Showing 21001 words to 24000 words out of 82977 words

Chapter 8 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt

27 Sep 2025

3154

kitchen din ya tsaya ya dafa bango,

"Kinji kuma abinda yaron nan yake son jawo mana ko?"

Cikin rashin fahimta mama tafito tana cewa "wanne yaron kuma?"

"Kabeeru mana, wai aure yake nema auren kuma yarasa wacce zai zabo sai yar bariki, duk yan matan garin nan basuyi masaba sai yaje ya auro wadda bata da tarbiyya, wadda tabaro gidan iyayenta ta taho yawon tazubar.."

Salati mama tafara yi tana tafa hannu,

"Kabeerun ne zai janyo mana wannan abin kunyar agari?"

"Shi dai.., amma yanzu zan kirashi zan gargadeshi da babbar murya, wallahi wannan auren ban yarda dashiba, mutukar nine ubansa ni na haifeshi kuma yana ganina da wannan darajar to kuwa bazai auri asabe mc ba.."

"Yo Alhaji ai dama maganar auren wannan yarinyar ma babu ita, ga matarsa nan yar mutunci jininsa wacce tataso cikin tarbiyya, wallahi bazai yiyuba.."

Zaro waya daga cikin aljihu abbanshi yayi ya kirashi yana dagawa yaji yace,

"Kai kabeeru idan kagama abinda kake kazo gida ina son ganinka"

Cikeda murna yabar abinda yake yi zai fita nadiya dake kitchen tana girki sai sallama kawai yayi mata yace zaije abbanshi na kiranshi, adawo lafiya tayi masa saboda bata san abinda ke faruwa ba, cikin kwarin gwiwa ya nufi gidan iyayensa saboda duk a zatonshi andace akan maganar aurensa da asabe mc........



_Sakon fatan alkhairi ga masoyan ummi shatu masu sonta masu kaunar rubutunta akoda yaushe suna bibiyarsa..._






*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/22, 7:43 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(True life story)_




