Showing 57001 words to 60000 words out of 82977 words
Chapter 20 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt
drewar din jikin gadonshi ya dauko plane sheet da pencil ya bata, abayanta ya zauna ya rungumeta,
"To zana ingani, nafi son ki zana da kanki saboda kar ayi miki wanda bashi kike so ba..."
Zanawa tafara duk da bata san yanda ake yiba, falo ta fara fitarwa sannan sai bedrooms guda uku, biyu suna opposite da juna daya kuma takaishi can gefe da nisa shi kadai kwal,
"Baby wannan bedrooms din guda biyu nasu waye?"
"Nawane daya, guda dayan kuma na baki.."
"Shikuma wancan wanda kika kai gefe fa?"
"Naka ne.."
Murmushi yayi, "wato ni aka kai gefe kenan..."
Mika mishi takardar tayi wai tagama,
"Baby baki zana bathroom ba, baki fitar da kitchen ba bare store..."
Ita shaf ta manta sai lokacin ta tuna,
"Nuna min a inda kike so asaka miki kitchen din..."
Nuna mishi tayi ya zana, haka yayita tambayarta idan ta nuna sai ya zana mata har zanen gida ya kammala.
Da dabara ta samu tafita daga dakin ta koma falo wurinsu hajiya da anty siyama saboda tasan idan zamansu yayi yawa a daki itada amadi su hajiya zasu zargi wani abu,
Tana zaune awurinsu hajiya har amadin yafito daga dakinshi idonshi fes akanta,
"Anty siyama kinzo da driver ne ki ara min shi ya mayar min da baby school..?"
Kunya maganarshi tasaka nadiya jin agaban hajiya da yayarshi yana kiranta da baby,
"Ehhh yana nan yaya amadi, yaushe zata tafi?"
Anty siyama tabashi amsa,
"Sai zuwa anjima..."
"To shikenan"
Zama yayi akusa da nadiya ita duk sai take jin nauyinsu hajiya tana ganin kamar zasu ga rashin kunyarta amma shi sai sake matsawa yake kusa da ita.
Har misalin karfe 6 na yamma tana gidan saboda shi amadi tashin tsakar dare zasuyi, ganin 6 ta dan gota yasa nadiya tace mishi zata tafi, albarka sosai hajiya ta shiga sanya mata tareda yimata godiya kamar wacce takai musu wani abu, sallama sukayi da anty siyama wacce keta faman janta da hira kamar ba yayar miji ba,
Hannunta yakama bayan sun fito daga falon hajiya,
"Baby ki kular min da kanki dan Allah, ki kular min da kanki,nasan zanyi missing dinki mutuka but ako ina nake akuma duk inda na tsinci kaina kina nan acikin zuciyata, soyayyarki daga Allah ne bani na sakawa zuciyata ba, namanta ban fada miki ba shekaran jiyafa naje rano nayiwa su mama sallama,baby zan tafi nabarki a lokacin da nake da tsananin bukatarki amma babu komai insha Allah kamar yaune zaki ganni nadawo gareki, zan kiraki anjimabkafin mu tashi..."
"To shikenan Allah ya kiyaye hanya" tafada batare data iya kallonshi ba, kiss ya manna mata akan lips dinta sannan ya rakata wurin motar anty siyama inda drivernta malam mudi yake tsaye yana jiran karasowar nadiya, amadi da kanshi ya bude mata kofar motar ta shiga ta zauna ya mayar ya rufe, gefe yakoma ya tsura mata ido ta cikin glass din motar daga karshe yafara daga mata hannu yana yimata sai wata rana......
