Showing 63001 words to 66000 words out of 69262 words

Chapter 22 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1038

Hassana sai na falla maki tafi gaban mijin naki ni ba qaramin aikina bane kin sani, dan uwaki inna zama taku kuka zama na Allah ai na shigangadi,"

Dariya akai tayi cikin nishadi da so da qauna.

Ameerah ce ta farka daga baccin da take a jikin Maman Khaleefa, sabods hirar da ake ta yi, tana farkawa ta fara baza ido, akan Aeeshaa idon ta ya tsaya, can ta qara juyawa tana kalle2,tana hango Sabeer ta bangale bakin ta da yake dauke da haqora jefi2, ta sa dariya tare da furta,

"Baabaa,"

Shima dariya yayi ya je ya dauke ta, kowa kallon su yake cikin sha'awar hakan, ba kamar Aeeshaa, da har wata kwalla ce ta taru mata, tana jin dadin bond din dake tsakanin su, kusan kowa yaga farkawar ta, kuma sun kula da abinda tai.

Kitchen ya wuce da ita ya hada mata madara, yana bata, tana ta masa surutai yana amsawa kamar ya gane me tace, sai da ta qoshi ya dawo da ita, suka zauna a ka ci gaba da hira.

Hajja ce ta fita, ta je bangaren su Khaleefa, yana zaune yana bin karatun qur'anin da ya kunna,qira'ar Manshawee na babba da yaro, wanda ake yi kamar ana koyar da yaro, Hajja taji dadi sosai d sosai, tana shiga da sallama, ya daga kai ya kalle ta, rungume shi tayi ta dade a hakan tana jin son jikan nata na qara ratsa ta, shima haka, dik wani haushin ta daya ke dan ji dik babu ko dugo daya,(daya daga cikin amfanin runguma kenan) a hankali ta zare jikin ta daga gare shi ta zauna.

"Khaleefa Allah ya maka albarka, ya qara kare mana kai daga fadawa sharrin zamani,na ji daɗi fiye da yanda kk tsammani, akan daidaituwar ka da lamuran ka,Khaleefa ka zama jika mafi soyuwa a zuqatan mu bayan Aeeshaa, ina son baya ta zauna a baya, yanzu kai facing gaba, ka kyautata gaban rayuwar ka, na sani ko a da akwai laifin mu a wajen lalacewar ka, ina son a yanzu za ka nuna mana akwai hannun mu wajen gyaruwar ka,komai da muka umarce ka kana aikatawa daida iyawar ka,sai abu daya ka gaza akai,"

Daga ido yayi yana kallon ta tare da tina me ye suka ce yayi bai ba a yanzu dai kam, bai gan shi ba.

"Hajja me ne kuka sani wanda ban ba a yanzu?"

"Shiga cikin 'yan uwan ka, sake fuska a tare da su, yin nishadi a cikin su, sada zumunci da. sallama a tsakanin ku, ka dai na qunta ta kan ka a waje daya, dik da ba zaman banza kk ba karatun qur'ani ka ke, amma shi zumunci shima yana da lada,dan Allah ka sakewa qannen ka, suji dadin babban yaya,daure masu da kk bai da amfani, kai a takure su a takure, plsss for Allah's sake,"

Shiru ya dan yi na wani lokaci daga baya ya numfasa yace

"Hajja a da son girma da kuma girman kai ke hana ni shiga cikin su, kuma yasa nake daure masu fuska, sannan ina daure wa ne kar wani ya shiga rayuwa ta mu shaqu ya san me nake aikatawa,amma a yanzu ina qin haduwa da su ne saboda kunyar abubuwan dana aikata a baya,"

"Habaaa Khaleefa ai kasan ku din gaba dayan ku gadon hankali ne, da nutsuwa, tare da karrama mutum, yau ko kafurci kayi ka dawo musulunci 'yan uwan ka zasu karbe ka hannu bibbiyu, dan haka kar kaji komai, yanzu ka tashi muje ayi hira da kai, an saka maku ranar aure daga nan zuwa sati biyu, ka sake ran ka,ka daina daure fuska, kaji, baka san da biri kk kama ba in ka daure fuska ko?"

