Showing 36001 words to 39000 words out of 69262 words

Chapter 13 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1041

kuma ki ke kan ci ma? Na taɓa d'aga kai na na kalli me wannan yaron ke maki? Kin girma kina aikin jahilan yara, dibi fa girman Khaleefa ɗan ki ne, kin ko san ke ba ta yau bace ko? Hakan bai sa kin nutsu ba wai kk zuwa roqo gidan danki? Tiiirrr da halin ki na ji matuqar kunya da ya kirani yana fad'an abubuwan da kk masu"

"Hajja qarya yake min ban ce zan tsine masa ba, tambayi Aeeshaa,Baba kuyi hakuri ban kyauta ba,ku yafe ni,"

"Kin ban kunya, Maman khaleefa, me na rage ki da shi? Wannan ai qasqanci ne, da kuma tozarci, ki zo gidan suruka kina wannan abun, Aeeshaa fa diyar ki ce in akwai mutunci da kara, diyar qanwata ce fa,amma kk wannan zubar da qimar a gaban ta,kin ban kunya gaskiya,"

"Gwal da kk sa wa ido ni na sai mata, ni na bada kudi aka siyo mata su, kayan d'aki da na lefe da komai da kk gani Hajja ce ta je da kan ta ta siyo su, wasu ta bada izinin a shigo dasu daga waje, da kudin mu muka aura wa Khaleefa ita mukai komai, sisin shi babu, in banda yaro ne mai biyayya itama yarinya ce mai biyayya ba son juna suke ba mukai had'in, amma yanzu ba gashi komai ya wuce masu ba, ba za ki gode Allah da zaman lfyn da suke ba sai kin yi wannan qasqancin? Ashe in ba a tsaida ke tin yanzu ba har gidan yaran ki.mata sai kije ki saida daraja da mutuncin ahali na ko?"

In ji Baba General da ya kafe ta da ido.

Nadama ce mai yawa ta shige ta, nan da nan ta fara kuka tana bada hakuri akan halayyar data nuna ta son zuciya, ashe in kana da manya ba zasu barka ka yi rayuwa mara kyau ba komai girman ka, ba dan khaleefa ya kira su sun tsawatar mata ba da bata san inda mugun halin nan zai tsaya ba,

"Allah ya maka albarka da ka kira min magabatana, suka nusar dani illar abinda nake shirin aikatawa,Aeeshaa ki yafe min d'iyar albarka, gaskiya khadeeja ta yi qoqarin baki tarbiyya mai kyau, Allah ya saka maku da alkhairi, a gaskiya naji kunyar wannan mummunan abun dana aikata,"

Hawayen nadama ne ke zuba mata, Khaleefa ke ta latse video call din da Rebecca ke ta damun shi da shi, tin ba wanda ya kula har baba General ya kula,

"Go and answer ur call,"

A tinanin su tsabar ladabin shi ne yasa bai son amsa waya suna magana mai mahimmanci.

Qauri ne ya tirniqe gidan,da sauri Aeeshaa ta tashi ta nufi kitchen, farfesun zabbi ya qone, kunya ce ta sake kama mama,dan ta san dan ita aka dora abinda tafi garfin shi.

"Don't call me i am with my parents,"

"K zaka shigo?"

"No"

Abinda ya fada kenan ya kashe wayar,Hajja ce ta kalle shi, wani abu ya darsu a ran ta game da wayar da Khaleefa yayi,

"Wa ce ta kira ka?"

Tambayar data jefa masa kenan, cikin daburcewa da in ina ya ke amsa ta,

"Aaaaboookiiyar aikinaaa ce ta take tambaya ko zanje office yau,"

"Oookkkk, me zai sata kiran ka? Ko sama take da kai a wajen aikin?"

"Eehhhh itace babba dika wajen,"

"Oookkk"

Abinda Hajja ta faɗa ke nan tana ci gaba da kallon Khaleefa, akwai wani abu a qasa.

Ba zai iya jure wanan kallon na kusan kama barawon ba, tashi yayi ya bi bayan su Aeeshaa.

