Showing 6001 words to 9000 words out of 69262 words
Chapter 3 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
zai kankaro fatar kan nashi.
A kan gado ya fada, yana furzar da wata irin iska mai zafi, wannan wane irin hukunci ne haka? Shi yace yana son wannann kwailar yarinyar ne? Me zai da ita, manyan mata ma bai kalla ba balle ita, gaskiya an cuce shi, a rayuwar shi yana son ya ga ya samu mace babba, mai hankali, mai kyaun jiki,wadda ba zata na tara masa yara ba, dan kar jikin ta ya baci, wadda komai ta saka zai zauna a jikin ta yayi dass,ko Hassana abinda yasa bai son ta, tana da sakakkken jiki, ya sha ganin ta da daurin qirji, ko ya shiga kaida Bappan shi, ko kuma Baba General ya aikashi wani abun, gaba daya nonon ta sun sake, shi kuwa yanda ya saba kallon fina-finan turawa, yana ganin su kyam ba karkata, kamar zasu tsokane ma mutum ido ba abinda zai kai shi auren wadda nonon ta yake a kwance.
Su suke ganin shi shur2, amma shi ya san mugun dan duniya ne a qarqashin qasa, kallon fina2n batsa ba wanda ya fishi, a rana sai ya kalli film sama da kala biyar na batsa, ya toshe kunne dan kar a jiyo shi, dakin shi akwai bandaki, da dan qaramin parlour,lokuta da dama in ya dawo daga wajen aiki, musamman na dare, in ya fito kan ya isa gida, ta hanyar Airport yana karkatawa wani hotel, nan zai sha iska, yaci abinci, mata na gilmawa yana kallo, in yaga wadda jikin ta ya masa suyi ciniki, ya biya, ya huta da ita ya dawo gida, ba wanda ya san yana aikata hakan, daga Allah sai shi, sai kuma matan da yake hakan da su.
Halin shi mafi muni bai bawa ibada hankali ba, kwata2 shi khamsa salawat bai damu da sauke su ba, balle ya qara da nawafil, amma dan ganin ido, in yana gida,iyayen shi na gida yana riga kowa zuwa masjid.
Kowa a iyayen shi zasuce Khaleefa ba ruwan shi, sai dai yana da matsala wajen miskilanci, sannan sukan bada shaida akan shi din mai ibada ne, kuma mai riqo da addini ne.
Akan idon ta ya wuce, dan haka ta share hawayen ta,ta sake gyara jikin ta da fesa turaruka,powder ta gogawa fuskar ta mai cike da pimples, ta shafa man lebe, ta fice zuwa dakin shi, ta gaban Sabeer ta wuce bai ko san ta wuce ba, tsabar damuwar da yake ciki, shawara ya yanke ba zai koma gidan nan ba, ya bar zama dasu, dan ba zai iya ganin ta ba bayan an mallakawa dan uwan shi ita, da sauri ya bar gidan, dan kar Umma tace ya je su wuce gida.
Kwance ta ganshi, yana kallon sama.
Qamshin da take ne ya sashi kallon bakin qofa, ta lankwashe hannayen ta ta turo su gaba, alamar tsoro da fargaba.
Cikin isa da ikon shi ya furta.
"Me ya kawo ki dakina?"
Bata ji me ya fada ba, dan haka gab da shi ta matsa ta ce.
"Na'am? Me kace Yah khaleefa?"
A tsawace ya amsa ta da,
"Nace me ya kawo ki dakina?"
Cikn sarqaqqiyar murya tare da durqushewa a gaban shi tana mai zubda hawaye masu zafi na tsantsar son da take masa tace,
"Yah khaleefa dan Allah ka rufan asiri ka aureni, ka fada ma Baba General ni kk so, ko baka so na na amince zan zauna da kai a haka, zan baka kulawar da uwa ke bawa dan ta, kai fiye da haka ma, zan jiyar d kai dadin da ko a mafarki ba ka taba tsammanin samu wajen wata ba, Yah dik abinda kk so shi zanyi, ba zan aikata wanda baka so ba.."
