Showing 27001 words to 30000 words out of 69262 words

Chapter 10 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1047

mata, burin ta taga qannen ta da Umman ta abokiyar fad'an ta, in ta tina da fadan Umman ta sai tayi dariya tace,

"Ummana gwanda fad'an ki sau dubunnai akan halin da nake ciki  a yanzu,"

Aeeshaa ta d'ashe tayi wani irin fari, sai dogon hanci da dan qaramin baki, hips din ta da boobs ne suka qara  cika kamar an hura mata su, amma ta zuqe tayi ramin wuya, kamar wadda tai ciwo.

Kwance take tana karanta hadith,dodon nata ya tafi office kuma yace za yi dare, ta san bai wuce wajen Rebecca, dan yanzu ta san ta sosai.

Dan haka dole ta jira ko nawan dare zai dawo taje ta bude masa gate.

Horn ta ji kamar irin na motar Umman ta, kad'a kai ta yi tare da tunanin inaaa ba ita bace, ai da wahala ta zo sai dai ta sa a kawo su Ameena, murmushin yaqe tayi ta gyara kwanciyar ta, horn ta sake ji, da gudu2 cikin saka hope din ganin Umman ta da qannen ta ta miqe dan zuwa ganin waye.

Bude qaramin qofa tai, cike da murna ta koma ta fara bude babban, tana matse kwallar farin ciki.

Shigowa Ummah ta yi dauke da mamakin ganin Aeeshaa ke buɗe gate, ina gate man?

"Aunty Aeeshaa nayi missing din ki alot, ina ta son zuwa Umma sai tace ba yanzu ba, kuma...."

"To cakwaikwaiwa, zaki iya bari mu shiga ciki?"

Turo baki ameenah ta yi gaba, ta faɗa a hankali,

"Ta fara"

Murmushi Aeeshaa tayi, ita kam she missed this fad'a thing, how she wished everything will go back to normal.

Ruwa da lemo ta gabatar da abubuwan motsa baki, sannan ta zauna a qasa gefen umman ta gaida ta, tare da tambayar ta suna lfy?

"Ke za a tambaya kina lfy? Kinga yanda kk koma kuwa? Sai kace ana yankar ki ana miya? Meke damun ki, ina me gadi kk bude qofa d kan ki?"

"Ammm Umma ya aike shi ne, kumaaa immm...niii ba abinda ke damuna, Umma i missed u so much,"

Wani irin zazzafan hawaye ne ya ke kwaranya a idon ta, Abdul tabe baki yayi, a ranshi yana fadin

'Kukan gulma, ji gida kamar a waje, ga kayan alatu, dik ita daya, ga video game, wai take kuka, kamar a can wani daɗin take ji'

Umma ta tausaya matuqa amma a zuci, dan ji tai kamar ta dora hannu akai tai ta zunduma ihu,

"Meye abin kukan? Ke Ameena ce? Kowa haka aka masa auren ya zauna, da bamuyi zaman auren ba zamu same ku ne? Kema haka zaki yi hakuri....."

Cikin fad'an da hantarar ta bata shawarwarin da zasu mata amfani in kadaici ya dame ta.

Godiya tayi, ta miqe zata dora masu abincin dare, a zaton ta sai dare zasu wuce.

"Dawo mu wucewa zamuyi, yanzu na san wannan mara kunyan mijin naki na tafe, gwanda mu tafi kan ya gan ni ya raina ni, kar kuma naji labari a ko ina cewar na zo nan, in ba haka ba bazaki sake gani na ba,"

"Na gode Umma inshaa Allah ba zan fada wa kowa ba..... haba Abdul tinda kuka zo ko ci kan ki baka ce min ba, me yayi zafi?"

"To ci kan ki"

Wasa ta maida abun suka yi dariya da Ameena ya yi murmushin gefen baki shima, nan ta hada ma qannen ta abubuwan daɗi da na shafawa for Ameena, amma Umma ta hana karba, ran Abdul ya yi mugun baci, musamman daya ga chocolates din da yake so.