"Wannan amarya kamar a qauye,kin dora abu tsabar kin ga na sha kwalliya kin kasa dauke idon ki akaina shine kk babbake tukunyar da kk dorawa megidan abinci, dariya Mama da Baba suke, inda Baba ke kade hannun shi dan wajen taimaka wa Aeeshaa ta sauke tukunyar da tai baqi ya qone, Mama kam jikin ta qaura yayi isha'i, sai yaqe kawai take,Allah2 take a bar gidan kunyar su take ji yanzu.

Nasiha Baba General da Hajja sukai masu sosai, sanan suka sake yi ma mama gargadi da nasiha itama, wadda sai da ta sa Khaleefa ya ji ba daɗi shi ya janyo mata wannan tonon asirin, amma gwanda daya mata hakan, da ba dan haka ba da ba zai samu sakewa ba a gidan shi, kuma ba zai samu sakewa ba wajen zuwa yawon shi, dan yasan Mama in ta qafdari zuwa gidan, ba zai dinga sakewa da iyalin shi ba,kuma ba zai sake ba da kallace2n shi komai a darare zai dinga yi,sannan zuwa wajen Becca zai na masa wahala, so gwanda ya yiwa tufkar hanci.

Baba General sai da ya bama Aeeshaa kuɗi yace koda zata yi wani abu da su tinda ga ciki tana ɗauke dashi, sannan suka tafi,Hajja na qarewa Khaleefa Kallo, kallon ina ganin ka,kome kk qullawa zan binciko.

Dauke kai yayi, yana qoqarin saka fuskar shi ta ba abinda nake aikatawa mara kyau, rungume Aeeshaa yayi a gefen hannun shi, yana daga masu hannu bayan sun shiga motocin su, Hadiza na ganin manyan motoci suna wucewa sai zare ido take, ta qara tabbatar da lallai su din masu hi ne, burin dake ran ta sai qara habaka yake,yana qara girma.

Har zasu rufe gate din, ta yi saurin fitowa daga soron gidan nasu, tana taku daidai.

"Hadiza, kina gida dama? Dan Allah amson quli na dari biyar wajen Goggo in kin kawo na baki kudin,"

Wani kallo khalefa ya watsa mata, akan me zata masa gayya bayan ta kula da yanayin shi yana buqatar ta.

Shigewa ciki yayi, ita kuma ta sake iskar bakin ta, sarai ta gano shi, ita kuwa she is not ready, haka kawai bai da aiki sai yayi ta....... ba zata iya ba gaskiya.

Gudu2 sauri2 Hadiza take diban qulin nan dan ta kai ma Aeeshaa,fatan ta Allah ya sa khaleefa ba fita zai ba su hadu.

"Ina zaki ne kk sauri haka?"

"Amarya ke son quli na dari biyar,"

"Tam ki kyauta mata, ki kuma gaida min ita,"

Gudu2 take tafiya har ta kai soro,

"Za ta ji,"

Koda ta isa gate buɗe yake, dan haka shiga kawai tayi, sai da ta dan gyaggyara sanan ta fara kwankwasa qofar, Aeeshaa ta je fitsari, dan haka Khaleefa ne ya bude qofar.

Tana ganin shi ne,ta wani narke, tana lashe lips, tare da cizar lip din ta na qasa, tana wani kada ido, da banqaro qirji, ta miqa masa,

"Kace mata ta bar shi, Goggo na gaida ta,"

Khaleefa fa ya tafi da wannan salon, a iya sanin shi da mata in mace na haka tana son kasancewa da namiji ne, lallai wannan 'yar hannu ce, za a je da ita.

