Showing 21001 words to 24000 words out of 69262 words

Chapter 8 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1036

kirki, amma ba wanda ya bincika ganin shi din na gida ne, da mahaifin ta na nan ai da shi ya bincika kuma zai tsaya mata akan wannan lamarin da kowa ya rufe ido akai.

Sai lallashin ta suke, Balqis sarkin kuka da tausayi ganin Aeeshaa kawai na kuka ya sa ta kuka itama.

Haka akai ta shiga motoci abokan aikin Khaleefa na tuqawa suna wucewa da wasu gidan Amaryar wasu gidan Umma, Khaleefa na tsaye jikin motar shi data sha wanki, dan ya sha alwashin ba mai daukar masa mota da sunan wani kai amare, ai akwai motoci a gidan ayi amfani ds su, yaga me daukar tashi motar.

Niko nace rabon ka ɗauka da kan ka ne,tinda in baka bada key ba wa zai ja motar😂😂😂

"Dannema mai qaton kai, kai kullum a aske kamar bayahude, zo nan ka kaimu gidan Khadeeja, daga nan mu wuce gidan naku, tinda gaka tsaye,"

Juyawa yayi yana waige2 kamar ba da shi ake ba.

"Khaleefa  ka kiyayeni, da ubanwa nake da in ba kai ba,dare nayi kowa ya wuce kazo ka kaimu kana tsaye uban wa zai kaimu in ba kai ba?"

Cike da rashin kunya da qunquni yake takawa zuwa gefen driver, da qarfi ya zauna yana masifa, ko kula shi Hajja batai ba suka shiga suka zauna su Uku, Hamdiyya da ita Hajjan sai Aeeshaa, daga can Hamdiyya zata tsaya mijin ta zai dauke ta, su kwana gidan iyayen shi washegari su wuce garin su,anan zasu dauki matar Uncle din Aeeshaan su kaita gidan ta.

Har suka isa ba mai cewa komai,sai da suka fita zasu tafi Hajja ta dawo baya,

"In ka cika kai dan iska ne ka tafi naka waje baka kai amarya d'akin ta ba, zaka ga tijara, zan nuna maka ni kakar ka ce ni na haifi uban ka"

Banza yayi d ita, ya bude motar ya zira qafar shi ta waje, kallon bayan su yayi lokacin da zasu shiga gidan, wowww Aeeshaa ta yi kyau ba kadan ba.

Doguwar riga ce scarlet red,da wasu stones masu kyalli, ta baya tayi tsaho, ta gaba an barta daidai qafar ta, ta gaban rigar ya dago mata albarkatun qirjin ta masha'Allah, ba a cika mata fuska da kwalliya ba, an mata mai sauqi mai kyau,  ga kuma wani dauri da ta sha na zamani, mayafin shara2, hips d'in ta abin kallo ne, tana matuqar jin kunya, amma a dole haka a ka sa ta sanya wannan rigar.

Kauda kai yayi, ya zaro wayar shi, ya hau chatting da Rebbeca, hira kawai suke zubawa ta batsa kamar suna ganin juna ko suna taba juna haka suke jin su.

(Jarababbe kawai)

A zaune Umma take qawayen ta dik sun tafi sauran dangin mahaifin Aeeshaa, suna shiga gidan wata kwalla ta taru a idon umma, Aeeshaa da gudu ta fada jikin ta ta saki wani marayan kuka, qanqame ta tayi kamar ba zata sake ganin ta ba.

Umma shiru ta yi tana jin wani qaunar diyar ta na ratsa ta, hawaye sai zuba yake ta kasa tsaida shi, a hankali ta janye jikin ta tana fada,

"Meye haka zaki wani zo ki riqe ni, sai kace wadda za a kai ma dodo ita, dan uwan ki ne ba wani bare ba, dole ki masa biyayya, Allah ya baku zaman lfy ya sanya albarka, ta shi ki d'aga ni ni,"

"Ai shi mai hali in bai halin shi ba sai kowa ya zaci ba shi din bane, da an bi ta tawa ko ganin ta zaki yi ne ma?"

