Showing 1 words to 3000 words out of 69262 words

Chapter 1 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

222

*KUN MAKARO*

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 1:

*Ina farawa dasunan Allah,mai rahama mai jin qan bayin shi, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad sallahu alaihi wa sallam, bayan lokaci mai tsaho yau inshaa Allah zan kawo maku sabon labari, wanda nake fatan ya sauya rayuwar mutane da dama, ta fuska kala2, labari ne mai qunshe da darrusa mabayyana, ina fatan zaku bude zuqatan ku masu albarka, kamar yanda kuka saba, domin fahimta da daukan darussan dake ciki.*

Aeeshaa ke zaune a kan kujerar zaman mutum daya, dauke da wuqa da kwano, tare da kubewa tana yankawa, tana yi tana kallon lokaci, aiki take kamar wata inji ba bu hutu,babu abinda ke tsaida ita wannan aiki sai sallah.

Cikin sauri ta tashi hannun ta riqe da roba da plate ɗin da ta yanka kub'ewa ta koma kitchen ta dauki turmi da tab'arya, ta saba wannan kubewar da ta yanka, tana gamawa ta je ta zuba a tukunyar miyar data ji nama da kifi, ta kada ta zuba kanwa kadan ta sab'a murfin tukunyar a Saman tukunyar, sannan ta koma kan tuwon semo da ta tuqa tin minti biyar da ya wuce, tuqa shi ta sake yi ya na wani danqo danqo alamar ya dahu sosai sai ta buɗe locker ta dakko leda da mazubi ta fara zubawa tana murde ledar tana sawa a inda ya dace, da sauri ta juya kan miyar da ta ji ta fara alamar zubewa, ta kashe gas din, ta qarasa rufe tukunyar, sannan ta qarasa kwashe tuwon ta.

Tana kammalawa ta diba fridge taga zobon data haɗa ya d'au sanyi, murmushi ne ya kwace mata, da sauri ta koma ta wanke dik abinda ya dace, ta fara jera abincin akan dinning, sai da ta kammala komai, ta  juya da sauri dan wucewa d'akin ta ta yi wanka tare da yin shirin islamiyya sai sauri take zuba wa dan kar ta makara kamar yanda ta yi da safe a zuwa makarantar boko,Safar ta take sanya wa a qafa ta jiyo kiran Umman su, zuciyar ta ce ta buga da qarfi tsabar tsoron abinda zai je ya zo, cikin sanyin murya ta saddaqar wa ta furta,

"Na'am Umma gani nan zuwa"

Cikin azama ta nufi dakin Umman nasu, inda ta tsaya a bakin qofa, ta yi sallama tare da qwanqwasa qofar, shiru kafin daga bisani ta amsa mata cikin tsawa,

"Dan ubanki sai yaushe zaki riqe akan ki inna kira ki kina shigowa? Sai ki tsaya dan gulma kina wani jira sai na baki izinin shiga,kina abu sai kace wata uwar mata, da ban son ganin ki zan kira ki ne?"

Shiga Aeeshaa tayi, ta samu gefe ta tsaya tace,

"Umma kiyi hakuri,gani,"

"Yauwa nace kin gama abincin ne?"

"Eh na gama,na hada komai kan dinning, yanzu shirin islamiyya zan, kar na makara kinsan yau banje boko ba saboda makara da na yi da safe, na kammala komai har dare na yi abincin ma tinda naga tuwo ne"

"Waya saka ki yi har dare? Ni nace ki dafa har dare ko iyayi? Ko kin fini sanin me ya fi dacewa da ayi ne?"

"Umma dan Allah kiyi hakuri bana son ranki na baci, bari inna dawo islamiyya kome kk so zan dafa, dan Allah ko zan fashin boko bana son na yi na fashin islamiyya,"

"Alhuda huda kenan sarkin karatu, wuce ki tafi,kina dawowa kizo akwai wankin da zaki haɗa dana qannen ki kimin, kinga sai kisa uniform d'inki ma dika ki wanke ko?"

