Showing 51001 words to 54000 words out of 82977 words
Chapter 18 - MIJINA SIRRINA COMPLET BOOK BY UMMI AISHA.txt
tarin yawa ga sadeeya sunusi umar (antyn hafsat), this page is for you..._
*54*
aishaummi.blogspot.com
*H*ad'e fuska tayi taki koda sake kallonshi ne, ahankali yake share mata fuskarta da tafin hannunshi yana murmushi saboda ganin yanda ta daure fuska tasha kunu,
"Irin wannan shan kunu haka baby, Allah yabaki hakuri bazan sake ba.."
Bata bashi amsaba tayi shiru abinta amma fuskar nan murtuk take, koda ya kammala goge mata fuskar tata kin sakinta tatashi yayi nan ya sake hadata da jikinshi tsamtsam.
Sun dade ahaka har sai da yaji an kira salla sannan ya dago kanta yana kallon fuskarta,
"Baby kinji ana kiran salla.."
Kamar dazu yanzun ma shiru tayi masa har saida yasake maimaitawa,
"Naji"
"To tashi nayi alwala muyi sallah ko..?"
Dama kamar jira take dan haka cikin hanzari ta tashi daga jikinshi ta dauki mayafinta da dan kwalinta tana kokarin daurawa,
"Ina zakije ne?" Ya tambayeta,
"Ciki zan shiga inyi salla" tafada fuska abace,
"Tsaya tare ai zamuyi.."
Dayake akwai bathroom acikin falon nan ya shiga yayi alwala yafito, idonshi akanta fuskar nan tashi sai murmushi ketashi ajikinta,
"Baby nafito shiga kiyi alwalar.." Tana jinshi amma tayi masa shiru nan yasake maimaitawa amma bata kulaba,
Matsawa yayi gabanta yana balle maballin hannun rigarshi,
"Baby..., baki jina ne? Nace kema kije kiyi alwalar sai muyi sallar tare, yau ina son inyi salla da iyalina ne.."
"Banayi.." Tafada batare data kalleshi ba, murmushi yayi ya sunkuya asaitin fuskarta bayan ya dafa gwiwowinshi,
"Baby kenan, wallahi lada zaki samu indai kikayi salla tareda mijinki, ni nasan abinda kika fada ba gaskiya bane dan haka ki tashi.."
"Me zanyi idan natashi? Ba na rigada nafada maka ba, ko ahaka zanyi sallar.."
"A'a....." Yafada tareda mikewa tsaye,
"Idan har ba dagaske kike ba kije keda Allah.."
Sororo tayi tana kallonshi saboda jin abinda yafada,
"Wai komai sai kayi min Allah ya isa? Wannan wanne irin abune?" Ta fada cikin jin haushi,
"Ehh nasan hakanne kadai zaisa ki rinka bin umarni na saboda kin rainani, bakya sona bakya kaunata, tunda bakya sona kuwa nasan bazaki rinka yimin abinda nake so ba.."
Jin yace yabarta da Allah yasata tashi ta shiga toilet, nan ya zauna yana jiran fitowarta amma dama tun lokacin da tayi maganar yasan cewa badagaske takeba,
Kamar zata fashe dan bacin rai haka tafito, shikam murmushi kawai yake, sallah yajasu ta la'asar raka'a hudu, yana yin sallama ta tashi ta koma can gefe taci gaba da addu'o'inta.
Tashi yayi yana gyara agogon hannunshi yana kallonta yanda taci magani ta bata fuska,
"Baby zanje na tafi.., wai ina twins ne banji motsinsu ba ko zunje school ne?"
"Abbansu ne yazo ya daukesu sai anjima zai dawo dasu.."
Kai yagirgiza "ina fata dai bai kalle min fuskar matata ba..?"
Sanin bazata amsa ba yasashi saka takalminshi ya nufeta, mikewa tayi tana gyara mayafinta,
Hannunta taji ya kama, "muje to ki rakani intafi.."