Hannu ta sa ta shafo cinyar shi, a qoqarin ta na riqe masa riga, wata zabura yayi yai baya, tare da daga hannu ya wanke ta da wani irin marin da bai san ya mata shi ba, ko dafe wajen batai ba, ta sake jan rigar shi
"Yah khaleefa ka dake ni, indai zai sa ka ji daɗi a ranka, ni dai fatana dan Allah ka aureni, dan Allah kar ka gujeni,"
Fisge rigar shi yayi, ya ja hannun ta, kamar wanda zai ce mata wani abun, can kuma ya fasa, dan in ya sanar da ita dalilin da yasa bai son ta ya ci mata fuska, kuma wannan me nacin zata ce zata ci gaba da manne masa, dan hakan ba zai zama kwakkwaran dalili ba a wajen su, hanyar waje yayi da ita, still yanda ya riqe ta kamar zai mata magana, suna zuwa bakin qofa ya bude ya hankada ta ya rufe.
A parlourn gidan ta hadu da Ameena,wadda take zaune jikin Maman khaleefa suna hira, da sauri Ameena ta je kusa da ita,
"Adda Hassana sannu, faduwa ki kai?"
Wani kallo ta wurgawa yarinyar da sauri Ameena ta janye ta koma gefe, wani tsaki Hassana ta ja, ta fice a bangaren, ta na shiga sashen su ta ji maganar mahaifiyar ta ta na tambayar ta da cewa,
"Daga ina kk?"
"Daga wajen Yah Khaleefa nake,"
"Ki ka ce masa me Ya aure ki? Kar yabi umarnin manyan shi? Tinda ke kin zama baki jin magana, na yi qoqari na hakurtar dake akan son da kk ma Khaleefa ba mai yuwa bane, khaleefa ba cikakkiyar lafiya ne da shi ba da dikkan alamu, ko kin aure shi wahala zaki sha, namiji mai cikar halitta haka ace mace bata gaban shi? Me ki ke tinani?"
"Ummee, na maki alqawari sai Yah Khaleefa ya aureni, ko zan rasa raina wajen neman soyayyar shi ba zai auri waccan banzar ba, this is my promise, ki rubuta ki aje......."
*Hummmmm kuna ta abun ku ita wadda kukeyi ma domin ta bata san anayi ba baiwar Allah*
*KUN MAKARO*
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 4:
Da qarfi Ummen su Sabeer ta fizgo Hassana jikin ta fada jikin nata, har sai da ta bige qafar ta ta dama a jikin ɗaya daga kujerun da suke a zagaye a cikin parlourn,cikin tsananin nuna ɓacin rai Ummeen Sabeer ta ce,
"Idan na sake jin irin wannan kalaman abakin ki, zaki ga yanda zan saba maki Hassana
,namiji har ya isa ya shiga tsakanin ki da 'yar uwar ki, qanwar bayan ki ma kamar Aeeshaa? Kina nan kina haukan ki yarinyar nan ko sanin me ake ciki batayi ba, na tabbata bata son Khaleefa,in ba ke ba ban ga me son shi da aure ba, muma dan yana a matsayin ɗan mune muke son shi, ina kk hangowa kan ki rayuwa mai daɗi da wannan miskilin yaron da ko dariya ban taba ganin yayi ba da girman shi dai, kalaman ki sun tsoratar da zuciya ta ba kaɗan ba Hassana,me kk shirin aikatawa? Tarbiyyar da muka baki kenan kina cin alwashi? Kin san ma'anar cin alwashi kuwa? To ki gaggauta cire shi a ran ki ki nemo wani ki aura, wannan shine magana ta ta qarshe da ke, kin fi kowa sanin halina"
Kuka ta saki mai ban tausayi, wannan wane irin so take ma Khaleefa,bata san tana masa irin wannan son ba sai da hakan ta faru, cike da tausayawa Ummeen su ta rungume ta tana lallashin ta, tare da fada mata kalamai masu kwantar da hankali da nutsuwa.
