Showing 45001 words to 48000 words out of 69262 words
Chapter 16 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
zai dora idon shi ya kalli Ameerah ba ta kwanta mashi a rai ba, ba dan wai tsananin kyau ba, kawai haka Allah ya yi ta, har wanka Umma ke yi mata, sai dai a idon mutane ba ruwan ta da Aeeshaa balle wata Ameerah, da an ragu zata dauke ta tayi wajen su Sabeer ta mata wanka, ta gyara ta, taba Hassana ta maida ta ciki.
Yau su Hamdiyya, Bilqis,da Hussaina zasu koma gidajen su, bayan sun cika qanwar tasu da abubuwan gyara dan taimaka mata ta dawo kamar sabuwar amarya, sun gama shiri tsaf sun ma kowa sallama, zasu tafi Hajja ta fito dan yi masu sallama, Aeeshaa na ɗauke da Ameerah a kafad'ar ta,sai d'aga masu hannu take ta na jin kamar kar su tafi.
*********************
Dare ya yi, Khaleefa ya kasa samun nutsuwar dayake nema, Hajja ta hana Aeeshaa daukan wayar shi,Aeeshaan kuwa ko a jikin ta, dan ko ba komai ta samu hutu itama da jarabar shi,IG ta shiga tana kallon pictures, suna ta gani farkon kamar Hadiza, kuma can qarshen kamar wani yare daban, amma ga hoton Hadiza nan a jiki.
Dannawa tayi ta shiga, sai duba picture take, hotuna ne masu mugun kyau, kamar ba Hadizan data sani ba, kayan dake jikin ta kwata2 ma ita bata taba ganin ta da su ba, kaya ne masu tsada, daga jaka har tufafin da takalmi zuwa agogo, to ko dai kama ce ba Hadizan data sani bace, gidan ma da akai hotunan bata gane ko daya ba, dan ba gidan su bane, wani video da Hadizan tayi ta qawata shi da flowers dan kar a gane inda take ne ya tabbatar wa da Aeeshaa tabbas Hadiza ce, dan a parlourn ta akai videon, sai hotuna da ta dauka a dai2 dinning table, kuma da alama wannan rigar ta Khaleefa ce ga hular shi nan akan Hadiza,tana wani karairaya, tana fadin ta kusan yin aure masoyan ta su sanya mata albarka, nan ba da jimawa ba zata turo masu hoton mijin da zata aura.
'Ikon Allah, amma wannan parlourn kamar nawa, kuma rigar Yah Khaleefa ce na ke gani, da hular shi, sai ta dan yafa mayafi'
Dubawa tayi taga post din ya kai kusan sati daya.
Shiru dai tayi tana nazari, can zuciyar ta ta dinga saqa mata
'In ma Hadiza shi zata aura ko a jikina sun dace, suje su qarata, balle ma na san ba shi Hadiza ke nufi ba'
Dubawa tayi taga yana online, taso ta masa magana amma sai taqi, kawai sai ta saka hoton Ameerah a status, da Dp, sai ta rubuta, (Allah ya albarkaci rayuwar ki my baby Khadeeja, AKA Ameerah)
Yana hawa, Khaleefa shi ya fara gani, murmushu tayi, tace
"Kai da Hajja taurin kan ku daya, tinda ta kore ka kaqi dawowa, itama taqi neman ka,na tabbata ko sunan yarinyar baka sani ba,ta kuma hana kowa ya neme ka, ni dai ina gida ina hutawa ta abuna, ko a jikina,"
"Sunan ta kenan? Allah ya raya maki ita,gata kyakkyawa kuwa,"
"Ameen na gd,"
"Turon hoton ta,"
"No"
"Why?"
"Saboda tawa ce ni kadai,"
"Ohhhh"
"Yehhhhh"
Sauka tai online,ranta bai mata daɗi ba, wai kenan yana nufin har yanzu bai amshe ta a matsayin diyar dayake so ba, ita kadai ta mallake ta, ba komai, ta ji ta yarda, muje zuwa, zako kaga rashin M, dan kuwa komai Hajja ta yanke kan ka kai ka sani.