A cikin fushi ya buɗe mota ya zauna, Aeeshaa ma cikin hawaye ta bude masu gate suka fita.

Fitar su da minti sha biyar ta fara dora girkin dare bata san me yake so ba, kawai ta fara dora doya zata masa sakwara.

Doya na tafasowa Aeeshaa ta fara jin kamar zatayi amai, abu sai gaba yake, da gudu ta nufi wajen sink ta fara kwara amai, kamar wadda zata amayar da hanjin ta🤮........

*Tooooohhhh Aeeshaaa watahafen?*

2020

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 12:

*Iyaye na,mijina 'yan uwana, qawayena, addu'a ta a gare ku itace Allah ya muku albarka, ya saka maku da alkhairi, ya sa kuyi kyakkyawan qarshe, na gode sosai da soyayyar da kuke nuna min, Allah kuma ya amsa addu'o'in ku na alkhairi a Kai na, albarka itace addu'a madaukakiya da zaka yiwa masoyin ka, ina nema maku ita wajen Allah, na gode sosai❤*

Bayan ta gama ta wanke bakin ta, ta sauke doyar cikin toshe hanci ta tace ta ta saka a fridge, sannan ta koma dakin ta ta kwanta, tare da qudindinewa a bargo, saboda sanyin da take ji.

Kamar kullum yauma ya makara wajen dawowa gida, sai dai yau gida ya je ya kai ma iyayen shi ziyara da su Hajja, dan gulma har da cewa bari yayi sauri ya tafi yasan tana can tana jiran shi.

Hajja tai ta sa mashi albarka, tana yabawa halayen shi,

"Matsalar ka daya Khaleefa baqin hali, baka son hayaniya har yanzu, ince dai ba dinkim kk mata ba, ko 'yar hirar nan ta miji da mata babu?"

Ran shi ya fara baci, sun ma samu ya ziyar ce su sai sun kai shi maqura, cikin danne bacin ran shi yace.

"Seriously Hajja, ya ma kamata ki yi min wannan maganar kuwa?Ina da mata kamar Aeeshaa me zai sani b'ata rai?"

Hajja harda shewa ta fara tina masa lokacin auren su, tana yi tana dariya, Baba General na taya ta, nasiha Baba General ya mishi, kamar na Allah, ya nutsu yana saurare,amma ta shiga ta dama ta fita ta hagu ne ba ji yake ba, mahaifin shi ma sai da ya mishi nasiha, suka raka shi har bakin mota, da roqon ya kawo masu Aeeshaa, kar ya zama miji mai kulle, alqawari ya musu zai kawo ta ranar juma'a mai zuwa.

Qarfe 10pm a gida ta mishi, Aeeshaa bacci ne mai dankaren daɗi ya ɗauke ta a kujera ,dan abinda take yi kenan, yanzu, goma nayi zata zauna a kujerar dake daf da fita daga parlour dan jiran dawowar sa kar ya zo ya buga ta na ciki bata ji shi ba ta yi laifi.

Horn ya dinga zabgawa baiwar Allah bata ji ba, takaici ba irin wanda bai ba ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan shi gaban ta, ga yunwa yana ji, anyi2 yaci abinci yaqi, wai kar ya dawo tayi abinci bai ci ba, kuma a gaskiya tinda ya fara cin abincin ta ko a wajen aiki in an je cin abinci ci yake kawai, amma ba dan da dadi ba.

Kamar a mafarki ta ji bugun qofar tashi, cikin rawar jiki ta tafi ta bude gate, ya ko haske ta da fitila yaqi shiga, jikin tane ya hau rawa, dan ta san halin shi in ya dad'e bai abu ba to kallon ta yake da kallo kamar zai kashe ta.

Baya ta ja cikin tsoro, shigo da mota yayi, ya parker ya fito cikin fushi, ita kuma ta tsaya rufe qofar tare da yin addu'a, a zaune ta same shi, ya dora qafa daya kan daya, yana hura hanci.