Dariya yasa sosai, dan in ba son kai zai ba har matan gidan bayan Aeeshaa da Bilqis yafi kowa kyau,

"One zero Hajja, zan rama ne,"

"Sai dai ka rame, dannema mai goshi kamar an qunsa gorubar nera sha biyar,muje a fafata da kai,"

Fita sukai,sai sa shi dariya take har suka isa bai kula bama, yana ta babbaka dariya, itama tana taya shi, shiru wajen ya dauka, kowa ya nutsu ganin Khaleefa, dan baya wasa da kowa, Aeeshaa cikin sanda ta fada daki, Hassana ma tashi tai zata fece yace,

"In kin shiga ki kira ta ku dawo nan,"

"Nnaa'amm?"

"Eh cewa nai ki kira ta ku dawo nan,"

"To to bari na kira ta,"

Waje ya samu ya zauna, ya gaida iyayen shi mata dake wajen, sannan ya bama su Sabeer da Ammar hannu suka gaisa, Sabeer ya kalla yaga yanda Ameerah ta maqale shi, surutu kadan tace "Baba", yace "Na'am 'yar baba"

Murmushi yayi mai ciwo, YA MAKARO, ya rasa wannan damar ta zama uba a gare ta, amma ba zai cire rai ba wataqila a gaba ta so shi, koda kuwa taji me ya aikata.

"Gamu"

Sake gyara mayafin ta tayi, ya rufe har kan ta, dan nauyin shi take ji musamman da ta ga ya sauya halayen shi.

"Na zo nan ne saboda na nemi gafarar dik wanda na sabawa a cikin ku, musamman ke Aeeshaa da Ameerah, dik da tayi qanqanta ta san ina neman gafarar ta,amma na tabbata in kk yafe min itama zata yafe min ko a gaba ne, ina roqon ku gafarar dik abinda na maku physically and emotionally, ina son ku karbe ni a matsayin Yaya, wanda zai kula da ku da kare ku daga dikkan cutarwar da zai iya, ku dauken a matsayin aboki wanda zaku yi hira kuyi raha da shi, inshaa Allahu dik wani halina na baya mara kyau ba zaku sake ganin ko jin na aikata shi ba, ina fatan zan kar bu a wajen ku, a yi hirar dani nima,"

Dariya da sowa wajen ya dauka,Aeeshaa dik wani abu da ya mata ji tayi kamar bai taba yi mata komai ba a rayuwar su da sukai a baya, ji tayi koma me ya mata ta yafe masa har abada, kamar an zare mata qaya a jikin ta haka take ji.

"Na yafe maka Yah Khaleefa, Allah ya yafe mana baki daya, nima ka yafe min bisa abubuwan dana maka, musamman da cikin Ameerah,"

Dariya sukai dika tinawa da yanda take maida masa magana, dan da cikin ta fara masa hakan.

Su kadai suka san me suke wa dariyar, dan haka Hajja tayi gyaran murya,

"Alhamdu lilLAAH a gaskiya kun sani farin ciki mabayyani, yau inna koma ga mahaliccina na san na kyautata rayuwar iyalina, na basu tarbiyya cikakkiya, kuma na kula da buqatun su, dan haka ina son sanar da ku wani abu,ku yi hakuri da junan ku,ku so junan ku, saboda in baku so junan ku ba maqiyan ku zasuyi nasara akan ku, in kana tare da abokin zaman ka,kaga ya sauya, lamarin ka yana neman lalacewa, to ka so rayuwar da kk ciki, kar ka hango ta wani,

Saboda daga lokacin da dan adam zai daina son kan shi, ya fara hangen wasu yana sha'awar rayuwar su, to daga wannan lokacin rayuwar da yake ciki zata koma masa kamar wata dadaddiyar rayuwa koda kuwa bai dade a cikin ta ba. Lokacin da ya dawo baya ya fara son kan kanshi, ya bar hangen rayuwar wasu, ya fara sha'awar tashi, a lokacin rayuwar da yake ciki zata koma masa sabuwa filll, koda kuwa ya dade a cikin wannan rayuwar.

