Showing 36001 words to 39000 words out of 82977 words

Chapter 13 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt

27 Sep 2025

3169

domin hutun nasu da yawa.


Komawarta gida yasa ta mance da wani amadi saboda hatta wayarta ma sai ta gadama take kunnawa saboda kar ya takura mata, ita yanzu bata da wani bazawari ma domin hatta yaya kamal ma ya hakura saboda yaga ba aurensa zatayi ba, yanzu iya amadi ne kawai ke yimata naci,

Satinta uku da dawowa gida tana zaune da yamma a tsakar gida tana yiwa fadeela kitso ita kuma ameera tana yimata tsifa mama tana kitchen tana aiki, fadeel da husna da walida da amir suna yin ball,

Wayarta ce tafara kukan neman agaji, kamar bazata dauka ba saboda ganin amadi ne amma sai ta dauka,

"Ki fito gani a kofar gidanku.."

Jin abinda yafada yayi mutukar sata mamaki,

"Wanne kofar gidan namu?"

"Kunada wani kofar gidanne bayan wanda kuke ciki? Ke da wai kin dauka bazan biyoki ba?"

"Ni bana gida"

Murmushi yayi,

"Hmm nidai nace miki ina kofar gida ina jiranki".





*_Ummi Shatu_*👌🏻


*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_





*_BY_*

_*UMMI A'ISHA*_



® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_



_Fatan Alkhairi ga yan k'ungiyar haske writers, this page is for you...!_




*41*


aishaummi.blogspot.com




*A*jiyar zuciya ta ajiye sannan ta sake hade rai kamar yana ganinta,

"Nace maka bana gida naje unguwa.."


"To ina nan ina jiranki, sai kin dawo.."

Kasancewar duk abinda take fada mama tana jinta yasa mama fitowa daga cikin kitchen,

"Nadiya keda waye ne?"

"Mama wallahi wani nacaccen mutum ne.."

"Haba nadiya, kefa yanzu ba karamar yarinya bace akan me zaki rinka yin abu irin na kananan yara, ko Amira ce tayi haka ai zakiyi mata fada bare ke da kanki, ina ga mai sonka wanda yatako yazo har inda kake? Ki tashi maza ki shirya kije"

Jin abinda mama tafada yasata sakin kitson da take yiwa fadeela ta tashi tawuce daki,

Kallon amir mama tayi tace masa,

"Amir maza fita kofar gida kacewa bakon nadiya yayi hakuri tana zuwa, kabashi hakuri kaji, ai ba ayin haka.."

Fita Amir yayi yana fita yaga wani handsome jingine jikin motarsa baka sai sheki take, gayen yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda kalar ruwan toka, da hula akansa itama ash colour amma ya zameta ya turata baya can keyarsa, hannunshi daure da agogon azurfa fari,

Gaba daya kamshin turarensa na one man yagama cika ilahirin wurin, amir ji yayi gayen ya shiga ransa lokaci guda sannan gashi dan gayu dashi,

Sallama amir yayi masa, dagowa amadi yayi ya amsa tareda mikawa amir hannu sukayi musabaha,

"Mama ce ta aikoni tace kayi hakuri anty nadiyan zata fito yanzu"

Murmushi amadi yayi har lokacin yana rikeda hannun amir,

"Karka damu abokina, ai babu wani abu sai dai kawai yayarka bata sona ta tsaneni babu namijin da take jin haushi ahalin yanzu kamar ni"

"Ba tsanarka tayiba, kawai dai halin rayuwa ne ya mayar da ita haka" amir yabashi amsa,

"Amma dagaske wai ta taba aure?"

"Ehh tayi aure harda yaranta twins, sun rabu da mijinne"

Jijjiga kai amadi yayi, "nasan dai ba laifinta bane sai dai laifin mijin saboda nadiya tanada kalar mata nagari"

"Hakane, gaskiya kam laifin ba a ita bane a mijinta ne kuma cousin dinmu ne ma amma yanzu babu aure a tsakaninsu saboda saki uku yayi mata, kaga kuwa duk macen da irin wannan kaddarar ta hau kanta dole ta nisanta kanta da maza musamman ma anty nadiya wacce ko kadan bata tsinci wani dadiba acikin rayuwar aure.."

Amadi ya dago kenan da niyyar sake yin magana sai gata ta fito fuskarta adaure tasha kunu sai faman cika take yi tana batsewa saboda tilastata din da mama tayi ta fito ba ason ranta ba,

Hannun amir amadi ya saki yana murmushi, "abokina sai mun sake haduwa, meye ma sunanka?"

