Showing 24001 words to 27000 words out of 82977 words
Chapter 9 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt
dai abubuwan da dan dama dama babu tashin hankali har tayi sati uku da dawowa nan kuma al'amura suka fara sauyawa domin wani iskanci asabe ta tsiro dashi, duk ranar girkin nadiya sai ta rike kabeer adaki ta hanashi fitowa,da ranar girkinta da ba ranar girkinta ba koda yaushe tana manne dashi,
Sannan idanma ta barshi yatafi wurin nadiyan to kwana zatayi tana yimusu hayaniya ta hanasu bacci ko kuma ta kunna kida ta cika gidan da kara,
Ko kadan nadiya bata taba tankawa asabe ba domin shima kabeer din bashida yanda zaiyi kullum cikin bawa nadiya hakuri yake yana cewa ta rufa masa asiri karta tafi ta barshi domin idan har ta rabu dashi baisan yanda rayuwarsa zata kasance ba,
Tun nadiya tana hakuri har abin yasoma isarta domin asabe ta iya duk wani salo na bariki, sai ta daidaici kabeer zai shigo gida idan girkin nadiyane sai tafito half niket tazo ta tsaya akofar daki tana taunar cingum yana shigowa zata janyeshi zuwa dakinta,
Wannan abun yana mutukar kona ran nadiya amma duk lokacin da suka kebe dashi bata hakuri yake yi, dole take zaune dashi kawai dan babu yanda zatayi amma yana mutukar kyautatawa yaransa yana sonsu sosai haka itama asaben tana masifar son fadeela da fadeel uwarsu ce kawai bata so,
Yau kam tunda yamma nadiya ta tafka tagumi tana jin ihu ihun dake tashi daga cikin dakin asabe ita sam bata san abinda yafaru ba sai kawai ihu takeji gamida sautin kida daketa faman tashi,
Jin abin ya isheta yasata komawa cikin bedroom dinta ta dauki alqur'aninta tafara karantawa anan taji zuciyarta tayi sanyi,
Kabeer ne yashigo yana rikeda su fadeel yazauna akusa da ita ya riko hannunta,
"Nadiya kiyi hakuri nasan mun dameki.."
"Dame?..." Ta tambaya domin ta nuna masa abinsu bai dameta ba,
"Da ihun da mukeyi na birthday din asabe..."
Shiru tayi masa taci gaba da karatun alqur'aninta nan ya tashi yafice, haka suka raba dare suna bikin birthday dinnan har nadiya tayi bacci wurin 12 basu gamaba daga karshema bata san lokacin da suka tashiba.
Haka taci gaba da zama da asabe zaman hakuri da kunci domin kusan kullum sai kawayen asaben sunzo sun kafa daba suna zagin nadiya tareda aikamata da habaici ita kuwa bata taba tanka musuba idanma a kitchen take taji abin ya isheta sai ta kashe wutar data kunna tayi komawarta daki ta kwanta inyaso idan sun gama sun tafi sai tadawo ta karasa,
Ita aduk iskancin da asabe keyi babu wanda yake kona mata rai kamar rike yaya kabeer datake har sai tagadama zata barshi yazo wurinta koda kuwa ranar girkinta ne,
Wannan abu ba karamin yiwa nadiya ciwo yakeba, yauma kamar koda yaushe dakinta yake amma sam asabe ta hanashi fitowa sai hirarsu da shewarsu take jiyowa nan ta tashi tafita ranta abace ta nufi dakin asaben wanda bata taba shiga ba sai yau, su fadeel da fadeela ne ke zuwa subi babansu saboda yaga tana sonsu amma shi fadeel idan akwai wanda ya tsana aduniya to asabe ce idan sunje ya rinka kuka kenan har sai sun baro dakin,
Afusace ta bude kofar dakin ta shiga nan taga asaben daga ita sai wando three quarter da wata yar bingilar riga tana kwance akan cinyar kabeer sai dariya take kyalkyalawa can kuma gefe mai aikinta ce keta faman goge goge,
Ai asabe tana ganin nadiya ta shigo ta daure fuska,
"Yaya kabeer kaifa naketa jira.."
Zuruf asabe ta mike ta nufi nadiya tareda bude fefen bala'i,
"To mahaukaciya, jahila wacce bata san hakkin aureba mai son shiga tsakanin masoya, idan bakida hankali ni zan koya miki, uban waye yabaki izinin shigo min daki..."
