Showing 57001 words to 60000 words out of 69262 words

Chapter 20 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1043

masa Aeeshaa a bar maganar Hadiza, randa ya yi maganar Aeeshaa sai da ya gwammace uwar shi bata haife shi ba, dan yasha maruka ba su qirguwa, sannan Hajja ta sa John ya nada masa mugun duka, sai da ya dinga shiga ruwan zafi, kiran sunan Aeeshaa ya za masa bala'i da masifa, to ya zai yi da kewar ta da ta ke kama shi, ga son ganin abinda suka haifa dake dawainiya da shi, shi ko sau daya a bashi dama ya sa su a idon shi.

(U dey play with fire Khaleefa)

***********************

Wata shaquwa ce mabayayyaniya a tsakanin Aeeshaa da Umma, Ameena da Abdul, Abdul har baya son zuwa ko ina saboda Ameerah, soyayyar Ameerah ce ta sa ya fara kula Aeeshaa,har yake sakin jiki da ita, daga hirar Ameerah suka koma hira a tsakanin su, yakan fada mata damuwar shi ta bashi shawara akai.

Umma ta dage wajen maida Aeeshaa yar gayu, makarantar da ake koyar da kwalliya da girke2 ta saka ta, kwalliyar zamani Aeeshaa ta maida hankali akai wajen koya sai cakes da snaks data qara gwanancewa, abinci wataran har itama tana taya koyar da shi a wajen, saboda bata da matsala a wannan bangaren.

Tare da Umma yanzu take zuwa sarin kaya, manyan shaguna, musamman shagon Alhaji Shehu Dan Kwarai,da Mumtex masu Saida atampopi masu inganci da nagarta dake kantin kwari, doka shagunan ana saida kayyaki ko wanne iri kk so, akan farashi mai sauqi, kuma kaya ne masu quality matuqa, kowa yaga Aeeshaa ta saka kaya sai ya sake kallo, gani ake special order ake mata.

Sun saba sosai da mutanen shagon saboda karamci da karbar mutane cikin girmamawa da sakin fuska.

Watarana Aeeshaa da kan ta take zuwa shagon, dan yanzu ta waye tana iya fita ita daya ba tare da an raka ta ba, sai dai wataran ta kan dauki Ameena saboda ta riqe mata Ameerah.

Yah Sabeer kusan tarewa yayi a gidan, ko da yaushe yana dauke da Ameerah, yarinyar tayi sabo da shi sosai, dan in zai tafi ma sai ya mata wayo yake guduwa.

Umma tayi2 da shi akan ya sanar da Aeeshaa abinda ke ran shi, ya kasa, Ammar yace in ya wuce yau bai fada ma Aeeshaa abinda ke ran shi ba, shi zai sanar da ita, Sabeer ya yi roqon duniya Ammar ya rantse ya qara.

Dan haka yau ba shi da option din daya wuce ya sanar da ita, manyan kaya ya saka, wanda suka matuqar karbar shi, ga gemun shi daya tara wanda yake shan gyara a koda yaushe, ba mai ganin Sabeer a maza bai sake waige ba, balle mata, qamshi kawai ke tashi a jikin shi, sallama yayi ma su Ammar da Hassana wanda suka zama kamar gam, saboda liquwa ma junan su, Baba General ya ba shi Umarnin ganin ta, iyayen shi sun zo sunyi magana da Baba General din da manyan gidan, sunga Hassana kuma sun yaba da halin ta dana iyalin ta, sun aminta zasu hada zuri'a da su, yanzu suna jiran a masu izini su zo maganar aure.

"Sabeer kayi wa yarinyar nan a hankali, irin wannan gayu haka?"

"Ke dai baki rabo da ja na, da bana gayu kuke nufi?"

"Kana yi amma na yau kai kan ka kasan daban ne,"

Murmushi yayi ya fice, da Hajja ya hadu, zata je wajen Khaleefa, yau ya tashi da surutun wai ana masa abu kamar qaramin yaro, bayan shine babba a gidan, za a sa qannen shi su raina shi.

"Sai ina kuma?"