Batace komai ba yajata suka fara tafiya, dakin mama taje ta sanar da ita zai tafi nan mama tafito suka yi sallama, su Amira kuma basa nan sun fita itada husna walimar wasu kawayensu da sukayi saukar alkur'ani mai girma,
Yana ganin mama ta juya daki ya kama hannunta yana kallon fuskarta,
"Muje ki kaini mota sai ki dawo..."
Tafiya sukayi suna zuwa daf da soro sai ga fadeela da fadeel da abbansu yana rikeda hannuwansu, ganin kabeer baisa amadi yasaki nadiya ba dan haka kabeer ya harzuka ya cika dam, su fadeela na son zuwa wurin amadi amma haka ya hanasu furr ya kada kan yaranshi zuwa cikin gida,
Ita kanta nadiya da ba wai son amadi takeba saida abin yayi mata ciwo saboda tasan ya shaku da yaran gashi ko yanzu ma kafin ya fito sai da ya tambayesu,
Ji tayi ya matsa hannunta tareda tsayawa a cikin soron,
"Nima idan kin tashi haifa min yara twins nake so kamar su fadeela.."
Yace da ita bayan ya jinginata da jikin bango ya kama dukkan hannayenta ya rike,
"Ai ba nice mai...."
"Shhhhhhht..." Ya katseta bayan ya dora dan yatsanshi akan lips dinta,
"Insha Allah nima twins zamu haifa.."
Bata kai ga yin magana ba suka jiyo alamun takun tafiyar kabeer, dama amadi yana son ya rama abinda yayi masa yanzu dan haka yayi gaggawar zira hannunshi ta kugunta ya rungumeta, kokarin zamewa tafara yi,
"Baby idan kika gudu wallahi bazan yafe miki ba..." Ya rada mata acikin kunne, daidai lokacin kabeer din ya fito, ganinsu haka suna bawa soyayya hakkinta yasa kishinsa motsawa,
Ko kallonsa amadi baiyi ba,
"Wai dan Allah meyasa kake yimin haka..?" Tace dashi ahankali kamar mai yin rada,
"Saboda ina sonki baby..." Yabata amsa bayan ya kai bakinshi jikin kunnenta,
Karshen bakin ciki kabeer yajishi saboda yasan da biyu suka yi masa haka, sunyi ne domin su kona masa rai kuma gashi sunyi nasara,ganin nadiya da amadi ahaka shine gani mafi muni agareshi,
Cikin hanzari yawuce su ya fita daga soron zuciyarsa tana suya tareda tuno masa da wacece nadiya acikin jerin mata.
Duk da kabeer ya fice baiza amadi ya saketa ba sun dade atsaye acikin soron domin sam baya son tafiya yabarta dan dai babu yanda zaiyi ne,
Har bakin motarshi yajata yabude ya shiga sannan ya kalleta yana rikeda hannunta,
"Baby sai nadawo ko?"
"Uhm" ta amsa masa ciki ciki,murmushi yayi yasaki hannunta bayan ya sumbaceshi,
"Agaida twins dina sai kinjini.."
"Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda juyawa ta nufi cikin gida, ta mirror ya kurawa hips dinta ido yana kallonta har ta shige ji yayi yana kishin wasu mazan su ganta shiyasa ya kuduri niyyar hanata saka mayafi.
Cike da kaunarta yatafi, koda yaje gida ma kasa samun sukuni yayi har saida ya kirata yaji muryarta, tun daga ranar kullum idan ya kirata yace zai zo sai tace a'a, lokacin da ta gama shirin tafiya makaranta ma yace zai zo ya kaita shopping tace ita dai a'a, yace zaizo ya kaita makarantar nanma tace a'a,
Hak'ura yayi ya tura mata 50 thousands ta account dinta yace gashi nan ta siyi duk abinda take bukata dama ya rigada yayi mata registration tun tuni,
Ranar monday da safe ta shirya ta tafi, koda yaushe amadi cikin kiranta yake da yimata text, shi dinma yana can yanata shirye shiryen tafiyar da zaiyi.