Iya wuya nadiya tazo domin zagin da asabe ta tisata agaba tana yimata ba kadan bane dan haka itama ta rama,
"Gaki nan babbar jahila, ai idan ana maganar mai raba masoya to bazaki saka bakiba domin da mijina kika ganni amma kike burin ganin kin rabamu, banza yar bariki marar tarbiyya wadda tabaro gaban iyayenta tafito yawon karuwanci.."
Wani mari asabe ta zabgawa nadiya tana kokarin kai mata na biyu kabeer yatashi ya riketa,
"Ka sakeni in koya mata hankali, wallahi da sai na yimiki shegen duka acikin gidan nan.."
Mai aikin asaben ce ta taso tazo tana basu hakuri tareda rike nadiya, "hajiya kiyi hakuri kinji, dan Allah kuyi hakuri.."
Wata ashar asabe ta mulmulo ta jefawa hajjo mai aiki nan jikin hajjon ya dauki rawa tabar wurin da Sauri, fita nadiya tayi tana kuka ta nufi dakinta.....
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[7/22, 8:20 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *MIJINA SIRRINA...!*๐น
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
*30*
~~~Nadiya nafita asabe taci gaba dure duren ashar tana zage zage shidai kabeer yarasa me ma zaice yayi shiru yana jinta,
Nadiya tana daki tana kuka ta dauki waya ta kira abbansa ai kuwa lokaci kadan sai ga abba agidan nan yazo kabeer din yafito abba ya ringa surfa fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba dama asabe bata fitoba domin abba yace shi ba wurinta yazo ba wurin yayansa yazo,
Saida abba yayiwa kabeer wankin babban bargo sannan yatafi da sharadin indai aka sake batawa nadiya to zaizo yatafi da ita kuma bazata dawoba sai dai yasaketa,nan ita kuma nadiyan abban ya bata hakuri yatafi,
Abba na tafiya kabeer yabi nadiya daki shima ya bata hakuri dama kuma yaji dadin zagin da tayiwa asabe domin shima ta isheshi saboda kazantarta da rashin bashi girma ga wulakanci da rashin mutunci,
Iya kuluwa asabe ta kulu dan haka ta shirya tanata masifa ta fice bayan ta kira kawayenta awaya tanata dure duren ashar tana sanar musu da abinda yafaru,
Tana fita hajjo mai aikinta tazo kofar dakin nadiya ta kwankwasa nan nadiya tazo ta bude mata, hakuri tafara bawa nadiya gamida karfin gwiwa domin ita hajjo kirkin nadiya take gani sannan gata da hakuri sabanin uwar dakinta, nunawa hajjo cewar babu komai nadiya tayi domin dama lokuta da dama idan asabe bata nan hajjo nazuwa wurin nadiya suyi hira,
Tunda haka tafaru asabe tasake shirin rashin mutunci agidan koda yaushe kawayenta da wasu yara guda biyu yanmata wadanda take ikirarin cewar kannenta ne sai suzo gidan suyita shewa da zage zage kadan suke jira nadiya ta tanka musu suyi mata duka amma nadiya bata taba kulasu ba haka zasu karaci abinsu su tafi, domin ita yanzu abinsu bai dameta ba saboda yan uwan mijinta na tsananin sonta, kowa wurinta yake zuwa babu wanda ya taba zuwa wurin asabe sannan har yanzu mamansu kabeer tana yimata hidima kamar da kuma tana ji da ita,
Haka suka cigaba da zama asabe koda yaushe tana kule acikin daki itada kabeer koda kuwa ranar girkin nadiya ne, nadiya kam ta zubawa sarautar Allah ido kallonsu kawai take, mamanta kuwa koda yaushe cikin bata hakuri take tana nuna mata cewar komai mai wucewa ne haka shima yaya kamal dan uwanta koda yaushe hakuri yake bata yana nuna mata cewa ko wanne mutum da irin kaddararsa,
