Showing 15001 words to 18000 words out of 69262 words

Chapter 6 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1045

naushe shi da guiwar hannun ta ba sai da ta ji ya saki 'yar qara ya dafe ciki,da sauri ta kai hannun ta kan nashi, tana taba cikin tare da furta,

"Wayyoo Allah na, dan Allah kayi hakuri, Yah khaleefa ban sani bane, dan Allah kar ka dake ni, na tuba, ba zan sake tafiya ina waige ba,"

Sake baki ya yi yana kallon cikin idon ta, wanda ya ciko da hawaye,ya yi wani irin kyau ya na kyalli,wani iri yake ji a jikin sa sakamakon hannun ta mai laushi data dora akan nashi, ba dole hannu yayi laushi ba tana shafa HAMIBRAH SKIN OIL

Labban ta yabi da kallo, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tai saurin janyewa tare da dirircewa, bai da niyyar motsawa ko bata amsa, da gudu ta nufi cikin gida, Hassana da  komai ya faru akan idon ta kasancewar tana qasan bishiyar mangwaro dake gidan ce ta saki tsaki, ta juyar da kan ta ta sake qanqame wayar ta, a ganin ta da gayya ma sukai hakan dan ranta ya baci, Khaleefa ji yayi kamar an zare masa laka.

"Allah ka gaggauto da ranar bikin nan kusa".............

*Kuna cikin 'Yan Ameen ko kuwa? ni dai nace.........🙊😆*

*KUN MAKARO*

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 7:

Har Khaleefah ya tashi daga wajen aikin shi bai dena shafa inda ta riqe mashi ba kan ya fita,har wannan lokacin hancin shi yana jiyo qamshin ta, ga wani irin laushin da fatar ta ke da shi,lumshe ido yayi, ya shafa kan shi da baya rabo da aski, karkata kan motar shi yayi zuwa Hotel ɗin daya saba zuwa, yaci abinci kamar kullum, Rebecca itace yarinyar dake dauke masa hankali in yazo wajen, bai taɓa taya ta ba saboda ganin ita arniya ce shi musulmi, dan haka tana gilamawa ya ɗauke kan shi, bai sake kai kallon shi inda take ba, lemo ya ɗauka ya kai bakin shi,ya fara kurba a hankali ya ji hannu  na shafa qirjin shi, hannu ne mai dauke da zara2n farcen da yasha fentin ja, ga laushi da qamshi, lumshe idon shi ya yi, ya daga kan shi, bata bata lokaci ba wajen kai ma lallausan lips din shi kiss,kamar wanda yake jira kuwa sai ya ja ta jikin shi, dik da cewar bai san wace ce ba salon ta ya yi masa kuma qamshin ta ya tafi da hankalin shi, sai da ta zauna saman cinyar shi ya gane fuskar ta da kyau, yarinyar da ya ke ji ana kira da Rebecca ce ashe ,iya ɗin babbar karuwa ce a wajen, sai wanda ya isa take bi, amma son kasancewa da Khaleefa ne kawai ya ja tsayawar ta gare shi, ba dan haka ba bashi da kud'in kashewa akan ta.

Ta yi matuqar kwadaituwa da shi, tin ranar da ya fara zuwa ta gan shi, amma jan aji da girman kai, ya hana ta ta kai kan ta, a zaton ta ta kai haduwar da da kan shi zai bita, sai gashi ajin da yake da shi ya dame nata, kuma hakan ya qara mata wutar son kasancewa da shi, yau kuwa ganin yanayin shigar shi, da zaman da yayi, yana cikin shauqi, koma shauqin wace ce today is her day.

Barin wajen suka yi cikin gaggawa, suka hau sama, dan sabawa Allah, dik wani tinanin arniya da musulmi ya kauce wa Khaleefa, ba zai bari wannan damar ta wuce shi ba.