"Hajja dan Allah ku bar wannan maganar, muje kunsan halin Yah Khaleefa, yanzu na san yana can ya qagu mu kai masa amaryar shi, aunties ku tashi muje, dare na yi"

Da sauri Umma ta nufi d'akin ta, kuka sosai take ji, tabbas yau tasan ba zata taɓa iya bacci ba.

Aeeshaa bin qofar tayi da kallo tana tsananta kukan ta, dik fuskar ta tayi jawur, ga wani matsanancin ciwon kai da ke damun ta, a hankali ta miqe kamar ba zata iya tashin bama, ta fara takawa zuwa waje.

Da gudu Ameena ta fito tana kuka ta qanqame Aeeshaa, ta kasa magana sai kuka take,Abdul na tsaye yana kallon su,dik rashin kunyar shi yau sai yaji baya son Aeeshaa ta bar su, amma a fuskar shi sam ba wani emotion.

Da kyar aka raba su, Aeeshaa ta kasa cewa komai itama, sai shessheqar kuka.

Yana ganin su ya yi saurin shigewa motar dan ba zai so su ga yanayin dayake ciki ba, kashe data yayi ya zauna kamar su yake jira, ya bata rai.

Da gudu yake tafiya sakamakon titin da ya zama ba motoci sosai

"Dan uban ka ka tafi damu a hankali, kar ka je ka kashe mu, mara mutunci, ni ban san haka kk ba, ko dan da ba na shiga harkar ka ne, oho, amma iskancin ka Khaleefa yawa ne da shi"

Auntyn Aeeshaa ce tace

"Hajja kiyi hakuri, kar ki mai faɗa gaban amaryar shi, Allah ya kaimu lfy,"

Hajja dai bata samu tai shiru ba har suka isa zagin Khaleefa take tana kumawa, sai masifa take masa, har suka isa.

Bayan sun aje amarya suka hau masu nasiha gabaki dayan su, Hajja harda shafa kan Khaleefa ana masa nasiha cikin lallashi, da kuma dan kokawa, ita a dole ya rage baqin rai.

Ganin dare na yi ya sa Hajja miqewa, Aeeshaa ji tai kamar ta bita su koma, tsananin tsoron Khaleefa ya hana ta shan iska da kyau.

Drivern gidan Baba General ne zai maida su, dan bai wuce ba yana jiran su zo ya maida su dama.

Gida ya rage daga Khaleefa sai Aeeshaa ko mai gadi babu, saboda sabon gida ne, ba su samu mai gadi ba tukunna.

Sai da ya tabbatar kowa ya tafi, ba mai dawowa, dan haka ya shiga ya watsa ruwa, ya sauya qananan kaya, ya feshe jikin shi da turarukan shi masu qamshin gaske, ya dau key din motar shi ya nufi dakin Aeeshaa.

A zaune take bakin gado, tayi kuka har ta gaji, sai shessheqa take, idon ta na zubo da hawaye, lokaci zuwa lokaci tana sharewa.

Ba ta ji sanda ma ya bude qofar ba, sai jin an jefo mata abu tayi a cinya.

"Tashi muje ki rufe gida zan fita, in bani kk ji ba kar ki sake ki bude qofa, dan akwai 'yan iskan unguwa masu shiga gidan amare su masu fyade kuma suyi sata,"

Wani irin mugun tsoro ne ya kama ta, da sauri ta miqe tana waro manyan idanun ta waje, shi ko murmushin mugunta ne ya subuce masa,

'Zaki san an maren akan ki, azaba sai kin sha ta har kin gudu da qafafun ki'

Wasu sabbin hawaye ne ya sake balle mata

'Oh Allah in laifi na yi ka yafe ni, ka sassauta ma rayuwata wannan azabobi da nake sha'

"Kina ma jin me nake fada kuwa?"

"Immm.....ammmm yi hakuri me kace,"

"Oh ba ki ji ma me nake fada ba ko? Kiyi bacci na dawo baki buden ba ki gani,"

Ficewar shi yayi, kamar ta bishi ta hana shi barin ta ita ɗaya da zai yi, a parlour ta zube tana kuka mara sauti, dan muryar ta ta dusashe sosai saboda kuka.