A kullum muna tina wannan sai rayuwar mu ta yi ta sabunta, Allah ya muku albarka, bari naje na huta da dan tsohon mijina nima,"

"Mun gode Allah daya bamu ke a matsayin tsayayyar uwa kuma kaka, a wajen Yaran mu,kin zama mana babban jigo, Allah ya baki babban sakamako mai kyau duniya da lahira, ba abinda zamu ce sai dai mu maki addu'ar fatan yin kyakkyawan qarshe, mun gode Hajja mun gode sosai,"

"Ummeen Sabeer yi wa kai ne,in na so kai na na zama tsohuwar banza zuri'ata ce zata lalace, inna so kaina na zama tsohuwar kirki zuri'ata na gyara,Allah ya muku albarka,"

"Ameen tsohuwa mai rannqarfe,"

Dariya kowa yayi, ta tafi, suka ci gaba da hirar su kamar me, yanda khaleefa ya zaqe yana basu labarai kamar ba shi ba, har mamaki suke dama yana tare da wannan labaran fal cikin shi yake kakkamewa yana wani daure face.

***********************

Kwanaki hudu suka rage saura ayi bikin su Hassana da Aeeshaan.

Hussaina,Hamdiyya,Bilqis, duk sun zo, da yaran su, masu gidajen su sunyi alqawarin zuwa banda mijin Hamdiyya da baya qasar yayi tafiya,dan kasuwanci, tin kan su zo Hajja ta dakko mutan maiduguri da na Sokoto(Deejee yau na fadi abun alkhairin Sakkwatawa🤣🤣🤣akwai ku da kayan mata ance) sai gyara amare ake, Ammar ya koma gida tini suna can suna nasu shirye2n, mutan Yola akwai kashe dukiya wajen aure, dan haka gidan ma da za a kai Hassana abin kallo ne ga kowa dik kudin ka kuwa, ba wai dan girman gidan ba, a'a sai dan kyau da tsaruwar shi.

Har da su Bilqis aka hade akai ta gyarawa, Aeeshaa wataran gudu take saboda yanda ake dirka mata kayayyaki, wai saboda ita bazawara ce, ana son a gyara ta sosai, yanda Sabeer ba zai banbance bazawara da budurwa ba,(na lie him go ganewa aradu, dan dai samrayi ne bai san banbancin su ba, kodake samarin fa yanzu sun san komai😨🙊).

An fitar da anko kala biyu, na dinner, da ranar yini, masu kyau sosai, amare kuwa an masu sabbin dinki har ba zan iya lissafa maku ba.

Su Sabeer unguwar su daya da Umman su, sai dai akwai nisa sosai sai ka dan hau abun hawa ko ka isa kana nishi, Baba Abubakar ne ya mallaka masa gidan, gida ne daya yake dauke da sama da qasa, mai kyau, kowanne bangare an cika shi da kaya na alfarma, komai na gidan purple da ratsin pink, hatta fentin gidan haka yake, ta waje an masa purple mai haske, gwanin sha'awa tsarin gidan.

Hadizan Goggo ma ana can ana shirye2, Hajja tayi2 Goggo ta bada ita a mata gyara amma tace kar ta damu zaqewar zatai yawa.

Dan haka Hajja ta samu wasu masu gyaran su je can ayi mata na ta, Ahmad na ta girma abin shi, an gyara masu gidan nasu, dik da ba wani matsala ke gare shi ba, amma an kwashe kayan ciki an kai ma Goggo, tana a'a a'a haka Hajja ta sa dole aka aje mata su, Baba General ya sauya masu sabbi.

Hadiza ashe baqa ce irin baqinnan mai matuqar kyau da daukan ido, amma ta bata shi da man banza, nan da nan aka dage a kan fuskar ta, sai ga qurage babu, tabo ma ba wani sosai ba, dama ita kan ta gwana ce wajen son gyaran, ana yi tana riqe dik wani hadi da akai mata amfani da shi, Hadiza an sha kayan mata anyi tatul, kun san dai mutuniyar taku ba dama.