***
Cikeda damuwa kabeer yabar kofar gidansu nadiya ya tasamma gidansa,
Lokacin da ya shiga gidan asabe mc na daki itada kawarta Lola suna tattaunawa akan kabeer,
"Ni matsalata dashi yanzu tunda ya rabu da matar nan tasa abubuwansa suka dagule, yanzu maganar da nake yimiki hankalinsa yafara komawa kan yaransa domin dazu dazun nan sai gashi yazo min dasu..."
"Wannan duk mai sauki ne mc, yanzu dai maganin dukan da yake yi miki nake so muyi sannan kuma malam mai dogon zamani yace inyi miki albishir da cewa da zarar ya ketara wannan abun da zaki ajiye akofar daki shikenan kin gama dashi sai yanda kika juyashi..."
"Lola naji dadin wannan batu to amma duk ba wannan ba, kudinsa fa yanzu basa shiga hannuna.."
"Mc kenan ai duk wannan mai saukine da zarar kin fara juyashi shikenan sai yanda kikayi da dukiyarsa.., amma ni menene kasona aciki?"
"Babu bukatar kiyi gaggawa wajen jin kasonki lola domin kinada kaso mai tsoka.... Kinji ma kamar yadawo"
Mikewa lola tayi ta leka window nan kuwa taga kabeer dinne, mayafinta ta saba da jakarta asabe ta rakata ta kofar baya ta fita bayan ta ajiye wani dan siririn bakin abu kamar gashi akofar dakinta......
***
Satin nadiya daya da komawa makaranta amadi yaje amma shi akwai abinda ya kaishi, tunda ya shiga makarantar yayi mata waya tace lecture zata shiga, sai 2 tagama lectures dinta sannan ta nufi office dinsa yana zaune ya dora kafafuwanshi bisa table dinshi, da sallama abakinta ta shiga, ansawa yayi ya dago yana kallonta,
"Baby sai yanzu?"
"Uhmmm"
Murmushi yayi "nima har yanzu kinga ban samu na kammala ba kuma inajin gobe ne tafiyata fa.."
"Allah sarki..." Tafada batare da ta kalleshi ba,
"Meyasa kika yafa mayafi bayan riga da skirt ne ajikinki..?" Ya tambayeta bayan ya kura mata ido, shiru tayi bata amsa ba,
"Ko kina so ne wasu mazan su rinka kalle min halittarki? Dan Allah kidaina saka mayafi.."
"Naji..."
Shine amsar da ta bashi, ta dan jima a office din amma kusan shi kadai yake zancenshi saboda sai yayi magana uku kafin tayi guda daya, daga karshe ta tashi ta tafi hostel, girki tayi masa farar taliya da miyar danyen kifi, sai da tayi wanka ta sake kwalliya ta saka wasu english wears riga da skirt bakake sannan ta dauki abincin ta fita bayan ta saka babban hijabi ash colour....
_*Ummi Shatu*_👌🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_
*55*
aishaummi.blogspot.com
*L*okacin da ta shiga office din nashi baya ciki da alama ya dan fita,
Wuri ta samu ta zauna tana kallon yanayin office din nashi,
Tashi tayi taje ta leka ta window nan dinma babu alamun tahowarshi hakan yasa tasake komawa ta zauna tana jiranshi,
Jin zaman ya isheta ita kadai yasata daukar phone dinta ta kira mama suka gaisa ta hadata da fadeel suka fara hira,
Tana cikin yin wayar amadi ya shigo shima wayar yake yi amma shi da hajiyarshi yake wayar saboda taji yana cewa,
"Hajiya may be fa ni anan ma zan kwana saboda har yanzu ban gama dasu ba wallahi..."
Bata san me hajiyan tace ba tadai ji yace,
"Ehhh Gata yanzu ma muna tare bari na bata ku gaisa.."
