan itada zee kanwar mijinta, jin baya nan yasa Anty siyama kiranshi a waya lokacin har yakusa fita daga cikin Kano,
Yana tuki yaga Kiran anty siyama ya shigo, dagawa yayi yana murmushi,
"Anty amadi ya muka tafka sabani?"
Yaji anty siyama tafada cikin tsokana,
"Anty siyama natafi wudil neman aure.."
Dariya yaji tayi saboda duk azatonta wasa yake yi,
"Kaji yaro da rainin wayo,to dama zee nakawo maka kuyi sallama saboda gobe zata koma Malaysia hutunta ya kare.."
"Allah ya kiyaye hanya anty.."
"Ba Allah ya kiyaye hanya zakace ba zuwa zakayi idan ka dawo kuyi sallama kaji..?"
"To anty naji.."
"Dan Allah yaya amadi karka shanyamu kaki zuwa fa.."
"To anty sai nazo"
Katse wayar yayi yana dariya saboda yasan idan bai amsawa anty da to ba yau wuni zatayi tana aikin yimasa waya.
A b'angaren nadiya kuwa tun ranar laraba ta tafi gida saboda su fadeel basuda lafiya nan hankalinta ya tashi duk da mama tace mata sunji sauki dama zazzabi ne amma hankalin nadiya kasa kwanciya yayi sanin idan ta zauna a makarantar ma ba iya karatun zatayi ba yasa ta shirya kawai tatafi gida,tana zuwa ta samesu suna wasansu Amira tana yi musu wainar fulawa,
Da gudu suka zo suka dale jikinta ajiye jakar hannunta tayi tana kallon su gaba dayansu huciyar zazzabi ta fito musu a kan lebensu,
"Fadeelan momy kawo bakin mu gani.."
"Momy nima kinga.." Fadeel ya matsa jikinta yana nuna mata,
Tsalle suka fara suna murna saboda ganin nadiya suna kiran "momyn mu tadawo, momyn mu tadawo.."
Jin ihunsu yasa mama fitowa daga dakinta nan kuwa taga nadiya,
"Ashe dagaske suke, ni ai nazaci wasa ne.." Mama tafada tana kokarin karasa fitowa daga cikin dakinta,
"Wallahi dagaske ne mama gani nayi kawai gara nataho..."
"Kai anty nadiya dama dai kina son zuwa inbanda haka ai sun samu sauki.." Amira dake zaune acan gefen kitchen tana suyar wainar fulawa ta fada tana dariya,
"Yarinya dan dai ke agida kike ne baki san zafin barin gidaba.."
Tunda nadiya tazo gida tace bazata koma school ba sai ranar Sunday, dan haka koda amadi yaje makarantar sai bai samu ganinta ba haka ya dawo gida yana cikeda damuwa,
Gaba daya amadi yana cikin damuwa dan haka alla alla yakeyi litinin tayi yaje yaga nadiya, kwanakin ma ganinsu yakeyi sam basa gudu sunki yin sauri,
Ranar lahadi da yamma nadiya tayi sallama da gida takoma makaranta, ranar litinin ta fita lecture, wata maroon din atamfa tasaka ta yafa bakin mayafi mai stones ajiki, ba karamin kyau tayiba tayi makeup dinta daidai misali,
Tana shiga class ko minti biyu batayi ba amadi ya shigo,farin yadine ajikinsa da hula ko kadan yau bata yarda ta kalleshiba bare su hada ido amma kuma tana jin gabanta yanata faduwa,
Lokacin da yagama lecture yace ayi question kowa sai yayi shiru jin haka yasashi rubuta musu snap test,
Nan kowa ya dauki paper ya rubutu test din wadda yace 10 minutes test ce kawai,
Lokacin da nadiya tazo yin submitting ta mika masa kin karba yayi yabarta atsaye har saida yagama karbar ta kowa sannan ya juya ya kalleta nan yaga ta wani hade rai ta tamke fuska kamar zatayi kuka,
"Lafiya?" Ya tambayeta tareda karbar paper dinta,
"Lafiya lau.." Tabashi amsa tareda saurin barin wurin,
Cije lip dinshi yayi nakasa yabita da kallo, bai san meke faruwa ba amma ya lura kamar bata son yin koda maganane dashi domin ranar farko da yafara ganinta haka yaga ta bata rai ta hade fuska,
Tattara takardun yayi ya dauki iPhone dinsa yafita aransa yana son sanin wacece nadiya.