"Eh hakan ma yayi Umma na tafi sai na dawo,"

"To"

Wata ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi jin ta samu nasara akan Umman ta ta yau ba zata yi rashin islamiyya ba, da sauri ta qarasa shiryawa ta fito, dan ko wanka yau bata samu yi ba gudun makara, in ta dawo tayi.

"Aunty Aeeshaa muma mun shirya,"

"To Ameena maza muje kar mu amshi bulalan latti ko? Ina Abdul hakeem?"

"Gani meye?"

"Kai dai Allah ya shirye ka baka da kunya ko kadan har yanzu,girma kk amma kana shiga daji,"

"An shiga din, ni na tafi kar ku taho ku tsaya surutu,"

"Aunty Abdul baida kunya, amma kar ki fada masa nace haka,"

Murmushi Aeeshaa tayi, ta shafa kan qaramar qanwar ta, sannann suka fita daga gate din gidan nasu, sannan tace.

"Kar ki damu, ba zan fada masa ba,ai dama baida kunya ko baki faɗa ba, muyi sauri,kinga ga yara can sai gudu suke yi suma,"

Qara sauri suka yi, dankar su makara, suna zuwa suka shige ajujuwan su, Abdul Hakeem ajin su ɗaya da Aeeshaa,Ameena na ajin dake qasa danasu, domin itace qaramar su.

Karatu ake amma hankalin ta yau sam baya jikin ta,yana can wajen tinanin rayuwar gidan su, gaba ɗaya basu tausaya mata, basu san tayi abu a gode mata ba dik da qoqarin da take yi, tana bauta masu kamar bata son jikin ta,amma ko a jikin su, burin su kawai ta masu aiki, su amfana da ita kuma su zage ta, sai kace ba Umman tasu ce ta haife ta ba, tinawa da mahaifin ta da ya rasu ne yasa wata kwalla me zafi ta saukar mata,to ko dai ba Umman ce mahaifiyar ta ba da gaske? Tinda mahaifin ta ya rasu tin tana shekara bakwai, sabida cancer, .......

"Aeeshaa tinanin me kk haka har da kuka?"

A firgice ta miqe tsaye ta fara rera karatun da ta haddace jiya,a zaton ta an tashe ta ne dan ta yi karatu, nan da nan kuwa ajin ya dau dariya,banda Abdul,wanda ya bata rai, ya juya ido, ya kalli waje.

Shiru tayi,dan ta kula da abinda ta yi, nan ta sunkunyar da kan ta, tana son ta ji me malamar tasu ta faɗa da farko.

"Aeeshaa tambayar ki nake me ya same ki?"

"Kaiii...kaiinaaa ..ke ciwoo"

"Wayyoo sannu maza jeki gida,tinda ba nisa, sai kisha magani, ki zauna, gobe kin bada haddar ki,"

Da sauri ta fara karatun ta,dan bata son abinda zai sa ace ta koma gida ba a tashi ba aiki na can na jiran ta, bata huta da aikin da ta gama tiqa ba tin safe.

Kyale ta malamar tayi, ta kammala, sannan suka dora sabon karatu.

Qarfe 5:30pm suke tashi,dan haka suna tashi gida ta nufa,ita da qannen ta.

Suna shiga ta ga kan dinning kaca2,ga qawayen Umman ta a parlour suna ta hira, ana shewa, an barbaza kayan sayarwa a qasa,ga cups nan da plates an ci snacks, sai ciniki sike ma Umman nata,suna yi suna hirar batsa, lura da dawowar yaran yasa suka nutsu,

"Ah Aeeshaan Umman ta,kun dawo kenan, yanzu nake cin wani daddad'an abinci, Umman ki tace ke kk dafa, ina matuqar mamakin ki Aeesha, dika dika shekarar ki sha shida amma kin iya abinci kala2, kamar wata babba,"

Wani irin daɗi ne ya kama Aeeshaa,yau a rayuwar ta gaba ɗaya an samu wandda ta yabe ta, ji ta yi kamar ta kama Aunty Safnaa ta rungume dan murna, ta buɗe baki zata yi magana kenan Umman ta ta amshe.

