Showing 30001 words to 33000 words out of 69262 words

Chapter 11 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1040

ta da ido, ya sa a handsfree, Aeeshaa tayi sak kamar ba abinda ke faruwa, sai sun gama waya ta sha kukan ta, ko zuwan Ameena ma da kyar ya yarda tazo,bayan sharuda daya yi ta kafa mata.

Aeeshaa tsoro take ji ko wata cutar ce ta kama ta, dan kuwa cikin ta na dagawa, ga qirjin ta da ya cika taff, sai ido da ya zurma mata, ga shi sai kwadayin da take yawan ji ke qara tsorata ta.

'Oh ina ma ina da waya ko gida dana kira na sanar ma da ummana meke damuna yanzu, ko ba zata kula ni ba a qalla ko mutuwa nai an san meke damuna,'

Hawayen ta ta share, ta gyara kwanciya a kujera, wani qamshi ta ji yana tashi, kamar ana soya man gyada irin asalin man gyadan nan, kamar kuma ana soya nama, qamshin dai mai dadi sosai, da ga dikkan alama daga maqotan ta yake fitowa, tashi tayi ta zauna tana ta shaqar qamshin, hankalin ta ke qara tashi in tana shaqa, tana mutuwar son taci ko me ake soyawa dinnan.

Ga shi ita ko irin gaisawa da maqotan nan bata yi ba Khaleefa ya hana, ko sau ɗaya bata taba shiga masu ba,kuma ya bata umarni in an zo indai ta leqa taga bata san mutum ba kar ta bude ta koma ciki, ta tabbata sun sha ganin inuwar ta tana leqa su kuma ba ta bude masu ba, Ohhh wannan zaman kafurci haka, in ta mutu ba wanda ya sani sai ya dawo daga yawon ta bididin shi sannan.

Kasa hakuri tayi, dan yanda take jin ta ko zai kashe ta ne in ya dawo sai ta ci me ake soyawa.

Hijab ta saka ta dakko makulli ta fita, sai da tai addu'ar fita daga gida sannan ta taka waje, wata ni'ima ta ji ta daki hancin ta, tinda aka auro ta aka kawo ta bata sake fita ba, iyaka ta hango waje in tazo bude gate da safe ko da dare in zai fita.

Inda qamshin ke fita nan ta bi, tana zuwa soron gidan ta ji inaaa ba zata iya shiga ba, juyawa ta yi zata koma suka ci karo da wata matashiyar budurwa, ta girme ta amma ba sosai ba,

"Baiwar Allah sannu,"

"Yauwa"

"Wajen wa kk zo?"

"Ummmm.... damaaa... ni..nii maqociyar nan gidan ce, ni ke zama a wancan gidan dake dama da wannan, na dan leqo ne a gaisa, kuma na ji ba zan iya shiga ba, na dad'e a unguwar ban shiga ba sai yau na ce bari na leqa a gaisa,ke fa? Wace ke?"

"Hummm... Ayyaaa ashe kece amarya me rowa ko?"

Dafe qirji tayi ta fiddo ido,

"Me rowa kuma? Rowar mi na maku? Anan gidan kk kema?"

"Hhhhh kwantar da hankalin ki, ina nufin rowar ganin kan ki, eh anan gidan nake, suna na Hadiza, mu shiga ciki, ai na sha zuwa baki bude ba, ni da Goggo ma mun sha zuwa baki bude ba"

Suna shiga ciki Aeeshaa ke bata hakuri,ta nuna mata mijine mai kulle take da shi, ba laifin ta bane, mamaki Hadiza tai, dan ita ba qaton da zai mata kulle tabbb, dama har yanzu ana kulle? Kusan akan kulle ta koma qaramar bazawara fa, inaaa, ba ɗan da zai mata kulle ta zauna.

"Goggo ga amarya mai rowa nan ta zo gaida mu yau,"

Wata dattijuwar mata ce mai tsananin kamala, da nutsuwa,tare da annuri a tattare da ita, tana ta soya quli2.

