Showing 48001 words to 51000 words out of 82977 words
Chapter 17 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt
acikin halin da na samu kaina dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi amma bawai samun farin cikiba.."
"To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma ba iri daya bane.."
"Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya banbanta su.."
"A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya Ahmad da yaya kabeer"
"Menene shi?"
"Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na mamajo"
"Shi Ahmad din waye yafada miki baya kula yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji domin bashida tabbas"
"Da yana kulawa ai da zaki sani"
"Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi?"
Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani dariya.. Amma dai ya kamata ai ki sani"
"Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani tunani takeyi.
Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda zai tafi zuwa London,
Batare da matsalar komai ba baki sukayi sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki.
Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro yayi sallama yace wai ana kiranta awaje, hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye yazo ba,
Gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya kabeer da tayi domin yau bata san da wacce yazo ba....
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
_Gaisuwar yau takice ke kad'ai STYLISH BITCH, wanna shafin tukwicine agareki together with Baby Rashid_
*51*
aishaummi.blogspot.com
*T*unda nadiya tafito kabeer ya zuba mata ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta amincewa bukatarsa,
Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki fuskarta babu yabo babu fallasa,
"Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda wannan ya haifar mata da tsananin mamaki domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba,
"Kina mamakine nadiya? Bai kamata kiyi mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da muhimmancinki acikin rayuwata da kuma rayuwar 'yayanmu.."
"Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin fuskarta tana dauke da mamaki,
"Nadiya nasake shawara, naga kamar bai daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu koma yadda muke ada"
"Ban fahimceka ba yaya kabeer.."
"Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu kulawa"
Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta kalleshi,
"Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.."
"Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa wani abu bane sabo,da yawa daga cikin ma'aurata wadanda suka samu matsala irin tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su koma suci gaba da rayuwarsu..."
"Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin yanzu ma da ranar auren wani akaina.."
Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya ya dubeta cikin tsantsar kishi,
"Yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida aurenmu"
"Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da har zan aikata babban sab'o.."
"Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa,
"Sai anjima...."
Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita kadai.
Cikin satittikan da basu wuce 2 zuwa 3 ba Amadi ya kammala komai nashi na tafiya karatun da zai koma lokacin saura sati 2 daurin aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan akan dokin rigimarta bata sauko ba,
Duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata lefe ba idan taje gidanshi.
Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye shiryen komawa makaranta domin hutunsu yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer yaketa yimata akan dole sai sun hada baki sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma gidansa,
Ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin komawa makarantarta take,
Ana saura kwana biyar daurin auren amadi yaje gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar biki,
Adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu, mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa,
"Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba, aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata, nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin Amira.."
Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma zan sake auren..."
"Allah dai yasa ayi cikin nasara"
"Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar kayan tashiga daki.
Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar gaban da take ji nan mama tace mata tayita addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi.
Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance bata da niyyar tashi domin dama tace babu abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan abbansu kabeer za adaura auren domin shine waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da kannenshi suka zo gidan sannan umman sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa, shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu kakeji,
Duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata iyaba daga kan baki har zuwa ja,
Lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson ma tunda dai abune na lokaci guda sannan gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta take,
Wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga daurin aure har andauro,sadakinki dubu 50.."
Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a, shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda yana son yazo yaganta amma bata dauka ba gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima guest palace domin tayashi murna, duk danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka gidan acike yake da baki,
Bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana son taje dinner din amma yasan dakyar idan zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida hankali kan wayar,
"Baby ina kika shigane?"
"Meya faru?"
"Babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne shiru bakiyi picking ba"
"Bana kusa ne"
"To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki saboda da akwai dinner da..."
"Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba, kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama"
Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya.."
"Nifa babu inda zanje.."
Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace yaturo masa da number din mama, babu bata lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa ba,
Kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi yakai kararta wurin mama.
K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya, acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar nan murtuk babu fara'a ko kadan....
*_Ummi Shatu_*👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
_Fatan alkhairi ga Maman Samha, zee gajouh, Maman humy, firdaus, pheey,Maman haneef, Maman Fati,da duk wani masoyin Amadi & Nadiya.._
_Gaisuwa ga aminiya maryam qaumi, u are always in my mind...._
*53*
aishaummi.blogspot.com
*L*okacin da ya kirata suna hanya dan haka taki dagawa, cigaba da kiranta yayi harta dauka amma fa ba don ta so ba,
"Baby shine kika b'ata min bakina da jan bakinki ko?..".
Abinda taji yafada kenan cikin muryarshi mai sanyi domin amadi ko kadan bashida zafi shiyasa muryarsa take sanyi kalau,
"Uhmmm baby.." Taji yasake magana,
"Ban gane abinda kake nufi ba.." Tabashi amsa,
"Kin gane mana, kuma nasan kin gani kawai rabuwa kikayi dani nashiga cikin mutane ahaka.."
"Wai me?" Ta tambayeshi,
"Jan bakinki da kika goga min abakina.."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi magana acikin zuciyarta, "nagoga maka kodai ka goga.."