"Wannan me shegen son zaman d'akin? In ba dan nayi qoqari na tsaya tsayin daka ba da ko ruwan zafi bazata iya dafawa ba,sai shegen son karatu, kamar wata babbar mace, kullum ina nuna mata hanyar kasuwancin nan tana kauda kai, bata san ko kayi karatu ba ba wani aiki zaka samu ba, maza ma wahala suke sha bare ke mace da zaki qare a dakin miji,"

Aeesha bata ji daɗin kalaman Umman ta ba amma cikin murmushi tace,

"Umma me za a dafa? Ko kawai naje na dora abinda ya dace?"

"Ki je ki yi dik abinda kk ga ya dace, ga wankin nan kar ki manta"

"To Ummana"

miqewa ta yi ta shiga ciki ta sauya kayan jikin ta, sannan ta koma Office ɗin nata wato kitchen, taliya ta dafa da miya, dan ta samu sauqi, da sauri cikin kazar2 ta wuce d'akin Umman nata ta haɗa kayan wankin su, ta koma ta ɗauki na qannen nata ta fita qofar baya ta kama wanki,ba ita ta gama ba sai ana kiran magrib.

Bayan tayi sallar magrib, tayi azkar,tayi karatun ta na qur'ani sannan ta yi isha'i, bayan ta idar da ibadun ta kamar yanda ta saba sai ta miqe  tsaye ta hau nade abun sallahr ta,daga nan ta leqa wajen umman ta ta tambaye ta ko akwai abinda zata yi mata?

"Ba abinda za ki min yanzu, ki tabbatar dai kin gyara kan dinning kan ki kwanta,"

"To Ummana sai fa safe,"

"Allah ya tashe mu lfy,"

Tana mamakin Umman ta, wai ace magana mai daɗi bazata haɗa su ba, komai a cikin faɗa yake da kushewa da kyara da tsawa,ga qannen ta nan suma sun dauka musamman Abdul,gwanda2 Ameena, wataqila itan ma dan yarinya ce,ba zata wuce shekara 5 ba shi yasa.

D'aga komai ta yi ta kai kitchen, ta kashe fitulu ta kulle masu qofa sannan ta tofa ayatul kursiyyu sannan ta yi dakin ta.

Tana Assignment din ta bacci ya dauke ta ko kammalawa bata yi ba tsabar gajiya.

********************

"Wai makaranta nan da can ki taka ki je sai na kai ki na dawo dake, ga su Ameena dake nesa, suma sai na kai su na aje su, ke ko tausaya min ba ki yi,"

Hawaye ne ya gangaro ma Aeeshaa, tai saurin saka hannu ta share, ita dik wahalhalun da take ba'a gani sai kai ta makarantar da ake shine zai zama abin magana, lallai bin iyaye yana da wahala, Allah ya bata ikon cin wannan jarabawa, yanzu in ta amsa ta tace ta barta tana zuwa ta jama kan ta aiki, taje ta dawo ta tiqi aiki, ga shi dama ta fita a gajiye, a boko sam ba ta da wani qoqari, saboda aiki ya mata yawa, ga uban fashi datake dokawa.

"Kiyi hakuri Ummana"

"Mtss da an magana kiyi hakuri, kiyi hakuri, ya zan ai dole na hakura"

Su na isa gida, kowa ya fita ya rufe qofa, a tsaye a baƙin qofar shiga parlourn gidan suka tadda shi riqe da Cup a hannin shi, shi da Umma ne su kai dariya a lokaci d'aya, dan kuwa ita ta san da dawowar shi.

Abdul da Ameenatu ne suka yarda jakunkunan su bakin su sake zuqatan su cike da murna suka nufe shi a guje, banda Aeeshaa da ta kasa koda motsawa.

Binta yake da wani irin kallon da ba mai iya fassara shi, dan shi kan shi bai san meke cikin zuciyar shi ba game da wannan halitta da ya gani a gaban shi........

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 2:

Kallon ta yake yi tare da lumshe idanun sa akan fuskar ta, cikin muryar shi mai amo mai daɗin sauraro ya furta,

"Ke wato kin girma shine ba zaki zo ba ko?"