"Ahhh lale maraba da ke amarya me rowa,"

Dan dariya Aeeshaa tayi, tare da hadiye yawun daya yanko mata, ganin quli mai zafi, ga qamshin nan kamar ana soya kaza.

Gaisawa suka yi, ta gabatar masu da kan ta a matsayin Aeeshaa, sannan ta basu hakuri akan mijin ta ne bai son kowa yana zuwa mata, kuma bata son kowa yaje, ta masu bayani yanda zasu fahimta, suka kuwa fahimta din, sannan ta musu alqawarin xata na shigowa in dai ta samu izinin shi, sannan zata roqe shi yana bari ko Hadiza ce tana shiga mata hira.

Nan da nan Goggo ta gane me ke tattare da Aeeshaa, dan haka bata bata lokaci ba wajen debo mata quli mai zafi ta aje mata a gaban ta.

Aeeshaa kamar wata mayya haka ta dinga cin qulin nan,Hadiza nata bata labarin su,inda Goggo ta koma suyar ta.

"Mahaifina ya rasu, a da mahaifina na da hali dan kasuwa ne, muna cikin rufin asiri, kinga dik girman gidannan da kyaun shi abinda zamuci ma wahala yake mana, ba mai taimaka mana daga ni sai mahaifiya ta, mahaifina ya rasu sakamakon rashin lfy da yayi na qanqanin lokaci, kafin ya rasu ya min aure da dan abokin kasuwancin shi, muna zaune lfy, lokacin da mahaifina ya rasu ya fara sauya min, yana min rashin mutunci harda duka da zagin iyaye, ni kuwa na ga ba zan dauka ba na nemi saki, da farko yaqi, amma daga baya iyayen shi suka zuga shi ya saken na dawo gida, yanzu haka ina zaune da mahaifiyata danake kira da Goggo, dangin mahaifina va mai taimaka mana, a da kuwa kan ya rasu qofar gidannan da cikin gidannan dik dangin mahaifina ne, Gaoggo tai ta dawainiya da su, dangin ta ma basu cika zuwa ba, saboda kowa ya kama qasa, zumuncin su suke yasu yasu na masu akwai, da da take da shi da ita ake yi, kasancewar ta babba, amma yanzu da ta rasa ko rashin lafiya tai ba mai zuwa duba ta.

Yau dinnan ta fara soya quli saboda tace ana samu a sana'ar ga quli ga mai da zata fidda, amma akwai wahala,"

"Wayyoo Allah ya jiqan mahaifan mu, ya qara rufa asiri, bari na koma bamu kula da lokaci ba har an kusan magrib,"

Suna can suna hira zuwan Khaleefa uku bata nan, dik inda hankalin shi yayi dubu ya tashi,ina taje to?

Hadiza ce ta rako ta dauke da ledar quli2 a hannun ta, da gyada mai gishiri, wanda sukai ta ja in ja da Goggo kan ta anso, musamman da taji halin da suke ciki, sai dai ta digawa Hadiza ayar tambaya akan wasu abubuwa data gani a tare da ita.

Bude gidan take Hadiza na riqe da ledojin a hannun ta, ya qaraso.

Hadiza na ganin shi ta kafe shi da ido kamar tsohuwar mayya, jikin Aeeshaa ne ya dauki rawa, cike da tsoro ta qarasa budewa ta bude gate ta shige, ko amsar kayan wajen Hadiza batai ba,

"Wayyooo Allah ka kawon a gaji, tabbas ban kyau ta ba na fita ba da izinin shi ba, ya Allah ka tausaya min kar ya kashe ni😭😭"

Khaleefa ne ya gama parking ya fito,

"Ke ina kk qoqarin shiga ne?"

"Amarya zan bawa ledar nan, quli taje siya gidan mu, tana son ta maka kwadon letus,"

Aeeshaa da ta dawo rufe gate, a tsorace baki sake take kallon Hadiza, irin wannan qarya haka nan take ba ko gezau a tare da ita,kamar iyakar gaskiyar ta ta fada.