Hannu ya miqa dan karba, aiko wajen bashi sai da ta san yanda tai ta goga hannun ta sosai a nashi, wani abu ya ji ya jashi, nan da nan ya sakar mata murmushi, wayar shi ya zaro da sauri, yace ta sa mashi no ta, ba bata lokaci ta saka kuwa ta miqa masa, murmushi suke sakar ma junan Su,

"Hadiza kin kawo? Ga kudin, yi hakuri na dan zaga ne,"

"Ba komai zan bata koma ciki, na hana ki yawo a gida da wannan qaton abun ko, wuce ki je ki sauya, itama tafiya zata yi, bana son ana takuramin a gida,"

Jiki ba kwari da kuma kunyar hadiza a ran ta ta bar wajen, yanzu a gaban maqota ma sai ya nuna halin shi, kuma a fakaice yana nuna ma Hadiza kar ta na zuwa masu gida fa kenan.

Bayan ta shiga ciki ya rage murya.

"Zamuyi waya, zan fada maki inda zamuna haɗuwa,kinyi min"

"Nima ka yi min,ina jiran ka,"

Juyawa ta yi tana tafe tana rausaya, Khaleefa ya gama kwadaituwa da Hadiza kwarai Allah2 yake dare yayi, yau in bai kadaita da Hadiza ba akwai matsala..................

*Ina da tambaya, shin kuna ganin akwai miji kamar Khaleefa? Ko kuwa kuna ganin Inaaa ba za a samu miji haka ba? Ina jiran ra'ayoyin ku, koda kuwa da labari ne na makamancin halaye irin na Khaleefa*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 16

Daki ya wuce tare da rufe qofar shi, dik da ya san bata shigo masa d'aki sai ta nemi izini.

Hadiza na shiga gida ta zauna ta gilla qarya, wai ba canji shiyasa ba a bata kudin ba.

Tana zaune wayar ta tayi qara, waya ce da zata kai dubu talatin da 'yan kai, Goggo tayi fadan tayi lallashin akan ta sanar da ita inda take samun kudi amma sam taqi,in fita zatai Goggo ta hana ta sai ta fita, dan gani take ai yanzu ta girma, tinda zawarci take,bata ga dalilin da zai sa a kulle ta a gidan ba.

Da sauri ta miqe ta shige dakin ta, ta rufe qofar, kwantawa tayi a gadon ta, dan ko bata san waye ba tasan ba za a rasa daya daga cikin samarin ta da take harkar ta da su bane, a ido in ka gan ta sai ka rantse da Allah ba zata aikata zance bama ba da izinin iyayen ta ba, dan ko mayafi zata saka manya take sakawa, ga wanda bai san ta ba sai ya fada tarkon ta.

"Helloooo"

Ta furta, cikin wani irin salo, mai tafiyar da numfashin wanda ya saurare ta, aiko ta samu nasara, dan kuwa Khaleefa har da qanqame wayar yayi ya kwanta,

"Heyyyy"

Shima ya maida mata in a husky voice, cije lip din ta tayi na qasa, lallai guy dinnan ya hadu matuqa.

Nan da nan hira ta barke tsakanin su, a hankali ya fara tambayar ya take, tana ina, a kwance take ko a zaune???? Dik tambayar da ya mata sai ta tabbatar ta saka ta ta yanda zata tada masa da sha'awar shi, kuma ta samu nasara matuqa, Khaleefa ne ya fara qoqarin kai ta duniyar da ba a taba kai ta ba ta waya.

Nan da nan suka fita hayyancin su, Goggo na can na kwada mata kira taje tai alwala tai sallar magrib ko jin ta bata yi ba.

Ba su rabu ba sai da Khaleefa ya ce gaskiya ya kamata yau dinnan su haɗu,

"Ba komai, zuwa bayan magrib, ka fito da mota zan fito sai kawai na shiga muje dik inda kk so,"

"Wowww u ar hot babe, kin haɗu gaskiya, ina me tin da ban kula dake ba?"

"Laifin wa?"

