Showing 33001 words to 36000 words out of 69262 words
Chapter 12 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
dubu dari, in aka dauke dankunnen ta na gold, murmushi take ta zabgawa da masu lale, a babban parlourn nasu suka zauna, Khaleefa ya gaida Maman nashi. Aeeshaa ma cikin kunya sosai ta gaida ta, amsawa tai tare da debo masu abinci ta aje masu a dinning, ta masu izinin zuwa su ci.
Aeeshaa ta ci abincin sosai, sai ta ji daɗin shi sosai, Khaleefa sai kallon ta yake, dama haka take da ci? Lallai dole ta cika tai fam haka.
"Khaleefa in kun gama ka zo,"
"K mama na gama ma muje,"
Murmushi ta yi ma Aeeshaa wanda bai kai zuci ba, Khaleefa ya bi bayan ta.
Suna shiga d'akin ta hade fuska sosai kamar bata taba dariya ba.
"Mama lfy?"
"Ba qalao ba, yanzu da hankalin ka, ka kashewa yarinyar nan kudi haka a jikin ta, ka duba kayan ta daga jaka har takalmi zuwa suturar dake jikin ta sun kai dubu dari zuwa sama.da hakan, banda dankunnen zinaren dake kunnen ta,tinda akai aure baka kawo ta ba, yau da kuka zo in banda baqar rowa irin taku ko 'yar tsaraba ba zaku zo mana da ita ba, ku kuma kuna can kuna cin daɗin ku, dibi yanda yarinyar nan ta yi qiba tai mui da ita, kai kan ka kalle ka, da haka kk? To bari kaji, yanda kk kula da ita nima haka zaka na kula dani, in ba haka ba zaka hadu d fushi na,"
"Dan Allah kiyi hakuri,inshaa Allahu dik abinda kk so shi za ai,"
Kuɗi ya sa hannu a aljihun shi ya bata,kimanin 20k, amsa ta yi ba dan ta yaba ba qoqarin shi ba, ko ita tana da sama da su a gidan, dan haka a ciki ta masa godiya, tashi yayi zuciyar shi ba daɗi,ko da ba son Aeeshaa yake ba, baya son kowa yana mata abu mara kyau, a bar masa matar shi, in yaga dama ya mata kirki, ko akasin hakan.
"Tashi muje,"
"Ka bari na ma mama sallama,"
"Dalla malama.nace muje ko? Ko taurin kai zaki fara min a nan d'in ma,"
"Ayya ba haka bane, kayi hakuri,ba zan sake maka musu ba,"
Kan ta a qasa suka fice, mama na kallon su ta window tana qara lissafa kudin kayan jikin Aeeshaa.
Bangaren su Sabeer suka nufa, a tsaye ya tsaya yana gaida Ummeen su Sabeer, Hassana na kitchen ta fito, kallo ɗaya ta masa zuciyar ta ta hau harbawa da mugun gudu, saboda Khaleefa ya yi wani irin kyau, bata jima da dawowa daga gidan Bilqis ba data raka komawa gidan ta, hadiye wani abu tayi da ya tsaya mata a wuya, ta gaida shi, Aeeshaa ma saurin gaida ta tayi, ta amsa mata cikin sakewar fuska, dan yanzu bata jin haushin ta sam, itama ba laifin ta bane da aka aura mata shi.
"Mu je,"
"To,..... Ummee ya labarin Yayana? Shiru, kuna waya kuwa? Ko ya dawo?"
"Yana nan lfy Aeeshaa,kullum......
"Zaki wuce mu je ko kuwa?"
Da qarfi ya dage labulen da ace bai kafu da kyau ba daya fado,tashi ta yi cikin sauri bata sake waiwayar kowa ba ta fice, daga Ummee har Hassana sun fuskanci wani lamari a tare da hakan, lamarin tsoro da fargaba tare da tashin hankali a tsakanin ma'auratan.
"Ikon Allah, sai kace wani kububuwa,"
"Babu ruwan ki Hassana, Allah ya kyauta,kin gama ne?"
