Showing 9001 words to 12000 words out of 69262 words
Chapter 4 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
saka wancan ya cire, a haka ya biya ma kan shi buqata ya kwanta yana hutawa, kafin daga bisani ya dauke komai ya shiga wanka ya dawo ya kwanta, nan da nan bacci ya dauke shi.
Innalillahi wa innailaihirrajiun, wannan shine kalmar da zamu iya yi ma wasu daga cikin matasan wannan zamanin,matasa sun maida biyawa kan su buqata shine mafitar rashin auren su,wanda Allah ba haka yace ba, Annabi Muhammad ba haka yace ba,bin umarnin su kuma wahala yake ma matasa, kuma anjima in wani yace masu basu son Allah da manzon sa ayi ta bala'i dasu, sunace an kafurta su, shin idan mutum ya na son abu ba umarnin abin yake bi ba? Umarnin Allah ne zai maka/maki wahala? Allah ya kyauta ya tsarkake mana zuqatan mu.
Abdul ne ya je kiran Sabeer domin su karya ga mamakin shi sai ya ga dakin shi ba komai, da sauri ya koma ya sanar da umman tasu, aikuwa wayar ta ta dauka ta kira shi,cikin sa'a ya dauka, cikin fad'an ta daya zamar mata jiki ta bashi umarnin zuwa yanzu, amsa mata yayi da yana zuwa dama yanzu hakan ma ya na hanya ne,nan take ta ce ta bashi minti 3 ta na son ganin shi, kashe wayar tayi ranta a bace, ko zai tafi a qalla she deserves an explanation.
Kusan minti biyar sannan ya shigo, yara dik suka gaida shi,Aeeshaa ma gaida shi tayi, ta kafe shi fa ido, sai ta ga ya rame mata idon shi kamar wanda bai yi bacci ba, shi ɗin ma ita yake kallo, zuciyar shi har wani sauri take wajen bugawa, gaskiya Baba General bai kyauta masa ba, tinda ko ra'ayin yarinyar ba a ji ba ma, wannan shine isa da mallaka.
"Kai ku tashi ku shiga ciki, zan magana da yayan ku,"
Tashi suka yi har Aeeshaa, sannan ya gyara zaman shi,itama shi take kallo.
"Yanzu abinda kai ka kyauta kenan?"
"Ban kyauta ba Ummana, shi yasa na dawo yau dan na maki bayanin dalili na,"
"Wanne dalili kk dashi daya wuce ka nuna min ka isa da kan ka?"
"Umma ba haka bane, maganar da aka yi jiya ne naga bai kamata naci gaba da zama da Aeeshaa cikin rufi ɗaya ba,bayan an bama wani ita, wahala kawai zan yi ta sha, zuciyata zata ci gaba da son ta, bayan kuma na san ba zata zama mallakina ba, na so ace muna da zaɓi akan abokan rayuwar mu,da na koyar da iya yanda za ta so ni, ta qaunace ni har zuwa lokacin da zata kammala makaranta a aura mana junan mu, sai kuma wannan lamarin ya ɓullo kai, Ummah ya zan yi?"
Umma ta tausaya masa matuqa har ta kai ta kasa magana, daga qarshe dai dole ta amince da dalilin shi, sannan ta roqe shi daya dinga zuwa suna gaisawa, koda lokaci zuwa lokaci ne, anan ya karya,ya wuce wajen neman aiki, dan shi yafi son yayi fafutuka da kan shi,baya son a nema masa aiki a gida, hakan na ɗaya daga abinda ke burge Ummah da shi ya na sanya wa tana tuna wa da Baban su Aeeshaa,Sabeer tun tasowar shi ya na san zama independent, baya so ya ɗora wa kowa nauyin sa, duk wata qaramar sana'a yi yake a lokacin ya na secondary school, in zai dawo gida zai shigo wa da qannen shi wani abu, ya na wahala ya zauna ba wata sana'a, har lokacin tafiyar shi jami'a ya gabato a sannan ne ya kama duk wata sana'a ya hakura sai da ya tafi can makarantar ne ya ci gaba da displaying shaddodi da lesuna a da atampopi a status duk mai so sai ya masa magana, a haka ya dinga tara yan kud'ad'e har ya na musu aike, ko in zai zo hutu ya zo masu da tsaraba mai yawa, sannan be cika tambayar kuɗi ba sai abinda ya zama dole ya nema.