"Wani sabon salon iskanci kk fito dashi? Ina ta horn amma baki ga damar bude min gate ba, ni da gidana?"

Durqusawa tayi kamar kullum, ta fara bashi hakuri, banza yayi da ita dan bai niyyar hakuri ba sai ya fanshe a wani abun,

"Kawon abinci,"

Nan da nan tinanin ta ya dawo mata ashe fa bata masa komai ba, amma a wautar ta bata ji damuwa ba, tinda kullum baya yabawa zagin ta yake yana cewa ci yake dan kar yayi asarar kayan abincin.

"Yah Khaleefa ban yi ba yau, na fara naji banda lfy sai na kwanta shine bacci ya dauken bayan nayi sallah, kayi hakuri, u dn't like the food anyway, amma in kana so sai na maka ko indomie ce,"

Wani irin qunci da danasani ne ya shige shi na qin cin abincin Hajja da ya yi, a harzuqe ya miqe ya kifa mata mari, sai da ta ga duhu dummmm na wani lokaci, sannan ta dawo hayyacin ta, kuka ta sake mara sauti mai qarfi a zuciya, meye laifin ta? Taga bai ma son girkin na ta, shine dan zalunci zai dake ta.

Janta yayi har kitchen, ya dangwarar da ita gaban electric da suke amfani da shi wajen girki,

"Oya hadamin tea mai kauri, ki hadon da snaks, sannan ki dawo ki dafan abu mai nauyi,"

Kuka kawai take dan ta san ba zata iya moruwa ba yau, bata da lfy sosai, ga jikin ta ya dau zafi ya iya damqar ta ya daka amma bai iya jin zafin jikin ta ba, Allah na nan.

Tea ta dora, ta jingina da kitchen carbinet tana kuka.

Shigowa yayi daukan juice, ya ganta tsaye, dauke kai yayi, ita kuma ta hau goge fuskar ta.

Yana budewa yaga doya a wata roba kalar pink, qamshin doyar na fitowa ta toshe hancin ta, saboda wani yunqurin amai daya taso mata.

"Me wannan take yi anan?"

"Da sakwara zan maka, sai naji banda lfy, shine na ajiye, inna shaqi qamshin doyar amai nake, yanzu ma ji nake kamar zan amai,"

"Amai kuma? Yanzu ina qamshin nata yake har da ke da kk nesa zaki ji ni ban ji ba,"

"Kayi hakuri amma da gaske ina ji ni,"

."zo nan,"

Hawaye ne ya taru mata again, ta taka a hankali ta isa gaban shi, hannun ta toshe a bakin ta da hancin ta.

"Dakko,"

Kallon shi ta yi, with pleading eyes, amma ya basar, dakkowa ta yi hannun ta na rawa, ai kuwa kafin ta kai ga ajewa a kan sink amai ya taso mata gadan2, gudu take son tayi dan ta yi aman, ya tsaya a hanya, sai nuni take masa alamar ya matsa zata wuce yana ta kallon ikon Allah, yarinyar nan kamar wata mai allergy akan doya?

Yana nan tsaye qiqam, wani amai mai mugun yawa da tsaho ya taho ya wanke masa jiki daga fuskar shi har daidai jikin wandon shi.

Aeeshaa saboda amai kasa tsaiwa ta yi, tana ta yin shi ga tsoro a ran ta da damuwar aman da ta masa a jikin shi.

Ta rasa ya zata yi ta tsira akan wannan lamarin, kawai sai ta faɗi a wajen, ta kwanta kamar ta suma, this is her only way to save her skin.

For the 1st time ta yi qarya, Khaleefa na nan qame kamar wanda aka dasa, mamaki da takaici da qyanqyami sun haɗe sun masa katutu.

Bai bi ta kan ta ba sai da yaje d'akin shi ya sauya kaya ya wanke jikin shi musamman bakin shi, sannan ya dawo, kuka take tayi ta gefen ido, yanzu da suman gaske ne sai ya gama uzurin shi zai dawo, in ta mace ma baida matsala, to in da mutuwa ta yi qiyayyar har ta kai ko duba ta ba zai ba ya wuce? Dan uwan tane fa.