Cike da jin kunya ta kalle shi, ta isa gare shi, hannu ya kai zai taɓa ta ta ɗan ja da baya cikin dabara,

"Barka da zuwa Yayanmu, saukar yaushe? Shine ko ka sanar dani,na maka kyakkyawar tarba da girkina me tsinka kunne ko?"

Murmushi ya yi tare da fad'in,

"Iyyeeee ! har yaushe kk girma? Yaushe2 ma na daina daukan ki muna zuwa gidan Hajja dake? Yaushe2 ne na daina....."

Cike da shagwab'a ta furta,

"Yayaaa plsss ya isa haka, kana ganin wannan mara kunyar har ya fara dariya,"

Ummah ce ta kalle su cike da sha'awar su ta ce,

"Dan Allah mu je ciki, na gaji da tsaiwa, dan na kula in aka barku nan sai ku kwana hira,"

Hanya suka bama Umman nasu ta shige, sannan suma suka shiga suna ci gaba da hira tare da murnar dawowar yayan nasu, wanda yake dan Yayan umman su ne uwa ɗaya uba ɗaya, amma anan gidan ya tashi, hasalima shi ke kiran Umman nasu da suna Umma har sika tashi da hakan suma.

Kulle dakin ta tayi, ta sauya kayan ta, har zata fita, ta tsaya, gani nai ta koma ta dakko mayafi mara girma sosai, ta yafa a jikin ta, sannan ta fita, dan ta tina cewar yanzu ba su kaɗai bane akwai wanda ba muharramin ta ba a gidan, malaman Islamiyyar su sun yi masu bayani game da wanene muharrami da wanda ba muharrami ba, Muharrami shi ne duk namiji ko macen da ta haramta ga mutum ya aura,misali kamar Yaya uwa ɗaya uba ɗaya,ko qanin baba uwa ɗaya uba ɗaya,ko Uwa ko uba...wanda ba muharrami ba ya haɗa da total stranger,Wanda baka sani ba sam ba wata alaqa ta jini, da wanda yake cousin ɗin ka ne, misali dan yayar baban ka, dan qanin Babar ka ko yar Babar ka, da sauran su.

Kamar yanda ta saba, girki ta je ta fara dora wa sannan ta koma suka ci gaba da hirar su,yana basu labarin karatun nashi daya je na koyon tuqa jirgin sama, Abdul dik sha'awar tuqa jirgi ta gama kashe shi, tambaya kan tambaya, ita kuwa Aeeshaa abun bai wani bata sha'awa wai tuqa jirgi, ita taso ace aikin asibiti yayi,ko dan sanda ko soja, dan su take son namiji ya zama yana yi, amma ba wani abu wai shi tuqa jirgi ba, gani ya yi gaba ɗaya hankalin ta baya tare da su dan haka sai ya kalle ta ya ce,

"Qanwata ya dai naji kin b'ata shiru?"

Dan yaqe haqora ta yi kaɗan ta ce,

"Ammm ba komai, dama ina tinanin kamar abincin nan yayi bari na je na duba,"

"Yes dear pls go, yunwa nake ji sosai,"

Dariya sukai dika kafin ta tashi, ya bi bayan ta da kallo, yana mamakin saurin girman da tayi, kamar ba yar shekara sha shida ba,komai na jikin ta sai dai a ce masha'Allah kawai, ko da ta shiga ta ga abinci ya yi zuba wa kowa ta yi aka zauna ana ci ana hirar yaushe gamo.

Bayan sun kammala cin abinci har Umman nasu, sai ya yi masu tayin raka shi zuwa gidan Hajja dan acan gidan iyayen shi yake.

"Yehhhhh Yah Sabeer zani, na dad'e ban je ba dama"

Cikin zumud'i Aeeshaa ta ce

"Nima zani,"

Ummah ce ta banka mata harara sannan ta ce,

"Ina zaki? Ke qaramar yarinya ce? Ki zauna ga dakina nan jiya ko sharar yamma baki min ba, ga gidan nan kaca2 in muka je dake wa zai gyara d'akin?"

Ameena ce ta zauna a jikin Umman ta na kallon kyakkyawar fuskar Umman nasu ta ce

"Au Umma kema zaki je ne?"