Bai tsaya a ko ina ba sai gidan Rebbeca, ta masa alqawarin kan ta yau, indai ya baro amaryar shi ya je gare ta, amma da alama ba zai samu ba, dan in ban bata ji ba abinda na jiyo a cikin gidannan shi khaleefa ya jiyo😨😨😨😨

*Allah sarki Aeeshaa me kuke gani game da rayuwar ta? Shin mutum mumini dama na shiga wahalar rayuwa haka? Dan na ji wasu na cewa bai kamata ta auri mazinaci ba,Mu tattauna dan samun ilimin junan mu*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 10:

Da sauri ya kashe motar shi ya qarasa jikin qofar shiga qayataccen parlourn, yana kusantar wajen kidan da dariyar Rebecca na qara shigar masa kunne, murda knob din yayi ya tura kai ciki, mummunan gamo yayi da wani garjejen magidanci, Rebecca na kwance saman cinyar shi tana rawa a jikin shi, yana saka mata kudin qasar amurka a dan kamfan ta, ta juya baya dan haka bata ga shigar shi ba.

"Kaii ! waye kai zaka shigo mana waje haka?"

Banza Khaleefa yayi dashi, daidai lokacin Rebecca ta waiwaya ganin wanda ake wa magana ne ya ɗan rikita ta, wani abu ta hadiya sakamakon ganin wani irin kallo da Khaleefa yake mata, bata son ta rasa shi, tana matuqar jin daɗin mu'amala da shi, in ta rasa shi wadannan Alhazan sai dai su samu natsuwa da ita, bata wani morar su sai kudin su.

"Give me a minute Alhaji na,"

Kissing din shi tayi a lips ya lumshe ido,ya gyara qaton tumbin shi ya kwanta a kujerar yana jiran ta.

Hannun Khaleefa ta yi niyyar kamawa ya kwace ya dau hanyar fita.

Da gudu ta bishi ta sha gaban shi, direct qasan shi ta kai hannun ta tana juya jikin ta a nashi, kundai san Khaleefa da jaraba, nan da nan ya rikice, ya manna ta da jikin motar shi,

"Me yasa zaki min haka, kin san wannan me kama da aladun zai zo zaki gayyacen?"

"Ka yi hakuri my sugar, ban san zai zo ba, na gama shirya maka kaina kawai yamin waya wai naje na dakko shi a airport nan zai kwana, in banda jaraba ko gidan shi bai je ba fa, ya sauka anan, daga tafiya suka dawo da His highness amma ya zo min nan, ka san ina samu a wajen shi sosai, shi ya sai min motar danake hawa yanzu, ka min hakuri zuwa jibi ko gata,"

Janye ta Khaleefa yayi dan takaici, har gata? Yaushe zai iya kaiwa gata bai jishi daidai ba, inaaa.

Komai bai ce ba ya bude mota ya shige, bin shi ta yi tana ta kwankwasa glass din ko kula ta bai ba ya fice, yarfe hannu ta yi ta kama goshin ta, ta san kan ya sakko sai ta dad'e tana lallashi, damuwar ta kar ya je ya kwana da amarya tafita komai ya aje ta a gefe, haske ta yayi da fitilar motar shi sanda zai fita, wani matsanancin sha'awa ke dawainiya da Khaleefa, musamman da ya ganta daga ita sai pant da bra.

Da mugun gudu yake tuqi dan komawa gida.

Zaune take tana ta rera karatun qur'ani a hankali, kuma cikin ikon Allah a hankali ciwon kan ke sauka, amma goshin ta na dan mata zafi wannan kuma ta san harda bacci.

Horn ta ji ana dannawa da qarfin tsiya,aiko da gudu ta miqe ta je waje, tana son ta bude bata san waye ba, ko barayin ne suka zo, wani qara cikin ta ya bada, in sune anya zasuna horn haka?