_*Ummi Shatu*_👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*59*
aishaummi.blogspot.com
*T*saye yayi ya harde hannuwanshi a kirjinshi yana kallonta, dagowa tayi itama ta kalleshi nan ta hangoshi ta cikin glass din motar yana yimata murmushin shi mai tsananin tsada,
Saurin kawar da kanta tayi bata sake kallonshi ba har suka fita daga gidan,
Shima bai bar wurin da yake tsayeba har saida yaga fitarsu nadiya sannan ya juya ya koma ciki wurinsu hajiya,
"Kai yaron nan gaskiya kanada matsala yanzu saida ka dauko yarinyar nan kaji dadi.." Anty siyama tace dashi tana daddanna wayar dake hannunta,
"Anty kenan to wani abune? Ni jiyama awurinta na kwana"
Yabata amsa yana kallonta yana dariya,
"To ya isheni haka marar kunya kawai"
Dariya yayi yatashi yabi hajiya cikin kitchen inda take soya masa dambun nama wanda zai tafi dashi.
Bayan sallar magrib sosai su nadiya suka shiga wudil, har cikin makaranta drivern yakaita, fita tayi tashiga hostel, tana zuwa dakinta ko zama batayi ba amadi ya kirata,
"Dan naci..." Tafada ahankali kafin ta daga wayar,
"Baby kunje ko?" Taji yafada cikin muryarsa mai sanyi,
"Ehhh mun sauka harma drivern yatafi"
"To naji dadi tunda ya mayar min da matata lafiya..."
"Uhmmmmm" tafada,
"Kin san abinda anty siyama tace bayan kin tafi? Wai saida na daukoki nikuwa nace mata ai jiyama awurinki na kwana..."
"Kafada mata haka?"
"Ehhh mana ai ba karya nafada ba ko ba tare muka kwana ba?"
Shiru tayi masa saboda taji yafara neman sakin layin da suke,
"Uhmmmm? Baby ko bahaka bane?"
Nan dinma shiru tayi masa bata amsaba, kasancewar idan da sabo yasaba da halinta yasashi cigaba,
"Jiya najini acikin wata duniya ta daban, ban taba samun kaina acikin wannan yanayin ba, naji dumin jikin matata Sosa...."
"Kaima wallahi ka iya maganganun...." Sai kuma tayi shiru bata karasa ba saboda nauyin da kalmar tayi mata abakinta,
"Meyasa baki karasa ba? Wata nafadawa ba matata nafadawa ba? Idan banyi hira dake ba dawa zanyi? Uhmmmm"
"Uhmmmm" tafada,
"Uhmmmmm?" Yasake fada,
"Uhmmm" itama tasake bashi amsa,
"Uhmmm?"
"Nace uhmmmm"
"Haba baby kiyi magana mana.." Yafada yana dariya saboda tabashi dariya sosai,
"Umhum.." Tabashi amsa,
"To tunda bazaki yimin magana ba shikenan sai anjima, yunwa nakeji abinci zanje naci"
"Toh"
"To sai anjima, ki kular min da kanki, i love you..."
Ko jiranta baiyi ba ya katse wayarshi saboda yasan ba amsa mishi zatayi ba,
Tun 9 ya kirata yake yimata hira wacce kusan shi kadai yake yin kayarshi domin ita daga uhm sai um um, bashi yayi sallama da itaba sai karfe 2 nadare saboda lokacin zasu tafi airport domin 2:30 zasu tashi,
Lokacin da yaje airport dinma saida ya kirata yasake yi mata sallama daga karshe kuma taji yayi shiru kamar wanda yake jiran wani abu,
"Shikenan baby sai nadawo..." Yafada tareda goge kwallar idonshi, duk sai taji wani iri,
Ita dai tasan bata sonshi ko yaya amma kuma saita gagara bacci, daren ranar gaba daya kasa bacci tayi tun lokacin da yace mata yatafi sai yaje zai kirata.
Haka tatashi da safe duk jikinta sanyi kalau kamar marar laka ajiki, duk da bata damu dashi ba sai da taji hankalinta ya tattara yatafi kanshi gaba daya,
Haka haka dai ta wuni ranar har dare yayi shiru bai kirata ba, ta karfi da yaji tasamu ta yakice damuwar taci gaba da al'amuranta,
Tunda yayi kwana biyu da tafiya kuma sai tafara mantawa da tunaninshi saboda dama bawai wani shiga ranta yayi ba domin yanzu bazata yi gaggawar sakashi aranta ba har sai ta fahimci wanene shi,
Kwananshi 5 da tafiya tafito daga lecture sai taga number din waje na kiranta domin akwai plus ajiki,
Jikinta ne yabata cewar amadi ne,
"Hello..."