"Eh sauran kadan,"
"K wuce ki qarasa abinda kk, ba ruwan mu a lamarin su, Allah ya kare abin qi,"
"Ameen Ummee,"
A waje kuwa Khaleefa ya haɗe girar sama da ta qasa, akan mi Aeeshaa zata tambayi Sabeer, sai kace an faɗa masa wani abun ne dan ta tambaya, tinda ita bata san ma halin da Sabeer ke ciki ba game da ita har yau.
Tana shiga ya ja mtar da qarfi, Baba mai gadi ya je ya bude shima da gudu.
Basu tsaya ko ina ba sai wani asibiti, dake kan hanyar unguwar tasu, private hospital ne mai tsada da kwararrun ma'aikata, nan da nan ya bude mata file, ta bi layi, akai mata BP da gwada nauyin ta, tana zaune kamar minti goma, aka kira ta ta shiga.
Miqewa yayi ya bi bayan ta.
Gaisawa sukai da likitan, sannan ya fara bayani.
"Doc dama na kawo mata ta ne dan Allah a taimaka a cire mata cikin da take dauke da shi, yarinya ce, ba zata wuce 20 ba, bana son abinda zai taba lfyr mata ta, beside i am not ready to have a baby,"
Kan Aeeshaa na duqe tana ta share hawaye masu zafi, dan tin da ta ji ciki gare ta ta ji son cikin ya kama ta kwarai, itama tana son ta ga dan ta a duniya,amma qarfi da ya ji ana neman a raba ta da shi, kallon Doctor ta yi, idon ta yana nuna a tausaya mata,ba wanda zai ga Aeeshaa a lokacin bai tausaya mata ba.
Likita ya karanci halin Khaleefa a bayanan shi, mugunta ce kawai zata sa a cire cikin ba komai ba, kuma in yaqi amsar request din shi zai iya zuwa wani wajen a cire cikin da qarfin tsiya.
"K yallabai an gama, amma zan baka shawara, yanzu wannan gwajin da akai ma matar ka ya nuna tana dauke da mummunan hawan jini, wanda cire cikin nan zai iya jawowa a rasa rayuwar ta, so zan baku magani, ta dinga sha, nan da wata biyar inshaa Allah zai fice gaba daya, yanzu da tasha zai dinga fita kadan2, har ya gama fita dika, sannan zan saka mata wata kwayar magani yanzu a gaban ta, inshaa Allahu, za a samu nasara, shawara dai da zan baku shine ku dinga yawan zuwa ina duba ta ana saka wannan kwayar maganin"
Aeeshaa kukan ta ne ya qaru, lallai wannan likitan bai da imani, kuma bai san aikin shi ba, Allah ya saka mata ta dinga maimaitawa.
"Yanzu zamu je mu auna muga wata nawa ne cikin, in ba damuwa?"
"Nooo ba damuwa,nima zan so na ji wata nawa ne ai, amma likita kana ganin wata biyar bai yawa ba?"
"Kar kaji komai, ai kamar yau ne, a hankali zai dinga fita sabida matsalar datake da ita,ba dan matsalar nan ba ni da kaina zan markade ko meye a mahaifar ta ya fice,"
"Innalillahi"
Aeeshaa ta furta hakan cikin zaro ido da fashewa da kuka mai tsanani,
"Shut up stupid, anan ma sai kin nuna halin naki ko, na ji maganar nam wajen Hajja kiga yanda zan maida ki,"
Murmushin yaqe yayi kula da Doc. Na kallon su.
Nan take Dr. Ya qara tabbatar da zargin shi, ba yau ya saba ganin maza na son a zubar da cikin halak ba, masu shegu su zubar masu na sunna su zubar sabida dalilin son zuciya.
"K madam muje damin scanning din, ba anan ake ba,ki kwantar da hankalin ki ba wani matsala, zai fita a hankali, ba zaki san ma yana fita ba saboda maganin da zan baki zai hana maki jin zafi,"
Wani daki suka je, likita yayi yayi Aeeshaa ta fada masa meke faruwa a tsakanin ta da mijin ta,amma sam taqi, wannan abinda ya shafi iyalin su ne, ya yi aikin shi kawai tinda shima ba imanin gare shi ba.