"Nidai nan gaba idan kin goga min dan Allah ki rinka goge min karki barni na fita ahaka ko kuma ma ki daina shafawa gaba daya..."
"Saboda...?" Ta tambayeshi cike da gajiya da yin maganar,
"Saboda indai muna kusa bakinki zai sha tsotsa.."
"To sai da safe.." Tace dashi tana hararar shi ta cikin wayar kamar yana ganinta,
"Ai ban sallameki ba, wallahi karki kashe idan kika kashe kuma.."
"Kuma me?"
"Nabarki da Allah tunda kinki jin maganata.."
Fasa kashewa wayar tayi ta jingina kanta da jikin kujera tana sauraronsa bawai don tana son hirar ba sai dan babu yadda zatayi,
"Baby kiyi min alfarma guda daya ki yarda gobe nazo naganki"
"Yau ba gashi ka ganni ba..?"
"Ai ganin da nayi miki yau bai isheni ba shiyasa nake son sake ganinki gobe.."
"To gaskiya nidai ba sai kazo ba"
Murmushi yayi ya zauna abakin gadonshi,
"Yanzu baby ko nauyin fadar Kalmar bakiji ba? Cewa fa kikayi basai nazoba, nikuma ina son nazo saboda ina son ganin matata..."
Shiru tayi hakan yasashi sake yin magana, "idan nasake yimiki magana kika rabu dani keda Allah.."
"To wai dan Allah me kakeso ince maka ne? Ni agajiye nake ko gida fa bamu jeba muna hanya.."
"To ai laifinki ne tunda sai da nace ki zauna ki kwana amma kika ki furr kikace ke tafiya zakiyi.."
Shiru tayi batayi magana ba, jin taki yin magana yasashi fadin,
"To yanzu so kike inbarki sai kinje gida?"
"Uhmmm"
"To shikenan zan barki amma da sharadi.."
"Name?" Tafada agajiye domin tagaji da yin maganar ma,
"Gobe zanzo naganki.."
"Naji" tabashi amsa amma acikin zuciyarta cewa take "zaka zo ka dameni dai malam ina zaman zamana"
"To shikenan sai goben, Allah yakaiku gida lafiya"
"Amin.." Tafada tana mai alla alla da taji yakashe wayar amma bai kasheba kun san mutumin naku da d'an karen naci,
"Sai anjima..?" Taji ya tambayeta,
"Uhmmmm"
"To sai anjima, i love you....!"
"Uhmmmm" shine kawai abinda tafada, jinshi tayi yabata wani kiss na musamman ta cikin wayar sannan yakashe,
"Ikon Allah.." Tafada ahankali bayan ta cire wayar daga kunnenta. Basu suka karasa gida ba sai 11:30 lokacin harsu mama sun kwanta,
In banda yunwa babu abinda takeji nan taje tayi alwala tayi salla tana idarwa ta zubo abinci taci, ko kayan jikinta bata cireba ta kwanta saboda tsabar gajiyar da ta kwaso,
Washe gari umman sumaila ta tafi haka suma su A'isha kannen kabeer sun tafi shiyasa yanzu gidan babu kowa sai su yasu,
Fitowar nadiya kenan daga wanka tafara jiyo maganganu atsakar gida, hijabi tasa ta fita nan taga yaya kabeer zaune ra'as yanata faman gursheken kuka agaban mama, mama sai hakuri take bashi akan yadaina wannan kukan,
"Mama dole inyi kuka tunda har narabu da nadiya, ashe nadiya zata iya auren wani mijin baniba? Ashe aure aka daura mata jiya? Ni najawowa kaina amma har yanzu ina son nadiya wallahi, ina kaunarta, dan Allah mama ki taimaka min nadiya tadawo gareni.." Yafada yana kuka kamar ba namiji ba,
"Kayi hakuri kabeeru kadaina kuka, ka dauki kaddara, haka Allah ya zabar muku kasan kowa da iri tasa kaddarar, kayi hakuri kaci gaba da addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.." Mama tafada jikinta asanyaye,
"Mama wallahi rabuwa da nadiya bashine alkhairi ba arayuwata.."
"A'a kabeer ya isa karka yi sab'o kayi hakuri kayi shiru"
Ita dai nadiya tsayawa tayi kawai tana ganin ikon Allah,ganin kabeer ya kura mata ido yana kallonta yasata saurin juyawa takoma daki saboda yanzu ita matar wanice gashi daga wanka tafito, bata san yanda suka kwashe ba tadai jiyo gidan yayi shiru alamun ya tafi, ko tausayinsa bataji ba domin tasan abin da zaisa taji tausayinshi yana gaba lokacin da duniya tayi masa atishawar k'uda.
Shiryawa tayi cikin wata shadda ja mai mutukar tsada in banda maiko babu abinda takeyi, kwalliya ta danyi sama sama tasha turare ta fito tana kokarin daura dan kwali anan mama take sanar da ita wai kabeer ya dauki fadeel da fadeela yatafi dasu sai yamma zai kawosu,
"Damuwarsa.." Tafada acikin ranta amma afili sai ta amsawa mama da to,dakin Abba ta shiga ta gaisheshi, bayan sun gaisa ya dauko mata kudin sadakinta yabata yace gashi nan hakkinta ne, rasa me zatace tayi saboda idan ta karba bata san abinda zatayi dashi ba daga karshe dai tacewa Abba ya ajiye mata awurinshi.