*********************
Kwanaki na tafiya, watanni na kamawa suna qarewa, shekaru sun ja, Aeeshaa ta kammala makarantar ta ta secondary, jarabawar su ta fito ta samu 5 credit, fad'a a wajen umma ba a magana, yaran qawayen ta dik daga mai 8 credit sai mai 9 dan me Aeeshaan za ta samo 5 credit da me suka fi ta.
"Dik karatun naki anan ya qare? Dik alhuda hudancin naki iya 5 credit kk tsaya?"
"Umma su fa biya sukai aka masu, ni kuwa da kaina na zauna na rubuta jarabawar, ba satar amsa, Umma murna ya kamata ki tayani a wannan ranar ba faɗa ba, dan Allah i want to be happy just for today,"
"Ba za a barki ki yi happy ɗin ba, na bata kuɗi na da lokacina ina kai ki makaranta da dakko ki a banza, sai ki fadan wace makaranta zaki ci gaba yanzu? In ba aure ba,"
Cikin zazzaro manyan idon ta ta maimaita kalmar aure, tana kada kai, bata da burin yin aure yanzu.
"Kwarai aure zamu maki,dan kuwa Baba General ya tsaida maki da miji tun tuni dama na bari ne sai sanda ki ka gama makaranta na sanar da ke, gobe ki shirya kije can, ki masu hutu sannan ku san juna ke da mijin naki,"
Aeeshaa zama tayi a wajen hawaye na sauka a kuncin ta, tana karanto addu'ar neman samun sauqi akan wannan hali da take ciki,
"Aure za a min ni Aeeshaa,nawa nake?".......
*Goma kk yannan, aure dai ba fashi🙊*
*KUN MAKARO*
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 5:
Washegari Aeeshaa ta haɗa kayan ta cikin umarnin Ummah, gaba ɗaya abun ya haɗe mata ya zama biyu,na farko dai akwai murnar zuwa taga 'yan Uwanta, bayan tsahon lokaci, na biyu kuma akwai taraddadin me zata je ta tarar a gidan sannan waye mijin da zata aura, tinani tai tayi ta na ci gaba da haɗa kayan ta,shin ko wannan dalilin ne ya hana Umman ta barin ta zuwa gidan kakannin nata, to ko Yah Sabeer ne mijin da aka zaba mata? Tinda ya bar xaman gidan sai dai yazo ya tafi, wataqila ma bai son ta shiyasa ya rage yi mata fara'a an qaqaba masa ita,komawa ta yi ta zauna tare da aje hijabin da take ninkewa ta dafe kan ta, bata san me zata ji ba ma, murna yau zata sarara, ko kuma tinanin mijin da za a bata, Ameena ce ta shigo, wadda a yanzu ta kai shekara takwas, iyayin ta da surutu sai abinda ya qaru.
"Yah Aeeshaa, ya naga baki qarasa haɗa kayan ba Umma ta gama komai, kin san in ta shigo bata ga kin....."
Ai Ameena bata gama magana ba ta tattare sauran kayan ba ninki ta tura a akwatin ta,ta saka hijabin ta, ta fara jan akwatin, dariya Ameena ta dinga mata,dan in ta ga yayar ta ta na tsoron Umman su abin dariya da mamaki yake bata, sai kace wasu mage da bera, sam ba sa zama inuwa ɗaya lafiya ba tare da ummah ta yi kamar ta cinye Aeeshaa danya ba.
A bakin qofa sukai kacibus,
"Ai na zaci sai na shigo na d'akko maki kayan naki ne mai sarauta,"
"A'a gani nan na gama ma,"
Tafiya suka fara yi, cikin ran Umman nata tana hango damuwar da d'iyar ta ta zata shiga in ta ji waye mijin nata.