"Zanje wajen Aeesh...... ammma wajennnn Ummana,"

"Hummm Sabeer kenan, ka gaida min Aeeshaa da Khadeejan da kuma sauran yaran, Allah ya tsare ya bada sa'a,"

Yaji daɗin addu'ar ta sosai, dik da yaji kunya yana ganin ta gano shi ma.

Hajja zuciyar ta fari qal, domin tin da ta sa Khaleefa ya saki Aeeshaa burin ta ace Sabeer ya aure ta, amma bata son ta faɗa dan bata san ya zai dauki abun ba, kar a kuma irin na Khaleefa, so sai ta bada qarfin ta wajen yin addu'a akan lamarin, in alkhairi ne Allah ya hada zuqatan su, in ba alkhairi Allah ya ba su abokan zama masu alkhairi a rayuwar su.

Aeeshaa na zaune tana bawa Ameerah Nono bacci ya dauke ta, Sabeer ne yayi sallama, ya dad'e a bakin qofa ba wanda ya amsa, Umma ta tafi wajen kasuwancin ta, yara na makaranta, Ameerah na jin maganar shi ta fara takawa zata fita, tana ta murna.

Sabeer ne ya shiga dan jin Ameerah dake tahowa,yana shiga yayi arba da Aeeshaa dake zaune tana bacci n*** daya a bude, da sauri ya juya yana hadiye yawu, tare da zazzaro ido, bakin qofa ya je ya hau kwankwasawa, bude ido tai a hankali bata ga Ameerah ba, gyara rigar ta tayi, ta fita dan dubawa tare da kwalawa Ameerah kira, dariyar ta ta ji a waje, ta leqa da gudu2, ganin Sabeer dauke da ita ne yasa ta dafe qirji tana dariya.

Sabeer ba abinda yake hangowa sai hoton ta tana bacci da zu, hakan ya sa masa tsoro da wani irin faduwar gaba, wanda yake jin kamar ba zai iya fada mata ba.............

*Wai kai wanne irin matsoraci ne dallah malam, kar ka fada ta samu wani ya shige ran ta ai ka huta🙄😚 na kula gidan naku juyawa abun yake, Khaleefa ko da tsohuwa ba ruwan shi zai tinkara,kai kuma ga ka a gaban masoyiya ka kasa bayani, RAGON MAZA🙊🙊🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀*

KUN MAKARO

PAGE 27

Bayan sun shiga ciki sun zauna, Aeeshaa ta yafa mayafi dan rufe jikin ta (bata san an gane mata n*** daya ba🤣🤣🙊🙈) hira suke tayi, tana satar kallon da Sabeer ke mata, in yana mata kallon wani iri take ji a zuciyar ta, ba qaramin shigar ta kallon yake ba.

Cikin zaquwa taji ina zashi yayi wannan gayun haka ta ke magana.

"Yah Sabeer wannan gayun yayi kyau gaskiya, shin wai yaushe zan ga auntyna ne? "

Kafe ta yayi da ido, cikin wata iriyar murya da shi kan shi bai san yana dauke da ita ba, tare da lumshe idanun shi ya ce,

"Ke ce auntyn kan ki da kan ki, dan kuwa wajen ki na zo,"

Wayyooo Allah, Sabeer ka isar da babban saqo da wannan kallon naka, zuciyar Aeeshaa ke bugawa da sauri2, nan da nan hankalin ta ya tafi kan lips din shi yanda yake fidda kalamai cikin natsuwa da kwarewar zance, tinda take bata taba jin wani feelings ba game da namiji sai yau, da sauri ta dauke idon ta, ganin shima ita yake kallo,

"Ammm Yah Sabeer na kawo abinci? Na gama tin dazu, saboda 'yan makaranta,"

"Ni dai bana son na ci abinci, so nake ki qosar da ni da amsar tambayar da zan maki yanzu,"

Wata kasala ce ta ziyar ci Aeeshaa, Sabeer yaushe ya iya irin wannan abubuwan haka? So yake da gaske sai ya sace zuciyar ta, shi kuwa magana kawai yake ta hanyar umarnin da zuciyar shi ke bashi, amma ba wai dan yasan yana samun wani effect akan ta ba.