Yau dai bata san abinda yahada asabe da kabeer fada ba amma tanata jiyo hayaniyarsu domin hayaniyar tasuce ma ta tasheta daga bacci nan kuma tafara jiyo karar alamun duka kabeer yana dukan asabe sai da yayi mata lilis sannan ya kyaleta yafice daga gidan gaba daya, yana fita babu jimawa itama asaben ta hada kayanta ta fita,
"Auren bariki kenan.." Nadiya tafada acikin ranta domin ita tunda take da kabeer bai taba yunkurin dukanta ba sai dai fada kawai amma ita asabe ji yadda ya nada mata duka kuma tasan yadaki banza,
Tunda asabe tatafi gidan yayiwa nadiya dadi suka dawo rayuwarsu ta da babu takurar kowa nan zama yayi dadi har kabeer yana cewa zata koma makaranta tunda bata sake samun wani cikinba nan yaje ya siyo mata form din jami'a ya cike yayi submitting, bikin cousin dinta kamal ya tashi a kura nan kabeer yakaita gidansu mama saboda tare zasu tafi sannan yabata 30,000 yace takaiwa kamal gudun mawa,
Bayan dawowar nadiya daga bikin kamal da sati uku sai ga asabe mc ta dawo amma wannan dawowar kamar da lumana tadawo saboda ko fita zatayi sai ta yiwa nadiya sallama cewar tafita haka idan tadawo ma zata leko tace mata tadawo sai dai kuma wannan bai hanasu kulewa acikin daki ita da kabeer ba wannan abu shi yafi komai yiwa nadiya ciwo, gashi ko abu zai siyo agidan to bai isa ya siyowa nadiya ba sai asabe tayita tijara tana zage zage gamida dure duren ashar,
Makarantar ma da yace nadiya zata koma lokacin da admission din ya fito nan asabe ta tada rikici dolensa yahakura itama nadiya tace bazata yarda ba nan tatafi taje ta fadawa su abban kabeer din fada abba da mama suka fara sukace dole sai tayi karatu ko bayaso, abu dai ya zama rigima da tashin hankali ganin yana neman yayi yawa abban nadiya yakirata yabata hakuri yace ta hakura da karatun tunda shima kabeer din yanzu baya so, nan nadiya tayita kuka itafa gaba daya yanzu tagaji da zamanta da yaya kabeer, zaman gidansa yagama isarta,
Ahaka ta hakura ta dawo gidan amma kullum cikin bacin rai take domin ada kome kabeer zaiyi yana fada mata kuma yana neman shawararta amma banda yanzu, yanzu duk abinda zaiyi sai dai kawai taganshi da abinsa sun gama magana da asabe,
Kudin kunshi da na gyaran kai ya bata yau ta fita tatafi gidansu mamanshi domin a unguwar takeyi, can tawuni agidan mama tareda su A'isha sai yamma suka dawo itada yaranta suna shigowa gidan suka iske asabe mc ta dora daya akan daya akan farar kujera akofar dakinta tana taunar cingum tayi daurin nata kamar yadda ta saba na ture kaga tsiya,
Kallon nadiya tayi tana farfara ido, "Ashe bakya nan?"
"Ehhh" nadiya ta amsa mata,
"To sannu da zuwa"
"Yawwa" nadiya ta amsa a takaice tawuc,
Tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira kabeer tana tambayarsa yana ina, nan yace mata mota yaje daukowa amma yakusa dawowa,
Tana daki tana shiryawa tafito daga wanka taji knocking nan taje ta bude, asabe ce ta shigo har cikin falonta yau tana kallon falon cikin mamaki domin bata taba zaton haka falon nadiya yahadu ba bata san nadiya tanada gata hakaba,
"Lafiya?" Inji nadiya,
"Ehh lafiya kiranki nazo kije kiga sabuwar motar da muka sake.."
Asabe nagama fadin haka ta juya tafita, hijab nadiya tasa ta nufi packing space nan taga sabuwar mota dal hadaddiya mai tsada, tsayawa kawai tayi tana kallon kabeer cikeda takaici domin lokacin da yake neman shawararta tasha fada masa cewar ya runka adana kudinsa yana alkintawa domin yanada yara sannan nan gaba zai sake haifar wasu kuma ya rinka yiwa gidansu da yan uwansa abin arziki ba albazzaranci ba,
"Kizo muje dani.."