Amadi bai samu zuwa da wuriba saboda yana can gida anata biki domin sai yau bikin yakare baki duk sun tattafi amma yayunshi duk suna nan babu wadda yatafi,
Karfe 2 yasamu ya karasa gidansu nadiya koda ya kirata awaya ma sai da tagama jan ajinta sannan ta dauka duk da yanzu ma taji tarage jin haushinsa acikin zuciyarta, cewa tayi ya shigo lokacin da yace mata yakaraso,
"Dakinki zan shigo?" Yafada cikin zolaya,
"A'a kamanta kan gadona zaka zo.." Tana gama fadin haka ta kashe wayar, dariya yayi yafita daga cikin motarsa ya rufe ya shiga cikin gidan, yau tsakaninshi da mama 'yar surukunta sukayi dan dakyar ya iya gaisheta tareda yimata godiya daga nan yatashi ya shiga falon baki ya zauna, wayarshi ya zaro ya shiga Facebook yana duba sakonnin taya murnar da friends dinshi suka turo masa na auren da yayi, husna ce ta kawo masa ruwa da abinci da lemo,
Yana nan zaune gimbiyar tasa ta shigo sai faman kamshi take budadawa gashi shaddar jikinta ba karamin kyau tayi mata sannan skirt din ta bayyanar da hips dinta sosai kasancewar dinkin riga da skirt ne,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna suka gaisa daga nan tayi shiru bata kara magana ba,
"Baby zo muga kunshin naki..." Yafada yana kallonta,
"Wanne kunshi kuma? Tun jiya bakaga kunshin nawaba sai yau" ta bashi amsa tana latsa wayarta, bai kuma yin magana ba ya rabuda ita yaci gaba da kallonta, ita kuma tanata faman latsa wayarta,
Tashi tayi taje ta zuba masa abincin, faten doya sannan ta tsiyaya masa juice,juyawa tayi zataje ta zauna ya kirata,
"Baby zo"
Kasa yimasa musu tayi saboda ayanda yayi maganar babu alamun wasa, kamar kazar da kwai ya fashewa aciki haka ta karasa tana zuwa yasa kafarshi ya hardota jikinshi,
Akanshi ta fada yasa kafa ya hardeta ta yadda bazata iya tashiba,
"Shine nace kizo naga kunshin naki kika ki zuwa ko? Uhmmm?"
Ita gaba dayama tarasa me zatayi kunya ko haushi? Shiru tayi taki amsa masa, hannayenta duka biyu yakamo yana jujjuyasu cikin nashi yana kallon kunshin, kamar zata saka kuka dan takaici,
Bata gama wannan bacin ranba taji ya zame dan kwalin kanta,
"Wowwww, baby kitsonki yayi kyau, waye yayi miki?" Yafada yana shafa kitson, hancinshi yakai bisa kitson yana shakar kanshin man kitson dake tashi akan nata,
"Baby ashe dai kema kinada gashi, wowwww..!"
Shiru tayi kawai tana jinsa sai tafiyar tsutsa yake yimata akanta wai shi ala dole shafawa yake,
"Baby waye yayi miki kitson?"
Shuru tasake yi,
"Idan har baki amsa ba keda Allah.."
Jin yahadata da Allah yasata amsawa, "Amira ce.."
"Gaskiya dole nabawa Amira tukwici saboda ta fito min da ke sosai, ji kunshinki ma yanda yayi kyau..." Yakarasa maganar yana shafar hannayenta,
Rungumeta yayi gaba daya acikin jikinshi nan kuma tace bata san zance ba tafara yimasa mutsu mutsu,
"Allah idan kika tashi ban yafe ba.."
Komawa tayi ta lafe ajikinsa tana turo baki,
"Ai da sai kace min damuna zaka zo kayi, shiyasa dama ka matsa sai nabarka kazo.."
Ko amsata baiyi ba saboda ya tafi wani uzurin daban a wuyanta,
"Wallahi Ahmad dinnan bashida kunya ashe ana ganinsa haka.." Tafada acikin ranta saboda ita dai arayuwar aurenta na baya bata san wani abu waishi soyayya ba amma shi wannan gashi daga jiya da aka daura musu aure zuwa yau yana nuna mata kauna kamar zai hadiyeta.
Babu yanda ta iya haka taci gaba da zama ajikinsa har yagama fitinarsa, juice ya tsiyaya yasha tareda jan jelar kitsonta, hade fuska tayi ta kalleshi nan suka hada ido fessss taji ya fesa mata juice din bakinshi afuskarta,
"Kai, kai.." Tafada cikin masifa,
"Allah yabaki hakuri.." Yace da ita sannan yafara goge mata da hannunshi.......
_Jinjina ga babbar yaya mom minal..._
_*Ummi Shatu*_👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Gaisuwa mai