Cikin fara'a da shafa kuncin yarinyar ta bata amsa da,

"Zani mana Ameena, nida gidan mu? Ku kuka je balle ni?"

Aeeshaa na jin haka sai kawai ta sauke kan ta qasa ta miqe ta bar wajen dan tana buqatar zama ita ɗaya ta koka abinda ke ran ta, in aka mata abu in bata koka ba wani irin baqin ciki ke tokare mata zuciya,

"Allah ya kai ku lfy ya dawo da ku lafiya,ina gaida tsohuwa me ran qarfe, sai kun dawo,"

Ta na fad'in haka ta bar parlourn ta wuce d'akin ta,

Sabeer bai ji daɗin hakan ba ya so su tafi dika, kwata2 baya son abinda Umman nasu take ma Aeeshaa da sunan wai kunyar 'yar fari,wannan ai shirme ne da kuma rashin wayewa, dik da suna da alaqa da fulani ai ita ba haka Maman ta ke mata ba, tinda ko shawara da ita maman ta keyi, amma ita taqi jan ta ta d'iyar a jiki, tashi yayi jiki ba laka, dan ya sauya kayan jikin shi su wuce.

Tana wanke2 ya same ta, ya jingina da qofar yana kallon yanda ta juya baya take sharbar majina saboda kukan da take,dan kuwa ta shiga d'akin ta ta ga zaman ba zai amfana mata komai ba gwanda ta fito ta wanke kwanukan da ta san dole ita za ta yi aikin su to barin su su bushe ɗin na menene? Ba tare da ta san sanda ya zo ba ta ji muryar Yayan nata na fad'in,

"Kar ki damu, inshaa Allahu zan kai ki da kaina, ki daina kuka, in mun je da yawama bazaki wani ji daɗin zuwan ba, ki bari sanda Umma bataje ba sai na kaiki, ki sake sosai abinki kin ji yar qanwata?"

Juyowa ta yi tare da qaqalo murmushin dole ta ce masa,

"Na gode yaya, amma ni bansan me yasa Umma bata son jerawa da ni mu je gidan Hajja ba, rabona ma da gidan har na manta, ko ina za a fita ba ta zuwa dani, kullum sai dai a barni a gida kamar me gadi, innai magana sai tace wa za a bari a gidan in mun fita dika,"

Kuka ne ya kwace mata ta juya da sauri ta ci gaba da wanke2n ta.

Cikin nutsuwa yake takawa zuwa gare ta, jin shi ta yi daf da ita,a hankali ya furta,

"Kar ki na saka damuwa a ran ki kina qaramar yarinyar ki, zaki jawa kan ki wani ciwon,komai dake faruwa dake yana da dalili, Umma kunyar 'yar fari kawai take nuna maki, ba wani abu bayan nan, a bayan idon ki ba ki ji yanda take yabon ki ba ne,"

Da sauri ta juya wani farin ciki ya bayyana a fuskar ta,

"Yah Sabeer da gaske tana yabona a bayan idona?"

Ya buɗe baki zai bata amsar qaryar da ya shimfida kenan yaji kira daga waje, ana qoqarin shigowa,

"Sabeer in bazaka kaimu ba mu mu tafi ai munsan hanya, ka samu waje ka yi zaman ka daga bari ka sauya kaya,"

"Umma kiyi hakuri nayi wanka ne, yanzu na shigo ina ma wannan 'yar qauyen sallama"

"To mu je,ke kuma ki tabbata kan mu dawo kin yi komai da ya dace,kar na dawo naga wajen nan kaca2"

"Umma ku dawo lfy, ina gaida Baba General, kice ya baki abun daɗi ki kawo min,"

"Eh tinda akai na rashin kunya ta qare sai na je ina faɗa masa saqon ki, keni bana ciki da rashin ta ido,"

Ɗan dariya suka hau yi mata, dan gaba ɗaya ita kamar ba wayayyiya ba, kunyar ɗan fari tin yaushe aka daina?

Cikin kuzari Aeeshaa ta yi qoqarin kammala komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login