"Baby nah..." Taji yafada cikin muryarshi kamar mai jin bacci,
"Na'am.."
"Baby ya kike? Inata missing dinki sosai,ke kuwa bakya missing dina ko?"
"Hmmmm"
"Ban gane hmm ba, kinga daga zuwana har mura ta kamani"
"Allah ya sawwake"
"Amin baby, abar sona, ina sonki baby..."
Shiru tayi tana jinshi, ya dan jima yana fada mata kalamai na soyayya zalla amma har yayi yagama bata mayar mishi da martani ba daga karshe dai yayi mata sai anjima ya kashe wayar wai yayi fushi tunda bata taba cemishi tana sonshi ba,
Bata kirashi ba har dare, shi da baya zuciya shine ya sake kiranta,
"Har ka huce kenan?" Tace dashi lokacin da ta dauki wayar, murmushi mai sauti taji yayi,
"Da anfada miki nayi fushi dake ne? Ni ai bazan taba yin fushi dake ba arayuwata... Ni yanzu bacci ma zanyi shine naji baccin bazai yiyu ba har sai naji muryar matata, ki cemun you love me..."
"Uhmm"
"Uhmm ki fadi abinda nasaki mana..."
Shiru tayi batayi magana ba,
"Baby..."
"Na'am"
"Kiyita fada min kalaman so har sai nayi bacci, idan kuma bakiyi ba Allah zai saka min..."
"Ni gaskiya ban san me zance ba..."
"Tunda baki saniba to kiyita cewa kina sona, kinga nasanar dake abinda zaki fada.."
Shiru tayi shima yayi shirun yanata yimata dariya kasa kasa tayadda ba zata jiba,
"Baby kina son nabarki da Allah? Idan bakya so kiyi abinda nace kinga mu dare yayi sosai anan, oya start...."
"Me zance?"
"Kice kina sona, kuma kiyita fada har sai nace ya isa haka.."
Kamar zatayi kuka taji saboda ita gaskiya bata son fadin abinda yace,
"Nidai gaskiya ka sauya wani.."
"Wallahi wannan zaki fada kuma idan baki fada ba ban yafeba..."
"I love you..." Tafada tana bata fuska kamar yana ganinta,
"To ai fada zakiyi tayi har sai nace ya isa..."
Cigaba da fada tayi shikam har wani lumshe ido yakeyi saboda yanda Kalmar take yimasa dadi duk da yasan adole take fada bawai dan tana son nashiba.
Saida tafada fiyeda sau 20 sannan yace mata ya isa haka, shiru tayi fuskarta akumbure dan takaici da bacin rai,
"Nagode my baby, sai munyi magana gobe kinga yanzu bacci zanyi, nagode Allah yayi miki albarka, I love you..."
Katse wayar yayi yana dariya ita kuma ta katse tata cikeda takaici, tun daga wannan ranar kullum haka yake mata shiyasa wata rana har bata son bude wayarta kuma idan yakira yaji arufe idan yasake kira sai yace mata idan takara kashe masa waya itada Allah, babu yanda ta iya dolenta haka ta hakura ya zatayi da nacin amadi.