Kashe tata wayar tayi shi kuma ya matsa kan kujerar dake kusa da wacce nadiya ke zaune ya zauna tareda kai wayar jikin kunnenta, karba tayi ta makala a kunnenta,
Sake matsawa yayi sosai da kujerar shi kusa da tata dama kuma kujerun suna facing juna, gaba daya kafafuwanshi da gwiwowinshi manne suke da nata, tsareta yayi da ido yana kallonta saboda yadda ta saki jiki sosai suna gaisawa da hajiyarshi,
Mika mishi wayar tayi bayan sunyi sallama da hajiya nan ya hada da hannunta ya saka wayar a kunnenshi, basu wani jima suna magana ba ya cire wayar daga kunnenshi har lokacin yana rike da hannunta,
"Me kika kawo min baby..?" Ya tambayeta yana kallonta,
"Abinci ne.." Ta fada fuskarta babu yabo ba fallasa,
"Me kika dafa min?"
Sauke idonta tayi a kasa bata bashi amsaba haka kuma bata bari sun hada ido ba,
"Ni ai baby nafi son..." Kiss ya kai mata akan lips dinta ya dago yana murmushi,
"Kinci abincin ke?"
Kai ta daga masa, "no ban yarda ba Allah sai dai muci tare.." Yayi magana cikin shagwaba irin tasu ta yan auta,
Shiru kawai tayi tana jinshi irin yanda yake yi mata shagwaba da sauran abubuwa kamar wani karamin yaro,
Sai da ya sake sumbatarta a kumatu sannan ya mike yaje wurinda ta ajiye masa abincin a saman fridge,
"Baby ina zuwa.."
Fita taga yayi, bai jimaba sai gashi ya shigo rikeda babbar dadduma, shimfidata yayi ya sauke abincin ya dora akai sannan yaje ya riko hannunta,
"Tashi muje muci abincin.."
"Nifa na koshi.."
"Allah tare zamuci bazan ci ni daya ba.."
Tashi tayi tabishi har zuwa kan carpet din, zama tayi shima ya zauna yana facing dinta,
"Tun kafin naci abincin naji kamshinshi ya cika min ciki, baby kin iya girki sosai.."
Ita dai bata yi magana ba ta bude abincin ta saka miya ta dauki spoon tafara juyashi,
Kallonta yake yi ganin ta dan tsakuro zata kai bakinta yasashi saurin kamo hannunta tare da sauya akalar spoon din zuwa bakinshi,
"Wai wai... Baby wannan abincin da kifin kan tudu kikayi amma ba da kifin ruwa ba saboda naji dadinsa yayi yawa.."
Duk da bata son tayi dariya sai da yasata yau ta dan dara akaro nafarko da yaga tayi murmushi har hakoranta sun bayyana kuma wai shine silar sata dariyar, ba karamin dadi yaji ba ganin ta dan murmusa,
"Dan kara bani inji.." Yafada yana langab'ar da kai, kamar bata jiba tayi,
"Baby kibani nace... Ko sai nabarki da Allah zaki bani?"
D'iba tayi ta kai bakinshi nan ya debi rabi ya sa mata rabi abaki,
"Yawwa baby ai haka akeyi, kibani inbaki kinji... Uhm babyn amadi..."
Babu yadda ta iya haka taci gaba da diban abincin tana bashi idan tasa mishi abaki sai ya ci rabi ya bata guntun, tasan idan bata bashi ba yanzun nan zai cemata yabarta da Allah ita kuma bata son Allah yayi fushi da ita akan ta sabawa mijinta,
Taliyar bakinta ce ta nemi zubowa saboda yunkurin magana da tayi sakamakon babban dan yatsanta da taji yaja, ta bude baki kenan taliyar da ya sa mata ta taho,bakinshi yakai kan nata,
"Baby rigimammiya idan kika b'ata min darduma ta sai kin wanke min.."