_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



ยฎ *HASKE WRITERS ASSO*




*26*


~~~Babu b'ata lokaci yaya kabeer ya shiga motarsa ya figeta bai zame ko inaba sai gidansu duk a tunaninsa abba da mama sun amince da maganar auren da zai kara amma koda yaje sai ya tarar da sabanin haka,

Mama tana ganinsa ta zabga masa wata harara wacce rabon da yaganta tayi irinta tun yana yaro karami,

Zama yayi yagaishesu nan kowannensu ya amsa fuskarsa adaure,

"Kabeeru maganar auren wannan yarinyar da kayi ina mai baka umarni a matsayina na mahaifinka ka janyeshi sannan ka nisanceshi har abada, ko bayan raina ban yarda ban kuma laminta ba ka auri asabe mc.."

Cikeda fargaba gamida mamaki mai hadeda tashin hankali kabeer ya dago ya kalli abba saboda abinda yaji abban ya fada ba karamin sakashi acikin rudu yayiba,

"Abba saboda me?... "

"Saboda mune muka haifeka ba kaine ka haifemu ba dan haka yazama dole kayi mana biyya,

Kabeeru ai kabani mamaki ban taba sanin cewa haka kakeba sai yanzu, ashe dama baka da hankali baka da nutsuwa?

Ai kabeeru ko mutuwa mukayi bai kamata kaje ka cusa kanka acikin abinda zai dameka ba, kana zaune da matarka lafiya babu tashin hankali babu komai shine zakaje ka auro gantalalliya marar mafadi,wadda bata samu yabo ba, yarinyar da bata gaban iyayenta zaman kanta take..."

Mama ta karasa maganar tana faman numfarfashi,Kafin ta dora da cewa,

"To wallahi baka isa ba, ba zaka shigo mana da ita cikin zuriyarmu ba muddin mune muka kawoka duniya.."


Tana rufe bakinta abba ya dora daga inda ta tsaya nan suka hadu suketa yimasa fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba,

In banda gumi babu abinda yake hadawa domin babu abinda yake so yanzu kamar asabe, nan su abba suka yimasa kaca kaca ya tashi ya tafi,

Hankalinsa ya tashi iya tashi, amma bai bari nadiya ta ganeba haka ya daure yabar abin acikin ransa shi kadai da niyyar idan su mama sun huce zaije ya shawo Kansu.

Sati daya yabasu kullum yana zuwa gidan amma bai kara tada maganar ba har sai da sati daya yacika da fadan da suka yimasa aranar yaje gidan yafara lallashin mama,

"Mama dan Allah kubarni nayi auren nan, kuyi min afuwa domin kamar jihadi zanyi..."

"Kai kabeeru idan baka tashi kadaina yimin maganar nanba wallahi sai naci mutuncinka"

Abba ne yafito daga cikin dakinsa yana kallon kabeer din ransa abace,

"Kabeeru maganar nan bata wuceba? Ai mun gama magana aure nace bazaka yishiba mutukar nine na haifeka dan haka katashi kafice karka kuskusa ka sake zuwar min da magana makamanciyar wannan, kaje ka kula da matarka yar uwarka da yayanka idan kuma kaki zan sassaba maka.."

"Kayi hakuri abba.." Kabeer yafada tareda tashi ya fita,

Abubuwane suka hadu suka dagula masa lissafi domin kullum asabe damunshi take akan maganar aure sannan gashi iyayensa sunki amincewa alhalin shikuma yana mutuwar sonta,

Shiryawa yayi yaje wurin asabe ya sanar mata da halin da ake ciki nan ta rinka famfashi tana zugashi tana nuna masa cewar ko babu yardar iyayensa zai iya aurenta dafarko bai yarda ba amma koda tafiya tayi tafiya sai ya amince, nan yabata makudan kudi yace ta hadawa kanta lefe,

A Tsakaninsu suka saka date din daurin aurensu sati uku masu zuwa,

Sati ukun na cika kuwa shida abokansa suka tafi jos aka dauro masa aure da asabe mc batareda iyayensa sun saniba ita kuwa nadiya dama ko zance makamancin wannan bata taba saniba,


Aranar da aka dauro auren suka dawo shida abokansa, nadiya na cikin daki ta fito daga wanka tana shiryawa ya shigo cikin gidan nan ya iske su fadeel afalo da fadeela suna wasa akan motar wasansu,

Wasa ya danyi musu sannan ya shiga wurin nadiya, tana kokarin daura dan kwali kenan ya shiga nan ya zauna agefen gadonta yana kallonta,

"Nadiya magana nazo muyi.."

Zama taje tayi akusa dashi, "to gani"

"Nadiya dan Allah ki fahimceni, karki ga laifina, ba laifina bane haka Allah ya kadararta ki dauka cewar wannan abun kaddara ne.."

Gaban nadiyane yafara faduwa saboda sai ta zargi cewar ko rasuwa akayi ko kuma wani abu makamancin haka,

"Yaya kabeer wai menene? Dan Allah ka gaggauta fada min.."

"Nadiya na kara aure yau, an daura min aure da asabe m..."

Tsaye ta mike tana kallonsa afirgice nan hankalinta ya tashi,

Bakinta yana rawa ta furta, "yaya kabeer aure ka kara? Shine baka sanar dani zaka kara aureba..?"

Tashi yayi ya rikota zuwa jikinsa nan ta fincike tana zubarda hawaye, ko takansa bata biba ta fita tana kuka, hijab dinta ta dauka afalo ta saka su fadeel agaba suka fice nan yabiyota yana kokarin tsayar da ita amma taki,

Kafafuwansu fadeel ko takalmi babu amma haka ta tisasu agaba suka hau titi....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/22, 7:49 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(True life story)_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*



*27*



~~~Ko sauraron kiran da yake yimata nadiya batayiba tayi tafiyarta tareda tare adaidaita sahu nan ta shige itada yaran, da hannu take yiwa mai adaidaita sahun kwatance saboda kuka take yi har sukaje kofar gidansu kabeer,

Mama tana daki tana salla su aisha nafalo sai ga nadiya na kuka, dukkaninsu rudewa sukayi saboda basu san abinda ke faruwaba gashi kuma sun ganta sai kuka take,

Kafin mama ta fito har abba yashigo yana cewa,

"Wacece tazo tabar dan adaidaita sahu awaje bata bashi kudinsa ba..?"

"Anty nadiya ce.." A'isha tafada tana kallon nadiya cikeda tausayawa, komawa abba yayi yaje yabiya dan adaidaita sahun sannan ya dawo cikin gida,

Fitowa mama tayi tana yin sallama daga sallar da takeyi ko addu'a bata zauna yiba,

"Nadiya menene? Meya faru? Keda kabeerun ne?" Mama tayi mata wadannan tambayoyin cikin rudewa,

Kai nadiya ta daga alamun ehh,

"To meya hadaku?"

"Wai aure ya kara shine sai bayan andauro auren yazo yana fada min.."

Salati mama ta rafka tareda rike habarta, nan abba ya shigo cikin falon cikeda mamaki,

"Kikace aure yayi? A ina?"