"Sunana amir"

"To amir sai mun hadu next time, nagode"

Wucewa cikin gida amir yayi ita kuma ta karasa fuskarta babu fara'a,juyawa yayi ya dora hannunshi asaman mota ya jingina yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi,

Ba karamin kyau yaga ta kara yiba domin tayi kumatu ta yi haske, tana sanye da atamfa kalar ruwan toka da hoton dutsin guga ajiki, ta yafa mayafi ash colour tasaka flat din takalmi baki,

Haushi taji saboda ganin sunyi anko da amadi, ji takeyi kamar ta koma gida ta sake wasu kayan,

"Meye kuma harda sako kaya kalar nawa?" Yafada cikeda tsokana yana kallonta, sake daure fuska tayi,

"Ni ban ma san kalar kayan da kasako kenan ba.."

"Bawani nan kin sani kawai dai kidai nagane so kikeyi muyi anko"

Sake k'uluwa tayi nan ta juya tana harare harare shikuma abin dariya yake bashi, sake niyyar tsokanarta yayi ya kalleta,

"Har kin dawo daga unguwar? Ai da kin yi addressing dina naje na dauko ki"

"Nagode.." Tafada batare data kalleshi ba saboda ta gane tambayar rainin hankali yayi mata tunda ai yana gani ta fito daga cikin gida,

"Ina twins dina?" Ya tambayeta,

"Dama kanada twins ne?"

"Au da ke baki saniba?"

Shiru tayi masa, dan haka ya kalleta yayi dan murmushi,

"Kizo mu shiga mota karki gaji da tsaiwa ni kinga nasaba tsayawa a aji"

"Basai na shiga ba, nifa aiki nakeyi ka fito dani.."

"Daga dawowar taki daga unguwa kika hau aiki?"

Sake yin shiru tayi dan haka ya kalleta yana duba agogon dake daure a hannunshi,

"Nima ba zama nazo yiba dama ganinki kawai nazo nayi sannan naga gidanku, tunda nagani shikenan zanje natafi amma karki dauka natafi kenan, no i will be back soon, ko yanzu dai nasan kinyi believing cewar bazan taba barinki ba har sai kin zama mallakina koda kuwa bakya sona tunda ni ina sonki shikenan.."

Juyawa tayi ta kalleshi fuskarta a tamke,

"Nagode da sona da kakeyi amma kasani auren matar da bata sonka babban kuskure ne, sannan budurwa itace tafi dacewa dakai ba bazawara mai yara har biyu ba, Allah ya kiyaye hanya.."

"A'a ni bazawara ce tafi dacewa dani ba budurwa ba saboda manzon Allah ma da bazawara yafara kinga kenan idan nayi haka na dabbaka sunna babba.."

"Allah ya kiyaye hanya.."

Tun kafin ya amsa tayi gaba abinta, binta da kallo yayi yana jujjuyawa kalmominta acikin ma'auni,

Duk maganganun da take fada masa yana ji acikin ransa cewar akwai wani abune da yake damunta acikin zuciyarta wanda yakeda alaka da wannan sannan kuma ga maganar da amir ya fada masa dangane da ita cewar bataji dadin rayuwar aurenta nafarko ba, to indai hakane bawai sonshi dinne batayi ba kawai dai akwai wani abune wanda ta ajiyewa ranta,

Waya yayi mata ta dauka dakyar murya a dakile,

"Please turo min amir zamuyi sallama"

Katse wayar tayi ta kalli amir, "kaje yana kiranka"

"Wai waye wanda yazone?" Mama ta bukata,

"Wallahi mama wani classic guy ne anty tasamu.."

Daukar takalmi tayi ta jefeshi yayi saurin fita yana dariya,

A tsaye jingine da mota yasamu amadi,

"Abokina yi hakuri nasake fitowa dakai ko"

"A'a wallahi babu komai"

Kallonsa amadi yayi, "amir ni dagaske nake son yayarka amma kuma taki kwata kwata bani hadin kai mu fuskanci juna ban san dalili ba, shin mijinta nafarko ya cutar da itane?"

"Gaskiya bakai kadai yaya nadiya ke yiwa hakaba, kaga bayan mutuwar aurenta manema da yawa sun fito suna sonta amma taki tace ita karatu zatayi saboda kamar yadda nafada maka abaya ko kadan bataji dadin aureba,

Wannan dalilinne yasa yanzu bata sha'awar sake yi kwana kusa saboda kasan bahushe yace naji dadi shine gari ba na saba ba, abubuwan da anty nadiya tagani agidan aure suna da yawa, taga rayuwa kala kala daga karshe suka rabu da mijin babu arziki, to kaga wanda yaga haka ai fiyeda irin wannan ma zai iyayi"

Jijjiga kai amadi yayi, "na fuskanceka amir, nagane dalilin nadiya na tsanata da kin amsar soyayyata, nikuma nayi maka alkawarin mutukar na auri yayarka bazata yi kuka daniba sai ko na farin ciki, bazan wulakantata ba, zan kula da ita sannan zan bata gatan da bata samu a aurenta na farko ba.."