"Laifi na gaskiya, dana hana ana shiga min gida, da tini na gano ki ashe dana dad'e da kauda kwadayi na dake ashe,"

"Sosai ma,ina maka albishir zan shayar da kai zumar da baka tab'a sha ba a rayuwar ka,"

"Wowww,kinga ya isa haka jeki ki gama dik abinda zaki mu hadu, nan da 2hrs"

"K bye"

"Bye I want u so bad baby,"

"I want u too,"

Ku ji wasu kalamai da suke nuna tsantsar inda suka dosa ba boye boye, sun tabbatar wa da kan su ba son juna suke yi ba, sabon Allah kawai suke da burin aikatawa.

Kashe wayar sukai inda Hadiza ta sake wani shegen ihun daya sa Goggo zuwa qofar dakin tana bugawa a gigice.

"Hadiza meke damun ki? Ko gamo kikai ne? Tin dazu ina ta kiran ki kizo ki alwala naji shiru, sannan yanzu naji ihu?"

"Goggo wani qaton bera na gani amma ya fice,"

"Ohhh Allah ya shirya ki, yanzu meye abin rufe qofa da yamman nan? Na hanaki sarar rufe qofa ki shige daki, ba fata ake ba in wani abu ya same ki fa?"

Budewa ta yi ta fito tana turo baki tana banqara,

"Goggo anjima inna yi sallah zan leqa amarya ban san me zan mata ba dai ta roqen naje, kin san cikin ta ya fara nauyi,"

"Allah sarki 'yar aljanna, yarinyar nan ina son ta ba dai hakuri da kauda kai ba, mijin ta da gani zai masifa duba da yanda yake kullen ta, maza masu kulle yawancin su azaba ne da su, wasu kuma kishin tsiya, wasu basu da halin kirki suna tsoron kar a ma matan su abinda suke ma na wasu sai suna kulle,ita dai ta hakura ta jure, Allah ya bata lada,"

Juyawa Hadiza tai ta kada ido da murguda baki, tace

"Ameen,"

Wanka ta shiga,ta fesa wanka, tayi sabon askin hammatar ta gaban ta da dik inda ya dace, ta samu musk din ta fari ta shafa har gaban ta, ta samu aloevera da suke da ita ta bare gel din ta matsa a gaban ta, can ciki, (domin matsi) sannan tayi alwala ta fita.

Sallah tayi, ta samu mayukan ta na bleaching ta shafa, sannan turaruka, dik wani angle a jikin ta sai da ta shafa masa turare, bata yi kwalliya ba gudun zargi amma ta shafa powder, da mai a lips din ta.

Sallama tayi dakin Goggo ta ga tana sallah, kawai sai ta fita abin ta, flashing ta manna masa, yana gani ya miqe, dama a shirye yake, Aeeshaa na ta hada table, ta wahala sosai wajen dafa masa fried rice, da salad da pepper meat, ta masa drink na gwanda, wanda ya sa ginger da lemo, ya yi kyau a ido ga dadi a baki, sai zufa take dik da AC dake parlour, ga cikin ta da yakai wata shida, dik da ba wani nauyin shi take ji ba amma aiki na bata wahala.

"Ga abinci, na gama"

"Ai na gani,ko ban da ido,"

Shiru tayi, dan yanzu ba wuya take jin haushi, kawai dai bata nuna masa ne, amma shi kan shi ya san akwai sauyi sama da da can, da in ya mata abu zata bashi hakuri.

Ji tayi kamar ta watsar da abincin, zama tai a daya daga cikin kujerun, can kuma ta miqe ta bi shi dan rufe gate.

"Ina zaki? Koma, ki barmin a bude inna dawo zan rufe, ban key din,"

Baki ta bude sosai dan mamaki, for the first time tin da tazo gidan itace mai gadi, yau me ya same shi ya ce zai bude ya rufe da kan shi?

"Bani mana, naga kin yi aiki ne kawai kin gaji ba wata tsiyar ba, in kuma baki son taimakon sai kije ki ci gaba da bude gate da rufewa,na dauke maki budewa da rufewa daga yau,"

Miqa masa tai, tare da dan yin murmushi, ko ba komai yau ya mata mutumci, as a brother ba miji ba.