A bakin gate d'in gidan nasu ta aje Aeeshaan, ta ce ta gaida mata mutan gidan ta wuce kai kaya inda aka kira ta aka ce ana da buqata a can gidan qawayen ta, dan ta saro wasu sabbin kayan zafafa.
Mai gadi ne ya yi saurin amsar mata akwatin ta ya shiga da shi bangaren Hajja, da sallama da tsalle da murna ta shiga, ba kowa a parlour, dan haka ta qarasa bakin qofar dakin Hajja tana ta doka sallama.
"Wace tsohuwar ce haka, take mana sallama kamar bata san hanyar shiga ba?"
"Tsohuwa ce mai kama dake, kuma mai suna irin naki,"
Idanun Hajja har kwalla suka kawo dan ganin jikar ta ta, hali irin na Khadeeja sai a bar shi kawai,ace ka na da jika ku na gari ɗaya ganin ta ya gagare ka, Banda ma Allah ya bata yarinya mai ladabi da biyayya da wata ce ai ko yanka ta za ai sai ta ratse daga makaranta ta je inda aka hana ta, yanzu dai ai ga Aeeshan ta tako qafa ta shigo gidan taga wanda zai fidda ta ba da izinin ta ba.
Rungume junan su suka yi, Aeeshaa kuka ta sa, tana shagwaba.
"Hajja kowa baya so na, unguwannin mu a kusa ba wai gari ne ba ɗaya ba, amma ba ku taɓa tinanin ku ce Umma ta barni na zo ba, kullum daga makaranta sai gida,"
Shafa bayan ta Hajja tayi, cikin lallashi, sannan suka koma d'akin, zaunar da ita tayi a bakin gado, suna fuskantar junan su,
"Aeeshaa, ba wai rashin so bane, dik a jikokina banda wadda nake qauna a zuciya ta kamar ki, amma dole na kauda kai akan ra'ayin mahaifiyar ki, tana da wauta ta nuna kunyar 'yar fari, ba irin abinda bamuyi mata ba dan ta daina wannan halin, amma abin ya gagara, bana son ya zamana tana maki tarbiyyar da take ganin ita ce ta dace dake, ni kuma na shiga na ce ba haka ba, ita ke da iko dake sama dani, beside tana boye ki ne saboda yanda zamani ya lalace, a cikin gida ma sai a lalata maka yaro ko yarinya balle kin samu qafar yawo, baki nan baki can, ko kuma ace kin tara qawaye kala2, wani lokacin ina matiqar jin haushin ta akan yanda take maki, amma wani lokacin sai na ji daɗin tsayawar da tai akan ku, kuma bamu son ki san waye mijin da zaki aura dan kar ki zama distracted, karatun ki nada mahimmanci."
"Na fahimta yanzu, amma Hajja zumunci ma nada mahimmanci kuma ya na da lada mai tarin yawa,ni na riga da na sani tun ba yau ba Ummana bata son jerawa dani mu zo gidan nan, amma a qalla ko sau ɗaya in zata zo da sai muzo tare, amma sai tace in naga zan zo sai in ba da ita za a je ba, ni kuma tsoron fita nake ni ɗaya, ta saba min kaini makaranta da dakkoni,"
"Kiyi hakuri tabbas bamu kyauta maki ba ta wani bangaren, haka Allah ya qaddaro, yanzu tashi muje mijina ya na hanya na dora masa abinci mai daɗi,"
Dariya Aeeshaa tayi, tana rufe baki, ita kalmar mijina ya kusa dawowa ya bata mamaki, da kunya, Hajja ta tsufa fa, yaran ta ma ba wai na zamanin yanzu bane balle ita.
"Hajja ke kam baki tsufa, ai yanzu yanda kk tsufa masu aiki ne ya kamata suna yi maki hidima tunda ko da na shigo na ga gilmawar mutum biyu mata anan sashen,"
"Waaaa niii Allah bai tauye ni ba daga halitta har lafiya na zauna sai mai aiki sun ma mijina hidima? Ba dani ba gad'a a kushewa,in banda halin yaran zamani zama waje ɗaya ba qiba zan ta tarawa ba kitse yamin yawa na fara ciwon qafa da hawan jini? Yanzu da na ke ma mijina abinda ya dace baki ganni kamar ban kai shekaru na ba? Ki zauna ki koyi dikkan tattali da dawainiyar miji a wajena 'yannan,"
Dariya Aeeshaa ta yi sosai, ita dai gaskiya kunya Hajja ke bata, aiki suka shiga yi na abinci, da abin sha, na gargajiya,masu qara lafiya a jiki, Aeeshaa gwanace wajen girki, amma sai taga kamar bata iya komai ba da ta ga yanda Hajja ke girki.