"Wace amsa ce haka da zata qosar da ciki,"

"Wannan amsar daban take,ba ciki ba kadai, harda zuciya da ruhi zata qosar,"

"Ina jin ka,"

"Ina SON KI, kina SO NA?"

Wayyoo Allah, Aeeshaa ji tayi kanta na wani irin juya mata, idanun su hade dana junan su, zuqatan su na bugawa a tare,wani iri take ji daga kan ta har qafar ta, Sabeer na neman sace mata zuciya  da furucin shi da body language din shi, cikin sauri da sarqewar murya tace,

"Ban sani ba......ban san me ne so ba....ban san ya ake ji ba in ana yin shi....banda amsar da zata qosar da kai Yah Sabeer, i am so sorry for disappointing u,"

Idon ta ya kawo kwalla yana haske, Sabeer ke kada mata kai,tare da miqa mata tissue dake kan center table din wajen.

"Kar ki kuka, ban so tambaya ta ta saka ki kuka ba, bana burin aikata abinda zai saki zubar hawaye, bayan irin abubuwan da kk fuskanta a baya, dan Allah ki yafe min, inshaa Allahu zan ci gaba da adana son ki a raina, har qarshen rayuwa ta, na rayu da son ki tin kafin auren ki, yanzu ma zan iya jurewa indai hakan ba zai sake saki zubar hawaye ba,"

"Dama kana so na.... kana sona ka bari aka bayar dani inda zan azabtu? Me yasa tin tini baka furta kana so na ba sai yanzu?"

"Aeeshaa abinda magabatan mu suka yi mai kyau ne had'in zumunci, kinga da yayi daɗi da tini kina cikin farin ciki, rashin yin daɗin shi ne babban baqin ciki na da dana sani na,"

Aeeshaa bata san wanne irin baqon feelings bane wannan, nauyi da zafi take ji a qirjin ta, na meye to? Ko dan bai sanar da ita yana son ta bane? To in ya sanar da ita ita din sanin meye so ta yi da zata damu akai? Tabbas wannan ne so abinda take ji yanzu, wani irin hadi ne na farin ciki, tausayi, haushi da nishadi, in fact ba zata iya expressing din me ye a ran ta ba,

Ameerah ta janye a jikin ta ta shige daki da sauri2, fadawa tayi kan gadon ta, tana tsiyayar da hawaye, daga baya kuma ta fara murmushi, tana qanqame pilo,

"Ashe da rabo na a duniya da wani zai furtan kalmar INA SON KI, ashe ban MAKARO BA, kalma mai dadi daga bakin mutum kyakkawa da kyawun halaye da dabi'u, Allah na gode maka, Allah na gode maka, ina son ka Yah Sabeer, Allah ya sa alkhairi ne hakan,"

Ameerah ce ta shigo dugui2, ta furta

"Baabaa....baabaa.."

Dariya Aeeshaa tayi ta daga ta, tana ta murna sannan ta fita,

"Yah Sabeer kaji me Ameerah tace yanzun nan?"

"Me ta ce?"

"Cewa tayi Baba, ina zaune na ji ta shigo ta ce baba,"

"Kaiiiii Aeeshaa,"

"Da gaske nake, na taba maka qarya?"

"Sosai ma"

"Yaushe?"

"Dazu"

"Me nace?"

"Cewa kikai baki so na na maki yaro da yawa,"

Ya turo baki irin na shagwaba tare da maqale hannayen shi a qirji, shi a dole yayi fushi,

"Yah Sabeer ni fa ban ce bana son ka ba,in ban so ka ba wa zan so? Kai ne mutum na farko dana kasa tantance wane hali nake a ciki idan na gan ka, daga sanda ka furta min kalmar So, shiga ta daki na gano nima ina son ka Yah Sabeer, Ina son ka, Ina son ka,"

Hawaye ke zuba a idanun su sosai, musamman Sabeer, da har wani kukan daɗi ya saki, ji yake yau kamar an dauke masa wani abu mai nauyi a qirjin shi,

(Sai kace budurwa, ko meye na kukan😚)

Nan suka zauna ta debo masa abinci,itama ta zuba nata, suna ci suna hirar masoya, Sabeer sai aman soyayyar dake ran shi yake mata, ita kuwa gaba daya daɗi ya sa bata jin ma daɗin abin cin, ajewa tai a gefe kawai tana sauraren shi, wani irin daɗi da farin cikina ratsa ta, sannan son shi na qara shiga cikin kowanne saqo na gabban ta.