Khaleefa yau dai ko gida bai koma ba, abinda bai taba yi ba kenan, yanda Rebecca ta ririta shi, ta kai shi gajimare,ko gida bai tina ba sai da komai ya lafa, yana fara maganar tafiya ta kwantar da shi saman qirjin ta tana zuqar sigari da dayan hannun, tana shafa kan shi da ɗayan cikin sigar lallashi, nan da nan bacci ya ɗauke shi, wani shu'umin murmushi ne ya kwace mata, cikin hausar ta da sai ka rantse itan diyar sarkin hausawa ce na arewa dika,ta furta,

'Lallai wannan irin gasasshen nama har gida? Ai ni da kai sai sanda na gama zuqe ka tasss zan aje ka na qara gaba, kayi min, kuma kai din gwarzo ne'

Glass cup dake gefen ta ta janyo ta kurbi abinda ke ciki, ta sake zuqan sigarin hannun ta, tana gamawa ta ja masu abin rufa.

Khaleefa bai tashi farkawa ba, sai wajen 11:22am, cikin sauri a gaggauce da kuma kidima yake magana,

"Subhanallahi, ....anan na kwana?..... Wayyo Baba General yau sai ya kusan kashe ni da magana, .........shit ! .......Yau fa yarannan zasu zo maganar biki, ya salam,"

"Bikin wa za ai?"

"Bikina mana"

"What? Kana nufin kace min as young as u ar, aure zakayi? Who is the lucky gurl"

Tana karairaya tana shafo shi take maganar, can qasan zuciyar ta kuwa wani irin azababben kishi ne ta ji ya kama ta, a rana daya da tai da shi ta banbance shi da dikkan mazan da tai mu'amala da su, ta bashi lambar yabo mai girma, dan haka dik yanda zata yi ta ajema kan ta shi sai tayi,ba aure ba Allah yasa shine tantabara, sai ya raba mata kwana da matar shi, in ma bata dau kaso mai tsoka ba kenan.

"Look young gurl,thanks for the company, i really enjoyed yesterday, in fact, it was the best nyt ever, but u c the problem is that, i can't......"

Hana shi qarasa mai zai ce tayi, ta hanyar sakar masa da kasala, da salon ta.

Khaleefa mabuqaci ne sosai,dan haka ba abinda yafi masa a yanzu irin ya biye mata kawai.

Sai da suka nutsu sosai sannan take fada masa,

"Kaga ni ba zan hana ka aure ba, wa ce ce ni? Wane matsayi na ke da shi a wajen ka? Daga biya ma kai buqata? Ni ba sai ka biyani ba,nima na gani ina so, so kawai in kaje kaga amarya bata maka ba zaka iya dawowa nan, ko da yaushe qofa bude take a wajen ka, haka zalika koda ta maka in kaji kwadayin zuwa ka shana zaka iya zuwa nan, baka da case,"

Bai musa mata ba, kuma bai amsa mata ba, wanka ya shiga,biyu har ta gota a wannan lokacin, alwala ya yo, ya fara sallolin da bai yi ba, yana idarwa tana kwance daidai tana kallon shi, ya kula in bai da gaske ba ba zata barshi zuwa ko ina ba,

"Ai ka bari kaci abinci ko?"

"No thanks zani gida,qanne na na san sun zo, nemana da zasuyi tayi ne zai tabbatar ma da mutan gidan mu ba gida na kwana ba, so sai wataran,"

Har bakin qofa ta raka shi, tana zuba masa salon karuwancin ta.

*******************

"Gaskiya amarya ki fito mana da angon nan naki haka, mun gaji da jira, tin dazu ko wayar shi ma ta daina shiga,"

Cikin jin kunya Aeeshaa ta sauke kai qasa,

"Adda Hussai ni ina ni ina boye babban mutum kamar Yah khakeefa, na san aiki ne dai ya boye shi,"

Hassana dake gefe tai murmushi, dan yanzu ta sauke komai a ran ta, tin bayan zuwan 'Yan uwan nata da suka bata shawarwari, da kuma nuna mata rashin dacewar su ma kwata2 da Khaleefa, suka bata shawarar ta yi hakuri, ta tsananta addu'a inshaa Allah mijin ta na nunawa sa'a na nan tafe, sun yi ta bata misalai kala2 kafin zuciyar ta ta aminta da bayanan su.