Shi kuwa sai maimaita kallon hoton Yarinyar yake, saboda ba laifi ta masa kyau,
Sake hawa Aeeshaa ta yi, ta yi ta saka hotunan su na suna, wanda tayi kyau sosai,da wani irin bacin rai Khaleefa ya mata audio,
"Kina hauka kk saka hotunan ki haka? Gaba ɗaya qirjin ki ya fito, dalla malama ki cire kafin ran ki ya baci,"
"Kar ka damu muna da Omon wanke wa koda baka siyo ka kawo mana ba,"
'Wayyooo ina yiwa mijina rashin kunya, na shiga uku'
"Baki da mutunci dama, ni kk fadawa baqar magana haka, ki jira gobe kiga abinda zan maki,"
"Allah ya kaimu, zan so ganin me zaka iya aikatawa ina gaban Hajja gatana,😂😜😜"
Abun ma dariya ya koma bata, haka sukai ta Chatting da audio yana mata masifa tana kunna shi tana bashi haushi, daya kula bata masa rai kawai take son tayi sai ya sauka online.
Cikin fushi Khaleefah ya ce,
"Zaman yarinyar nan a gidan hajja ya zo qarshe, Hajja ke koya mata dik wani walaqancin da zatamin, yarinya mai nutsuwa da kamun kai, komai na aikata sai dai ta ban hakuri, ita ce ke faɗi in faɗa da ni yau, inaaa koya mata akai, Allah ya kaimu gobe,"
Balqis ce ta yi wa Aeeshaa magana dan ganin ta online a wannan lokacin,
"Ahhh Ummu ameerah baki bacci ba?"
"Auntyyy🙈 eh ban yi ba,"
"Yah d'iyata?"
"Tana lfy, ya nawa babyn? Hope kuna lfy?"
"Lfy qlou, bari gobe zan bada no ki wajen wata qawata Haermeebraerh ta samin ke a group din ta, zaki qara samun wayewa akan zaman aure inshaa Allahu, na san baki wani group dan qauyancin ki yawa ne da shi Aeeshaa,"
"Hhhhhhh aiko Adda Bilqis na gode sosai,sai da safe, ki kwana lfy,ina gaida yarona,"
"Allah ya kaimu, ki shafan kan babyna,"
Sallama sukai, a cikin daren Bilqis ta turawa Haermeebraerh no Aeeshaa, cikin sa'a kuwa tana online, nan da nan tayi adding din ta.
Aeeshaa tai sallama ta gabatar da kan ta, nan mutanen dake kusa suka amsa mata daga nan ta yi shiru ta nutsu tana kallon yanda ake shan hira a gidan, tin daga nan ta fara gane halayen mutane kala2 a duniya, kowa da irin halin shi, ita a rayuwar ta banda iyalin ta bata taba intermingling da wasu mutanen ba.
Washegari kuwa da ta tashi da sassafe ta duba sai taga hira har ta kasa bi, saboda yawa,
'To su kwana suke hira ne? Bari zan tambayi Adda Bilqis naji mutanen nan akwai surutu'
('Yan group din Haermeebrah basu surutun banza malamar su komai aka ce mai amfani ne😚🙄ba laifi wasu har gudu suke wai hira tayi yawa🤣🤣🤣🤣)
********************
Wasa2 Aeeshaa tayi wata biyu kenan a gida, amma Khaleefa zuwan shi uku, Hajja na kora shi,daga baya yace ba zai sake zuwa ba, dama yana zuwa ne dan Baban shi dake masa fada akan yazo ya bada hakuri banda haka shi me zai kawo shi, Hajja kuwa na nan tana qara bincike akan shi.
Wata ranar asabar da Aeeshaa ba zata taba mantawa da ita ba, da safe, ta hau IG, kawai tana duba picture, sai ta shiga inda taga hotunan Hadiza kwanaki, tana shiga tai ta kallon rubutu da hotunan flower masu kyau, tana kalaman soyayya, sai da ta duba pictures wajen guda biyar sannan tayi gamo da hoton daya birkita mata lissafi,hankalin ta ya tashi, tana maimaita kallon hoton dan tabbatar da anya gaskiya ne Hajja ta banko qofa cikin rudani itama, dauke da wasu takardu masu kama da hotuna a hannun ta................