Ruwa mai sanyin gaske ya watsa mata, a gigice ta miqe tsaye, tana zaro ido tare da dauke numfashi.

Wuce ta yayi ya kashe electric ya tsiyayi ruwan tea ya debi abinda zai ci ya wuce ta, ba sannu ba Allah sawaqe, ba meke damun ki ko ina ke maki ciwo? Ko gobe zan kai ki asibiti je ki kwanta, nothing nothing, the mst sweetest thing shine ba duka ba zagi ya wuce ta.

Tana ganin haka daɗi da murmushi suka kwace mata,lallai yau Allah ya so ta, da tai dabarar nan, da ba dan haka ba bata san wanne irin kisa Khaleefa zai mata ba yau.

Cikin jin daɗi ta gyara wajen, ta toshe hanci da dankwalin ta, ta juye doyar a leda ta sa a shara.

Tea itama ta haɗa mai kauri ta hada sandwich, da ita da shi, ta dau nata ta kai d'aki, sannan ta dau nashi ta kwankwasa qofa, ya bata izinin shiga,yana zaune yana kallon wani American movie mata kamar tsirara suna ta yawo da maza ana shan iska ana ta kisses, saurin dauke kai tayi tana istigifar, ta aje masa, ta sake bashi hakuri sannan ta fita.

Ko kula ta bai ba, ta na fita yayi sufa ya dauke plate din ya fara ci.

"Yarinya qarama sai iya girki da kuma ......."

Aeeshaa sai da taci ta qoshi, tai nawafil sannan ta kwanta.

Bacci tasha mai dadi, ba takurar Khaleefa for the first time tin da aka kawo ta.

Yana can yana video call da Rebecca, gaba dayan su tsirara suke daga shi har ita, hankalin shi kwance.

Suna cikin aikata masha'ar su Rebecca ta mai tambayar data ja mata katsewar harkar su.

"Where is ur sweet wife, da ake kirana da sunan ta wataran, tsabar daɗin ta?"

"Shut up, i said shut up, don't u ever mention her name again, in kk sake maganar ta,  daga yau alaqar mu ta yanke, na faɗa maki kar kina sa kan ki cikn iyalina, stupid"

Duqawa yayi ya kashe dik da kiran sunan shi da ta yi tayi tana bashi hakuri,haka nan baya son matan banzan shi na waje suna maganar iyalin shi, ko ma meye matar shi ce.

Takaicin ta yasa ya kwanta rufda ciki har bacci ya dauke shi.

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, what if ya mutu a haka fa? Shin ya ku masu biya ma kan ku buqata da kallon fina2n batsa da karanta novels na batsa in kuka mace a lokacin da kuke aikata wannan sabon fa? Aka zo ganin ku a ga film na playing na batsa? Mala"ikun daukan rai suga novel din batsa? Ko kuwa ki/kaje lahira da record din last abinda kayi shine biyawa kan ka buqata ko kallon haramun? Wallahi mutuwa na kusa da mu fiye da yanda muke tsammanin ta. Ya Allah ka kare mu ka tsare mu ka katange mu daga aikin dana sani, Allah ka kare mu daga zina babba da qarama, ya Allah ka yafe mana laifin mu babba da qarami, wanda mukai bisa kuskure ko bisa ganganci, ameen ya Rahman.

Da safe Aeeshaa wainar flour take kwadayin ci, tinawa ta yi ta kwan biyu sosai rabon ta da cin ma wainar flour, murmushi ta yi dan daɗin da ta ji ya kama zuciyar ta data tina zataci din.

