Showing 3001 words to 6000 words out of 69262 words
Chapter 2 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
da wuri,dan tana da kazar2 da saurin aiki,sai dai tana yi a nutse da kulawa, yanda dik saurin da takeyi tana aiki me kyau, nan da nan gidan ya dau qamshi da kyalli, wanka tayi ta kwanta dan hutawa, in Umman ta ta dawo bata san kuma wanne aikin ne a gaban ta ba shi yasa ta yi tunanin hutawa kafin su dawo.
********************
Babban gida ne, kusan nace dik unguwar yafi kowanne gida kyau da girma, daga farkon layin zuwa rabin layin gaba daya gidan General Muhammad Mustapha Dan Bauchi ne, tsohon soja ne, wanda ya halarci yaqi kala2, kuma ya samu babban muqami, da kyaututtukan girmamawa, yayi ritaya amma har yanzu mahukuntan qasar nan suna damawa da shi, yana da matar shi guda ɗaya, mai suna Aeeshaa, wadda suke kira da Hajja, auren soyayya suka yi, wanda har yanzu soyayyar nan a kullum ba dan tsufa ba sai mutum yace sabbin aure ne, yana matuqar girmama matar shi,bai haɗa ta da kowa ba, itama kuma haka, akwai fahimtar juna mutuntawa da kauda kai a tsakanin su.
A shekarar farko da auren su ta samu ciki, inda wata tara na yi ta haifi yaron ta na miji, aka maida sunan mahaifin shi wato Muhammad, amma suna kiran shi da Basheer, sai Abubakar, sannan daga qarshe sukai auta da Khadeeja.
Basheer shine babba, wanda yanzu haka suna tare a gida daya da mahaifan nashi, a bangare daban, yana da mata guda daya, yar garin Kano ce, mai suna Huwaila, mace ce mai mutunci da mutunta kowa, sai dai akwai ta da son abin duniya da son girma, gata kwata2 ba zaka taba mata kyauta ko wani abun alkhairi ba tace maka na gode, amma tsakanin ta da mijin ta sai son barka,kullum a cikin yabawa kyakkyawan halin ta yake, son abin duniyar ta kadai ke haɗa su faɗa, in yayi magana takan kashe bakin shi da cewa,
"Haba Abban Khaleefa, komai na siya ko na saka ai domin ka ne,"
Ta hakan yake ɗauke kai akan yawan bani2n ta. Suna da yara uku, Khaleefa wanda ya ci sunan kakan shi, (Muhammad Basheer Muhammad) sai Hamdiyya, da Bilqis. Matan sunyi aure dika, Khaleefa shi bai yi aure ba har yanzu saboda girman kai, da ganin ba wanda ta isa ya kai kan shi wajen ta, ma'aikaci ne a filin jirgin sama dake nan a garin kano.
Sai Abubakar wanda yake shine mahaifin Sabeer, mahaifiyar shi 'yar uwa ce ga Hajja, dan haka auren zumunci ne suma, suna da yara Uku suma, Hassana,da Hussaina,Sannan Sabeer, Hussaina a tare aka aurar da ita dasu Balqis, yanzu ya rage sauran Hassan kadai a 'yan matan gidan.
Khadeeja itace autan Hajja, kuma itace mahaifiyar su Aeeshaa, ita kaɗai ce ta yi wa Hajja takwara, wannan dalilin ne yasa Hajja ta hana a boye sunan Aeeshaa, Aeeshaa na da qanne kamar yanda kujaji sunan su a baya, Abdul Hakeem da Ameena.
Mahaifin Aeeshaa mai suna Salihu Adam maraya ne, ɗan garin Katsina ne, yana da Yayan shi da ya rage masa, mai suna Isma'el Adam Katsina, yana can zaune tare da iyalan shi.