Akwana atashi ahaka wannan semester din takare akayi musu hutu ta koma gida yanzu semester daya ya rage mata, time din watan amadi 3 a birnin London,
Kullum cikin kiranta yake sannan kuma ya tsareta lallai lallai sai tayi masa kalaman soyayya ko kuma tace masa i love you, amma wani lokacin bama ya kulata da ya kirata zaice ta hadashi da twins susha hirarsu,
Ganin har yanzu bata kamu da son amadi ba abin yabawa Amira mamaki, gaba daya takasa gane nadiya wacce irin mace ce mai tsaurin rai da taurin kai tunda ai kodan kyautatawarsa agareta itada yaranta ya kamata ace tafara sonshi Sannan bai rageta da komai ba duk karshen wata kudi yana shiga account dinta saboda yace mata yanzu nauyinta akanshi yake,
Wurin nadiyan ta nufa a inda take zaune tana gyara fuskarta su fadeela kuma sun tisata agaba suna son suyi mata kuka wai sai sun bita ita kuma tace babu inda zataje dasu,
"Anty wai sai ina da yamman nan?" Amira ta tambayeta tana kamo hannayen twins,
"Amira gyaran gashin nan zanje saboda wallahi kaina yacika da yawa.."
Karar da wayar nadiya tafara yine yahana Amira yin magana, dauka nadiya tayi saboda ganin amadi ne dama tana son kiranshi ta tambayeshi cewar zata fita,
"Hello baby" taji yafada lokacin data daga wayar,
"Na'am, dama yanzu zan kiraka"
"Sai kuma gashi na kiraki, meya faru?"
"Ina son zan fitane"
"Ina zakije?"
"Gyaran gashi zanje"
"To, waye naji yana kuka?"
"Su fadeel ne wai sai sun bini nikuma bazanje dasu ba.."
"Akai suke kuka kenan?"
"Ehhh"
"To kema bazaki jeba nahana, idan kuma kina son zuwa ki tafi dasu.."
"Ni bazanje dasu ba"
"To shikenan kema ban yarda kijeba dama ai gashin nawane so abar min kayana ahaka basai an gyara ba"
"Bazanje ba kace fa?"
"Ehhh" yabata amsa,
"Hmmm" tafada tareda katse wayar wadda ko ba afada masaba yasan fushi tayi, kallon su fadeel tayi ta hararesu,
"Sai na zaneku idan baku daina yimin kuka ba, shima harda wani cewa bazanje ba to kar Allah yasa yabarni naje din sai me.."
Tafada cikin bacin rai tareda cire dan kwalin dake kanta ta wulla kan gado ta sulale awurin tayi kwanciyarta.
Ba afi mintuna biyar da faruwar hakaba sai gashi ya sake kiranta, kin dagawa tayi shikuma bai hakura yadaina kiraba har saida taji karar ta isheta sannan ta dauka,
"Baby fushi kikayi ko? Kiyi hakuri to, kije nabarki,sai kin dawo..."
Shiru tayi masa tana cije lip dinta nakasa,
"Baby kije nace, kiyi hakuri tunda ranki ya baci, karki yi fushi dani kinji... Uhmmm baby, kinji?"
"Naji"
"To adawo lafiya, ki kular min da kanki"
Kit ya katse wayar, zama Amira tayi akusa da ita,
"Anty nadiya nikam Yaya Ahmad yana bani tausayi, wai har yau kinki sonshi bare ki nuna masa kulawa"
"Lallai Amira bakida hankali, anfada miki ni sakarya ce da har zan sake garajen fara sonshi? Idan ku kun manta da butulcin Yaya kabeer agareni ni ban manta ba,ni yanzu babu filin so acikin zuciyata"
"Karki ce haka anty, ni ina ganin kibawa Yaya Ahmad dama domin ki gane irin son da yake miki, idan kina son fahimtar shi waye akwai hanyoyi da yawa da zaki iya gudanar da hakan"
Lipstick ta dauka tana gogawa lips dinta, "kamar wacce kenan?"
"Kina iya gwadashi ta hanyoyi da dama, ma'ana ki rinka kiranshi ko yi mishi text da wata number ta daban wacce bazai taba tunanin cewa kece ba kinga ta haka zaki fahimci inda yasa gaba"
"To Amira kin kawo shawara kam, bari amir ya shigo zan bashi kudi ya siyo min sabon sim.."