Kasancewar anbashi office yasashi nufar office din nasa bashi ya bar school dinba sai yamma, saboda bai tafi da wuri ba ahanya ma yasha ruwa.
Daga nan bai sake dawowa makarantar ba sai da wani satin yayi bayan yayi marking din test din su nadiya, sosai yaji tasake burgeshi domin yaga tana da kokari sosai, boye test dinta yayi acikin motarsa yabarta anan dan haka koda yaraba test din nadiya bataga tataba dan haka ta daura niyyar binshi tayi complain bayan yafita,
Shi kuwa dama amadi da saninshi yayi haka yasan dolenta zatayi magana mutukar bataga test dinta ba, komai rashin son maganarta sai tayi,
Yana fita daga class din tafita tabishi, yana sanye cikin wata shadda light brown, ita kuma nadiya doguwar riga ta atamfa tasa kalar atamfar farace sai ko digon kaloli ajiki ta yafa jan mayafi,
"Excuse me sir.."
Yi yayi tamkar bai jitaba har saida ta sake maimaitawa anan ya jiyo caraf suka hada ido take gabanta ya fadi,
"Ya akayi..?" Ya tambayeta yana tafiya batareda ya tsayaba saboda office yake son kaita,
"Sir banga test dinaba.."
"Bakiga test dinki ba?" Yayi mata wata tambayar maimakon yabata amsar tambayarta,
"Yes Sir.."
"Ok biyoni office.."
Jin abinda yace yasata yin dan turus kamar bazata bishiba, nan tafara tunanin to tabishi kodai tayi tafiyarta, shikuwa tuni har yayi gaba bai jira tagama shawarar ba....
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[7/27, 8:24 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *MIJINA SIRRINA...!*๐น
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
*_UMMI A'ISHA_*
ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert and perfect writers_
_Gaisuwa mai kima ga k'awata takaina kuma aminiyata Maryam Qaumi ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike.._
*36*
aishaummi.blogspot.com
*G*anin har yayi mata dan nisa yasata daga kafarta tabishi zuciyarta nacemata,
"Tunda kece akasa ya zakiyi, ai durkusawa wada ba gajiyawa bane.."
Da sake sake cikin ranta har ta isa office din nashi wanda shi tuni har yabude ya shiga ya zauna,
Ahankali itama ta bude ta shiga, idonsa fes akanta domin dama k'ofa yake facing kuma nan ya ajiye idanuwanshi,
Ji tayi kamar ta koma saboda irin yanda taga ya kura mata ido,sannan office din nashi ba karamin haduwa yayiba,
"Sir gani.."
"To zauna mana.." Yafada yana mai yimata nuni da hannunshi izuwa wata kujera dake gaban tabur dinshi, zama tayi batare data kalleshi ba,
"Mema kikace..?"
Jin tambayar rainin hankalin da yayi mata yasata saurin kallonshi amma babu shiri ta dauke idonta saboda ganinshi tayi dafe da kumatunsa yana kallonta,
"Sir cewa nayi ni banga test dinaba.."
"Kuma kinyi test din?"
Kallonshi tayi tace "ehhh nayi.."
"Kinyi?"
"Ehhh"
"Waye shaidarki idan har dagaske kinyi..?"
"Sir kaima shaida ne cewar nayi.."
"Tayaya?"
"Saboda ranar sai da ka gama collecting din ta kowa before ka karbi tawa,
Hular kanshi ya cire ya shafa sumarsa,
"Ohhh anyi haka.."
"Ok let me check.."
Nan yafara bincike binciken karya dan haka ya Karaci bincikensa yagama batare da yagani ba, kallonta yayi yanda tasha kunu sai abin yanemi bashi dariya,shi yarasa bata ran me takeyi,
"Nadiya... Kinyi satar amsa ko?"
Cikin sauri ta kalleshi, "wallahi Malam a'a"
"To ya akayi taki ta bata amma ta sauran bata bata ba..?"
"Shine ai nima abinda yabani mamaki"
"To kodai kina da aljanun sata ne?"