"Abba a jos, yanzu yazo yana fada min"

Kafin wani yasake magana sai ga kabeer din ya shigo afirgice,

Fada abba ya rufeshi dashi tun kafin ya zauna,

"Auren da muka hanaka sai da kaje kayi ko saboda baka daukemu da muhimmanci ba baka ganin mutuncinmu, to tunda ka zabi haka kaje kayi duk abinda ka gadama amma kasani yazama dole ka saki nadiya, dole ka sakar musu yarsu domin bazaka hadata da cutar hawan jiniba"

"Cutar hawan jini kuma ta nawa? Ai yadade da dora mata ciwon hawan jini sai dai aguji ciwon zuciya kuma.." Mama tafada cikin fada,

Cikeda bacin rai abba yasake magana cikin tsawa,

"Ka saketa nace, ka sakar musu yarinyarsu tun kafin bakin cikinka ya kasheta.."

Zubewa kabeer yayi akasa ya fara rokon abba,

"Dan Allah abba kayi hakuri wallahi ina son nadiya, dan Allah karku raba auren nan wallahi ina sonta.."

"Tashi ka fice daga gidan nan, ko bakaji? Katashi ka fita tun kafin ranka ya baci"

Abba ya nuna masa hanyar fita, nan kabeer yatashi yafita nadiya kuwa inbanda kuka babu abinda takeyi, fada mama da abba suka cigaba dayi abba yana cewa bazai yarda ba kuma yazama dole sai yasaki nadiya,

Kowa nagidan saida hankalinsa yatashi amma gidansu nadiya har lokacin su mama basu san abinda ke faruwa ba, cikin wannan tashin hankalin aka kwana, yanda nadiya taga rana haka taga dare sai kuka data kwana tanayi domin hankalinta yatashi sosai,

Washe gari da sassafe saiga yaya kabeer ya dawo gidan nan abba yasake fatattakarsa yatafi, A'isha da Fati abba yatura sukaje suka debowa nadiya kayanta da kayansu fadeela, daukarsu yayi zuwa gidansu nadiya,

Tunda mama tagansu tasan ba kalauba nan jikinta yabata cewar da akwai abinda yafaru, rungume mama nadiya tayi tana kuka mai ban tausayi nan itama maman tafara hawaye mai zafi,

Abbansu nadiya abban kabeer yasamu ya kwashe duk abinda yafaru yafada masa sannan kuma yace raba auren nadiya da kabeer zaiyi tunda kabeer ya nuna masa bai isaba,

Nan mama tasake jin wani tashin hankalin, iya jiya kadai har nadiya ta fita hayyacinta tayi wata iri da ita,

Saboda tsananin tashin hankali hawan jininta saida ya tashi gashi kwata kwata takasa cin abinci ko ruwa takasa sha,

Nan abban kabeer yace tatashi sutafi itada yaran, ko uffan batace ba tatashi tabishi nan ya kwashesu sai garin sumaila gidan kanwarsu hajiyan sumaila,

Can yabaro su nadiya ya juya yakoma rano, hajiya wacce su nadiya ke kira da umman sumaila saka nadiya tayi agaba tayita yimata nasiha tana bata hakuri, dakyar tasamu taci abinci dan kadan ta kwanta bayan ta kashe wayarta domin kabeer sai faman kiranta yake shiyasa takashe,

Sai da tayi sati lokacin hankalinta yafara dawowa cikin jikinta sannan ta kunna wayarta nan taga massages rututu na yaya kabeer naban hakuri, ko kulawa batayi ba bare tabada reply,

Shikuwa kabeer ya shiga damuwa mutuka domin abba da mama sun juya masa baya, hatta kannensa babu wanda yake kulashi, yaje gidansu nadiya kuwa yafi sau ishirin mama tana cemasa wallahi bata san inda abbanshi yakai nadiya ba,

Sati biyu ya dauka yana zirga zirga amma babu me kulashi, duk da yana cikin damuwa haka ya karasa gyaran part din asabe wanda yake dauke da babban falo da bedroom da toilet aciki kamar na nadiya amma kitchen dinsu awaje yake saidai kowa da nata,

Ana gama gyaran gidan akazo aka yiwa asabe jere nan aka kawota gidanta, Sam kabeer baya cikin hayyacinsa amma saida asabe tasan yanda zatayi ta kalallameshi ya kulata nan kuma suka fada duniyar soyayya koda yaushe suna tare suna shan soyayya amma kullum yana zuwa gidan iyayensa duk da babu wanda yake kulashi idan yaje.