(Lallai kunyi dacen uwa, tabbb da wata uwar ce, ba zata yarda d'iyar ta ta zauna ranta na quna ba akan saurayi, sai sun shiga boka sun shiga malam sun janyo hankalin shi, wanda daga qarshe abun kansu zai juye, tinda the moment da zai gano asiri aka masa kashin su ya bushe, dan tsanar da zai ma mace sai tafi ta da, ga shirka an aikata, zunubi kan zunubi, kuma a qarshe an rasa son da aka nema, ko shekara nawa zakuyi da namiji, ko kantin kwari kk haifa masa saboda yara, da asiri ya karye zai ta mamakin yaushe ya aure ki? Nan zaki fara fuskantar walaqanci kala2, mu kiyeye, asiri da tirsasa so ga namiji baida kyau, akwai wanda suke ganin ya halatta ka ma miji asiri dan ya so ka, sai suke juya abun da neman taimako, kinemi taimako wajen Allah mana, nasara na wajen Allah, shima bokan ko malam din Allah ne ya bashi iko, yake abinda ya ga dama, dan Allah ya kama shi a lahira, dan haka in kinga zaki bi boka ko malam ku dunguma zuwa wuta bismillah, in kuma zaki tashi ki motsa jikin ki ki rage kitse ki yi sallah, kuma ki samu lada, sannan Allah ya biya maki buqata, marhabun dake)
Umma ce ta leqa bangaren su Khaleefa domin kiran su Ameena su wuce gida, da sallama ta shiga, da gudu Ameena ta fada jikin ta,bayan ta zauna Maman Khaleefa ta koma ta zauna itama, shiru suka yi, yanzu sun zama surukai, cann Maman Khaleefa ta nisa tace,
"Khadeeja in kina ganin wannan hadin bai maki ba kar ki ji komai ki sanar dani, zan ma Abban su magana, a yi wa Baba General bayani sai a fasa, dan na kula kamar baki son wannan hadin, kar ki damu ba zan ga laifin ki ba, Khaleefa mutum ne a baibai, ba ka gane gaban shi bare bayan shi, ni kaina hakuri nake da shi,balle qaramar yarinya kamar Aeeshaa."
"Aunty ni ba ni da wata matsala ta bangare na, matsala daya ce dama, naga kamar Hassana ke son shi, kuma an juya an bawa Aeeshaa shi, hakan anya anyi daidai kuwa?"
"Kar ki damu, Baba General na sane da hakan, ya duba yanda Khaleefa bai son Hassana ne kwata2, a haka da halin shin nan na shiru2 ma ya aka qare, balle bai son abu? Amma a qalla sukan gaisa da Aeeshaa, na kula har 'yar tambaya yana mata ya makaranta? Ki fadan a gidannan banda ina kwana ko ina wuni wa Khaleefa ke kulawa? Tin da ya shiga shekarun balaga yaron nan ya sauya halaye, ya tashi daga mai son mutane zuwa wannan mummunan hali, mun kai shi asibiti yafi a qirga dan aga ko akwai abinda ke damun shi, amma inaa,"
"Aunty babu wata matsala,Allah ya shige mana gaba,"
"Ameen"
"Ku shirya mu wuce ku kuma,"
"To Umma, amma ni fa naga Yah Sabeer ya fita kamar yana kuka,har yanzu bai dawo ba, wa zai maida mu gida?"
"Muje na gani, in ya dawo ya maida mu, in bai dawo ba sai mu tafi,"
Sallama suka yi wa Maman Khaleefah sannan suka shiga bangaren su Sabeer, cikin fara'a Ummeen su ta masu maraba, Hassana kuwa sai ta haɗe girar sama da ta qasa, dan ummeen su ta mata faɗa taji ba shi zai sa ta sakar wa da goggon nata fuska ba, har yanzu haushi suke bata.