"Allah yasa, Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Amin"

Hannu yasa a aljihu ya dauko kudi sabbi fil yan 500 na dubu biyar yabawa amir yace ya siyawa twins sweet daga nan ya shiga motarshi yatafi yana mai jin son nadiya yana sake ratsa duk kofofin jinin jikinsa,sannan yanajin wani tausayinta yana shigarshi,

Tunda amir ya kawo sakon mama ke kallon nadiya tana son jin yanda zata karbi zancen amma ko uffan batace ba shikuwa amir sai yabon amadi yake tayi yana cewa mama wallahi guy din ya hadu sannan ga hankali ga class gashi dan gayu.

Tunda yatafi nadiya bata kirashi ba ganin haka yasa shi ya kirata, kamar koda yaushe shiru tayi masa har fadeela ta shigo ta haye jikinta tafara yimata surutu jiyo surutun fadeela da yayi yace tabashi ita, mikawa fadeela wayar tayi ta kara mata ajikin kunnenta,

"Momy waye?"

"Dady ne" yabawa fadeela amsa ai kuwa nan ta hau tsalle saboda tazata dadyn tane duk da tafara mantawa dashi....




*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_




*_BY_*

*_UMMI A'ISHA_*



® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of perfect & expert writers_




_Jinjina ga babbar yaya anty maijidda musa, nagode da kokarinki agareni, Allah yabarmu tare.._


*42*

aishaummi.blogspot.com




*T*salle fadeela tahau yi tana yiwa amadi surutu, nan yasamu abokiyar hira tanata yimasa labarin school dinsu harda su abcd da sauran karatun da ake koya musu a makaranta,

Ita kanta nadiya sai da abin ya bata mamaki irin yanda amadi ya biye fadeela taketa yi masa surutu, shima fadeel ya shigo nan fadeela tabashi wayar tana cewa,

"Ga daddy"

Karba shima yayi nan hirar takoma amadi da fadeel, daga karshe ita nadiya ma baccine ya dauketa tabarsu sunata faman surutu bata san lokacin da suka gama ba,

"Ina momyn take?" Amadi ya tambayi fadeel,

"Gata nan tana bacci"

"To kyaleta karka tasheta",nan yayi sallama da yaran ya kashe wayarsa.

Tun daga nan kullum idan ya kira wayar dasu fadeel suke shan hirarsu suyi tayi masa surutu suna sashi dariya,


Satinshi biyu da zuwa yasake shiryawa ya dawo acikin weekend ranar asabar, sai kawai waya yayi mata yace yana waje, amir ta kira tace yaje da bako awaje saboda ita tana kwance cikin bargo tana baccinta,

Amir na ganin amadi ne yamaza ya koma cikin gida yafadawa mama, nan mama tace ashigo dashi falon baki,

Amira mama tasa tayi masa girki nan Amira ta shiga cikin kitchen ta dora,

Dakyar nadiya ta tashi tayi wanka ta shirya bayan mama ta leko tayi mata kaca kaca, shiryawa tayi cikin leshi dark brown da mayafinsa ta fita,

Lokacin da zata shiga sai ga Amira itama rikeda faranti zata shiga, bata hanya tayi ta fara shiga sannan tabi bayan amiran,

Sai da Amira ta gaisheshi sannan ta tashi ta fita kallon nadiya yayi yau dinma fuskarta adaure,

"Wannan kanwar taki tanada hankali kamar amir.."

Shiru tayi masa bata tanka ba,

"Ina twins dina.."

"Basa nan sunje islamiyya"

Murmushi yayi bai kara cewa komai ba illah kawai kallonta da yake yi,

Babu wanda ya kara magana haka suka cigaba da zaman kurame sai da suka dade ahaka sannan amadi yayi magana saboda yasan ita dai ba magana zatayi ba,

"Nadiya....,ina so kiyi hakuri ki bani dama saboda komai arayuwa da kika ganshi kaddara ne sannan kuma bawai yana nufin cewa saboda mutum daya yayi maka butulci kowama butulu bane, a'a ita rayuwa ahaka take tafiya, yayinda wani ya bata maka sai wani ya dad'ad'a maka, nidai indai nine nayi miki alkawarin bazan taba cin amanarki ba.."