"Ni tashi ma zanyi tunda dama na k'oshi.."
"To ai ni ban koshi ba dan haka ba zaki tashi ba.."
Haka ya hanata tashi taci gaba da bashi abincin yana ci, yaya kabeer ta tuno shi sam bai taba cin abinci tareda ita ba duk lokacin da ta jirashi ma inyazo masifa zai tisata agaba yanayi.
Dan mugunta haka tayita tura mishi abincin yana ci har sai da ya cinyeshi tsaf ai kuwa ba karamin mugun koshi yayiba shi kansa jin cikinsa yake yayi masa nauyi,
"Baby akwai juice a fridge idan zaki sha.."
Tashi tayi ta dauko ta cika cup ta mika mishi,
"Baby wallahi na koshi da yawa.."
"Ai kuwa sai kasha.."
Karba yayi ya dan kurba ya fara bata a baki tasha,
"Washhhh, baby bazan iya tashi ba kamani in tashi.."
Dakyar ta iya dagashi ya mike tsaye, "gaskiya nayi over feeding... Zo kiji"
Matsawa tayi batare da ta kalleshi ba,
"Rufe office din kizo kiji.."
Saida gabanta yafadi saboda bata san nufinshi ba,
"Rufe mana.."
Zuwa tayi ta rufe ta dawo, sunkuyawa yayi,
"Cire hijabinki in goya ki inyi exercise,wallahi na koshi da yawa dakyar nake motsi..."
Tsayawa tayi sororo tana kallonsa saboda jin abinda yace,
"Dan Allah baby cire kizo ki hau..."
"Kayi tsalle kawai.."
"Wallahi baki isaba bayan kece kika dura min abincin.."
"Nidai gaskiya a'a.." Tafada tana daure fuska,
"Wallahi sai kin hau idan kuma baki hau ba kije keda Allah"
Zunbura baki tayi ta kama hijabinta ta cire ta ajiye,
"Ni kayi min tudu ka sunkuya sosai.." Tafada tana turo baki,
Tsugunnawa yayi, "to zoki hau.."
Cikeda bacin rai ta tattare skirt din jikinta ta dale gadon bayanshi, mikewa yayi yafara kai kawo acikin office din, jin taki rikeshi yasashi yin baya kamar zai kada ita babu shiri ta rungumeshi sosai,
"Baby ashe dai kinada tsoro gashi bakida nauyi da yawa... Nauyinki nawa ne?"
"Nima ban saniba.."
"To baki fi 50 ba gaskiya, jifa yanda kike shafal dake duk kibar nan taki..."
Ita dai bata kara maganaba tana kwance a bayanshi tana shakar kamshin turaren black man dake tashi daga jikinsa,
Ya dade yana zagaya cikin office din da ita abayanshi sannan ya direta,
"Baby sauko haka nagaji...."
Juyawa yayi yana kallonta, kayan jikinta sunyi mutukar kamata sannan sunyi mata kyau kasancewar roba ne,
Kan kujerarshi yaje ya zauna ita kuma ta dauki hijabinta ta saka, drewar ya bude ya dauko chewing gum ya dauki daya ya mika mata sauran,
"Ashe ma inada chewing gum namanta.."
Kwanukanta ta tattara ta nade mishi dardumarshi ta ajiye,
"Bari natafi, idan ka tafi shikenan Allah ya kiyaye hanya.."
Kallonta yayi yana murmushi,
"Wai kina nufin sallamar kenan? Lallai, to shikenan sai anjima...."
Fita tayi shima yabi bayanta ya rufe office dinshi yayi wani wurin.
Bata sake jin duriyarshi ba sai bayan sallar isha wurin karfe 8 yakirata wai tazo yana jiranta,
"Wai dama bai tafiba?" Ta tambayi kanta, hijabinta kawai tasa ta fita, akusa da library ta sameshi yana tsaye ajikin motarshi,
"Baby zuwa nayi na daukeki muje ki tayani kwana, anan garin zan kwana yau saboda ban gama abinda nazo yi ba sai gobe da safe.."