Asabe tace da nadiya tana murmushin naci gari,
"A'a sai kun dawo"
Nadiya tafadi tareda juyawa tayi tafiyarta, nan asabe da kabeer suka fita asabuwar motar, ahanya asabe take ta tambayar kabeer wai dama nadiya iyayenta suna da kudine ko shine yayi Mata wadannan kayan falon shi kuma yabata amsa da cewa ai baban nadiya yafishi kudima domin tun duniya tana kwance yake da arzikinsa,
Al'amura sun sake kwabewa abubuwan babu sauki nadiya kawai tana zaune agidan kabeer ne amma asabe ita ke juya gidan domin duk lokacin data raya mata zata biyawa kabeer kudin jirgi da ita kanta suyi tafiya sai sun dade sannan su dawo, duk lokacin da sukayi tafiyar sai dai nadiya tatafi gida idan yadawo sai ta dawo nan zaita bata hakuri,
Haka take zaune zaman hakuri tun tana ganin saukin abin har abu yazama babba domin yanzu sunkai matsayin da kabeer ko abincinta baya ci, baya zuwa dakinta, baya kulata koda yaushe Allah take kaiwa kukanta tunda ada duk da masifar asabe kabeer yana kwana adakinta sannan yana cin abincinta domin nadiya mace ce mai tsafta amma yanzu gaba daya ya sauya,
Ita kanta nadiya jin zaman gidan take ya isheta kamar tana kan kaya, burinta kawai shine tabar gidan nan takira mama take fada mata, kamar koda yaushe nasiha mama tayi mata ta bata hakuri tace taci gaba da addu'a, haka ta hakura ta zauna amma rayuwar babu dadi atattare da ita,
Fada kuwa tsakaninta da asabe kullum ne sai dai idan bazata fito wajeba, yauma daga fitowarta zata kitchen asabe tafara zaginta akan wai kawai dan jiya yaya kabeer ya siyo musu lemo da ruwa dukkaninsu wai akanme zai siyowa nadiya, zagi sosai asabe keyiwa nadiya, dama nadiya tagama gajiya nan tafara ramawa asabe tazo ta kamata da kokawa wai zata daketa itama tarama tuni suka kaure da fada nadiya ta jefarta tahau ruwan cikinta tana duka ahaka kabeer yazo ya iskesu nan ya janye nadiya, dakinta ta koma ita kuma asabe taci gaba da zage zage, daga karshe takoma daki ita da kabeer nadiya bata san me asabe ta fadawa kabeer ba kawai tana zaune adaki sai ganinsa tayi ya shigo nan ya juya mata baya ya mika mata takarda,
"Nadiya na sakeki saki biyu.."
Wata mummunar faduwar gabace ta dirarwa nadiya duk da tagama gajiya da zaman gidansa sannan yanzu ta tsaneshi bata sonshi amma saida hankalinta yatashi, juyawa yayi ya fita ita kuma ta hada kayanta tana kuka taja yaranta suka bar gidan suka nufi gidan mahaifinta........
*_Ummi Shatu_*๐๐ป
[7/23, 7:37 AM] Ummi A'isha๐๐ป: *MIJINA SIRRINA...!*๐น
_(True life story)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert writers)_
*31*
aishaummi.blogspot.com
*D*a kuka nadiya taje gidansu mama na ganinta ta tashi agigice domin tasan ba lafiya ce ta kawota ba,
Cikin kuka mai ban tausayi nadiya ta mikawa mama takardar sakin da kabeer yayi mata, mama na karantawa tafara hawaye, daga mama har nadiya kuka suke babu mai rarrashin wani,
Sai da sukayi kuka mai isarsu sannan mama ta goge hawayenta tace,
"Babu komai nadiya kiyi hakuri kinji ki dauka duk abinda yafaru dake kaddara ce sannan jarrabawace daga Allah kuma insha Allah zakiyi farin ciki agaba, insha Allah zaki samu ribar hakurin da kikayi, kiyi hakuri kidaina kuka kinji.."
Tashi mama tayi taje ta damawa nadiya kunun gyada mai zafi ta kawo mata amma ko kadan nadiya takasa sha,
Ahaka abba yadawo ya iskesu, shi kansa yayi mamakin sakin da kabeer yayiwa nadiya lokaci guda dan kawai sunyi fada da asabe,
Waya abba yayiwa abban kabeer ya sanar dashi abinda ya faru nan ran abban ya baci iya baci babu shiri yataho zuwa gidansu nadiya fada yake yi sosai daga karshe yace koda kabeer yadawo bikon nadiya to kar akuskura asaurareshi sannan tunda kabeer yayi haka to babu ruwanshi da shi ya fita sabgarsa,
Haka suka gama jajantawa juna abban kabeer yatafi yaje ya sanarwa da mama abinda yafaru, iya tashin hankali itama mama ta shiga ranta duk ya baci akan wannan maganar, ita kuwa asabe danma kar kabeer yace zai dawo da nadiya sai ta biya musu kudin jirgi suka bar kasar.