"Hhhhhhhhh Yah Sabee ka cinye abincin fa, ko na qaro maka ne?"

Dubawa yayi yaga ashe abincin ya qare yake ta kai spoon yana kwaso babu, dariya sukai tayi,

"Wata rana fa tare zamu ci abincin nan ko? Ina baki kina bani a baki,"

Kunya ce ta kama ta ta rufe idon ta, amma cikin ran ta fata take Allah ya nuna mata wannan lokacin.

Har Umma ta dawo, da yaran, Sabeer na nan bai tafi ba, Umma ta fahimci akwai wani abu dake faruwa, tabbas kuma koma me ne ne mai dadi ne.

Bayan magrib Sabeer ya tafi gida, ya bar Aeeshaa da kewa, dan ji tai kamar kar ya tafi.

"Umhummm a bani labarin wannan abun farin cikin,"

Umma ce ta fadi hakan, a daidai lokacin da take zaune a bakin gadon Aeeshaa, tana taya ta ninke kayan Ameerah, suna sakawa a wajen kayan ta.

"Ummaaaa....ni ba komai"

"Yanzu ba da ba ne Aeeshaa, in da dane ko kula da ke ba zan ba bare na gane halin da kk ciki,kuma har abada zan koma ga mahalicci na ina dana sanin hakan, ki sanar dani ko me ke saki farin ciki, ko Sabeer ya furta maki maganar da ke ran shi ne?"

"Kin san me ke ran shi ne?"

Cikin share hawaye Ummah tce

"Kwarai na sani, wannan dalilin ne ma yasa na so kar a hada auren ku, da Khaleefa, amma ba zan taba iya yiwa iyayena musu ba, musamman akan ki,"

Hadiye wani daci tai a ran ta, ta yafe ma Umman nata, wannan na cikin abinda ya faru a baya ne, so ba wani abun kokawa a ciki, sai su fusknaci gaba.

Dan haka hira suke tayi akan yanda abun ya faru, Ummah na ta jin dadi kamar wata qawar Aeeshaan, daga baya ta bata shawarwarin yanda zata yi ta qara samun mazauni a zuciyar shi na dindindin.

***********************

Hadiza ciki ya shiga watan haihuwa, Goggo ta maida hankali wajen kula da ita sosai, Hadiza kullum kuka da daga hankali take, what if ta mutu fa wajen haihuwar dan shege me zata ce wa Allah? dik iya qoqarin Goggo na kwantar mata da hankali abun ya gagara, ta rame tayi baqi, dan ta daina shafe2, kalar ta ta fito, amma sai quraje kamar a kankare mata su, da ka hango ta ciki kawai zaka fara gani, sai sirisirin qafafun ta.

In ba Goggo data haife ta ba wanda ya santa da girman ta ba lallai ya gane ta ba.

"Ki yi wa Hajja waya ki sanar da ita yanda ake ciki Goggo,matar nan na da kirki kin kasa sakewa da ita, da ba ta da halin dattako da ko gidannan ba zata zo ba, kina ganin cin mu, shan mu, da komai namu yanzu su suke yi, kayan jarirai da komai ta siyo ta kawo, ba abinda ya dame ta da wai mutane zasu ce dan su ne ya min ciki, fatan ta ta rabu da duniya lfy, ta tadda Allah cikin aminci,kinga sauran kwana uku, yanda likitoci suka ce na haihu, ya kamata a sanar da su,"

"In kk fara magana ko gajiya baki yi, ba za a fada ba,sarkin wawaye, zama zatazo tayi dan zaki haihu?kin ma bari ki haihu a sanar da su ko,"

"Shi kenan Goggo yanda kk ce,dan Allah kwadanta mana zogalen nan mu ci,"

"Haka dai kuka iya ke da cikin naki ci ba,sai kun cinyen dan jarin qulin, in ya fito bai kawo kudin cefane ni da shi ne, in mace ce wanke2 na kullum sai tayi sau biyu,"

Murmushi mai haɗe da jin nauyi Hadiza tayi,da ma ace cikin nan na sunnah ne da taga gata, a haka ma Goggo na nuna mata gata, lallai da cikin Sunnah ne sai ta rasa ina zata saka ta.