Ba karamin bata mata rai maganarshi tayiba dan haka ta sake daure fuska tana deciding cewar gara kawai ta hakura ta tashi tatafi tabar masa test din,
"Bari nasake yimiki wata yanzu saboda gaskiya i think bazan kara yimuku second test ba.."
"To Malam bari naje na dauko biro da paper.."
Drawer dinshi ya jawo yaciro biro da plane sheet ya ajiye mata,
"Basai kinsha wahalar komawa ba inada su anan.."
"Wannan wanne irin rainin wayone?" Ta tambayi zuciyarta, "yama rainani.."
"Sir gaskiya am not ready yanzu..."
"Ok duk ranar da kika zama ready sai kizo inyi miki.."
"Ok" tashi tayi ta nufi hanyar fita nan yaji tamkar ya tsaidata ya sanar mata da sirrin dake cikin zuciyarsa amma kuma yagagara yin hakan haka yanaji yana gani ta bude kofar office din tafita.
Naushin iska yayi cikeda takaici,
"Meyasa nakasa fada mata irin son da nake mata?"
Zuciyarshi ce tabashi amsa,
"Ai yanzu idan ka fada mata yayi wuri kabari kabata lokaci tukunna.."
Shawarar zuciyarsa ya dauka na zai cigaba da bibiyarta inyaso sannu ahankali sai ya amayar mata da sirrin zuciyarsa.
Tun daga lokacin babu abinda yasake hadasu sai dai idan yaje yimusu lecture yaganta, ita kuma nadiya duk yabi ya takura mata saboda ko question ya tashi yi a class to ita zai fara jefawa wannan abu ba karamin bata mata rai yakeba gashi koda yaushe idan taganshi gabanta ya rinka faduwa kenan,
Wannan dalilin ne yasata niyyar fara saka nikab a fuskarta domin amadi yana mutukar takura mata,
Amadi kam yanata son yasamu kofar da zai yimata magana amma yarasa sannan kuma haduwarsu a iya class ne ba ganinta yake awaje ba nan yafara tunanin yanda zaiyi yaganta,
Dabarace tafado masa nan ya kira class rep din su nadiya yace masa wacece nadiya mu'az, nan class rep din yace watace itama a ajin take,
"Ok kace ta kirani yanzu.."
Nadiya tana zaune tagama hada kayanta ajaka tana shirin fita class rep yazo ya fada mata sakon amadi,
Karbar number din amadi din tayi tai saving sannan ta mike ta fita,
Gabanta ne yafara faduwa lokacin da zata kira number, tana shiga taji gabanta ya tsananta faduwa,
"Hello.."
Tana jin muryar ta tabbatar da cewar shi dinne nan taji tana neman rikicewa,
"Sir nadiya mu'az ce class rep ne yace wai kace na kiraka yanzu.."
Shiru yayi yana jinta har sai da yaji tayi shiru sannan yasaki ajiyar zuciya mai nauyi tareda yin mika daga kwancen da yake akan gadonshi,
"Nadiya bakiyi test ba sannan nace kizo kiyi kin k'i zuwa ko kina son kiyi carryover din course dinne next year kidawo ki gyara?"
"No sir"
"To meyasa da kikace zaki dawo baki dawoba.."
"Am sorry Sir.."
"Ok to next week ki tabbatar kin zo kinyi.."
"Ok sir nagode.."
Katse wayar yayi tareda yin saving din number dama dabararshi ya samu contact dinta to kuma gashi ya samu yanzu saura stage nagaba.
Kamar yadda tafada masa ranar monday bayan yagama yimusu lecture ta dan zauna ta dudduba lecture note dinta sannan tatashi tabishi office dinshi,
Zaune ta sameshi ya kishingida yana waya cikeda barkwanci, katse wayar yayi ya kalleta,
"Are you ready..?"
"Yes Sir.."
Murmushi yayi tareda jan drewar dinsa yaciro test dinta da ya boye ya mika mata,
"Ga test dinki.."
Mamakine ya bayyana a fuskarta bayan ta karbi takardar,
"How comes..?" Ta furta har afili batare data saniba,
"Uhm nadiya ina son zanyi miki wasu yan tambayoyi..?"