Saida ta daure fuska ta hade rai sannan tace,
"Gaskiya kayi hakuri ni babu inda zan bika"
"Haba baby, dan Allah kizo muje.."
"Kasan Allah babu inda zanje.."
"Amma dai baby idan kika barni naje na kwana ni daya baki yimin adalci ba, iya yaune fa kurum zaki rakani.."
"Zancen kake so, nidai ko nan da gate ban binka.."
Bai sake magana ba taga ya ciro wayarshi daga cikin mota ashe mama zai kira kawai sai jinshi tayi yana cewa,
"Lafiya lau mama dama nadiya ce nace ta rakani unguwa shine tace sai kin amince.. Gata"
Mika mata wayar yayi yana murmushi, nan ta karba,
"Mama..."
"Ke nadiya haka akeyi dan mijinki yace ki rakashi wani wuri shine zakice sai na amince ba yafini iko dake ba yanzu, maza kije ki rakashi karki sake cewa sai an tambayeni..."
"To mama..."
Mika mishi wayar tayi tana kallonshi cikin bacin rai, haushinta daya ko wanka fa batayi ba kayan dazu ne ma ajikinta,
Ko kulashi bata yiba ta zagaya daya side din ta bude ta shiga fuskarta adaure,
Murmushi yayi ya shiga ya zauna yana kallonta tareda yiwa motar key......[truncated by WhatsApp]
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_
_Kina ina? Nana fiddausi (Feedohm), wannan k'warya k'waryar shafin nakine ke kadai yar d'akina....._
*56*
aishaummi.blogspot.com
*J*uyawa yayi ya kalleta kafin yafara driving,
"Baby... Ya naga kinbi kin bata rai kodai bakya son bina ne?"
Rabuwa tayi dashi saboda jin tambayar rainin hankalin da yayi mata,
"Uhmmm baby..?"
"Kafi kowa sanin idan ina son binka ko bana so.." Ta bashi amsa cikin fada,
"Wowwww....! Dadina dake masifa, baby gaskiya kemafa masifaffiya ce, ohhh shiyasa akace ba ahada biyu dole sai kasamu daya mai fada daya marar fada..."
"Naji ni masifaffiya ce" tafada a k'ule,
"A'a baby ni bance ba..." Ya fada harda daga hannuwa,
Reverse yayi ya fita daga cikin makarantar nan kuma yafara tunanin wurin zuwa domin babu inda yasani acikin wudil bai taba shiga cikin garin ba iyakacinsa makaranta sai ko bakin titi,
"Baby babu wani guest house da kika sani anan...?"
Juyawa tayi ta kalleshi cikeda masifa shikuma harga Allah zuciyarshi daya yayi maganar bada wata manufa ba,
"Ohhhhhh ga yar iska ko? Dole ka tambayeni guest house tunda ni cikakkiyar yar bariki ce..."
Packing yayi agefen titi ya kunna fitila yana kallonta, fuskar nan tata sam babu fara'a ta daureta tamau,
Sai da ya kamo hannunta ta kwace ya sake kamowa ta kwace ya kuma kamowa nan ma ta fisge sai kawai yajata zuwa jikinshi,
"Baby wallahi ba nufina kenan ba amma tunda kinji haushi dan Allah kiyi hakuri, ni wallahi ban taba kawowa komai araina dangane dake ba wannan tambayar ma bada wata manufa nayiba amma kiyi hakuri..." Yafada cikin cool voice dinshi,
Yanda yafara magana har yagama bata tanka mishi ba,
"Kin hakura..?"
Yasake tambayarta yana kallon fuskarta,
"Idan fa baki hakura ba zamu zauna ananne inyita baki hakuri har sai kince kin hakura sannan zamuje mu nemi wurin kwana..."
"Nahakura.."
"Yawwa nagode to, dan Allah kidaina fushi dani baby,