Neman aiki ne ya kawo Salihu garin Kano, makaranta daya suka gama da Abubakar Mahaifin Sabeer anan Kano, dan haka yace ya zo gidan su ya zauna har ya samu aiki, ya na nan zaune har watarana Allah yasa ya samu aikin banki da sa hannun General,ba laifi daidai gwargwado kuma yana samun albashi mai tsoka, dan haka General ya bashi shawara akan yayi aure, matasan yanzu suna samun kudi ba aure musiba ne, cike da jin kunya ya sosa kan shi, ya duqar da kai qasa, Hajja dake gefe tana shan kayan marmari, tace,
"Au ashe fa General baka da labari,"
Cikin son jin qarin bayani General ya kalli Hajja sannan ya kalli salihu sannan ya ce,
"Na me fa?"
"Salihu Khadeeja yake so fa, dan na sha kama su suna hira, kullum ina son sanar da kai to ba ka zama sosai, sai na manta, yau dai Allah ya nufa kayi maganar a gabana, na san da ba zai fada maka ba,"
"Ahhh afff tooo... masha Allah, wannan abun ai yayi, yayi kyau hakan, na kuma ji daɗi sosai, Allah ya sanya albarka a ciki, yanzu abinda za ai shine, ya kamata ka je Katsina ka sanar da magabatan ka, ka ga shikenan sai a zo a sha biki ko?"
Cike da jin nauyin su ya musu godiya sannan ya sanar da su rasuwar mahaifan shi, ta hanyar hadarin mota, ya sanar dasu yayan shi ne ya rage masa, da baffanin shi da kawunan shi.
Sun masa ta'aziyya, sannan suka shaida masa za su je Katsinan tare da shi su ga dangin shi, dan basu son a bata lokaci tinda suna son juna Hajja ta shaida hakan.
Cikin qanqanin lokaci akai auren su, General yayi2 su zauna tare da shi, kamar sauran yaran shi, Salihu yaqi, dan shi mutum ne mai zuciyar nema, da kuma son ya tsaya da qafar shi, mace dik son da take maka da ta ga iyayen ta na maka wani abu, komai qanqantar shi to ta samu kafar rainaka kenan, haka ba dan Hajja taso ba suka samu gida a unguwar dake kusa da tasu, ya siya masu gida suka koma suka zauna a ciki da iyalin shi.
Khadeeja na matuqar son mijin ta, amma kunya ta hana ta sakewa ta nuna masa,kullum yayi ta tsokanar ta yace,
"Khadeeja ke fa ba zallar bafulatana bace, ki daina tauye mana rayuwar jin daɗin mu,"
Takan bashi amsa da,
"Mu fulani ne, dan kuwa kakannina na uwa da uba fulani ne, dole na zama me kunya"
A haka suka ci gaba da rayuwa cikin so da qaunar junan su tare da mutunta junan su har Allah ya sa suka samu albarkar aure ta haihuwa tare da qarin arziqi me yawa,Watarana Salihu yana wajen aiki aka wuce da shi asibiti, saboda matsanancin ciwon kai da yake fama da shi, likitoci sun dade suna masa gwaje², dan sai da suka dau kwanaki, suka gano yana dauke da ciwon cancer na brain, Khadeeja tayi kuka sosai kamar zata mutu, gaba ɗaya kunyar shi da nauyin su Hajja da take ji ranar babu ita, ga shayarwa ta na yi, ga tashin hankalin rashin lafiyar mijin ta, ko abincin kirki bata iya ci, yarinya bata samun ruwan nono sosai, shekarar Ameena daya da yan watanni aka yaye ta, an shirya za ai masa aiki a qasar India, suna shirin tafiya Allah ya karbi rayuwar shi.
Fad'in tashin hankalin da Khadeeja ta shiga ba zai misaltu ba, sai da ta kai har an kwantar da ita a asibiti, na sati ɗaya da kwana biyu, ta rame ta lalace kwata2 ko kyaun gani bata da shi, har Hajja ta dinga zargin ko wani cikin gare ta.