Shahada ta yi ta buɗe gate ɗin, koma waye ta san ba mai cutarwa bane tinda har yayi horn.

A guje ya shige ya parker motar shi ya fita, ko bi ta kan ta bai ba ya shige gidan.

'Ikon Allah ni zan rufe ma gidan kenan,'

Rifewa ta yi tayi ayatul kursiyyu ta tofa a qafar gate din tare da hura iskar bakin ta har ta jikin katangar gidan sannan ta koma ciki, yanzu hankalin ta ya kwanta tinda ya dawo lfy zata iya baccin ta.

Kayan ta ta cire bayan ta shiga band'akin dake dakin ta, wanka ta fara, sannan tayi alwalar bacci ta fito, duba kayan sawa ta shiga yi, da dikkan alamu, kayan ta anyi mistake an kai mata wani wajen dan nan daga atampopi sai laces da dogayen riguna ta gani.

'Ina to suka saka min qananan kayana da na bacci ni Aeeshaa?'

Dubawa take amma iya abinda take ta karo da su kenan atampa, leshi, shadda material, hijab ta saka babba, ta nufi dayan dakin, dan dubawa ko can aka aje mata.

Daki uku ne a gidan manya, sai parlour biyu babba da qarami, da store sai babban kitchen sannan wajen dinning, gidane wanda kwararren magini ya tsara shi, Hajja da kan ta ta zabi kayayyakin dakin, kai har na kitchen ma, da su Balqis na ganin za a saka kaya marasa kyau tinda Hajja ce zata zaba, a ganin su tsohuwa me ta sani na zamani, Aeeshaa mamakin ganin kyau da tsaruwar wajen take,tama manta me ya fito da ita,ta leqa nan ta leqa can.

Qarar TV ta ji a daya daga cikin dakunan, gashi irin nishin da ta ji watannin baya da suka wuce a dakin Khaleefa a gidan su shi take sake jiyo wa, duba lokaci tayi taga qarfe 2:12am, da sauri2 ta qarasa bakin qofar, ta kasa kunnen ta dan ta tabbatar da me take jiyowa.

Khaleefa wanda ya maida hankali wajen sabon Allahn shi da ya saba ne ya ga inuwar mutum a bakin qofar d'akin shi, dakatawa yayi, yana kallon wajen, murmushin mugunta yayi daya ga ba a bar wajen ba, ya tabbata ita ce, yau zai maganin ta, ta yi na biyu gobe bazata sake na uku ba.

Sauka yayi a gadon nashi, ya qarasa fidda boxern shi, ya nufi bakin qofar dakin, shiru yayi na wasu daqiqu da basu wuce biyar ba, da qarfi ya bude qofar, aiko da ka ta fada d'akin, cike da tsananin tashin hankali da kidima take qoqrin yin magana,amma A ta kasa fita a bakin ta,

Da hanzari ta rufe idon ta, ganin Khaleefa ba komai a jikin shi, tsaya mata yayi qere2 yana kallon yanayin yanda take a tsorace, murmushi yayi sannan ya bata rai

"Ke me kk min a qofar daki? Labe ko?"

"Ahhhh.....ahhhh Yah Khaleefa, naji kamar hayaniya ne shhhhshiii neee na ce barrrii na ji mene,dan Allah ka rufan asiri kayi hakuri ka yafemin ba zan sake ba,wannan alqawarri na ɗauka har abada ba zan sake zuwa inda kk ba sai ka kirawo ni, tsautsayi ne ya sa na kasa maka kunne,"

Hayaniyar ta na damun shi, cike da tsawa ya dakatar da ita,

"Keep quit stupid! In kk qara cewa tak anan sai na babballaki, ba mai taimakon ki, wuce muje,"

"Ina😨"

"Ciki"

"Ayi me?"

"Irin wancan, kar ki sake magana or else...."

Gum tai da bakin ta tana tsinewa karambanin daya sa ta kasa masa kunne,ba halin ta bane, azal ce ta janyo ta,yau ta shiga uku.