"Aunty Sabeer fa? Yana ciki ne ya zo mu wuce gida, dare nayi,"
"Sabeer kam ban shigo na isko masa ba, sai dai ki gwada wayar shi,"
"Ok to bari muje waje, na jira magariba ta gabato,"
Keys din su Hassana ta miqa mata ta dauke kai, a ran Umma tana tausaya ma d'iyar yayan nata, amma ba yanda za ta yi, karba ta yi, ta kama harda hannun ta, Hassana ta daga kan ta suna fuskantar juna,Ummah ta ce,
"Hassana ki yi hakuri, na jima da sanin matsayin Khaleefah a wajen ki, amma sai ga wannan lamari ya kunno mana kai,gashi ba ni da yanda zan yi ni ma na hana faruwar haka saboda dukan mu umarni muke bi, ki yi hakuri Hassana ki rungumi ƙaddara mu yi fatan Allah ya sa haka shine Mafi alkhairi,i wish i can do something to help you, u ar both my children, and i love u so much, bana son abinda zai bata ran ku, yanzu abinda nake son ki maida hankali akai shine, addu'a, in rabon ki ne Khaleefa Allah zai baki shi,koda kuwa ya auri Aeeshaa ne, tinda ba haramun bane, share hawayen ki kin ji? Ki daina fushi"
Kuka Hassana take sosai, sannan haushin Goggon nata ya ɗan ragu mata, ta fuskanci itama ba a son ranta akai had'in ba.
Goge hawayen ta tayi, daga nan suka yi Sallama suka fita, ta kira wayar Sabeer amma taji ta kashe, tasan za ai haka, yara ta sa a gaba suka nufi gida.
**********************
Azkar take koda suka shiga gidan, direct Ameena ta je wajen ta tana murnar ganin ta, kamar wadda suka shekara basu tare, Abdul dakin shi ya wuce danyin alwala yayi sallah, Umma ce ta zauna a kujera tana nazarin abubuwan da suka faru, tana tinani ta sanar da d'iyar ta ta ko ta bari sai ta kammla karatun ta?
"Umma nace sannu da dawowa, ya kuka baro su?"
"Lafiya, debon ruwa kuma mara sanyi, me kk dafa?"
"Tuwon masara nayi da miyar busasshiyar kubewa da busasshen kifi, da ganda,"
"Zubomin, ki ajen a d'aki, bari na je na yi sallah,"
Amsawa tayi sannan ta miqe dan cika umarnin mahaifiyar ta ta,
Aeeshaa ce ɗauke da babban faranti ɗauke da kayan abinci da ruwa a Saman shi sai cup ta nufi d'akin Ummah dan kai mata abinci ta, ta na shiga ta ga yanda Umman nata ta wurgar da kayan ta, jaka takalmi a qasa, mayafin data yafa a gado yana reto yana taba qasa, sarqa da dan kunnen data saka a gado ta watsar, d'akin da ya sha gyara mai kyau,ga qamshi mai daɗi ta bi ta hargitsa shi daga dawowar ta.
Cikin yar shagwaba bayan Umman ta idar da sallar Aeeshaa tace,
"Umma baki ga yanda na gyara maki dakin ba ne? Diba yanda kk bata Ummaaa,"
"Na bata din,nace na bata din, dakin ki ko nawa? Gyaran ma da dik qura,"
Saida Aseeshaa ta yi dana sanin wannan magana da ta yi, dan kuwa fada Umma ta dinga yi ba kama hannun yaro kamar an ce ta tashi ta sake gyara abinda ta bata.
Kanta a sunkuye ta fara ɗebe kayayyakin, tana saka komai a muhallin shi, wai ace magana mai daɗi ta gagara a tsakanin su, tana kammalawa ta fita, ranta na mata suya.
******************
Cikin dare Sabeer ya dawo ya kwashe kayan shi ɗaya bayan ɗaya, ya sa mai gadin gidan ya rufe gate, shi kuma ya wuce, ba zai taɓa iya ci gaba da zama da Aeeshaa a gida daya ba, bayan sanin wannan mummunan labari.
