Showing 24001 words to 27000 words out of 69262 words
Chapter 9 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
ta, ashe Yah Khaleefa tantiri ne haka?
Kiran sallah take taji a kunnen ta, ba halin tashi,har ta gaji da kukan ma, sai sauke ajiyar zuciya take.
Tana ji tana gani aka gama sallah ta kasa tashi, daga baya ma bacci ne mai nauyi ya dauke ta, ga gajiyar biki, ga ta Khaleefa.
8:00am ya farka, saboda alarm da ya saka a wayar shi, kullum in 8 tayi sai ya buga saboda koda ya makara ya tada shi, a hanzarce ya tashi yayi wanka ya shirya, zai fita ya kalle ta,sai ya ji wani irin abu ya tsarga masa a jikin shi, na tsantsar gamsuwa da yayi da ita a daren jiyan, kad'a kai yayi tare da shafar cinyar ta.
"Zamu je dake, kina da abinda nake nema a wajen mace sosai,"
Farkawa ta yi, suna ido hudu ta zabura tana kare qirjin ta, ido tsilli2 take kallon shi cike da hawaye, tana kada masa kai.
"Calm down babes, ba yanzu ba, ki jinyata min kan ki ni ai yanzu naga waje, sai na dawo,"
Ficewa yayi ba tare da ya ji me zata ce ba, kamar mutumin kirki, manyan kaya ya saka, wanda suka karbi cikakken halittar jikin shi mai kyau, ka rantse dan gidan limamin makka ne, a nutse ya durqusa gaban ta, dan bai taba zaton zata zo da sassafen nan ba.
"Hajja ke ce da asussuban nan?"
Baki ta bude daga baya ta wara hannayen ta alamar daquwa.
"Amshi naka, nace amshi naka, maras kunya, yanzun ne asuba, ka duba agogon hannun ka kuwa? Tara na safiya yanzu, ga abinci can na sa an dafo maku, ina Aeeshaan take?"
Cikin alamar wai shi ya ji kunya, ya shafa kan shi, ya nuna mata hanyar dakin, murmushi Hajja ta yi, da dikkan alamu, an yi nasarar gamuwa, kuma yanda fuskar shi take dauke da annashuwa ya samu abinda ake nema a wajen kowacca diya mace ta kai gidan auren ta.
Miqewa ta yi cikin kuzari irin nata,dan ita sam badan fatar ta data fara nuna alamar ta kwan biyu ba ba za a ce mata tsohuwa ba.
Har ta kusan isa dakin ya yi wani sufa sai gashi a qofar dakin, hannu ya daga mata, ya bude qofar ya shige da gudu ya tattara disc din dake qasan d'akin, ya tura qasan gadon, ya daga dik wani abun iskancin shi, sannan ya fice.
Hajja dai qara murmusawa ake, jikar ta ta kai budurci gidan aure lfy, lallai Khadeeja an gaishe ta, ta yi qoqari, dik wani haushin ta da Hajja ke ji sai taji ya kau.
Aeeshaa dai na bakin gado, tana zare ido, kan ta ya daure, meye hakan ke nufi? Ko wani abun ya gani zai gudu ya barta, kuka ta fara, ta ja jiki da kyar zata tashi, da hanzari hajja ta tare ta, tana jera mata sannu.
Zubewa ta yi a jikin Hajja tana kuka kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, sai kuka take tana gwama numfashi.
Tsam hajja ta rungume ta tana matsar kwalla itama, tare da zagin Khaleefa a ran ta, na rashin tausayin marainiyar Allah da bai ba, da dikkan alama ta mai gardama ya hada mata da duka, bai la'akari da sabuntar ta ba.