Qarar motar shi ce ta sa Balqis miqewa da kyar tana tura tsohon cikn ta gaba,

"Sai na riga ku, dan na gane qarar motar shi har na gaji,"

"Taka da sauri Iya beji, Allah ya sa kije ya gwasale ki, kin san halin shi ai, ba a iya masa ya dangin gidan maza,"

"Habaa kar ki masa mummunan zato, muna kyautata wa 'yan uwan mu zato, yanzu mu dad'e bamu ga juna ba haka ya gwasale ni?

Miqewa tayi da kyar da qaton cikin ta a gaba, ta nufi waje, rufe mota yayi ɗauke da tarkacen shi a hannu, ya nufi cikin gida, cikin zumud'i ta tarbe shi,

"Yah Khaleefa barka da dawowa, mun dad'e muna ta jiran ka, sai yanzu ka dawo, nayi missing din ka sosai,"

"Ah Balqis ya kk? Ya mai gidan? Sannun ku da zuwa, bari na dan huta a gajiye nake,"

"Muna lafiya Yah, ban so hakan ba, na so mu zauna mu yi hirar yaushe gamo,"

Murmushi ya mata sannan ya yi gaba, ba tare da yace komai ba.

Dariyar su Hussai ta ji a bayan ta, aiko nan da nan ta hau,su kuma cike da tsokana suka maimaita me Khaleefa ya fada,

"Ah Balqis, ya kk? Ya mai gidan, bari na dan huta a gajiye nake,"

A tare suka kwashe da dariya, banda Aeeshaa da take murmushi, da kuma Balqis da ta cika tayi famm.

Bata kula su ba ta wuce bangaren Hajja, kayan lefe ne a qasa Hajja na d'agawa tana ajewa,tana ganin su kuwa ta manta da haushin su Hassana, cikin fara'a ta qarasa ta zauna daf da Hajja.

"Hajja ba ko gayya,abun 'yar haka ne ma?"

"Na so kiran ku sai na manta na bar wayata daki, shine nake ta roqon Allah ya kawon wani a cikin ku, sai a kira mutan gidan suga lefe, abinda babu sai a fada a saka,"

"Hajja hoo, wannan kaya haka meye babu, ai komai sai son barka, ni fa tinda aka fara maganar bikin nan ban ji kuna maganar Aunty khadeeja ba, ko ita ba ita a harkar ne?"

"Bar wannan baqauyiyar,ko wa ya fada mata ana kunyar ɗan fari oho, ni da nake da namiji ma, hirar mu muke sha, da auren baban ku ni na tsaya nayi komai, amma ita wai kunyar d'iyar fari take, d'iyar fari ai abokiyar hirace,abokiyar shawara ce, abokiyar farin ciki da koka baqin ciki ce,ita ta sani, ba abinda ba zan ma Aeeshaa ba tinda takwara ta ce,"

"Wannan gaskiya ne,mun shaida,dan baki haɗa son ta da kowa ba,"

Inji cewar Hussai da ta shigo, tare da Aeeshaa da Hassana,Aeeshaa na ganin kayan tasan na lefe ne dan haka ta gudu d'aki, dariya sukai ta mata, dan itama akwai kunya kamar maman ta.

"Amma Hajja banga turaren da nake matuqar so ba, wanda kk sai min zuwan ki Hajji na qarshe, har yanzu ko saudiya naji za aje sai na bada sautun shi,"

"Ohhh haka ne abun, ni ai ba turare aka ban ba, tashi ka fiya naci aka ba wa Mine, sai jallabiyya da aka ban, meye sunan turaren?"

"Ni da ke ɗaya ne? Ni ce qarama dole aban tsaraba tafi taki, sunan shi Sirrati Arebian ne, ya haɗu matuqa, suna shigen qamshi da lailatussahrah,"

"Ai kuwa sai an nemo shi, ko sautu sai a bayar,"

"Ohh yaran zamani, wato kun yaba turaren, nima ba a barni a baya ba, sai an siyo dani,"

Dariya sukai, a haka suka ci gaba da kawo abubuwan gayu da qamshi wanda ba a saka ba, sun kira 'yan uwan su dan ganin lefe, anyi2 Umma tazo taqi, ta turo Ameena da Abdul.