*Annnnngamuuuu bammmmm* 👏🏼👏🏼
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 20
Hawaye ne ke ta zuba a idon Aeeshaa, wa take gani, yau ko ba soyayya a tsakanin su bai kamata ba abinda Khaleefa ya mata, ko ba komai mijin ta ne, sun jiyar da juna daɗin auratayya har sun samu qaruwa, akwai 'yan uwantaka a tsakanin su,
"Me ne ne? Me kk wa kuka? Mijin ki ko? Taso mu je parlour, na kira kowa kafin na shigo, mu jira zuwan su,"
"Bar abincin nan kiga mu je mu ji me Hajja ke wa kira na gaggawa haka da safen nan,"
"To Babansu amma da ka dan sha tea din nima sai na sha kasan muna da ulcer bamu san za a dad'e ko ba za a dad'e ba, zauna mu shanye kawai sai mu tafi,"
"Mu yi sauri to kar ta jira mu,"
A gaggauce suka shanye tea wanda ya sha kayan haɗi yayi kauri, suka fito a tare, a hanya suka hadu da Hassana da Baban Sabeer da Ummeen shi, gaisawa sukai sannan suka rankaya.
Hajja da Baba General na zaune dik inda ran su ya ke ya kai qololuwa kuma qarshe wajen ɓaci, gaban su Baba ne ya dinga faduwa dan ganin yanayin iyayen nasu, yau me ye wannan ya faru mai tsanani haka aka tara su gaba ɗaya gidan,dika2 qarfe 7am ne yanzun amma tashin hankali irin wannan ya faru da zai dauke walwalar gidan gaba daya.
Umman Aeeshaa ake jira, dan zaman har da ita ya qunsa.
Sun gaida iyayen nasu inda suka amsa cikin daurewar fuska, suna zaune suka ji tsaiwar mota, a zaton su Khadeeja ce ta iso, sai suka ji shigowar mutum kai tsaye yana sallama a tsakar gida.
Baban Sabeer ne ya leqa, dan shi ne qarami a mazan, wani matashi ya gani baqi kyakkyawa, amma rudani da tashin hankali bayyane a fuskar shi, ko gaisawa da Baban Sabeer bai ba ya hau fadin abinda ya kawo shi.
"Suna na Ammar Abdallah, ni abokin Sabeer ne na wajen aiki, yanzu haka mun kai Sabeer AKTH saboda bashi da lfy matuqa, ciwon ya je ya dawo, yau abun yayi yawa, yace a kawo shi gida sai muka ga ya kamata mu kaishi asibiti ne in yaso sai nazo na sanar,"
Wata iriyar zufa ce ke karyo wa Baban Sabeer,
Baban Khaleefa ne ya fito
"Abubakar lfy? Meke faruwa,"
"Yaya Sabeer dina na asibiti ba lfy tin daga can Ibadan aka kawo shi nan AKTH"
"Subhanallahi, Hajja, Baba, ya kamata mu wuce asibiti Sabeer ba lfy,"
A kidime yake shiga ciki yake sanar dasu, inda suma suka tashi hankalin su a tashe suka nifi motocin su, sai AKTH.
Qarfe 10 daidai suka isa, Ammar ne ya musu jagora zuwa inda aka kwantar da shi, Aeeshaa kukan ta ne ya qaru, Yayan ta ba lfy, Ohh Allah yau wace iriyar rana suka tashi da ita ne?
'Allah ka sauqaqa mana abinda ya tinkaro mu na musiba, ya Allah mun miqa komai a hannun ka ka mana maganin dikkan abinda yake damun mu babba da qarami'
Ummeen Sabeer itama kuka take, Sabeer ne kwance sambal baya motsi sam, numfashin shi na fita kadan2 da gani da kyar yake samun shan su.
"Ina likitan daya ke kula da shi? Me aka ce yana damun shi?"