"Yawwa anty ko kefa"
Karasa shiryawa tayi ta mike tayiwa su fadeel wayo ta zare jikinta ta fita bayan ta yiwa mama sallama..
Jama'a wai ina labarin kabeer ne da asabe mc? Mu hadu a page nagaba domin jin inda suka makale.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
*60*
aishaummi.blogspot.com
*K*amar yadda amira tabawa nadiya shawara haka ta dauki shawarar acikin kwana biyu tabawa amir kudi ya siyo mata sabon sim special number,
Dayake wayarta 2 sim ne sai kawai tasashi acikin wayar,kiran amadi tafara yi Amira na zaune akusa da ita amma abin mamaki koda wayar ta shiga sai yaki dauka, kira taci gaba dayi nanma bai daga ba har saida ta kira sau hudu ana biyar dinne taji ya dauka,
Sai da ta lankwashe muryarta ta yadda bazai ganeba sannan tayi magana,
"Hello Ahmad..."
Shiru ya danyi kafin yayi magana,
"Wacece?"
"Amma ai kabari dai ma gaisa ko? Kamata yayi mufara gaisawa kafin nasanar dakai ko ni wacece.."
Kitttt taji ya kashe wayar, dariya Amira tafara yi harda rike ciki saboda jin yadda nadiya ta wani kashe murya dan kar ya ganota,
Sake kira tayi nan ya dauka,
"Haba Ahmad ya zaka kashe wayar bayan bamu gama ba? Dan Allah kayi hakuri wallahi ban son bacin ranka, sunana jalila ni daliba ce a makarantar wudil.."
"To meya faru kika kirani? Sannan waye yabaki number ta?"
"Hmm yaya Ahmad kenan ai duk wannan mai saukine tunda kasan bahaushe yace mai son kayanka yafika dabara, dalilin kiranka kuwa shine agaskiya ka dade kana burgeni gashi ina mutukar sonka.."
Sake kashe wayarshi yayi bai karasa jin bayananta ba, kallon Amira tayi tana dariya,
"Ji yasake kashewa,bari nabarshi haka sai zuwa gobe sai insake kiranshi inji"
Dariya Amira tayi "Allah sarki yaya Ahmad daga jin maganar so sai kuma akashe waya"
"Ke kyaleshi wai shi nan Jan aji, zan kureshi ne ai.."
"Anya kuwa? Anty banga alama ba"
"Kya gani ai..."
Rufe sim din tayi tabar wanda take amfani dashi kawai a bude, shi kam Amadi ko takan maganar ma bai kara bi ba bare ya binciki ko wacece saboda da farko ya tsammaci zee ce kanwar mijin anty siyama amma kuma daga baya sai yagane cewar ba ita din bace nan yayi watsi da maganar domin bama yason yasan ko wacece.
Bayan sallar isha tana tsaka da shirin bacci sai gashi ya kira,
"Baby" yakira sunanta cikin so domin akoda yaushe jin sonta yake yana sake ratsashi,
"Na'am.."
"Bakiyi bacci ba?"
"Yanzu zanyi shiryawa nake.."
"Shiri kuma? Baby wanne irin shiri bayan bana nan? Ki tattara duk shirye shiryenki ki ajiye har sai nadawo"
"Hakane"
"Ko baki yarda ba?"
Bata bashi amsa ba takarasa saman gado tayi kwanciyarta abinta,
"Baby ina yimiki magana shine kika rabu dani ko?"
"To me kakeso ince?"
"Ohhh aiki kike nema kenan ko? To bari inbaki kiyi, kiyita kissing dina har sai nace ki daina ya isheni.."
"Nidai gaskiya wallahi a'a.."
Murmushi yayi, " a'a fa kikace, kifara tun kafin kiyi laifi awurin Allah"
"Wallahi nidai indai haka zaka rinka yimin zan daina daukar wayarka.."
"Idan kin daina daukar wayata ma wani laifinne dai kikayi gara ma ki dauka.."