Komawa tayi, sai da ya tabbata ta koma sannan ya fice, waya ya mata yace gashi nan, aiko ta leqa kai ta gan shi, da hannu ta masa alamar ya matsa daf da gidan su, yana zuwa ta bude ta fada ciki ta duqar da kan ta,barin unguwar sukai kwata2, suka nufi wata unguwar nesa da tasu, a wani qaton fili yayi parking, anan suka fara buga masha'ar su, Khaleefa ya ji nutsuwa da ita amma Aeeshaa ta dabaan ce, Aeeshaa is so sweet and tight, komai nata a cike yake, Hadiza ma ba laifi, zai iya hada ta da Beccan shi, wajen gwanancewa a karuwanci, da salon tafiyar da namiji, wanda Aeeshaa kwata2 bata iya shi ba,ita ko kiss yake mata sai dai yayi ta yi amma bazata yi masa ba shima.

Sun dade manne da juna, suna maida numfashin su,

"Yanzu kinga shikenan mun samu dabarar kebewa ko? Gaskiya kin hadu, mijin ki yayi asarar macen aure,"

Wani walll tayi da idon ta, tana shafa shi,

"Ka daina ziga ni, na kai amarya ne?"

So take ta ji iya inda ta kai dan ta san mulkin da zata zuba masa

Wata bangaza ya mata da ta sa ta buguwa da marfin qofar motar, qarar azaba ta sake, ta daga kai ta kalle shi,

"Getout !"

"What?"

"Get the f***k out of my car,"

"Why? What did i do? Ohhhh ka ci moriyar ganga ko? Shine zaka yada kwabren ta, baka isa ba Khaleefa, in masifa kk ji ko kk taqama da ita ni na fika, ko kuma kana zaton ni matar ka ce da kk......"

Tauuuu taji wata walqiya ta gilma mata,

Nan take ta kula matar shi ce baya son a kira, kuka ta fashe da shi, na kissa da shagwaba, tana yi tana goga jikin ta da girgizawa, Khaleefa ya lallashe ta ainun, amma ba zai dauki iskancin kira masa mata ba a wajen kowacce karuwa.

"Kin daina jin hausa ko turanci ko? Bance ki fita ba?"

"To ni na san laifin dana maka ne? Haka ake hukunta mutum ba tare da ya san laifin shi ba? Ba inda zani, yanda ka dakko ni haka zaka maida ni, kuma daga yau alaqar mu ta yanke,"

Duqar da kan ta tayi tana kuka mai cike da sauti mai daɗi, yanda dik kauda kan shi sai da ya saurare ta, rintse hannun shi yayi da idon shi, tare da fusrzar da iska mai zafi,

"K kiyi hakuri, muje gida, amma daga yau sai yau, ko me zai faru ko ya faru kar ki sake saka sunan mata ta a bakin ki, balle har ki hada kan ki da ita,mata ta tafi qarfin wata ta hada kan ta da ita,"

'Munji mun gani, a hakan kk mana sadaka da......aikin banza kawai, kuma baka daki banza ba, zan nuna maka na dad'e ina zawarci na san kan kowanne dan iska'

Kukan kirsa ta ci gaba da yi sannan tace,

"To kayi hakuri, inshaa Allah na daina, muje gida, kar a fara neman mu, 10 ta gota fa,"

"Ke ce baki saba kaiwa haka a waje ba ni kam ai na wuce wajen,"

"Koh?"

"Yes,"

Sai da suka qara tattabe junan su sannan su ka koma gida, kuɗi ya bata masu yawa tai ta godiya, a nesa da layin su ya aje ta, ta taka a qafa ta koma gida.

Shi ma ya dau hanyar gidan shi, sanda ya shiga Aeeshaa bata parlour, ta ci abincin ta ta yi sallah tai wanka da brush ta kwanta, riga ce mara nauyi a jikin ta mai faɗi, amma bata da tsaho sosai, gashin ta sanye cikin hula, sai baccin ta take, kallon ta ya dad'e yana yi kafin ya ja qofa ya koma dinning, abincin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login