"Sannu Aeeshaa, Allah ya shiryi Khaleefa ya yi hankali, shi ko dan lallashin nan babu, ji fuskar ki kamar an gasa biredi ɗan ɗari bakwai, ji yanda ta tashi tai luhu2, wannan dan iskan yaron da bai fita ba sai na ci mai uba, Allah ya saka maki, muje na gasa maki jiki, jikina ya bani ba mutunci ne da shi ba sai kin wahala shi yasa na taho da kaina, tinda ba wanda zan aiko, Hussai ta koma ita da Hamdiyya, Balqis ba zata iya ba tayi nauyi, zata zauna har sai ta haihu, muje kar na cika ki da surutu"
"Hahhhaajjjaa kkkooo salllaaahh bann baa faa"
Sai ta fashe da kuka.
"Yi hakuri muje na taya ki ki gyara sai ki wanka kiyi sallar, Allah saka maki mugu azzalimi kawai,"
Ruwan zafi tin tana kuka in ta shiga,har sai da ta ji kamar kar ta fita ma, wankan tsarki tayi kamar yanda aka koyar da su a islamiyya, sannan ta fito.
Yana da matuqar mahimmanci malaman manyan aji na islamiyya suna koyar da mata harda mazan ma yanda ake gudanar da rayuwar aure a musulunce, in ma ba a koya masu anan ba yahudawa da nasara zasu koya masu, ta haka ake samun lalatattun yara, kuma namiji dik girman shi yayi aure bai san farillan daya kamata ya hau kan shi ba balle sunnoni, ayi aure namiji ya hau mace kamar awaki, ba nafila ba addu'a ba komai, saboda islamiyya ba a koya masa ba, iyayen shi ba su koya masa ba, wai ai mace kawai ake koyawa, to wasu matan ma ba a koya masu komai, akwai wanda wallahi iyayen su ne suke koyar da su komai na zaman aure kafin auren, har yanda zasu yi magana da tafiya gaban matan su, amma wasu wai kunya, gaskiya a daina kunya a inda bai kamata ba.
Kaya ta tarar Hajja ta debo mata marasa nauyi, doguwar riga ce da bra da pant sai dankwalin kayan da hijab.
"Bazan sallah anan ba Hajja muje can,"
Da kyar Hajja ta gane me ta fada, ta yi tsananin tausaya ma Aeeshaa, roqon ta Allah ya sa khaleefa ya dawo; sai ta masa dukan tsiya (kar dai ki ji ma kan ki ciwo yar tsohuwa).
Bayan tayi sallah, ta tsaya yin azkar, tana yi tana kuka, ita nata daren farkon a haka yazo mata, gaba kuma bata san wacce irin rayuwa za tai ba da Khaleefa.
Hajja ce ta leqo ta gan ta, zama tayi a bakin gadon, ta yi ta mata nasiha.
"Ba a yi ma miji musu, sai dai in ya umarce ki da aikata sabon Allah, wannan kuwa ko kashe ki za ai kar ki biye masa, amma in ba sabon Allah bane ba a yiwa miji musu, yanzu dibi fuskar ki? Wannan cin zali da mi yayi kama?"
Hajja sai da ta tabbatar Aeeshaa ta ci abinci ta qoshi ta yi bacci ta huta sosai, sannan sukai azahar ta wuce gida.
Tana wucewa Aeeshaa ta je dakin Khaleefa ta kwashe kayan baccin ta tsaf da komai nata da aka aje mata acan, ko wanne me neman maganan ne a cikin yayun nata ya aje mata kaya a dakin shi oho.
Tinani tayi, ya kamata ta sake dafa masa wani abu tinda akwai kayan abinci, wanda aka kawo ya jima aje, ga shi bata ko san lokacin da zai dawo ba.
'Ohhh ni Aeeshaa nan kuma Allah ya kawo ni, Allah ka dafa min kar ka barni d kaina ba zan iya ba'
Sai da tayi la'asar ta fara girki mai rai da lafiya ta gama, ta sake qalqale wajen, dan ba wani datti bane akwai, tana zaune taji ana buga gidan, hijab din ta babba ta zuba taje ta bude.
Wani dattijo ta gani, ya na ganin ta ya durqusa a qasa, yana kwasar gaisuwa, ai da sauri itama ta duqa, bata san ko wane ba, ba a mata tarbiyyar babba ya gaida ta ba har da durquso.