Kallonshi tayi, "To Allah yasa nasani"
"Nadiya ke yar wanne garice?"
"Rano.."
"Anyi miki miji?"
Tambayar tasa jinta tayi tayi mata zuwan bazata hakan yasata kallonshi da sauri tareda girgiza kanta,
"A'a"
Wani farin cikine ya ziyarceshi,
"Nadiya ina sonki kuma so na aure bana wasa ba, bana yaudara ba...."
"Kana sona?" Ta maimaita hakan tana kallonsa,
"Ehh ina sonki.."
Ya maimaita hakan with full confidence.....
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[7/28, 7:00 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *MIJINA SIRRINA...!*๐น
_(Labarin k'auna)_
*_BY_*
_*UMMI A'ISHA*_
ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
_This page is for you Nana Hafsat (miss xoxo), & your fighting partner Hafsat Rano,nice to meet you.... One love_
*37*
aishaummi.blogspot.com
*K*allonsa nadiya tayi cikeda takaici gamida jin haushinsa,
"To kayi hakuri kadaina sona saboda bazan taba sonka ba, kuma bazan iya aurenka ba.."
"Ko menene dalili?" Ya tambayeta yana yimata kallon mamaki,
"Babu ruwanka da dalilina kawai dai kabawa zuciyarka hakuri tadaina sona.."
"Bazan iyaba nadiya, bani nasakawa zuciyata sonki ba dan haka banida ikon hanata ko kuma cireshi daga cikinta.."
"To nidai bana sonka kuma bazan soka ba"
Tana kaiwa nan ta mike tabarshi da mamaki,shi mamakinta yakeyi yanda take fada masa kiri kiri cewar wai bata sonshi kuma bazata soshi ba,
Ganin tana kokarin fita daga office din yasashi hanzarin mikewa yaje yasha gabanta,
Nan ta kankace ido ta sake bata rai tana kallonshi,
"Nadiya meyasa bakya sona? Banyi miki bane kokuma da akwai wani abu atare dani wanda kike ganin baiyi miki ba?"
Kallonsa tayi babu annuri akan fuskarta ko kadan,
"Ni kawai sonka ne banayi"
"Naji bakya sona amma menene dalili?" Yana maganar ne zuciyarshi na radadi saboda yanda take fadar cewar wai bata sonshi kanta tsaye ko dan sayawa batayi,
"Nafada maka haka kawai nidai baka yimin ba kuma bana sonka.."
"Kenan bakida dalilin tsanata kamar yadda bakida dalilin kin karbar soyayyata..?"
Zuba mata ido yayi yana kallonta yana son yagane menene asalin damuwarta da har bata sonsa domin ayanda take yin maganar tana yinta ne cikin fushi da damuwa hadeda bacin rai,
"Nadiya.." Yakira sunanta tareda matsawa kusa da ita,
"Kisani wallahi ban taba soyayya ba, ban san ya ake yinta ba sannan bansan yanda takeba, kwatsam sai idanuwana suka ganki zuciyata tayi na'am dake har ta kamu da sonki"
Wani bakin cikine ya sake turnuke zuciyar nadiya domin yaya kabeer ma da irin wadannan dadadan kalaman yayi amfani ya gurbata rayuwarta, ya wahalar da zuciyarta, ya sanya damuwa acikin ranta, ya rabata da farin cikinta ya maye gurbinsa da bacin rai tareda damuwa dan haka take ganin anyi nafarko kuma na karshe, yanda yaya kabeer ya lahanta mata rayuwa akaro nafarko to bazata sake bawa wani dama yazo ya dora daga inda yaya kabeer ya tsaya ba,
Shiyasa duk wadannan kalaman na amadi take ganin na yaudara ne wanda babu komai acikinsu face karya da yaudara,
"Ai nafada maka kayi kokari ka bawa zuciyarka hakuri domin ni bana sonka sannan bazan taba sonka ba"
Runtse idonsa yayi cikeda takaici ya budesu sun danyi ja saboda dacin da maganarta keyi masa,
"Naji bakya sona kuma nayarda amma kiyi min alfarma guda daya, kiyi hakuri kibarni na aureki nikuma nayi miki alkawarin zan koyar dake yanda zaki soni, zan mantar dake kiyayyata.."
"Ni bazanyi aure ba har