Yana mota yana tafiya, cike da tinanin rayuwar da ya fara tsara masu ta jin daɗi cike da so da qauna ya ga motar Khaleefa, baqin glass gare ta ta kowanne gefe da gefe, amma ta gaba haske ne da shi, ta nan ya hango an kwantar da kujerun motar, tsayawa yayi da tashi motar daga nesa da su, sai da aka dad'e, sannan ya ga wata yarinya ta d'ago tana maida rigar ta, Khaleefa ne shima ya taso ya na gyara rigar shi, matsanancin mamaki ne a fuskar Sabeer, me hakan yake nufi? Bai gama tunani ba, yaga Khaleefa ya fito, yarinyar ta fito itama, kuɗi Khaleefa ya bata, ta tsaya tana kadasu, tare da yi masu kiss, tana wani karairaya a gaban shi, shi kuma ya rungume hannayen shi, d'aga masa hannu tayi zata tafi, ya daki mazaunan ta ya na murmushi,ita kuwa sai ta sake kada masa su, sannan ta yi gaba.
Sabeer sumane kawai bai yi ba dan tsoro da mamaki tare da tashin hankali, yaushe Khaleefa ya ke harka da mata? A kusa da unguwar su, dama haka halin shi yake ko kuma dai yau ya fara saboda damuwar da yake ciki? Dan ya kula bai son hadin shima sam, anya yau ya fara, kuma khaleefa ne harda wani dariya da wani yi mata wasa, kaiii mafarki yake yi ba gaskiya bane.
Yana nan yana tunani bai san khaleefa ya wuce gida ba ma ya bar shi a wajen, da sauri ya tada motar shi ya nufi gidan, ko a hanya basu hadu ba, ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace,
"Alhamdu lilLAAH ba shi bane, habaa har zuciyata na neman bugawa, bari dai na tambayi Baba mai gadi naji,"
Sallama ya ma Baba mai gadi, sannan ya masa tambaya akan yaushe Khaleefa ya dawo, Baba mai gadi shiru ya d'anyi, yana tina kuɗin da Khaleefa ke bashi akan yana rufa masa asiri,ga tsoratar da shi da yayi dik sanda ya fada ma wani baya dawowa da wuri gida washegari zai bar aiki a gidan.
"Baba magana nake, yaushe Yah Khaleefa ya dawo?"
"Ai yau Khaleefa in ba masallaci ba yana ciki, da dikkan alamu baya jin daɗi ne yau ɗin nan, tinda shi mutum ne ba mazaunin gida ba ina ka fito aiki ina zaka je aiki"
Hankalin Sabeer ne ya sake kwanciya, dan ba zai taɓa yarda a aurawa Aeeshaa mai neman mata ba, nan ya fara jin ba daɗi daboda zargin da yayi ma dan uwan shi, tabbas kama ce kawai, da hukunci na Allah, dama yana ta mamakin dariyar wancan da ya gani da wasan shi, Khaleefa ba halin shi bane bakan sam, to amma kuma motar fa? Da sauri ya kau da tunanin komai a ran shi dan tuna wa da ayar alqur'ani da ya yi da Allah ya ce, kada mu tsananta bincike (wala tajassasu.....)
Kayan shi ya dinga diba yana kaiwa cikin dakin shi na gidan,sai dai d'akin duk yayi qura sosai, amma sai da safe zai gyara saboda dare yayi sosai, Khaleefa na hango shi ta window yana murmushin mugunta, domin ya hango shi shima a kokacin da ya juya zai shiga motar shi, wannan dalilin ne ya sa yayi sauri ya dawo kan su haɗu, dan zuciyar shi na raya masa yaron ya gan shi.
Sauke labulen yayi ya koma ya kwanta, ba dan Aslamiyya karuwa bace da ita zai aura, ta yi iya yi, ta kai dik irin macen da yake so, ita saboda ma yawon ta fito ta juya mahaifar ta, tsufa a tattare da ita ba shi kenan, ga jikin nan perfect yanda yake so, sabuwar sha'awar ta ce ta kama shi, miqewa yayi ya dakko laptop din shi, ya shiga wajen fina-finan shi na banza, ya saka wannan ya cire ya