"Bude idon ki da kyau ki kalla, dik abinda kk ga anayi kema shi zaki min,in kuma kk qi, sai jikin ki ya gaya maki yau, ba dai an aura min ke ba? Ai kin halatta a garen, so kar ki damu"

"Dan Allah, dan soyayyar ka da Annabin rahama ka tausayamin, ni ban taba kallon irin wannan sabon Allahn ba, ka tausaya min ka barni na tafi, inshaa Allahu hanyar ma da kabi ba zan sake bi ba, in ba kai ka kirani ba, ka tausayamin bani da lafiya,sannan kallon irin wannan abubuwan na janyo wa bawa fushin Allah da tsinuwar shi,dan Allah kar ka sa ni na aikata abinda Allah zai tsine min"

Yanda take maganar ya mugum bawa Khaleefa dariya,dik iskancin shi na shiru2 yau ji yake kamar ya kwanta dan dariya.

Sai da ya yi dariya sosai, ita kuma tana tsugunne tana kuka, sannan ya bata rai, ya nufe ta gadan2, ya cire hijabin ta, mayafin da ta yafa sanda aka kawo ta shi ta daura, ba abinda yake boye a jikin ta, Khaleefa tinda yake kallon fina2n iskancin shi bai taba kallon mai dirarren jiki irin na Aeeshaa ba, wata matsananciyar sha'awar ta ce ta kama shi.

Dambe suka fara, zai cire zanin ita kuma tana qoqarin kwacewa.

Ta san ko a islamiyya an sanar dasu saduwar aure, da yanda miji ke zuwa ma matar shi a daren farko, ita kam bata ga ɗaya daga cikin wannan ba a wajen khaleefah, ko ba komai ba zata so Allah ya azurta su da zuri'a a wannan halin qazantar ba,yana kallon film din batsa sannan ya sadu da ita inaaa, yau sai dai ya mata duka, amma ba zata bar shi ba.

Hannun shi ta kama ta sakar mashi cizo, tin qarfin ta, da sauri ya sake ta, yana yarfe hannu, diba ta yi a guje zata fita, ya sa qafa ya yarfar da ita a qasa, faduwa ta yi tare da sake qarar azaba, ta gaji matuqa, qoqin tashi take ya bi ta ya kwanta a jikin ta, shi kan shi ya gaji, bai zaci tana da qarfi haka ba.

Mutsu2 take dan ya daga ta ta gudu, amma da ta san me xai haifar da bata yi ba, domin dik wani motsin ta sake kunna shi yake, nan da nan kuwa jarabar shi ta dawo dabuwa.....

Qarfe 4:01am, Khaleefa ne kwance a gefen Aeeshaa, wadda ajiyar zuciya kawai take saukewa,tana tsiyayar da hawaye ta gefen idon ta, sama take kallo, ido bude, bata gane komai a saman, ji take kamar ba a duniyar take ba.

Qasanta kamar an sa abu mai kaifi an yanka haka take ji, ko hannun ta bata iya d'agawa,ba abinda ke mata yawo akai,illa abinda ya yi mata a daren jiya kamar ba zai barta da rai ba, ga shi yana yi ya na sake maimaita film din da yake kallo, ba addu'a, ba komai daya danganci sunnah, sai kace arna.

Kuka mai qarfi ta fashe da shi, mara sauti, saboda muryar ta ma bata fita, ta dad'e tana kuka, ko motsawa bai ba, dan tini bacci ya share shi

Yunquri ta dinga yi dan tashi amma ta kasa, ko dukan da ya mata ma da ta qi tsayawa ai ya isa sa jikin ta tsami, fuskar ta har kumbura tayi saboda marin data sha, wai ace musulmi ne ke saduwa da mace yana kallon wannan iskancin, remote ta qoqarta ta janyo daga hannun shi, kashe wa ta yi gaba daya, tare da sakin tsaki,

"Yan iska kawai, Allah sai ya sakamin ba zan taba yafe maku ba dikan ku,"

Juyi yayi ya ringumo ta, ya ci gaba da baccin shi, hawayen baqin ciki da tsana mai tsanani ne suke zubar mata a idon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login