Duk wannan maganganun da yayi bawai sunyi tasiri agareta bane kawai dai ta daukesu a matsayin zallar karya irinta yaya kabeer,

"Dan Allah nadiya kibani dama domin na nuna miki irin son da nake yimiki"

Har lokacin dai bata ce dashi ko ci kanka ba,shiru yayi yazuba mata ido kawai yana kallonta,

"Bakaga an kawo maka abinci bane.." Tafada batare data kalli gefen da yakeba,

"Kin damu da naci ne? Ai baki damu da koshina ko yunwata ba.."

Bata sake tanka masa ba dan haka yajawo farantin abincin nan yabude yaga potatoes mix da wata hadaddiyar sos wadda tasha curry da hanta sai kamshi take,

Kwallo biyu kacal ya dauka ya debi sos din yafara ci,

"Kanwarki ta iya girki, ko kece kika yi?"

"Bani bace.." Tafada tana sake hade rai,

Shiru yayi yaci gaba da cin abincin yana binta da ido,

Ihun sallamar su fadeel ce ta cika musu kunne sai gasu sun shigo cikin falon aguje suna ihu wai dadynsu yazo,

Zuwa sukayi suka rungume amadi suna ihun murna, amir dake biye dasu yana cewa "karku bata masa kaya ku cire takalmin"

Kasancewar milki colour din yadi ne ajikin amadi,

Tunda su fadeel suka dawo amadi yasamu abokan hira bai sake bi ta kan nadiya ba, mama ma tashigo sun gaisa daga nan kuma amir ya rakashi wurin abba suka gaisa ai nadiya ji tayi kamar zatayi kuka da bakin ciki saboda ita bata da burin sake yin aure kwana kusa,

Fita yayi zai tafi yana rikeda su fadeel amir yana binsu abaya, boot din motarshi ya bude yace amir ya kwashe kayan ciki yakai gida na twins ne yakawo musu, ita kam nadiya tana tsaye tana kallonsu kayane sosai yasiyo irinsu bobo, biscuit, chocolate, indomie da sauran kayan makulashe na yara,

Bin amir sukayi zuwa cikin gida dan haka amadi ya matsa kusa da ita,

"Baby zan tafi.." Wani haushi taji ya rufeta saboda ta tsani baby dinnan da yake kiranta dashi,

"Allah ya kiyaye hanya"

"Amin nagode da addu'a, sai yaushe?"

Jin tayi masa shiru yasashi yimata sai anjima yatafi,

Haka sukaita fama koda yaushe yana kiranta awaya sannan yana tura mata da kati,

Har yanzu ita bata ji alamun zata soshi ba saboda zuciyarta ta dade da cire soyayya daga cikinta,

Tana kwance taji yana kiranta awaya, dauka tayi bayan tayi tsaki,

"Baby kina lafiya?"

"Lafiya"

"Dama fada miki zanyi zanzo ranar Thursday ko Friday"

"Bana nan"

"Ina kika tafi?"

"Basai kajiba, sai anjima yanzu aiki nake"

Kitt takashe wayar bata san mama na tsaye tana jinta ba,

"Ke nadiya wai meyake damunki ne? Ashe dama bakida wayo? Allah ya dubi zuciyarki da irin halin da kika shiga yakawo miki wanda yake sonki tsakani da Allah shine kuma zaki butulce masa?

To wallahi ki zauna kiyi karatun tanutsu saboda wannan yaron da gaske yake sonki idan har kika wulakantashi kika koreshi to bazaki samu wanda yakaishi ba agaba,

Kuma wallahi idan har ke bazaki aureshi ba to ni ashirye nake da in bashi Amira ya aura, wallahi indai bazaki aureshi ba ki fada min sai ince masa yazo ya auri Amira, haba yaro mai mutunci mai son yayanki, ya dauki yaranki kamar nasa amma kekuma babu wanda kike ciwa mutunci sai shi, to yakamata ki yiwa kanki fada.."