Bayan arba'in da rasuwar Salihu, Hajja suka yanke hukuncin ta koma gida, aikuwa sunga tashin hankalin da basu taba zatan zata yi ba, kuka ta dingayi, tana sambatun zasu raba ta da gidan mijin ta, mijin ta zai iya dawowa ko wanne lokaci ya ga bata nan, tafiya yayi ba mutuwa ba, da kyar aka lallaba ta aka bar ta, dan gudun kar ta samu wani ciwon, a hankali2 ta fahimci cewar mijin ta fa ya rasu, ya barsu bari na har abada, dik da ta san hakan tafi son ta zauna anan, daga wannan lokacin halayen ta suka sauya, a da Aeeshaa yar gata ce a wajen ta, amma yanzu kwata2 gani take in ta sa ta a rai itama wataran mutuwa zata yi ta bar ta, dan haka take janye ta a ran ta da jikin ta,Sabeer shi ya ci gaba da zama da su, bayan rasuwar mijin goggon tashi, nan ya ci gaba da karatun shi kafin daga baya ya tafi qarin ilimi, sun shaqu sosai da Aeeshaa, ba kadan ba.
*Ci gaban labari*
Suna shiga Khaleefa yana qoqarin fita a motar shi,Ameena ce ta miqe tsaye ta na d'aga masa hannu tare da fad'in,
"Lahhhh ga Yah Khaleefa Umma, Yah khaleefa !"
Cikin bata fuska Abdul ya ce,
"Malama ki daina cika mana kunne kin san ba kula ki zai ba,"
Murguda baki Ameena tayi, dan ita mai son mutane ce.
Khaleefa ne ya leqo kan shi ta window, ya daga masu hannu, tare da motsa labban shi, babu wanda yasan me yake fada, Sabeer ya ji haushin hakan sosai, dik da dama ba wani jituwa suke ba, amma a qalla yayi tafiya, domin zumuncin dake tsakanin su ma ai ya nuna kulawar shi.
Shima yaqen yayi masa ya daga masa hannu ya sa kan motar shi zuwa cikin gidan, Khaleefa shima ficewa yayi abin shi.
"Wai fa Yah Khaleefa na nufin wannan d'aga hannun da yaqe haqoran harda ke a gaisuwar,"
"Na sani, muje ciki, ai khaleefah matar shi na da aiki matuqa,"
Da murna Sabeer ya yi bangaren mahaifan shi, inda suka taru suna taya shi murnar kammala karatun shi da cikakkiyar nasara, Umman su Aeeshaa bangaren Hajja ta nufa.
Hira suke sosai, Hajja tayi gyaran murya, tare da kiran sunan Umma.
Cikin maida hankali kan mahaifiyar ta ta, ta aje cup din dake hannun ta, ta amsa,
"Khadeeja, na dad'e ina tattauna wannan maganar a zuciyata, amma bansan ya zaki ɗauke ta ba, shiyasa ban sanar da kowa ba sai General, dan ina son muyi maganar dake da farko na ji ra'ayin ki tukunna se na sanar da yayun ki,"
"Hajja wannan wace magana ce mai mahimmanci haka?"
"Magana ce akan Aeeshaa, ina ganin tinda yanzu tana aji biyar na sakandire, ya kamata a tsayar mata da mijin aure, danni ban yarda da dogon karatun nan na boko ba aure ba, me kk gani?"
Kunya ce ta kama Umma, wai yau ita ce ta yi girman da ake maganar aurar da d'iyar ta, nan take wata iriyar kewar mijin ta ta kama zuciyar ta, kamar daga sama ta ji sunan da Hajja ta ambata, sannan wai fa shi take jiyo muryar Hajja tana cewa za a haɗa auren shi da Aeeshaan ta...........
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 3:
"Me kuke tattaunawa ne haka, Tinda na shigo nake jin muryar ki?"
Zama yayi tare da kallon Khadeeja wadda ta bude baki, kamar tana cikin rud'ani.
Hajja ce ta ce,
"Ina fada wa Nana Khadeeja ra'ayina ne game da maganar da muka tattauna da kai jiya,amma naga kamar hankalin tama baya tare dani sam san,"
Da kyar ta tattaro murmushi ta saka a fuskar ta, ko ba komai Aeeshaa d'iyar ta ce, kaza na taka dan ta ba dan bata so ba, sai dan ta ladabtar da shi, sannan koma menene naka ai naka ne,amma kuma anya zata iya yin shiru akan wannan had'in da Hajja ke so ayi kuwa? Cikin sanyin jiki ta zame daga kujera ta ce,
"Baba barka da yamma,"
"Barka dai 'yar baba, ya abokina da matan nan nawa masu yanga?"