Baban su sabeer har Katsina ya je ya kai masu katin daurin auren Aeeshaa da Khaleefa, sunyi murna sosai, na nuna masu mahimmancin su, sun kuma yi alqawarin ziyartar bikin.

*********************

Sauran kwana uku biki, har yau ango da amarya basu zauna waje daya sun tattauna ba da sunan zasu zauna a inuwa ɗaya nan da wasu kwanaki, kullum sai dai su haɗu a kan hanya, General ya ma Khaleefa umarni yau ya je bangaren Ummeen su Sabeer ya gana da Amaryar shi, kar kuma yaji ance bai je ba.

A yau din ne mutan Kt suka iso, mata uku, namiji daya, wanda yake shine Yayan mahaifin Aeeshaa, ta yi kuka sosai da kuma murnar ganin shi, yana matuqar kama da mahaifin ta, matan shi masu kirki, kamar su goya ta dan murnar ganin ta,sun kawo mata tsaraba kala2, wanda yake namu na mata sai suka damqa shi hannun Umman Sabeer, yamma nayi Uncle din ta ya dau matan shi suka koma gidan su Aeeshaan, can zasu sauka, dik da cewar Hajja taso su zauna anan, a cewar ta, in Umman taga an barta ita daya ta zo harkar bikin dan dole ai.

**********************

Khaleefa ke ta tinanin ya zai yaje bangaren ummeen su Sabeer zance da wannan yarinyar da baifi ya aike ta kira masa budurwa ba, ga shi Rebecca sai waya take masa, dan yau kwata2 bai fita ba,  'yan kwanakin nan ko laptop bai cika dauka ba, dan ya samu mace ba sadakin kowa, ya more ya kama gaban shi.

Turaren shi ya qarasa fesawa, dan so yake daya gan ta ya wuce wajen Beccan shi.

Hussaina ce ke tsarawa Aeeshaa kwalliya, kamar yau za a kaita dakin ta, dik dan Khaleefa ya gani ya yaba, ta tsaya sosai ba dan komai ba sai dan Balqis da ke zaune tana miqo kayayyakin, yanda ta ke zumud'i kai kace wani auren soyayya ake shiryawa.

Simple make up suka mata, amma fuskar ta sai sheqi take dan kyau,hijabi ta dakko zata saka, har suna hada baki wajen fadin,

"Habaaa yarinya ai ko a riga aka haife ki ba zaki saka hijab dinnan ba,"

Dariya sukai dika, sannan Balqis ta yafa mata mayafi kalar kayan ta

"Adda a haka zanje?"

"Wataran ma ba kaya zaki yi yawo a gaban shi,"

Duka Hassana ta kai ma Hussai.

"Babbar banza kawai,"

Cikin jin kunya ta sinqe hijabin ta a jikin ta, tana zuwa gaban Parlourn ta warware ta saka, a ranta tace,

'Ina na isa yawo a gaban wannan mayunwacin matan da wannan shigar, inaaa Ya Allah ka taimakeni, ni tsoro ma yake ban'

"In bazaki shigo ba ki fad'an ina da abin yi,"

Da sauri ta shiga ta samu waje ta zauna nesa da shi, a takure, cike da jin tsoron shi.

'Ji wannan ko meye haka take yi oho? An fada mata kowacce mace nake bi oho?'

(Yo ba gwanda ita ba ma, kai da ke shiga ramin shaddar kasuwa dan rainin wayo kawai😏)

Shiru sukai,ba mai cewa komai, a qashin gaskiya turaren ta ya masa daɗi, ba kadan ba kuwa amma dan baqin hali ya hana ya yaba ko da kwalliyar ta ta ne ma.

Karkacewa yayi ya zaro kudi masu yawa, da gani zasu kai dubu dari ko sama da haka, wurgawa yayi a gaban ta.