"Look baiwar Allah, Aeeshaa kk ko? (Daga masa kai tayi) k, kinga na fahimci halin mijin ki, shi yasa na ke tambayar ki taimaka maki zan, dan inna bar shi ya kai ki wajen wasu, zubarwa zasuyi a banza,na sha ganin cases haka, so ki amince min zan taimaka maki,"
"Dan Allah ka tausaya min,ina son cikin nan, kar ka zubar min, bamu san ma cikine dani ba sai da muka je gida yau, kakar mu ke faɗa, yanzu tana jiran result ne, dan Allah kar a zubar min da abinda ke ciki na"
"Ki daina kuka, inshaa Allah sai kin haifi abinda ke cikin ki,"
"Allah ya yarda, na gode,Allah ya saka maka da alkhairi,"
"Ameen, kwanta yanzu na duba na ga ni,"
Scaning akai mata, daga qarshe likita ya gano cikin ta ya kai wata hudu, amma ya yi takardar qarya, yace wata biyu ne.
Ko da ya sanar da Aeeshaa plan din shi, tayi murna sosai, sannan wannan maganin da yace tana zuwa ana saka mata antinatal care zata na zuwa, ya rubuta har da lokacin daya kamata tana zuwa, ya bata magungunan da zasu qara mata lfy da abinda ke cikin ta.
"Yallabai u ar good to go, amma akwai shawara sai ka jure, zaka dan dakata da yawan saduwa da ita, ya zamana lokaci zuwa lokaci ne, saboda mu samu maganin mu yayi aiki da wuri,"
"Ba damuwa na gode Doc, na gode sosai,"
"Akwai bayanai dake cikin wannan takardun dana rubuta zaka samu dik abinda kk nema,"
Aeeshaa kan ta a qasa, ta qi bari su hada ido da Khaleefa kar ya fahimci kwanciyar hankalin da ta samu.
*********************
Khaleefa ya fita sha'anin Aeeshaa kullum amma yana sata gaba ta sha magani, ko neman ta ya hakura,sai dai sanda jarabar shi ta motsa akan ta zai je d'akin ta yayi ta romancing din ta har sai ya biya buqatar shi, Rebecca kuwa kamar sallah a ta bangaren ta tsabar murnar samun khaleefa akai akai, ba damar ta tambayi dalili.
Da lokacin Antinatal yayi Aeeshaa zata dau adaidaita sahu ya kai ta asibiti, da ta gama ta koma gida.
Umma tayi murna sosai da labarin cikin da Aeeshaa ke ɗauke da shi, amma ko da wasa bata sa maganar a labban ta ba balle wani ya ji, kayan yara unisex take siya a boye in ta je sarin kayan ta.
Lokaci zuwa lokaci takan je gidan, tai kicin2, wai ita a dole kar a gane murna take zatai jika.
**********************
Ziyara ce ta musamman yau Maman Khaleefa zata kai ma su Aeeshaa, dan ta kwana biyu bata ga dan ta ba, sannan bata ji aike ba, yau so take ta je taga meke hana shi zuwa, in ma dan Aeeshaa na da ciki ne ya daina bata kulawa zatai maganin su dika.............
*Allah ya kai hankalin Hajja kan ki Maman khaleefa kici.......🙊*
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 15
Aeeshaa na ta bacci Mama na ta kwada sallama bacci ya yi daɗi Aeeshaa bata ji sallamar nan ba, Mama dik ran ta ya baci, daki2 ta fara bi tana leqawa, ganin irin dukiyar da aka kashe a gidan ya qara bata haushi, yaran ta da akai ma aure ba wanda aka kashewa wannan dukiyar, (kamar Khaleefan ba dan ta bane) kwafa ta yi, lokacin da ta isa d'akin da Aeeshaa ta yi d'aid'ai take baccin ta cikin kwanciyar hankali, daga ita sai 'yar qaramar riga red mai hannun vest iya cinya, dik ta tattare sama, sai pant din ta red, ganin hakan bai sa Mama komawa baya ba ta yi sallama ko kwankwasawa ba har Aeeshan ta farka sai ma qarasawa da ta yi ciki ta tashe ta, cikin magagin bacci ta ture hannun ta, ta gyara kwanciya ta ci gaba da bacci, a zuciye Mama ta daka mata duka, ai kuwa da sauri ta miqe,
"Dan Allah kayi hakuri, b.... Mama???"