Sunkunyar da kan ta qasa ta yi sosai, saboda ita din akwai kunya matuqa, amma in ta bangaren kasuwancin tane, ko da qawayen ta ba wannan maganar wai kunya.
"Suna lafiya Baba munzo da su Abdul ma,Hajja qarama tana gida, kasan ta da aiki, ga son karatu, tace zata zo amma ba yau ba"
(Sannu Umma da gilla qarya😏)
"Allah sarki, gaskiya Aeeshaa tayo halayya irin ta ki uwar gida na, komai na dabi'un ta naki ne, Allah ya qara maku kyakkyawan hali ku yi koyi da Nana Aeeshaa,"
"Ameen,"
Suka amsa baki ɗaya, waya Baba General ya ɗauka, ya hau kiraye2, sai dai kawai su ji yana fadin,
"Assalamu alaikum,...... kazo da iyalan ka, ina neman ka......yauwa sai kun shigo,"
Miqewa Umma tayi dan zuwa wanke hannun ta, da tai ciye2,
"Ina za ki je kuma? Ai zaman kusan naki ne, dik da naga ba kizo da Aeeshaan ba amma maganar nada mahimmanci wajen Hajjan ku, ya kamata a yi ta a yau,"
Wani abu ta hadiya mai d'aci a maqoshin ta sannan ta koma ta zauna, dan indai bata b'ata ji ba, wannan had'in ba yi mata ba sam.
"Hannu zan wanke kafin su iso,"
"To...to... je ki, ki dan taho min da abin sha,"
Hajja ce ta miqe da sauri tana bawa mijin nata hakurin rashin kawo masa abin sha da bata yi ba, nuna mata yayi babu komai, tayi zaman ta, ga Khadeeja nan, ai ba sai ta tashi ba.
(Uwar gida wannan ba dalili bane da zai sa miji ya dawo taqamar kina da yara ki make a gefe, qafa daya kan daya, kina kallo kina watsa inibi, da juice, ki sa yara su kaima baban su komai, ke bazaki je ba, in mijin kine ya aminta, saboda baya son wahalar ki, baya son kin gama aiki sannan ki zo ki wahala kuma ya amince yara sukai masa, kuma ki ka tabbatar har ranshi amincewar take shikenan baki da matsala Allah ne ya kashe ya baki, amma baki da dalilin zama in ba shi ya aminta ba)
Ɗaya bayan ɗaya suka dinga shigowa, Abdul da Ameena kusa da Hajja suka zauna, amma daga baya Baba General yace su shiga ciki suyi wasa, sai da suka qara minti bakwai kafin mai sarauta Khaleefa ya shigo, yana wani babbata rai, ya samu gefe ya zauna shi kaɗai, da kyar ya bude baki yayi sallama ya gaida su, in badan sun kalli leben shi ba ma, ba mai gane me yake faɗa.
"To da farko dai zan yiwa Allah godiya daya bani zuri'a kyakkyawa,mai riqo da addini kamar ku, kuma ina maku godiya akan hadin kan ku da zumuncin ku, musamman kai Abubakar, ka riqe zumunci guda biyu, na farko na 'yan uwantaka, sannan na abokantaka, ka tsaya tsayin daka iyalin Salihu basu koka ba, kuma qanwar ka da take bazawara bata wulaqanta ba, Allah ya saka maka da alkhairi,"
"Ameen,"
Kowa ya amsa, banda mai muqami, (Khaleefa).
"Toh saboda wannan zumunci naku ya qara qarfi, hajja da ni mukai tinani, muka ga tinda Aeeshaa ta kusan kammala Secondaryn ta, me zai hana da ta gama a aurar da ita, tinda a wannan zamanin ba kowacce yarinya bace zata fara makarantar gaba da Secondary ba ba tare da ta lalata rayuwar ta ba,"
Khaleefa ne ya dan ja guntun tsaki, dan za ayi maganar yarinyar nan me zai sa sai an wani kira su? Kawai dan a hana shi shan iska.