Juyawa mama tayi tafita tabar nadiya tana kuka, ita kwata kwata yanzu auren ne bata so,sannan maganar mama ta tsaya mata arai wai zata bawa amadi Amira idan ita bata sonshi,

Koda yasake kiranta yace zai zo cewa tayi to, ranar kuwa na zuwa sai gashi yazo da misalin karfe 12 narana,shiryawa tayi cikin wani material ja mai kyau ta fita,

Acikin mota ta sameshi dan haka ta tsaya daga waje tana faman ciccin magani, ta cikin mirror ya hangota yayi murmushi ya bude ya fito, tana ganinsa tajuya tafara tafiya batare da tayi magana ba, binta yayi abaya tiryan tiryan har zuwa cikin gidan falon baki,

Zama tayi anesa dashi ranta ahade, suna zaune haka shiru husna tashigo dauke da faranti kato wanda aka doro kayan abinci aciki,

Fried rice da hadadden salad wanda yaji kwai da sauran kayan hadi sai juice,

"Zo muci abincin" yafada cikin tsokana,

"Na koshi" tabashi amsa, murmushi yayi yafara cin abincin yana kallonta tareda nazarinta sam shi abinda take yimasa baya bata masa rai bare ya daga masa hankali asalima hakan sake burgeshi yake yana kara rura wutar sonta acikin ranshi,

Suna nan zaune zaman kurame har yagama cin abincin ya kalleta,

"Baby ko babu komai ai yakamata ace mun gaisa ko?"

"Mantawa nayi" tafada tana dauke kanta, murmushin da yasaba yi kowanne lokaci yanzun ma shi yayi,

"Na sameku lafiya?"

"Lafiya"

Shiru suka yi na dan wani lokaci,

"Ina budurwata Amira yau ban ganta ba?"

"Tana ciki" ta amsa masa fuskarta adaure,

"Wannan ciccin maganin da kikeyi yakamata ki daina shi saboda nima yau ba wurinki nazo ba wurin Amira nazo domin na sauya shek'a....".






*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_




_*BY*_

_*UMMI A'ISHA*_


® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_



_Special gaisuwa ga aminan kwarai abin alfaharina, Pherty Xarah, Fido sodangi, Kausar m Hassan, Khaleesat Haidar, Mom Shakur, Sadiya I Bala,Khadija Sidi, Teemah Cool, Hafsat Bunxa, Aisha Dansabo,Zee Ruma,da duk wadanda ban ambata ba, ina alfahari daku kawayena..._



*43*


aishaummi.blogspot.com




*J*i tayi gabanta yafadi bata san daliliba, saurin kallonsa tayi nan taga shi ba ita yake kallo ba ma sam, wayarshi yake kallo yana daddannawa,

Maimaita maganar take yi acikin zuciyarta nan take kuma maganar da mama tafada ta sake dawo mata inda mama take cewa idan har bata sonshi bazata aureshi ba to zata bashi Amira,

Faduwar gabanta ce ta tsananta nan tasake kallonsa still dai wayarshi yake kallo ba itaba,

"Dama Amira ai itace tafi dacewa dakai baniba, Allah yabada sa'a.." Tafada cikin k'uluwa tareda tashi zata fita,

"Amin, dan Allah ki turo min ita idan kin shiga ciki.." Ya fada da niyyar sake tunzurata, bata ko waiwayo ba tayi gaba abinta amma kuma haka kawai sai take jin wani irin haushi yana bakuntar zuciyarta,

Cikin dakinta ta shiga nan taga Amira tana zaune tana gyara kayan sakawar su fadeel tana shirya musu shi acikin wardrobe, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace da Amira,

"Amira kije Ahmad yana kiranki.."

"To anty.." Amira tafada gamida mikewa da sauri,

"To Kodai dama yarinyar nan tasan da zuwanshi ne?"

Ta tambayi zuciyarta, zama tayi taci gaba da aikin da amiran tatafi tabari.


Amira nashiga falon baki ta iske amadi azaune,

"Yaya Ahmad ina wuni?" Tafada cikin ladabi,

"Lafiya Amira, yasu mama?"

"Suna nan lafiya"

"Yawwa dan Allah so nake ki shirya min su fadeela zamuje unguwa dasu.."

"To yaya Ahmad"

"Yawwa nagode"

Fita tayi zuwa dakin mama inda Maman ke shiryasu bayan tayi musu wanka nan Amira tafadawa mama sakon amadi na ashiryasu zai kaisu unguwa,

Kayansu Amira tasa musu tayiwa fadeela kwalliya sosai takama mata gashinta da ribom kalar kayanta pink din riga da bakin jeans skirt, shikuma fadeel pink din t shirt da bakin jeans ta fesa musu turare,

Kama hannunsu tayi takaisu wurin amadi tace gasu nan sun fito,

Kallon yaran kawai ya tsaya yana yi domin ba karamin burgeshi suka yiba ji yake aransa inama yaranshi ne,inama shine ya haifesu shida nadiya amma kowaye ya auri nadiya dafarko yayi masa overtaken ne kawai da tuni yanzu yaran nan nashine,

Kama hannunsu yayi suka fita yayinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login