"Baba ban san kai wane ba, amma koma waye kai dan Allah ka tashi, ka daina duqa min"
Dan miqewa yayi kadan, ya tsaya a gefe, kamar akwai wanda yake jira.
Drivern gidan Hajja ne ya leqo suka gaisa da Aeeshaa sannan ya mata bayanin mai gadin su kenan,
"Ok Allah sarki, dazu munyi maganar kuwa da Hajja, bismillah baba muje daga ciki, sai dai mai gidan baya nan, ka shiga ka zauna ka huta zan kawo maka abinci, kafin ya dawo, sai ku yi magana,"
"Allah ya miki albarka hajiya na gode, suna na Yahuza, Allah ya bani ikon yin abinda ya kawo ni,"
"Ameen Baba dan Allah kar kana kirana hajiya, Aeeshaa sunana,"
Driver sallama ya musu, a kullum shi dai yana yaba tarbiyya irin ta Aeeshaa.
Baba Yahuza d'akin data nuna masa ya shige ya aje yar ledar kayan shi, yana ta kallon wajen, yana godewa Allah, an sha gwagwarmayar rayuwa, yanzu ga gida harda katifa makekiya, ga wata kujera da ledar daki, ga bandaki ai shi kam sai godiya.
Abinci ta kawo masa da ruwa, ya ci ya kwanta baccin gajiya.
Daf d magrib Khaleefa ya dawo, ya maka horn kamar shi kadai ne mai mota a unguwar.
Baba Yahuza ne ya fita d sauri, dan budewa, Aeeshaa kuwa hantar cikin ta ce ta kada, da sauri ta dora qaton hijabin ta akan dinkin atampar data saka, tana zaune tana zare ido tare da cin farcan hannun ta, ko dame ya dawo yanzu kuma Sai Allah.
"Waye kai?
"Ranka shi dade nine sabon mai gadi da Hajja Aeeshaa ta aiko na zauna anan, dan kula da gidan,"
"Dan sa ido dai, ba gadi ba, zo nan,"
Matsawa yayi da mamaki a fuskar shi, kuɗi Khaleefa ya zaro masu yawa, ya miqa ma Baba Yahuza, ya ce yaje ya sallame shi, kar kuma ya koma gidan Hajja ya ja masa surutu, dan ko an dawo da shi ba zai zauna ba, bai son sa ido.
Cike da mamaki da jin takaici yaje ya dau kayan shi ya bar gidan.
Bude qofa yayi, ya fice yana ta tsaki, ya kwashe kayan shi ya shige ciki.
Lokacin da ya shiga ta tada sallah a d'akin ta, sai kwala mata kira yake yi kamar a wata unguwar take ba a gidan ba.
Daidai ta yi sallama tana qoqarin fita suka hadu, ranshi bace ya ke mata wani irin mugun kallon..............
*Khaleefa wu......rka daban yasin in baka tuba ba🙊🙊*
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 11
"Me kk yi ina ta kiran ki ba zaki zo ba, ba za kima amsa ba na san kin ji ni, raini ne ya shiga tsakanin mu?"
"Yah Khaleefa Allah kar ya nuna min ranar da zan raina ka, sallah nake ban ji ba, kayi hakuri,"
Tsaki ya ja sannan ya qarewa dakin nata kallo, lallai da gaske wadannan tsoffin ke son suyi zaman aure, meye babu a dakin nan? Ga wani qamshi dake tashi na musamman, kallon ta yayi yaga yanda take saka hannu a hijab tana kare qirjin ta kar su daga ya gani, cikin daure fuska ya ce,
"Meye hakan? Meye amfanin rufe qirjin ki da hannu bayan kin dora hijab? To bari kiji, daga yau sai yau, kar na sake ko da wasa na gan ki tare da hijab, in ba fita zaki yi ba ko sallah, kina jina ko,"
Tabbas ya shirya cin zalin ta ne wannan, cikin matse kwallar data taru mata ta daga masa kai alamar taji,
"Baki da baki ko?"