Tsabar damuwar da nadiya tashiga sai da tayi kwana 7 bata bacci, mama koda yaushe cikin yimata nasiha take haka ma kamal cousin dinta lokacin data fada masa cewar yaya kabeer ya saketa takanas yazo har gida yayi mata nasiha akan ta dauki kaddara sannan ta manta da batun kabeer,
Da taimakon Allah da taimakon addu'ar iyayenta tasamu tafara rabuwa da damuwa da bacin ran dake damunta, dangana tafara yi ta dauki kaddara domin tasan komai yasamu bawa daga ubangijine,
Cikin yan satittika ta fara mantawa da kabeer babu laifi tafara murmurewa, nan ta danyi kyau tayi fari domin yanzu ta rage yawan tunani,
Kabeer kuwa shida asabe sai da sukayi sati biyar akasar Holland sannan suka dawo Nigeria lokacin da suka dawo yaje gidansu mama yi tayi kamar zata dakeshi saboda tsananin bacin ran abinda yayi, nan yayita bata hakuri amma bata saurareshi ba bare kuma abba wanda dama shi yadade da zare hannunsa daga al'amuran kabeer,
Cikin lokacin bikin fati kanwar kabeer ya taso nan su nadiya sukaje itada mama akayi komai dasu basu nuna komai ba nan kabeer ya rinka bin nadiya da kallo domin ba karamin kyau tayiba,
Hankalin asabe ne yatashi da taji yana ta ambaton nadiya nan tasan yanda tayi ta zugeshi ya rubutawa nadiya cikon saki ukun domin bata son yadawo da ita,
Yaro ya tura ya kira masa nadiya nan tafito ganin shine yasata niyyar komawa amma sai ta daure taje envelope ya miko mata ta karba yaja motarsa yayi tafiyarsa, duk a tunaninta wani abune ko kuma takardar bada hakurice amma koda ta buda sai taga cikon saki dayanne da ya rage a tsakaninsu nan ta fashe da kuka,
Bata nunawa kowa ba hatta mama sai da suka koma gida sannan ta bata takardar tagani, itama mama da abba yadawo takai masa,
Nasiha sosai mama da abba suka hadu suka yimata cewar tayi hakuri ta dauki kaddara insha Allah bazata shiga halin kaka nakayi ba,
Kiran abban kabeer abban nadiya yayi yafada masa yanzu babu aure tsakanin kabeer da nadiya, bakin ciki iya bakin ciki abban kabeer ya shiga amma babu yanda ya iya tunda dan yanzu ka haifeshi ne amma baka haifi halinsa ba.
Nadiya ta shiga damuwa sosai duk wanda yaganta sai ya tausaya mata amma kuma da yake tana yin addu'a sai ta samu nutsuwa nan ta tattara kabeer da duk wani bacin ran da ya kunsa mata da tunaninsa tayi watsi dasu, tunda ta cire damuwa aranta tayi kyau tayi kiba tayi fari ta rungumi yaranta,
Koda yaushe tana cikin kannenta suna hirarsu domin yanzu kowa yagirma amir har yayi candy zai shiga jami'a ita kuma Amira tana SS 3 yayinda waleeda da husna sukuma suke SS 1,
Rayuwar gidansu dama tun fil'azal rayuwa ce mai tsari da dadi kuma har yanzun ma ahaka take shiyasa nadiya ta kwantar da hankalinta daga ita har yaranta sunyi kyau sosai,
Wata bakwai da mutuwar aurenta tana zaune agida da yamma amir yashigo yake cemata tayi bako, fuskarta ta gyara tafita nan taga musty abokin kabeer,
Gaisawa sukayi yayi mata jajanton abinda yafaru sannan yace shi idan zata bashi dama har yanzu yana sonta zai aureta duk da bawani jimawa yayi da aureba, nan ita kuma nadiya tace yayi hakuri ita wallahi ba yanzu zatayi aureba zata dade bata sake aureba, haka musty ya hakura yatafi, nadiya na shiga gida tabawa mama labarin yanda sukayi da musty sannan ta kara da cewa,
"Ni yanzu duk aure ya fita akaina karatu ma zan koma wallahi, zan dade banyi aureba"
"To Allah ya zabi abinda yafi