Sunyi kwad'on zogale da cabbage, wanda ya ji tumatur da albasa ga qulin da yasha kayan qamshi wajen daka, harda garlic a ciki, Sugar da maggi ta ga Hajja ta kwadanta da shi, sanda ta dandana, ji ta yi tana ganin wasu stars na gilma wa a idanun ta tsabar daɗi, ruwan da suka dafa zogalen Hajja ta matse lemo, da lemon tsami, ta saka sugar, kadan da flavor,ta juya sosai ta saka a jug, sannan suka mishi brabuskon alkama, da miyar kubewa danya, yasha man shanu, ga tantakwashi, yawun Aeeshaa ya gama tsinkewa, ita dai mamakin yanda Hajja ke komai a nitse take yi ta na yi tana mata bayani, sannan tana nuna mata nutsuwa a girki ba sauri ba garaje yana taimakawa wajen samar da abinci mai dadi, sannan mace ta kula ba zabga maggi ko gishiri bane abinci, barin abinci ya dahu da kyau yana daga cikin abinda ke dad'ad'a abinci.
Bayan sun gama,Hajja ta fara diban abincin Aeeshaa na taya ta, suka aje a kan tabarmar da aka shimfida a Saman carpet a kewaye dinning table, can nesa da table din kaɗan, Aeeshaa na ganin ikon Allah yanda tsohuwa ke kula da miji kamar basu tsufa ba, ko dan ita mahaifin ta ya rasu bata saba ganin yanda ake ma miji hidima bane oho?
Wanka Hajja ta umarce ta da ta shiga tayi, yau ita zata tari angon nasu, suna dariya da raha ta tafi dakin da Hajja ta nuna mata, zuciyar ta wasai, ji take kamar ta fito daga kurkuku, ga dai shi aiki tayi, amma cikin nishadi, ba kamar a gida ba tanayi ba godi bare na gode ga hantara, dik da aikin iyaye ne amma godiya da sanya albarka ma wani abune babba.
Wanka ta yi, ta saka kayan ta, ita din ba wani kwalliya ta iya ba, dan bata da wannan lokacin, ta fesa turarukan ta ta fito, dakin Hajja ta nufa,ta mata sallama ta nemi izinin shiga, Hajja ta amsa mata sannan ta shiga.
Baki ta sake dan mamaki, kwalliya ce mai ban sha'awa a jikin Hajja, atampa ce riga da zani, wanda aka ma rigar dinki mai kyau, ga sarqa kalar kayan, Hajja ta shafa kwalli da powder, ga mai ta shafa a bakin ta, sai tayi kyau kamar wadda akai wa hadadden kwalliya, kallon Aeeshaa Hajja tayi ta daure fuska.
"Me ne ne haka nake gani? Na daiji qamshi, amma ina kwalliya? Ke budurwar qauye ce?"
"Hajja me zan yi kuma?"
Jan hannun ta Hajja tayi, ta fara shafa mata kwalli, sannan ta shafa mata powder, ta shafa mata janbaki kalar rigar ta, mai pink, sama2, nan da nan sai ga Aeeshaa ta fito tauraruwa, girar ta ta taje mata ta kwantar dan tana da cikar gira.
"Wayyooo Hajja nice kuwa? Wayyooo Ina Ameena tazo taga yanda nayi kyau,"
"Ya dai kamata na dage na koya maki kwalliya mai kyau,domin wannan mijin naki miskili kwalliya ce zata ja ra'ayin shi gare ki."
Gaban ta ne yayi mummunan faduwa, dan tina me ye abu na biyu daya kawo ta gidan, tana son ta tambayi hajja waye mijin tana jin nauyi, kar a ce tayi rashin kunya.