"Ina da shi, naji, inshaa Allahu zan kiyaye.....ga abincin ka can na shirya maka,"
Banza yayi da ita yana kallon ta yana jiran ta fara bin umarnin shi tin yanzu, gane hakan ne yasa ta sauri cire hijab din, tana kame2n me zatayi next dan ta bar gaban shi.
Da sauri ta sakada ta gefen shi, tayi hanyar dinning, abincin ta bude ta fara zuba masa, dambun cuscus ne data dafa fari tas amma ta saka masa kayan lambu da albasa mai yawa, sai tayi miyar dankalin turawa da kayan ciki, sannan ta hada masa fruit salad mai mugun daɗi, ya ji ayaba, da madara, ga lemon abarba da lemon zaqi da ginger data masa, Khaleefa yaso yayi miskilanci yaqi ci,amma inaaaaa wane shi, abincin kwararru bai isa kauda masa kai ba.
Zama yayi yana wani babbata rai, ya fara cin abincin, wani irin gardi ne yake ji na ratsa shi, dan masifa sai dai yayi fada, kallon ta yayi, yana muzurai,
"Ina ruwa? Ko ahaka zanci ina shaqewa?"
"Yi hakuri ga lemo dana haɗa maka nan,"
Tsiyaya masa ta fara ya wani daki table din,
"Ruwa na ce maki ba wannan ba, kina gani yana shaqe ni ba zaki yi sauri ba?"
A kidime ta wuce dakko masa ruwa tana hawaye, meye abun fada, ga cuscus nan na ta shigewa, amma dan zalinci sai ya zabure ta haka.
Tana dawowa da ruwa taga jug empty, sai muzurai yake,
"Dakko ruwa ne kawai zai sa ki dad'e har mutum ya galabaita kisa shi shan abinda bai niyya ba, ke fa kina sani hayaniya, tinda na haɗu dake na zama me yawan surutu,ki kiyaye abinda zai sani magana, in ba haka ba ranki zai mummunan ba......"
Wata arniyar gyaza ya sake, alamar qoshi ya tabbatar masa, ita dai bata gama gane komai ba, abincin ba dadi ne? Bai qoshi ba haka ya tura? Kwata2 bata gane komai ba, fatan ta dai ya daina wannan daukan zafin, tinda ba abinda ta masa sai alkhairi.
Tana nan tsaye tana tinani ya wuce ta, wanka ya shiga ya fito, isha'i ake ta kira a unguwar tasu, abinci ta dauka da niyyar kai wa Baba Yahuza, ta saka hijabin ta qato har qasa abinci na qasan hijabin, tana fitowa daga kitchen ta gan shi ya dora qafa ɗaya kan ɗaya da remote a hannu, ya sauya wannan tasha ta rawa ya kai wannan ta kida, durqusawa ta yi a gefen shi sannan tace,
"Yah zan kai ma Baba mai gadi abinci,"
"Na kore shi,"
Zabura ta yi baya kaɗan,
"Yes na kore shi, ke zaki na buden gate ki rufe, ko da wasa kar naji magana a gida, in an tambaye ki kice tafiya yayi ko na aike shi,"
Hawaye ne ya zubo mata ta gyada kai, tausaya ma Baba Yahuza ta yi, bawan Allah dik inda ya fito a wahale yake, da yunwa, yanzu ya samu wajen da zai huta an kore shi,
"Wai ke kuka baya maki wahala ne? Zo nan aje abincin ki cire hijab din ki zo, sai ki yi ta kukan ina kalla"
Da hanzari ta hau goge idon ta,
"Bazan sake kuka ba inshaa Allahu, bari na je na ajiye wannan kayi hakuri,"
"Keee ! kar ki sake ban hakuri, ke wace iriyar yarinya ce wai? Aje hijab nace ki zo nan,"
Bakin ta na rawa da dikkan sassan jikin ta ta aje ta je gaban shi ta durqusa, hannu ya miqa mata ta dad'e kan ta kama, sai da ya kafe ta da ido kamar zai kashe ta sannan ta kama, janta yayi da qarfi ta faɗa jikin shi, kamar mai jira kuwa haka ya wurga bakin shi a nata.