"Baba sai dai kuje ku ji, muna kawo shi ogan mu ya koma ni na tsaya, so ban san meke damun shi ba"
"Mu je ka nuna mana office,"
Suna shiga Dr. Ya d'ago daga duba wasu takardu, da alama gwaje2n da akai ma wani ne,tashi yayi tsaye ya miqa ma su Baba General hannu, da su Baban Sabeer, bayan sun gaisa ya musu izinin zama a kujera, sun zauna cikin qaguwar su ji meke damun dan nasu.
"Da farko ni ne Kakan Sabeer Abubakar da aka kawo maku daxu, wannan mahaifin shi wannan kuma yayan mahaifin shi, munzo ne dan mu san meke damun dan mu,"
"K masha Allah, dama yanzu nake son naje na sa a taho da magabatan shi, ni suna na Dr. Naseer Umar, yaron ku a bisa gwaje2n da mukai mun gano yana dauke da matsanancin ciwon malayria, thypoid, da kuma hawan jini, jinin shi ya hau sosai, wanda muke tinanin ko tsananin ciwo ne ko kuma wani damuwa yake dauke da shi, yanzu mun masa allurai, na malayria da thypoid, an qara masa ruwa kuma mun saka mashi magunguna ciki, inshaa Allah muna saka ran samun nasara na da wasu 'yan kwanaki, na hawan jini ma mun samu muna kan bashi kulawa akai, inshaa Allah za a samu nasara nan kusa,"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun,wai me ya kawo ma sabeer hawan jini ni Muhammadu? Me zai dami yaro matashi haka?"
"Kar ku damu, ganin damuwar ku sai ya qara jefa shi wani hali, ku kula da shi sosai, muma zamuyi iya qoqarin mu, inshaa Allah,"
"Dr. Mun gode sosai Allah ya saka da khair"
Sallama sukai suka fita,Umma ce zaune tana ta sharbar kuka itama, mutuwar mijin ta ce ta dawo mata sabuwa, haka aka fada mata mutuwar miji katsahan, Allah ya kare mata Sabeer din ta, shi yasa bata son saka kowa a rai, kar abinda tafi so ya tafi ya bar ta, harda Umman Sabeer din aka hadu ana taba hakuri, su Baba General na fitowa suka miqe zuwa wajen su, tare da watsa masu tambayoyi, Baban Khaleefa ne ya masu bayanin komai, kuka suka rikice suna yi, Hajja ce mace mai kamar maza ta bankada masu tsawa,
"Bana son iskanci, me kukan ku zai masa? Sauqi zai bashi? Yanda kuke jin quncin ciwon nashi ya fi ku jin azabar, dan shi a jikin shi yake, kuda ya kamata ku masa addu'ar samun sauqi zaki cika masa kunne da kuka, ya tashi yaga kuna kuka ku sake rikita shi ya zaci ciwon ajali yake ko? Dalla ku rufe mana baki ku bar mu muji da abinda ke damun mu, kai kira min wannan dan iskan yaron naka,"
Khaleefa na can yana shiryawa yau za su shaqatawa Abuja da Becca,ga shi ya yiwa Hadiza alqawarin zai je Abuja aiki zai kai shi zai kai mata tsaraba in ya dawo, tana nan tana murna da masa fatan dawowa qalaou.
Wayar shi yaga tana walqiya, zuwa yayi ya daga a zaton shi Becca ce ko dubawa bai ba ya dauka.
"Babe gani nan zuwa ki shirya, yau sai Abuja ta san da zuwan mu, zamu raqashe, babban club zaki kai mu wanda ya amsa sunan shi, bana son qaramar harka,"
Jiri ne ya fara diban Baban Khaleefa,
"Khaleefa CLUB????"
Da gudu Khaleefa ya datse kiran, yana zaro ido waje, qirjin shi ne ya fara bugawa da qarfin tsiya, ji yake kamar ranshi zai fito dan tashin hankali da damuwa, qafafun shi da hannayen shi har zufa suke.
"Wayyoo Allah na ina cikin tashin hankali,"
Hadiza na gida, tana jiran taji motar shi ta masa Allah kiyaye daga qofar gidan su.
Shiru har 11 ta gota bai fita ba, Wuf tayi zata fita Goggo na ta kwala mata kira ko waigawa, a gidan Khaleefa ta tsaya tana maida numfashi.