Dangin Baban ta sun zazzo, musamman talakawan ciki, masu kudin sunqi zuwa wai tayi cikin shege, talakawan ma arziqi suka zo ci, amma a gefe sai zagin su suke, kamar ba a laifi a tuba ma Allah; kai bawa sai ka zagi wanda Allah ya yafe masa in aka hada zunuban ku ma kafishi zunibai, ko ya fika tarin lada, kana nan kana aikin zagin shi.

***********************

Yahhhhhhhhh yau ne ranar da za a fara gudanar da bukukuwan aure.................

*Yahhhhhhh i am so ready for this wedding,hummmm in kuka ga yanda na ke doki kamar nice Sabeer, dan na kula yafi kowa son auren, ko akwai wanda ya fishi?*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 30

Tsayawa fadin yanda bikin mutane shidan nan ya wakana ma a gaskiya bata lokaci ne, domin kuwa wannan dan qaramin page yayi kadan, sai dai zan so mai karatu ya hango irin dukiya da aka kashe da kuma qayatuwar wannan bikin, komai yaji sunan shi.

Hajja itama har irin kwalliyar nan ta zamani sai da akai mata, Baba General kuwa ya dinga tsokanar su Aeeshaa da cewar Hajja ta fisu zama amarya, suje su qara yin kwalliya mai kyau.

Ameerah na maqale da Sabeer, an mata gayu sosai, gashin ta ya sha gyara, saboda yarinya ce mai tsaho da cikar gashi, kowa ya gan su sai yayi sha'awar su, Ahmad kuwa yana riqe a hannun Bilqis, kowa yayi kyau masha'Allah, shirin tafiya dinner ake, wanda daga nan angwaye zasu dau matan su su wuce da su gidajen su, ba wani maganar kai Amarya, Hassana kawai za a kai zuwa Yola, (garin fulani gari mai tarin albarka❤).

Kowa ka gani dauke yake da tsananin farin ciki,Hassana tayi kuka tayi kuka har ta gode Allah,kukan farin cikin yau itama an daura auren ta da wanda yake son ta, take son shi, kamar sauran 'yan uwan ta, ashe aure lokaci ne ba wai sanda mutum ya ke son shi yake samu ba, Ammar sai lallashin ta yake, sai tayi shiru, da an gabatar da wani abun a wajen sai idon ta ya ciko da kwalla.

Dik abinnan da ake Hadiza Allah2 take a tashi, wato maganin nan da tasha ne ya fara aiki, sha'awa ce ke mugun dawainiya da ita ba kadan ba,da dai taga kowa sake sabin nishadi yake ba babba ba yaro,ta radawa Khaleefa a kunne, kan ta na ciwo su je gida.

Jimmm yayi yana tinani,yanzu dik idon mutane na kan su sai a neme su a rasa? Gaskiya yanzu ya san meye kunya, ba zai iya fara tashi ba.

A dayan bangaren Sabeer ma ya matsu su bar wajen kunya kawai yake ji, shine abinda ya hana shi tashi da amaryar shi, dan haka sai watsa ido yake ya ga wani daga cikin 'yan gidan su da zai iya cewa su tafi,ba tare da yaji kunya ba.

Baba General shine mutum na qarshe da ke sanar da taron labarin yarintar Khaleefa,Hassana, Sabeer da Aeeshaa, kowa na wajen dariya yake saboda labaran da Baba General ke bayarwa,Khaleefa kunya dik ta kama shi, mutane sai kallon hotunan su suke da suna yara, Sabeer kuwa hankalin shi na kan Aeeshaa da ta dage tana dariya, tare da tausayawa kan ta, ba wasu labarai akan ta masu tsawo, saboda kasancewar bata tashi sosai a cikin su ba.

A qarshe Baba General ya ba ango da amarya damar tafiya gidajen su in suna da ra'ayin tafiya da wuri.

Hadiza ce ta miqe tsaye, duba da yanda mutane ke kallon ta ne yasa ta wayance da kama goshin ta alamar ciwon kai, tare da riqe bayan ta,nan da nan Khaleefa ya tallabe ta, sai tausayin ta kuma ya kama mutane, da alama ta gaji ne.