Kallon Aeeshaa yayi, ya amshe ledar ya gani da gaske quli ne, ya gyada kai ya wuce tare da sake ledar a qasa.

Wata iska Aeesha ta sake, mai mugun qarfi tare da dafe cikin ta da taji yana murda mata.

"Hadiza yaushe kk qirqiri wannan maganar?"

"Shiiiiii.. maza rufe ki shiga kan kiyi laifi, in yace da magaribar nan kice nema akai tayi ba a samu ba,in kina da letus kin tsira in baki da shi ki ce kin zaci akwai ne,"

"Innalillahi, Hadiza qarya fa kenan,"

Ko kula ta batai ba ta wuce gida, Aeeshaa ta ja ta rufe gate, sai sanda take ta shiga gidan, bata gan shi ba,ta je kitchen ta ko yi sa'a tana da letus da cabbage, ba ma idean yin kwadon akan ta,nan da nan ta fara daka quli, tayi kwado, zuba nata tayi, ta zuba masa na shi, ta dakko da juice da snaks ta kai masa, bata rabo da snaks saboda yunwa ko baqi, uwar gida in kk saba koda cincin ne ba a rasawa gidan ki wallahi kin kama matakin riqe gidan ki, coz ko miji ya dawo baki gama a binci ba zaki zuba masa, wanda ba a fata ma ki zama daga cikin matan da basu gama girki da wuri, sannan in yara gare ki, kin makara baki masu abin tafiya da shi skul ba zaki iya hada masu da juice da wani snak din su tafi, kan su dawo kinyi abinci mai nauyi,da zasu ci su qoshi, kuma baqi kin huta da kame2n me zan basu?

Kwankwasa dakin shi tayi, ta ji ya yi banza da ita, ta jima a bakin qofar bai amsa ta ba, Khaleefa ko sallar isha'i bai ba, an wuni sabawa Allah jikin shi har wanu ciwo yake masa, dan haka yayi wanka ya kwanta yake bacci.

Gajiya tayi ta maida fridge, ta dau nata ta hau ci tana lumshe ido.

Bayan tayi sallah ta kwanta bacci itama.

**********************

Aeeshaa fa yau ta burkice masa, Khaleefa yayi tsawar yayi ihun taqi shiru, ba dan komai ba sai dan motsin da take ji a cikin ta, ga shi ta yi qiba yanzu, dik da ba sosai bane ramar nan ta kau, hasken ta har tsoro yake bata in ta kalli madubi, shi kuma baida masaniya akan masu ciki, dan ba wani shiga shirgin mutane yake ba balle yace ya san ya ake yi.

Ga takaicin ta yayi qaryar ba su gari, sunje yankari, ga shi tana jin boobs din ta na ciwo, dan haka yau dik yanda taso ta daure kasawa tayi, so take taga Hajja ko Umman ta ko Maman shi ko Ummeen Sabeer, haka akai sunan Balqis har ta koma bata je ba, ita kuma in zata zo yace mata sunyi tafiya, haka rayuwar ta zata qare ta fito daga kurkukun Ummah ta faɗa na Khaleefa.

Yau ba yankari ba ko cikin garin baushi suka je sai sun dawo, Hadiza ce ta koya mata wannan dabarar, tace tai ta kuka ko ya dake ta kar tai shiru, har sai ya gaji dan kan shi ya kai ta gida.

"Enough !!! ke jaririya ce dazakina min wannan dan iskan kukan kina wani buga qafa?"

Sake rikicewa tayi da wani kukan harda kwantawa a qasa, tana kiran sunan Hajja.

Takaicin ta ya kaima Khaleefa ko ina, dan haka ya bata rai yace,

"Dakko hijab muje,"

A duqe ta dakko ta bi shi, har ya shiga mota ya na jiran ta bude gate, tsabar rashin imani da tausayi irin na Khaleefa, mamakin shi ya daina kama ta yanzu.