Tana shiga ta gan shi a parlour yana kaiwa da kawowa, hankalin shi a mugun tashe, ya kai ya kawo, ya kai ya kawo yana sosa kai,
'To ai zama na ma a gida hadari ne, yana iya shigowa indai Baba ne ya ci mutunci na, gwanda naje gidan a gama komai a can, in anan ne maqota da mutan unguwa suka ji ai mutunci na ya zube'
Shafo shi tayi daga sama zuwa qasa ta baya,da sauri ya juya,
"Hadiza me kk anan? Bance maki tafiya zan ba?"
"Haba angon Deejee? Naga shiru baka fita ba shi yasa,"
"Ango kuma, baki da hankali, baki san tashin hankalin danake ciki ba ne shi yasa, fita kar wani yazo ya gan ki anan,"
"Daidai kenan, kaga sai kawai a jira na haihu a daura mana aure, dan ba a aure da cikin shege,"
"Whatttt????? Ciki? Nawa? Inaaa in kin isa shege ne ni, bar nan fitaaa!!!
"In fita inje ina? Ai Baba Khaleefa ko Daddy zan ce tinda ku 'yan gayu ne, ba inda zani, sai ka san ya za kai da ni, ka auren a haka ba wanda ya san ina da cikin ka na wata biyu, ko kuma ka kyale ni na tona mana asiri, kasan dai kai ne zai zama maka sabo, ni ko a jikina, kaji na fada maka,"
"Wayyoo Allah na, yau meke faruwa ne?............
*Shiga Google ka gani dan latsin hammata kawai*
*ku yi manaji da wannan dan ban son aje ku kuna jira ne amma wallahi yau na dan gaji da typing, thank u for the love and du'as, Allah ya amsa ya saka maku kuma da alkhairi*
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 21
"Tsakanin ki da Allah yanzu ba zaki bar gidannan ba? Kin san irin tashin hankalin da na ke ciki yanzu? Ji nake yanzu haka kamar na bace a daina gnina haka nake ji,"
"Hhhhhhh kasan me? Kana ban mamaki da kunya, kai fa namiji ne, ni mace ina murje ido na nayi abinda nake so, amma kai sai ka na wai tsoron gidan ku, zawarawa yanzu iri na daidai ne masu kame kan su a gidajen su, amma dik fita mike farauta, ba tare da an gane ba, yanzu ni in ba Goggo na ba mutan unguwar nan da ke yawan gani ina fita ina dawowa da dare ba a hanya muka hadu da kai zaka rantse ina ma da aure, ai ba dole sai ka yi abu kowa ya sani ba,(ta manta cewa Allah na ko ina, mala'iku na tare da ita, akwai mai rubuta komai take) look, u have to grow up, ka manta da wani zancen me mutan gidan ku zasu ce ka shana kafin lokaci ya qure maka, shawara na baka,"
Qwan !Qwan ! Qawan !
Cikin Khaleefa ne ya bada wata iriyar qara, kashin shi ya bushe yau,bai taba ganin fushin mahaifin shi ba,ba kuma ya fata, ya kama ta ya nemi mafita, gashi ba katangar da zaii iya kamawa ya haure a gidannan da ya haure, qara knoking akai da qarfi.
"Kaje kaga ko waye ko na leqa, bana son qara, tinda na samu cikin nan,"
"Fuck u Hadiza,don't u ever talk about that darn pregnancy, or else,"
"Or else what? Or else what ? Kana nufin wannan shaqar da ka min zata sa naji tsoron ka? Zata sa na aje dikkan qudirin dake zuciyata, Khaleefa sai na haife maka abinda ke ciki na, sai ka dauke shi da hannun ka ka rada masa ko mata suna, the best thing shine yanzu yanda ka shaqe ni ka qarasa kashe ni da dan ka ko 'yar ka sai na san kai tantiri ne,"
Da qarfi ya sake matse ta, amma taurin kai irin na Hadiza ko rintse ido batai ba, sake ta yayi daidai lokacin da wayar shi ke ta tsuwwa, cikin rawar hannu ya daga, Becca ya gani a screen har da hoton ta,kuma Hadiza ma ta gani,