"Eh ni ce, kin kwanta kina ta baccin asara in da barayi ne suka zo sai dai su yashe ku su wuce, ko ina sai da na shiga, da alama mai gidan wanka yake, dan naji motsi a wani daki dana leqa,ke kuma kina nan kina sharar bacci abin ki,"
Aeeshaa kunya dik ta gama lillibe ta, suruka ta shigo mata d'aki ga shi kayan jikin ta ba wasu masu arziqi bane, kuma da alama ita ko a jikin ta.
Hijabin ta dake ninke a kan sallaya ta ɗauka ta saka, dogo ne har qasa, sannan ta fara tafiya tana nufin suje waje, amma baiwar Allahn nan ta samu bakin gado ta zauna, ganin haka yasa Aeeshaa durqusawa ta fara gaida ta, a ciki2 ta amsa,Aeeshaa mamaki take wannan ba halin ta bane data sani, ko kuwa dama ta boye ne kamar dan ta da ba kowa ya san asalin halayyar shi ba?
"Bari na hado maki abin sha Mama"
"Ki dafan harda dan farfesu, na dan ci nima, ni da gidan d'a na a ce wai abin sha kawai za a kawon,"
A zuciyar Aeeshaa dan ta ce zata kawo ruwa ba iya shi take nufi ba, dama dole zata had'o da wani abun mana.
Amsawa tayi a ladabce ta wuce da sauri.
"Ke ! Uban wa ya sa kika shigar min d'aki? Ko wani abun kk so?"
Yana fadan hakan ya jata jikin shi,yana kai hannun shi qirjin ta,tare da matsawa da qarfi, qara ta dan sake saboda zafin da ta ji, nan da nan ya kai bakin shi cikin nata, yana qoqarin cire mata hijab Mama ta leqo,
"Ihun me nake ji? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, me zan gani? Auuu wato qarar tawa ce kenan, kirana kk na zo naga me kuke yi ko,wayyoo Allah na na shiga uku, wannan abun kunya har ina,"
Khaleefa ido tsilli2, yama rasa me zai ce, ganin Maman shi na neman tara masa maqota ya hau borin kunya yana masifa.
"Ke Mama dama wake zuwa gidan mutane ba sanar wa? Yanzu da na san kina nan zanyi hakan ne? Dan Allah ni ki daina mana kuka tinda ba haramun muka aikata ba,"
Cikin parlour ya qarasa shigewa ya zauna,tare da matse qafar shi, jarabar shi ta motsa iyakar motsawa, gashi ta tashi tazo ba sanarwa,gaskiya shi ba ai masa daidai ba.
Aeeshaa kan ta na qasa idanun ta cike da hawaye,
"Yanzu dan zan zo gidan dana sai na sanar? Kuna nan kuna cin mai kyau kuna shan mai kyau, ina can zaune ni ɗaya,ko zuwa ziyara ta ka daina, mace tafi uwa ko?"