Nadiya kam yanzu zuciyarta ta dan huce tayi sanyi saboda kullum umman sumaila cikin yimata nasiha take tana kwantar mata da hankali hakan yasata sakin ranta abu dayane yake damunta yawan tambayar dasu fadeela ke yimata kullum wai ina abbansu su suna son ganin babansu,

Duk lokacin da suka yimata wannan tambayar kuka take domin bata da amsar da zata basu.


Tunda asabe mc ta tare babu wani wanda ya leka gidan daga cikin dangin kabeer babu wanda yasanta itama babu wanda tasani acikin danginsa, sai dai koda yaushe cikin soyewa suke basa aikin komai sai soyayya, ko girki batayi sai dai suci take away,

Watansu uku da aure komai yafara sauyawa domin hankalin kabeer yafara tashi da rashin nadiya saboda yasan itace sirrinsa, gashi ko kusa bazaka taba hadata da asabe ba, domin asabe irin matan nanne masu son jiki ko kadan bata son aiki, bata girki sai dai aci take sway ko sharar dakinta bata iyawa nan gidan ya kazance idan yayi mata magana tace bazata iyaba dan haka dole yabarta tasamo yar aiki wata dattijuwa mai suna hajjo,

Fushin da su mama sukeyi dashi har yanzu basu huceba sannan kuma yanzu tunaninsa gaba daya ya raja'a akan nadiya da yaransu dan haka yafara nemarwa kansa mafita wato hanyar da zaibi yadawo da nadiya.....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/22, 7:54 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(True life story)_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*



*28*





~~~Gaba d'aya hankalin kabeer yanzu ya koma kan nadiya domin sai mutum baya nan kake gane amfaninsa, sai yanzu yagama tabbatarwa da cewar nadiya itace jin dadin rayuwarsa, itace farin cikinsa, itace sirrinsa,

Gidansu yaje duk da cewar yasan babu mai saurararsa, abba yasamu akofar gida yana kishingide akan tabarma yana sauraren radio nan ya tsugunna agabansa yana gaidashi amma abba ko kallonsa baiyiba daga karshema sai ya tashi ya kwashe shimfidarsa ya shigewarshi gida yabarshi, cikin damuwa da tashin hankali kabeer yabi bayan abba amma ko saurararsa baiyiba,

Wurin mama yaje wacce ke cikin kitchen tana fere doya nan itama tayi watsi dashi kamar bata san yana wurinba ko kallonsa batayi ba bare ta amsa masa gaisuwarsa,

Iya tashin hankali yashiga domin yasan fushin iyaye ba abun wasa bane, rokon mama yafara cikin muryar nadama kamar zaiyi kuka abin d'a da uwa sai ita ta dan sakko ta saurareshi nan yaketa rokonta akan ta taimaka masa nadiya tadawo gareshi, cemasa tayi yaje yasamu nadiyan yabata hakuri idan taga zata dawo to idan kuma bazata dawoba shikenan,

Tashi yayi yafita da niyyar zuwa gidansu nadiya, cikin sa'a itama ranar suka zo gida itada umman sumaila dasu fadeel domin umman sumailan ta fahimci cewar nadiya tana bukatar ganin gida shiyasa tace su shirya suzo,

Koda yaje gidan nadiya banza tayi dashi amma su fadeela na ganinshi suka tafi dagudu suka fada jikinsa nan ya rungumesu yana jin sonsu har cikin ransa,

Bin nadiya yayi daki bayan sun gaisa dasu mama Allah sarki mama mace mai kirki da kawaici domin tunda abunnan yafaru bata nunawa kabeer komaiba ko canjin fuska bai gani atare da itaba,

Tana kwance akan gado Amira na zaune tana assignment ya shiga, tashi Amira tayi ta fita shikuma yakarasa bakin gadon da take kai, jinshi tayi kawai ajikinta ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikin cikinsa, ko daga idonta ta kalleshi batayi ba nan taji yafara rokonta bayan yasake kankameta,

"Dan Allah nadiya ki kara yimin alfarma, ki sake bani second chance, kiyi hakuri ki dauki kaddara, wallahi ke ce rayuwata, nashiga damuwa na rashinki domin na tabbata babu macen da zata iya kula dani kamar ke, dan Allah kiyi hakuri ki koma dakinki.."

Har yayi ban hakurinsa yagama nadiya bata kulashi ba, duk yadda yaso ta saurareshi haka ya hakura yatafi batare da nasara ba, nan kuma tun daga wannan lokacin ya shiga kai kawo da sintiri agidan, ita nadiya yanzu haushinsa takeji sosai sannan bata jin sonsa ko digo acikin ranta dan haka ranar da umman sumaila zata tafi tace zata bita amma mama da umman suka hanata sukace tayi hakuri ta zauna nan tayi kuka kamar wadda aka yiwa mutuwa, ko hucewa daga kukan batayi ba sai gashi yazo nan ya tisata agaba da lallashi yana bata hakuri, yau dinma bata kulashi ba dai haka suka cigaba dayi kullum sai yazo amma bata yimasa magana sai yaransa ne kurum ke maraba da zuwansa,

Ahaka sai da suka dauki sati biyar yana wannan zirga zirgar daga karshe abba da mama suka kirata suka yimata nasiha akan tayi hakuri ta koma dakinta tunda mijinta nasonta, bata son tona masa asiri domin akoda yaushe ta daukeshi a matsayin sirrinta shiyasa tayi shiru bata fada musu irin rayuwar da suka yi dashi tun daga farkon aurensu ba, dayake abbanta yana son ta koma dakansa yaje ya zabo mata set din kayan daki masu kyau da kujeru, komai na daki sai da abba ya sauya mata sabo babu abinda yabari, kayan kitchen ne kawai yabata kudi yace ta siyi abinda take so,

Kannen kabeer fati da A'isha da Amira kanwarta sune sukaje suka shirya mata kayanta nan dakinta da falonta yafito tamkar na sabuwar amarya domin komai sabone, har suka gama aikin suka tafi asabe bata nan,

Adaren ranar yazo ya daukesu, ko kallansa nadiya batayi ba har sukaje gidan, dama dakinta shine na karshe na asabe na farko nanma ko kallon sashen asaben batayi ba tawuce abinta,

Har wani rawar jiki ta lura yakeyi amma ta shareshi, baiyi fushiba yabita dakinta lokacin tana kwantar dasu fadeela bayan sunyi bacci,

Zama yayi agefenta jikinshi cikin nata, jelar kitsonta yakamo yadora kansa akan kafadarta yafara bata hakuri,

"Nadiya kiyi hakuri ki yafe min kidaina wannan fushin dani dan Allah.."

Juyawa tayi ta kalleshi tareda zuba masa kyawawan idanuwanta......




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[7/22, 8:01 AM] Ummi A'isha๐Ÿ‘Œ๐Ÿป: *MIJINA SIRRINA...!*๐ŸŒน
_(True life story)_




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*




*29*