Kwana biyu da faruwar Hakan Hadiza da dare ta fara naquda, tin tana kuka har ta gaza kukan, fadi take tana kumawa..

"Da na san haka haihuwa take da naji maganar ki Goggo na rufe qafafuna , da ko qofar gida ba zani ba sai da izinin ki, wayyoooo Goggo mutuwa zan, Khaleefa Allah ya isa ban yafe maka ba, duniya da lahira Wayyoooo Aeeshaa ki yafe min,ban taba neman gafarar ki ba ki yafe ni mutuwa zan yi, wayyyoo a taimaka min,"

Bakin ta Goggo ta make,

"Dan girman Allah ki daina mana wannan dan iskan kukan, ba zaki kira sunan Allah ba sai tonon silili da iface2, in kk mutu kina wannan hayaniyar fa?"

"Na tuba, na tuba Allah na tuba ka yafe min,ba zan qara cikin shege ba, ni ko na halal din ma ba zan ba, wayyoo Allah na, natuba,"

Hajja suka kira ta aiko da mota, sannan tace suma gasu nan zuwa, asibiti aka wuce da Hadiza mai kyau da tsada, nan midwifes suka shiga dawainiyar taimaka mata dan ta haihu lfy.

Shigar su da awa daya da mintuna Hadiza ta sauka lfy, ta samu Yaro namiji, kar ku ga kuka wajen Goggo da Hadiza, Hajja ma dik qarfin zuciyar ta da ta zo sai da ta koka, kuka tayi sosai, ganin yaro lafiyayye sun samar da shi ta gurbatacciyar hanya.

Haka akai ta zuwa asibitin har da Aeeshaa, ta zo duba Hadiza ko dan Goggo, da kuma Umarnin Hajja, koma me ya faru ya faru, Hadiza dai zata shiga zuri'ar su, dan haka dole ta san ya zatai ta hada kan su, kuma ta kula da Aeeshaa bata dau abun da wani nufi ba, ko a jikin ta, har daukan yaron tayi, Hajja ce ta amsa waya.

"Ku shigo daki na biyar, nan muke, Auwal ku tsaya waje, ni dai yaron nan ya nuna ya nutsu ne amma har yanzu ina tsoron shu'umancin shi, kar ya samu hanya ya gudu,"

Khaleefa na tsaye kusa da Auwal yaji komai, kuma ran shi ya baci, ya gyarun ma amma matar nan har yanzu bata yarda da shi ba, a yanda yaci azaba, kuma ya sha wa'azi kala2 da take kunna masa, da wanda take masa in yau aka bashi mace karuwa ba sai dai ido ba, na dama kullum neman gafara yake, rai a bace ya shiga dakin

"Hajja ki daina min haka bana so, ki sallami wadannan qattan banzan, ni ba zan yarda ina tafe gardawa na bina ba,"

"Gaka nan qaton banza, barka kazo an maka haihuwa amma kana zancen banza, ku bashi dan shi, ya masa addu'a, da kiran sallah, ga shi nan,"

Amsar yaron yayi, nan take soyayyar shi ta shiga ran shi, kama suke sak, amma shi baqi ne yaron, kalar maman shi ya dakko kenan, kiran sallah ya mishi dama da hagu, sannan nan take ya rada masa suna da Ahmad, hawaye yake cike da quncin samar da wannan kyakkyawar halittar ta haram, ba su yaron yayi ya fita yana kuka sosai, waje ya samu ya zauna, Auwal na kan shi, hakuri yaji Auwal na bashi, yau ce rana ta farko da kalma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login