Zuwa tai ta kama tana son ta ja ta kasa, ganin ta kasa ya sashi fita yana ta masifa wai bata da amfani yanzu, komai ta daina masa, sai an magana tace bata da lfy,amma ya san maganin ta bari su dawo, ita dai tayi shiru tana jiran ya bata izinin shiga, kar ta shiga tayi laifi, in fact bata san ma ta ina zata zauna ba, gaba ko baya oho.

Tsayawa tai ya daka mata tsawa.

"Dallah ki shiga gaba mu je, in ba haka ba na fasa kai ki din naga abinda zai faru,"

Ai kafin ya rufe baki ta shige gaba, tsakanin murna da tsoron wanne irin ciwo ne za a ce yana damin ta, dan daga nan so take su wuce asibiti, ba dai ta son suje da shi ne kawai.

Sanda suka isa, Aeeshaa ta sha wani abu mainsuna mamaki, domin kuwa khaleefa ne ya bude mata mota, ya rungumo ta, sannan ya kai bakin shi kunnen ta, yana mata magana, tare da yashe haqora.

"In kk kuskura wani ya gane irin zaman da muke zan shayar dake mamaki in mun koma,kuma zan iya qoqarina naga baki sake zuwa ba sai kin shekara"

Murmushin yaqe ta fara, Hajja na zaune a waje tana shan iska cikin shuke2n dake bangare guda a cikin gidan, ta d'aga kai ta yi ta kalle su cike da farin ciki da tsantsanr sha'awar su ta qaraso tana fadin.

"Lale maraba da amare da angwaye lallai ne, shiyasa ashe aka daina ganin ku, wannan dan kad'afin ya bi ya maqalqale ki kamar zai shige jikin ki, bar ta ta zo nan dallah kamar wadda za a cinye,"

Yana sake ta Aeeshaa ta je da gudu ta fada jikin ta ta saka kuka, Khaleefa ya cika famm, bata ji me yace ba kenan,

"A'ah mene ne na kuka?"

"Hajja nayi missing din ki sosai,ina Baba General?"

"Ya fita, kin san shi in ana wani abun haka daya danganci sojoji yakan leqa, kar ya zauna a gida wai tsufa ya masa mummunan kamu inji shi"

Dan dariya suka yi, suna tafiya ciki Khaleefa yace,

"Ai ba ki ji yanda ta matsu mu zo ba, bata jin daɗi kwana biyu, nayi2 na kaita asibiti ta qi, wai ita na kawo ta wajen ku, shine nace bari dai na kawo ta, indai hankalin ta zai kwanta,"

"Ahhhh kayi dabara da ka kawon ita ai, Alhamdu lilLAAH ashe da rabon zan ga dan ku, Allah ya sauke ki lfy ya sa a haifi mai albarka,"

"What ar u saying? What do u mean?"

Shine tambayoyin da suka watsa wa Hajja a tare,

"Ina nifin kina ɗauke da ciki, sai dai ban san wata nawa bane tinda ni ba likita bace,ke in banda ke yaushe rabon ki da al'ada ? Ko kina yi ne?"

Sai a sannan ta yi nazari, tabbas yanzu kusan wata hudu bata gani ba, abun na damun ta kashhhh amma ita wawuya ce, ya bata taɓa wannan tinanin ba?

Hawaye ne ke zuba a idon ta ta rasa na me ne, farin ciki ko baqin ci.

Hajja da Aeeshaa ne  su juya gaba ɗayan su suka kalli Khaleefa dan ganin reaction din shi akan wannan lamari................

*Me kuke tinanin khaleefa zai yi? Zai zo cikin? Xai qi cikin? Shin zai yarda ma tana dauke da ciko?*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 14

'

Yanayin Khaleefa ba bu mai iya cewa ga shi, hangowa kawai yayi ta haihu, wannan kyakkyawan jikin nata ya sauya ya tattare ya tamuqe, aikuwa za a yi ta, dan kuwa sai dai su rabu, tinda ba wai son ta yake ba dama, yanzu ma saboda kyaun jikin ta yake daga mata qafa,

'Ai kuwa daga nan sai a asibiti a zubar da cikn nan, ba zan dauki hatsarin rasa kyakkyawan jiki irin wannan ba'

"Ya ya dai kayi shiru?"