"Indauka kayita sakani aiki.."
"Menene aikin aciki? Ai ban fara saki aikiba sai nadawo tukunna, yanzu dai fara ina jinki"
Wani haushi ne ya turnuketa saboda jin yana yimata dariya wadda tun yana boyewa har yafito fili,
"Ahmad" takira sunanshi,
"Na'am baby love"
"Meyasa kake yimin hakane?"
"Saboda ke matatace nikuma mijinki ne sirrinki..."
"Shine dalili?"
"Ehh shine, fara ina jinki"
Kamar mai shirin yin kuka haka tafara kissing dinshi ahankali ta cikin wayar, tafi minti biyar tanayi amma baice ya isa ba sai da ta kusan mintuna goma sannan ya dakatar da ita,
"Baby barshi haka dan wallahi za a iya samun matsala idan kikaci gaba dayi gashi kuma bakya kusa"
Shiru tayi masa saboda yanzu taga yagama zama marar kunya bata san meyasa ba kwanan nan wasu maganganu yake zarowa yafada mata kuma idan yafada ko a kwalar rigarshi babu ruwanshi da jin kunya,
"Washhh, baby wallahi yau akwai matsala..."
"Nikuma meye nawa aciki?" Tace dashi tana turo baki kamar yana ganinta,
"Meye naki aciki? Kekuwa kikeda ruwa da tsaki aciki tunda mijinki yana bukatarki yanzu gashi bakya kusa dashi"
Shiru tayi masa tana sauraron yanda yake yi mata wani ajiyar zuciya akunne,
"Nifa kaga ka cika min kunne gaskiya idan ka gama wannan ajiyar zuciyar taka ka kirani.."
Shiru taji yayi wanda tasan kasa maganar yayi badan hakaba da tuni ya bata amsa,
"Ina magana kayi min shiru..."
Har lokacin dai bai iya yimata magana ba yayi shiru abinshi sai ajiyar zuciyar da yake ta faman ajiyewa daga bisani kuma yafara wani tari babu kakkautawa sai da yajima yana yi sannan tarin ya tsaya sai kuma shakuwa, shak'uwa yake yi sosai,
"Maganinka ai, gobe ma dan Allah ka kara.." Tafada ahankali, ashe yaji abinda ta fada,
"Baby..." Taji yakira sunanta amma kuma sai yayi shiru saboda shakuwar da yaketa yi,
"Ya?" Tafada tana dariyar mugunta,
"Da biyu kikayi min wannan abun ko?"
"Bawani da biyu, bakaine kasani ba? Harfa rokonka nayi akan karnayi amma kaki kace sai nayi maka"
"Hmmmm" yace yana murmushi,
"Kaje kasha ruwa ko zaka daina wannan shakuwar.."
"Babu ruwanki dani malama.." Yace da ita wanda har lokacin shakuwar taki barinshi, jin abin bamai karewa bane yasashi tashi yaje ya dauko ruwa yadawo ya kwanta,
"Kaima ance maka kasha ruwa kaki"
"Gashi ai zan sha"
Saida ya shanye robar ruwa guda daya amma shakuwar bata barshi ba, nan kuma nadiya tasan abin nashi ba karami bane,
"Wai baka sha ruwan ba?"
"Wallahi nasha, roba dayafa na shanye baby"
"Ohh to zata daina"
Shiru yayi mata yaci gaba da shakuwarsa zuwa can sai yaji ta tsaya yadaina yi kwata kwata,
"Tunda kadaina shakuwar to saida safe ni bacci nakeji"
"To baby saida safe, i love you"
"Uhhhum"
Katse wayar tayi ta turata karkashin pillow, dariya ce ta subuce mata lokacin da ta tuno amadi,
"Yaro yasha tafi karfin cikinsa, maganinka ai" tafada tana dariya, nan bacci ya dauketa tayi abinta cikin kwanciyar hankali shikuwa bawan Allah yana can yakasa bacci sai juyi yake yi saboda kewar matarshi