~~~Ta dade tana kallonsa idonta cikin nashi batare data yi magana ba ganin haka yasashi rungumeta ajikinsa yana shakar daddadan kamshin jikinta,

"Kiyi hakuri nadiya dan Allah.."

Jin yanata bata hakuri yasata yin magana,

"Shikenan na hakura.."

Bai bari takarasa ba ya rufe mata baki da nasa, shi kansa yasan nadiya macece irin wacce kowanne namiji zaiyi burin mallaka to amma shi bai san abinda yake damunsa hakaba kawai dai ya tsinci kansa acikin wani irin yanayi.


Da safe nadiya bata nuna masa komai ba ta tashi fuskarta asake nan ta fita ta shiga kitchen ta hada musu breakfast tafito anan taga asabe akaro nafarko tana tsaye abakin kofar dakinta ta dafa bango tasha kwalliya sosai ga wani uban dauri da tayi samfarin ture kaga tsiya tana ta faman aikin taunar cingam,

Ko kallonta nadiya batayi ba ta wuce cikin dakinta tana dauke da farantin data doro kayan karyawar akai,

Cikin bedroom dinta ta shiga inda yaya kabeer yake kwance yana bacci shida su fadeel sun sakashi atsakiya yana rungume dasu,

Tsayawa tayi tana kallon dakin nata yanda ya hadu komai light purple haka ma kayan cikin falonta suma komai kalar light purple ne,

Ruwan wanka ta shiga ta zuba tayi tafito tafara shiryawa, tana cikin yin shirin yaya kabeer ya farka nan ya zauna ya zuba mata ido domin nadiya itace rayuwarsa,

Murmushi tayi masa ta cikin mirrior, "har ka tashi?"

"Nasamu natashi dakyar..."

Tashi yayi ya sauka daga kan gadon ya nufi wurinta,

"Kin yi kyau.."

Murmushi tayi ta kalleshi, "nagode"

Wucewa yayi zuwa cikin toilet yayi wanka ya fito ya shirya suka koma falo yaci breakfast,

Tunda tadawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login