"Wato Hajja murna ce ta min yawa, Allah ya sauke ki lfy Habibty, Allah ya kawon babyna lfy ko mace ko namiji, i will love u both with all my heart,"

Kafe shi da ido Aeeshaa ta yi, kalaman shi ina ma gaske ne,ko da ba son shi take ba itama amma ya na da daɗi ka ji kalmar so from ur husband.

Hajja ce ta qara rungume ta, tana taya ta jin daɗinkalaman Khaleefa,

"Alhamdu lilLAAHi yanzu ba ga shi har an wuce wajen ba, da kuna ta baqin rai za a hada ku aure, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala ba zai hango ba, yanzu gashi harda albarkar aure, kunga ko ai sai godiya, Allah ya kare ku daga dikkan abin qi, kuje yanzu ku gaisa da iyayen ku, in yaso muje asibiti tare kan General ya dawo,"

Wani baqin ciki Khaleefa ya hadiye tare da lumshe idon shi da suka fata sauya kala.

"Hajja ai ba sai kinje ba, kiyi zaman ki kawai, zamu je, abinda dubawa ne kawai za su yi suga wata nawa ne, kuma daga nan zan kaita ta dan yi shopping,ko kina nufin shima da ke zamu ki takura mana?"

Cikin dariya da jin daɗi Hajja ta shafa Aeeshaa ta baya, sannan tace,

"Ohhh yaran zamani ai sai ku tashi ku je, in yaso daga baya mun ji labari daga wajen ka, kuma ya kamata ka saima yarinyar nan waya, haba, yarinya na zaune in ka fita ai ko gida ta kira mu ji lfyr ta, in kuwa ba ku rage tafiye2n nan ba nan ma cikin nan na cikin hatsari, in naji ba daidai ba na zo na dauke ta, sai ta haihu na dawo ma da ita,"

"Bama zakiji komai ba, Hajja ba dan ba dan ba dana ce sa idon ki yayi yawa,"

"Kaci uwaka, ni in iya shege kk ji na fika, kaji min dannema, sa idon me na maka? Da Allah ya sa na aje duwais dina waje daya bana zuwa maku akai2, nan Mamar ka ta so taje na hana ta? Saboda ban ji labari Khadeeja ma taje ba, ya kamata a baku waje kar ana yawan xuwa maku, saboda gudun kar kuna daukan zugar mutane, shine zaka ce na sama ido, bari dik sati zan dinga zuwa dan uwaka kaga sa ido ai,"

Yasan zata iya da sauri ya duqa gaban ta yana dariya, inda jikin shi ke gugan na Aeeshaa,

"Yi hakuri uwar gida sarautar mata, wasa dama nake, ai in ba dan ke ba da nayi asarar samum mace kamar Aeeshaa, ke dai ba abinda zan iya ce maki sai addu'ar Allah ya qarawa rayuwar ki tsaho da imani,"

"Ameen,shi yasa kk burge ni, akwai tsoron Allah, da sanin ya kamata, yanzu bakin ka ya bude,wato ka samu wadda zaka na hira da ita ko? Mu ka maida mu 'yan iska ba mu isa ka mana magana ba da"

Dariya sukai banda Aeeshaa data matsu ya tashi a wajen, Khaleefa al'amarin shi yafi na tsohuwar karuwa ban mamaki. Yana namiji ya iya hada magana, da kissa da munafurci, da fuska uku.

Tausayin kan ta ne ya kamata ta lafe jikin Hajja.

"Ta shi mu je wajen su Mama mu gaida su sai muje asibiti ko dear,"

'Dear my foot, mugu kawai'

Ta ayyana a ran ta, a hankali ta miqe ta bi bayan shi ba ɗan ta so ba.

Sun shiga sun tarda mama tana cin abinci, ganin su ya sata tashi ta tari Aeeshaa, kallon kayan jikin ta kawai take, wanda gaba daya zasu kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login