Cikin tsananin bacin rai ya miqe tsaye,
"Dan Allah mama meye haka? Tin rannan kk maganar muna cin daɗi, ke wahala kk ci? Ki dube ki ki dube mu mu dake waye yfi kalar cin daɗi, meye Baba baya baki? Meye a cikin gidan ki babu? Dan wanda na kawo ma iyalina shine abin magana? To kar ki manta fa bani na aurawa kaina ita ba, Baba General ya aje mana abinci kala2, wanda zamu kai shekara ko sama bamu cinye ba, iyaka ta na kawo na cefanen yau da gobe,komai an sauqaqa min, in kuɗi ne sai dai ki bama wani, baki son mu zauna lfy ne? In na fadawa Hajja kina zuwa gidannan me kk zaton zata ce? Ko kuma Baba General ko Babana? Mahaifiyar ta tinda akai auren nan ban taba ganin ta zo ba, shi yasa ashe Hajja bata son kowa yazo mana saboda irin wannan,"
Aeeshaa bata saba ganin d'a yana ma mahaifa irin wannan rashin kunyar ba, dan haka da sauri ta durqusa gaban shi ta kama qafar shi,
"Dan Allah Yah Khaleefa ka daina yi ma Mama irin wadannan kalaman, mahaifiya ba abin wasa bace, Allah na fushi da wanda iyayen shi ke fushi da shi, meye a ciki, dik abinda take so dan Allah ka mata, ku rabu lfy,"
Kauda kai yayi, ya san maganar ta gaskiya ne, amma kun san mutumin mu da girman head baya ɗaukan shawara
Janye qafar shi yayi ya wuce yana tsaki da surutai, d'aki ya shige ya buga qofar da qarfi wajen rufewa, sai da suka rufe idon su.
Aeeshaa kallon ta ta mayar wajen Mama wadda jikin ta yayi mugun sanyi, kamar wadda ruwa ya daka,ba qaramin kunyata ta Khaleefa yayi ba, ba abinda ya fi damun ta yanzu sama da in bata lallaba shi ba ya fada ma Hajja ai ta shiga uku, zama ta yi tayi kalar tausayi.
"Ohhh ni yanzu in yaran nan ya fada ma Kakannin shi ai na shiga uku,"
Aeeshaa ce ta je ta dora dumamen farfesun naman zabbi data yi ta kasa ci, ta sa a fridge,ta fara daukar mata juice ta kai mata kan ya dumama ta kai mata.
"Mama ki kwantar da hankalin ki, na san Yah Khaleefa barazana ce kawai, amma ba zai fada ba, ki sha wannan bari na kawo maki farfesun in yayi, ina zuwa,"
Wani kallo ta watsawa Aeeshaan, dan a ganin ta ita ce ta jawo danta ya juya mata baya, tinda irin haka bai taɓa shiga tsakanin ta da dan ba,tsakanin su girmamawa ce, tinda a da yana mata ihsani sosai, amma tinda yayi aure ya rage.
"Dalla rufemin baki, farfesu? To da shi na karya a gidana, ke da uwar ki kun mallaken d'a ko? Dan ihsanin da yake min ya daina, to bari kiji,in baku janye asire2n da kuke yi wa d'ana ba matakin da zan ɗauka akan ku ba qarami bane,yanzu diba, irin dankunnen dake kunnen ki, na tabbata sai da ya saka kudi mai yawa sannan ya sai maki su, ni fa? Irin wannan babbar kyautar bata taba haɗa ni da d'a na ba, daga zuwan ki kin kankane ko ina,to da sakel an bawa mai kaza kai,"
"Hello, gate din a bude ne ku shigo kawai,"
Cikin Mama ne ya bada wata iriyar qara, qululuuuu, su waye zasu shigo????
Aeeshaa ma shi take kallo, shi ko fuska a daure ya isa bakin qofa ya buɗe yana jiran koma su waye su shigo.
Da sallama Hajja ta sa qafa ta shigo, sanye take da wani dakakken lace,ta sha gwalagwalai,kunne da wuya, sai Baba General daya sha shadda kalar kayan Hajja, sai Baban shi da ke biye a bayan su.
Mama kashi ne kawai bata saki ba a wando dan tsabar shiga rud'ani.
Aeeshaa bakin ta sake tana kallon ikon Allah, shi waye ya masa wannan gayyar dik irin iskanci da cin zalin ta da yake yi? Shine zai ma mahaifiyar shi wannan gayyar rashin mutuncin,lallai Khaleefa halayyar shi daban ce a mutane.
"Sannu mai d'a, wato nan kk zo kina zuba masu mulki da dokoki ko?ke wa ya maki haka? Eyye nace ke wa ya maki hakan? Har kina ikirarin tsine mishi in baya baki kudi da kayan daɗi, wai kayan daɗi sai kace wata mayunwaciya ko mayya, meye ke baki ci a gidan naki mijin ba