Hawaye ne kawai ke zuba mata, sai da Khaleefa ya gama romancing din ta, ya biya buqata da jikin ta, sannan ya wurga mata tarkacen rigar ta da dik wani abu daya cire a jikin ta,
"Bar nan,"
A guje ta kwashe wasu na fad'uwa a hanya ta shige d'akin ta tana kuka, kuka take kamar idon ta zai fito,
"Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, Allahumma ajirni fee musibati wa aklifni khairan minha, Allah ka qaramin juriya da hakuri na cinye jarabawar ka, Allah na gode maka daka zabe ni a cikin bayin ka ka min jarabawa daidai yanda zan ɗauka, baka dora ma rai abinda bazata iya ba, Allah ka san zan iya ɗauka ne ya sa ka min jarabawar nan, Allah ka bani ikon cinye wa ya kareem,"
Fadin wadannan golden kalamai ba qaramin tasiri sukai ba a ran ta, nan da nan ta nemi quncin ran ta ta rasa, illa zafi da qasan ta ke mata, Khaleefa hannu ya sa mata dik da ya san bata gama warkewa ba, a hankali ta je bandaki ta kunna ruwan zafi ta zauna ciki,tasbihi kawai take a cikin ran ta ga Allah, dan bata da abin yi da ya wuce hakan, nutsuwa ce sosai ke shigar ta.
Waman yatawakkal alallahi fa huwa hasbuh
Wanka ta yi ta fita ta d'aura alwala ta yi sallah sannan ta kwanta, bayan ta yi addu'ar bacci ta shafa, hannu ga miqa ta kashe fitila ta ja bargo, gajiyar zuciya da jiki ta sa bacci mai daɗi daukan ta, mafarkai ta dinga yi masu daɗi da faranta rai, ta jima tana baccin nan, ta ji ana shafa ta, bude ido tayi a hankali saboda nauyin da sukai mata, Khaleefa ne kunnen shi toshe da earpies,sai qaramar waya a kunnen shi, magana yake alamar waya yake yi, kuma magana yake ta batsa, qirjin ta kawai yake matsawa kamar ya samu fura zai dama.
Da hanzari ta janye jikin ta ta kunna fitila, hannun shi ɗaya ta gani a gaban shi, earpies a kunnen shi.
'Ahhh me wannan yake yi haka? Tabdi jam aiko za a yi ta,ba zata hana shi jikin ta ba amma ba zai yu yana waya da wata 'yar iskar ba ita kuma yana son ya sauke buqayar shi akan ta'
Bata rai ta yi sosai ta kai qarshen gado, da hannu yake mata nuni ta dawo, kuma ya mata alamar baya son surutu, maqe kafada tai, wani azababben kallo ya watsa mata, jikin ta nan da nan ya dau bari, amma data biye masa gwanda ta gudu waje in yaso ya dake ta in ya gama iskancin nashi.
Waje ta kwasa da gudu, a qasan dinning ta zauna, ta hade jikin ta sosai, Khaleefa ya duba dika dakunan bata ciki, dan haka anan parlour a tsaye ya gama tijarar shi ya shige dakin shi, dik ya bata mata qasan waje.
Toshe bakin ta tayi tana ta kuka, ya ilahi shi bunsuru ne? Baya gajiya da fidda ruwan jikin shi ne? Ina iyayen shi suke har ya yi wannan lalacewar under their roof? Ina Baba General da Hajja suke jikan su ya yi wannan lalacewar su na gida ɗaya?a yanda yake abubuwan sa kamar bunsuru watarana Watarana zai kashe kan shi in bai natsu ba.
A hankali ta rarrafa ta koma dakin ta ta rufe da key, bacci ta so komawa amma inaaa ba zai samu ba da dikkan alamu, alwala ta dauro ta yi ta nawafil har bacci ya kama ta, sannan ta sallame ta haye gado ta yi baccin.
*******************
Haka rayuwar Khaleefa da Aeeshaa take ta tafiya, sati biyu kenan a dangi qalilan ne suka je