Sabeer kuwa wani farin ciki ne ya lullube shi, musamman da ya ji an yabi mahaifin shi, kuma anyi zancen auren Aeeshaa, tabbas yau addu'ar shi ta shekara da shekaru zata amsu, musamman yau dinnan haka kawai yake sake jin ta sabuwa a zuciyar shi, tin da ya ɗora ido akan ta yaga yanda ta girma ta yi kyau ya ji bai ma kan shi zaben tumun dare ba.
Hassana dake zaune, tana qunquni a ran ta, na ganin ita da ta girmi Aeeshaa nesa ba kusa ba ba wanda ya yi maganar aurar da ita da abin son ta, sai qaramar yarinya kamar Aeeshaa, ita Degree gare ta bangaren Accounting, amma Baba General ya hana ta aiki yace sai sanda tai aure tayi a gidan mijin ta, a yanzu ma bata da samari, ina ga ta fara aiki? Ai gudun ta zasu nayi suce tafi qarfin su.
"Kai Khaleefa nayi2 ka samar ma kan ka macen aure, amma girman kai ya hana ka, na san komai lokaci ne, na so ace na baka dama ka zabi wadda ta yi maka, dan kai auren soyayya irin nawa da kakar ku ka more aure, amma ka tsaya ruwan ido, kamar jira kk a kawo maka mace daga gidan sarkin makka,to mun yanke shawarar aura maka Aeeshaa dik sanda ta kammala makarantar ta,"
Su ukun a tare suka miqe tare sa furta,
"Whattt!!!!"
"Yes, Khaleefa nace zai auri Aeeshaa, meye naku a ciki da kai da ke?"
Komawa Sabeer yayi, cikin tsananin takaici da qunar rai, tare da karyewar zuciya mai tsanani, idon shi ya kad'a yayi jawur, jijiyoyin kan shi duk sun firfito.
Hassana kuwa kuka ta saka, amma qasa2, yanda Maman su kawai ke jin ta, sai zungurin ta take da qafa amma bata daina ba.
"Ina sauraron ku, wannan reaction din da kuka nuna min na meye? Baku goyon bayan hukuncin mune ko mi?"
Shiru wajen ya ɗauka, Umman su Aeeshaa ba abinda take sai ambaton Allah, wannan wanne irin hadi ne? In bata manta ba, ta san Hassana ke matsanancin son Khaleefa, kuma daga alama Sabeer na son Aeeshaa, ba dan kar a ga rashin kunyar ta ba, lallai da tai bayani, amma bari ta jira ko yayun ta zasu fahimtar da Baba General.
"Ba fa na so ina magana ana min shiru, alama ce ta hukuncina bai ba, kuma a cikin ku ba mai iya bayyana meke ran shi, in ba zaku amsa ni ba kowa ya tashi ya bar min parlour,aure ne inshaa Allah ba za a fasa ba, dan in ta wannan shashashan ne ba zai aure ba ina jin, yaro kamar wanda aljana ta aura,"
"Allah ya sanya alkhairi, ya musu albarka gaba daya, ai bamu da abin cewa Baba, sai dai mu maka godiya da fatan qarin imani da nisan kwana mai albarka,"
Cewar Baba Basheer kenan.
Baba Abubakar ma addu'a yayi da sanya albarka, daga nan Umma ta san magana ta tsaya a haka kenan, itana addu'a tai ma mahaifan ta, da godiya, nan yaran suka fice, Hassana ko gaban ta bata gani dan kuka, tayi bangaren su, Maman ta taso bin ta, dan ta lallashe ta,amma ta zauna dan su ci gaba da hirar su ta zumunci kamar yanda suka saba bayan an yi taro makamancin haka.
Maman Khaleefa ita hadin ba wai ya dame ta bane, bata da wani ra'ayi akai, amma Baba Basheer yayi murna da hakan, dan yana zargin danshi aljanu sun taba shi, bai taba zancen mace ba a rayuwar shi, kuma bama yaso a masa.
Kamar zai tashi sama, haka ya ke tafiya dakin shi, hannun shi a kan shi, ya kai ya kawo haka yake shafa kan, kamar