"Ga shi nan na san wataqila ace na bada, dan ku mata akwai ku da bidi'a baku tinanin ya aka samo kudi amma kuna son kashe su,"

Wani kallo ta masa, sannan ta tura kudin har gaban shi da hannun ta.

"Kar ka damu Yah, ai ba kai ka nemi aure na ba dama, kar ka manta matar sadaka ce ni, baka ni akai kyauta,ba mai buqatar kud'in ka,"

Cike da mamaki, ya kalle ta, itan ma shi take kallo, tana jin tsoron shi yes, amma ba ta daukan wulaqanci musamman akan abinda bata roqa ba.

Miqewa yayi, cikin fushi, ya ja hannun ta da qarfi ya matse, dole ta sa ta miqewa tsaye dan azaba, wani irin kallo yake mata na tsantsar tsana da jin zafin rashin kunyar da ta masa, lallai yarinyar nan daga ta gan shi ba kaya shiyasa take qoqarin fara kawo masa raini?

Gyaran murya suka ji daga bayan su, cikin mamakin ta kuwa Sabeer ta gani, da qarfi ta fizge hannun ta ta gudu bayan shi tana kuka, kallon kallo sukai da Khaleefa,kafin Khaleefa yayi qwafa ya fice.

Juyawa Sabeer yayi, ya na son bata hakuri, amma qamshin ta, da kyaun ta suna fizgar shi, idon ta rufe, a hankali ya taka ya bar wajen.

Bude ido tayi tare da share hawayen ta, ta bude baki zata yi magana kenan taga ba kowa a wajen,

"Ina Yah sabeer? Ko dai gizo yake man? Me ye zai sa yamin gizo to? Yah Sabeerrr.............

*ku taya ta nemo Sabeer pls, tana cikamin kunne*

*KUN MAKARO*

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 8:

Duba shi ta shiga yi, idan ta sai zubar da hawaye yake yi, yau so take ya fada mata me ta mishi yake gudun ta, koba komai shi kaɗai ta sani yake kula da ita da damuwar ta tun ta na qarama, ta saba da shi ainun, shi take jin zata iya sharing komai da shi ba ta jin nauyi ko kunyar shi sam, bata sani ba wataqila laifi ta masa shiyasa yake gudun ta.

Qofar dakin shi ta je tai ta kwankwasawa, yana tsaye jikin qofar, a hankali ya saka key, shiru ta danyi, dan taji motsin saka key din, a zaton shi ta hakura ta tafi, da sauri ya murda ya bude,dan ya hange ta ko da daga nesa ne cikin rashin sa'a kuwa su ka yi gware, baya yayi yana taba wajen, itan ma haka, wayancewa ya yi da fad'in,

"Me qaton kai kawai, ji yanda kk sa na bige,"

"Yah ni da kai an ga mai qaton kai ai, Yah Sabeer me nama ne, in wani laifi na maka dan Allah ka yi hakuri ka yafe min na tuba ba zan sake ba, ba zan sake makamancin shi ba ma ko mene ne balle nayi irin shi, ka daina guduna, ka sauya wajen aiki, for only god knows why, Kuma haka ka tafi ko sallama baka yi min ba,ina ta bin ka ina kiran sunan ka haka ka fice baka tsaya ba,nice baka son gani ko?"

Tana maganar ne cike da zubar hawaye, kukan ta na qona masa zuciya, baya son ganin koda ɓacin ran ta ne balle kukan ta, yana son ya bata amsa amma me zai ce mata? Ina son ki? So nake ni na aure ki ba Khaleefa ba? Inaaa ba zai taba yuwa ba.

"Look dear, ni ba wai gudun ki nake yi ba, yanayin aiki ne ya sa ni gaba, kuma ranar na san inna tsaya sai na makara ban tafi ba, in ban manta shagwabar ki ba kina qarama ko nan da can naje sai kinyi ta kuka, kina rikici, ko dake ban sani ba yanzu kin zama babba wataqila kin daina ko?"

Cikin wasa ya qarasa maganar tashi, itan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login