"To yanzu kafin General ya dawo kije ku gaisa da Iyayen naki, kina jin dawowar shi dai kije ki tare shi, zai mmakin ganin ki sosai,kuma zaiji daɗi,"
Cike da fara'a ta fita, ta nufi bangaren su Sabeer, Hassana ta tarar a zaune a kujera, tana karatun hausa novel na *AURI SAKI*wanda marubuciyar HAERMEEBRAEH ta rubuta,hankalin ta dik ya tattare akan abinda take yi, qamshi ne ya daki hancin ta mai daɗi,a hankali ta daga kan ta, ido huɗu suka yi da Aeeshaa, gani tayi kamar ta san ta, dan gaba daya Aeeshaa ta sauya, kamar ba ita ba, ta qara girma ga kyau.
"Adda Hassana ina wuni?"
Aeeshaa ta kashe ta da daddadar muryar ta da kuma murmushin ta mai kyau, tare da zama kusa da ita tana murnar ganin ta.
"Aeeshaa?"
D'aga kai Aeeshaa tayi tana dariya, fuskar Hassana ba yabo ba fallasa, wani irin kishi ne ya tokare ta, ba yanda za ai Khaleefa ya ga Aeeshaa bai amince da had'in ba,
"Lafiya qlou, ya su Aunty? Ina Ameena sarkin surutu da Abdul?"
"Suna lfy, ina Ummee da Yah sabeer?"
"Ummee na ciki, amma Sabeer ban san ina yaron nan ya ke ba, dan yakan dawo daga wajen aiki 2 ne, amma yanzu kinga 4 ta wuce ma baya nan,"
"Bari naje na gaida Ummee, nayi kewar ku Adda, Adda baku nema na, amma ni kullum kuna raina,"
'Ki gode Allah ma na sakko daga qiyayyar ki dake raina, na fawwalawa Allah lamarina ya zaban wani mijin mai albarka da ko haqorina ba zaki gani ba yarinya,'
A fili kuwa tace,
"Allah sarki kiyi hakuri, kin san iyayen namu akwai su da kulle, tinda na gama makaranta ba a bari na fita niima, innace zani wajen ku sai ace ai Umman ku na zuwa kullum ba sai naje ba, amma kiyi hakuri bamu kyauta ba kam,"
"Ba komai ya wuce, ai gani na zo ba ranar tafiya,"
Wani abu mai daci Hassana ta had'iya, me yarinyar nan ke nufi, wato ta dawo sai anyi auren su? Ko dai ta san da maganar auren magana take dan ta qunsa mata haushi, kauda tinanin tai, dan kar ta bata rawar ta da tsalle.
"Ahhh ahhh ahhhh wa nake gani kamar Hajja qarama?"
Da sauri Aeeshaa taje gaban ta ta durqusa, tana dariya,
"Ummeen mu nice, ina yini ummee,"
"Lafiya qlou Hajja qarama, ya kuma mutan gida? Ina taya ki murnar kammala secondaryn ki, sai aure kuma yanzu,"
Sunkuyar da kan ta tayi, ta miqe sum2 ta fice, cike da jin kunya.
Motar shi ce ta shigo, daf da zata shiga bangaren Maman khaleefa dan gaida ta, juyawa tai ta koma baya da gudu cike da murna dan tarbon shi, bayan ya fito ne ta rufe bakin ta kadan, dan ba shi take tsammanin gani ba, da kallo ya bita, yana mamakin wace wannan kamar ta san shi ta zo tarbar shi, kamannin ta ne sukai saurin bayyana mashi wace ce, hade fuska yaso yi, amma ya kasa, cikin ladabi da girmama babban yayan su a dika familyn ta durqusa kadan tana gaida shi,
"Yah khaleefa ina Wuni?"
Dauke kai ya yi, ya yi tsaki ya shige cikin gidan,ya barta tsugunne a wajen.
Wata iriyar kunya ce ta kama ta da muzanta, ba a taba wulaqanta ta irin haka ba, masu aikin gidan na kallo, da tasan ba