Sabeer na ganin sun tashi shima ya miqe, Ammar da Hassana suka mara masu baya.

Suna fita farfajiyar Hotel. din da aka gabatar da event din Sabeer ya daga Aeeshaa har zuwa bakin mota, sai zillo take saboda kunya, amma yaqi sauke ta, murna kawai yake kamar ya gan su a gidan su yake ji.

Hadiza kam tin a mota ta kwanta ma Khaleefa a jiki tana shafa shi, Allah2 take su isa gida, sanin halin mutuniyar tashi ne yasa shi kama hannun ta daya yana murzawa a hankali.

Hassana kuwa gida suka fara komawa, a daren zasu wuce Yola ta jirgi, tare da su Bilqis Hamdiyya Hussaina, da Maman Khaleefa.

Khaleefa da hadiza sun isa gidan su lafiya nan suka tarar da koma kamar sabo, ga sabon mai gadi, tai saurin maqalewa a jikin Khaleefa, da kyar ya kwaci kan shi, sai ta fashe da kuka.

"Da na san haka maganin mata yake da ban sha ba, dik iskanci na da ban taba shan shi ba, ban san ya ake ji ba, wayyoo Khaleefa dan Allah muyi sauri, kar na mutu."

"Subhanallahi, mutuwa fa? Ahhh ba zaki mutu ba, bari muyi sauri mu gabatar da sallah domin godewa Allah, sannan kar ki manta bamuyi magrib ba ga Isha'i ta yi, ina ga zai fi kyau mu fara gabatarwa ko?"

Kuka ta sake saki, dan kuwa akwai matsala, a mugun matse take, Khaleefa bai biye mata ba wannan karon bayan sallah da nafila harda addu'a ya ma matar shi, ai yana idarwa Hadiza ta dale cinyar shi ta fara kissing din shi, Khaleefa mai tsananin sha'awa, nan da nan ya fara karbar saqon ta, sai dai wani babban al'amari daya same su, shine ga sha'awa sosai, amma gaban Khaleefa yaqi tashi yanda yake yi da, ya yi rauni sosai.

Sosai Hadiza ta shiga tashin hankali da damuwa, wanda ya sa na kasa gane tsakanin su biyun wa ya fi shiga damuwa?

Da kyar Khaleefa ya samu ya yi harkar nan, qarshe daya samu biyan buqatar shi Hadiza bata samu ba sai romancing din ta yayi ta biya buqata.

Abun ya basu mamaki, amma daga baya daya tina aikin banzan daya yi aikatawa da kan shi yana biyawa kan shi buqata, sai yaji ya cancanci dik wani hukunci da Allah zai saukar masa.

(Biyawa kai buqata na raunana gaban namiji,ko ba jima ko ba dade, a kiyaye,mace kuwa yana buda ta ta rasa budurcin ta wallahi, kunji rantsuwa kenan ta musulmi, sannan yana kawo infection both maza da mata, shi yasa nake mamakin masu lesbian suna manta wa da cututtuka ne bayan zunubin da suke ɗaukar wa kan su ko duk sun shirya shiga wuta da kuma karbar ciwukan da za su riske su a gaban rayuwar su?)

"Ka kula da abinda ya faru kuwa? Garin ya haka gaba daya ka kasa komai yanda ya kamata? Innalillahi na shiga uku ni Hadiza, yanzu haka rayuwar mu zata kasance?"

Rungumo ta yayi yana shafa jikin  ta.

"Inshaa Allahu ba haka zamu kasance ba, zan nemi magani, bana son na tauye maki haqqin ki ta kowanne fanni,inshaa Allahu zan dage na nemi magani, ki taya ni addu'a,"

Kauda kai tayi tana share hawaye, lallai sun aikata babban kuskure a rayuwar su.

*******************

Koda sabeer suka shiga gidan su da sauri ya bude mata mota, wannan karon kafin ya dauke ta ita ta maqale masa wuya, aiko cikin doki ya daga ta sama, a bakin qofar shiga parlour ya ajiye ta, ya bude masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login