Nama ta tafasa ta yanka qanana, ya sha kayan qamshi harda garlic, ga dandano, ta jajjaga attaruhu, ta yanka albasa mai yawa, ta dakko kwai, ta aje gefe, sai da ta fara kwaba flour da ruwa tai dan kauri kwabin ba tsululu ba, sannan ta saka maggi, da curry da yankakkiyar albasa da attaruhun data jajjaga, ta fasa kwai biyar, ta kada ta fara suya da man gyara, dakko yajin ta ta yi mai tafarnuwa, data soya ɗaya ta dale kujerar kitchen ɗin ta cinye, a haka tai tayi har sai da ta qoshi sosai.

Sannan ta hadawa Khaleefa nashi, ta kai dinning ta aje, ta san ko sallah bai ba, tinda baya kwantawa da wuri,yana aikin sabon Allah, haka zai makara wataran sai alarm ya buga ya farka, kuma sai ya sake bata lokaci wajen wanka, sa kaya sannan a jefe sallar a fita a ci abinci a fice.

Daki ta gudu dan bata son su hadu, amma yau Khaleefa baya jin fita ko ina, yana son ya fanshe daren jiya da bai samu yanda yake so ba, shi kuwa ba wai mai hakuri bane akan wannan harkar, gashi sunyi fada da mutuniyar tashi, balle ya je mata.

Bari ya gani in yarinyar nan ta iya yin girki yau a kan ta zai fanshe, in kuma batai ba sai yaje ya yi kallo har ya samu yanda yake so.........

*wayyoooo wa zan aika yaje ya fada ma Aeeshaa taje ta kwashe abincin dinning? Ga azzalumin nan zuwa😨😨😨😭*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 13

Sai da ya shirya tsaf, ya tabbatar ba wani qazanta a jikin shi, har da tirare sai da ya fesa, ya sake brush, sannan ya nufi dakin, ya daga hannu zai qwanqwasa ya tsaya, kakarin amai ya ke jiyowa a ciki, wai meke damun yarinyar nan ne? Kamar zai koma ya daure dai ya bude qofar, tana toilete so bai gan ta ba, shiga yayi tare da toshe hancin shi, dan tsakanin jiya da yau ya tsani ya maimaita ganin amai.

"Kin je kinci wani abun ko?"

Cikin nishi da kuma zazzabi da take ji ta daga kai ta ga yanda ya toshe hanci yake qyanqyamin ma ya isa gare ta,

"Wainar flour naci, na sha tea ban sani ba ko qarnin madarar ne ke sani amai,"

"Ke kk sani, kije garin kwadayi ki kashe kan ki,"

Juyawa yayi ya fita, ya koma dakin shi, ya shirya, dan ba zai wani zauna ba tana faman amai, gwanda yaje su daidaita da Rebecca ya dan yi buyagi yayi fushi a shirya a bashi abubuwa.

Tin da ya fita take kwance tana kuka, wai bata da lafiya ko zancen kaita asibiti baya yi, gashi ita ba wanda zata fadawa, iyalin ta basu damu da ita ba sam,Hajja ce ke damuwa da lamarin ta,ita kuma ta rasa me yasa kwana biyu bata neme ta ba bata zo ba.

Yunwa take ji amma bata san me zata ci ba, kuka ta sake fashewa da shi, wannan wace irin rayuwa ce.

Haka rayuwar Aeeshaa ta ci gaba ita da Khaleefa, a cikin wannan halin quncin, da takura, Ameena ta zo mata inda tai weekend ta koma, cike da farin ciki, yanzu amai da tashin zuciya ya ma Aeeshaa sauqi,sai dan banzan kwadayi.

Yanzu cikin Aeeshaa ya kai wata uku ba tare da ta sani ba, Khaleefa kuwa dik wata hanya da zai hana mutan gidan su zuwa yi yake, saboda yanda Aeeshaa ta rame tayi fari kamar mai tsutsar ciki, baya son a gan ta a haka, Hajja kullum sukai waya sai tace masa in bai kai mata Aeeshaa ba zata zo ta ci mai uwa a gidan, kullum qarya yake zabga mata, yau basu nan suna Abuja shaqatawa, gobe suna Kaduna, in tai waya ya ba Aeeshaa sai ya tsare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login