Showing 18001 words to 21000 words out of 69262 words
Chapter 7 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
ma murmushi tayi,
"Yah zauna na baka labarin abubuwan da suka faru da baka nan, kuma ina son ka ban shawara, akan Yah Khaleefa, akwai wani sirri nashi da ba na son faɗa, amma bana son abun, bana son mai yin abun, dan haka nake jin tsanar wannan auren namu, Yah dan Allah ka ban shawara ya zanyi?"
Gaba ɗaya ya shagaltu da kallon ta, a dan kwanakin da yayi ba ya ganin ta sai yaga ta qara kyau da girma, ga shi for the first time ya gan ta da kwalliya mai kyau haka, hannu tasa ta gaban idon shi,
"Yah magana nake fa,"
A dan firgice ya dauke kan shi, ya kalle ta again,
"Immm kin ga ko zamu bari nayi wanka na ci abinci, bana gane komai yanzu, muguwar yunwa nake ji, kin san ni da ci,"
"Kai Yah Sabeer kai kam akwai ci,amma dai matar ka ta shiga uku da girke girke, ko daga qafar girki na rana ɗaya na san ba za ta samu ba,"
Tashi ta yi ta na tafiya tana sanar da shi anjima zata dawo, su qarasa magana, ya amsa da to,ita kuwa ta na fita sai ta koma wajen su Hajja, nan ta samu Hussai ta dakko kud'in da Khaleefa ya wurga mata, suna ta mata dariya, wai amaryar qauye an mata kyauta ta ajiye, ango ya tafi tabiyo sahu ta dauka ta ga babu,tuna wulaqancin da ya mata ne ya sa ta ji tana son ta yi kuka, yaqe ta musu ta shige daki.
Yanda auren nan ke qaratowa haka zuciyar ta ke tsananta bugawa, Sabeer ya tare a gidan Umma, dan bai ma sake komawa ba balle ta gan shi tace za su yi magana, ba zai juri kallon ta ba, bai san me zai iya aikatawa ba da wanda ba zai iya aikatawa ba indai a gaban ta ne.
*********************
"My baby ina kake son tafiya ne wai? Gobe fa daurin auren ka, na sani in ka tafi ba zaka sake dawowa ba,ka bari na kwashi rabona mana plssssss"
Wani irin narkewa take a jikin shi, shi kuma yana lumshe ido,kamar wadda aka mintsina ta tashi, tambayar ta yayi
"Lafiya?"
"Lafiya qlou ina zuwa, zan ɗan qaro abin sha ne, naga wannan ya kusan qarewa kuma ina jin yunwa,"
A dan gidan ta madaidaici suka koma da sheqe ayar yasu , gidan akwai kyau sosai, dan gaskiya da alama a qasar waje aka gano tsarin itama aka yi mata irin shi, ko kuma wasu masu basirar ne suka tsara gidan, iya haduwa da kyau ya hadu, wani Minister ya mata kyautar shi, amma yanzu basu tare.
Kukun ta ta yi ma umarnin ya haɗa masu abinci, ta lissafa masa abinda take son ya kawo masu, sanan ta bashi wata kwaya ya saka masu dika a abin sha, cikin murmushi da takun qasaita ta koma dakin, in da sabo kukun ya saba ba yau yake mata aiki ba.
"Hey babe, sorry na barka kai ɗaya,"
"Ba komai, kamar wani baqo, come here,"
Takawa tai kamar mai tausayin qasa ta kwanta gefen shi, wasannin su suke, suna ta dariya waya ta shiga masa, yana dubawa yaga Baba General ke kiran shi, dan guntun tsaki suka ja a tare, bai ji daɗin yanda tai tsaki ba, dan ba hurumin ta bane, in shi yayi bai sa ta taya shi ba, wani mugun kallo ya mata for the first time.
"Meye naki na tsaki, ko zan iya sanin dalili?"
Kame2 ta fara,dan ganin wani irin kwarjini daya mata, nan take tsoron shi ya kama ta, inda inda ta fara yi, cikin tsawa ya fara mata magana,
"Kina jina ko, hurumin iyalina ba naki bane, ba ruwan ki da ya nake tare da su,in ina tare dake ina tare dake, in naga dama na je wajen su na tafi, kakana ne fa, kk masa tsaki, ko wayar ki ya kira?"
"Babe plsss kar ka min wannan fassarar,ni fa nayi tsaki ne kawai duba da yanda ranka ya baci, bana son abinda zai bata maka rai ne kawai,"
"Ba hurumin ki bane, ki san matsayin ki, this is my grandpa, ba abokin wasan ki bane, ki riqe wannan,"
"Yes babe, and i am so sorry, i will make it up to u, plss don't be angry, smile for me, plsss,"
Yau fa taga kalar Khaleefa da bata san yana da ita bama, ko alamar ya sakko bai nuna mata ba, kayan shi ya fara zurawa,cikin damuwa ta taso zata hana shi ya mata wani kallo ta koma ta zauna, me wannan yake nifi ne, zata sa a hada wannan uban abincin a banza ne? Kuma yau wai har ita namiji kema wannan kallon da rashin mutuncin bata ci....... tab di jam akwai aiki gaban ta kenan, Khaleefa bai jiqu da qaunar ta ba,
akan idon ta ya gama shiri ya fice ba ko magana.
Ranta in yayi dubu ya baci kuwa, cikin bacin rai,ta yi ma wani saurayin ta waya, ta gayyace shi ya zo su dora abinda ba suyi da Khaleefa ba, sigari kuwa ta sha ya kusa kara biyar, daga qarshe Shisha ta dakko ta fara zuqa
Mata da maza ku kiyayi shishar nan, illa take yi mabayyani ba a boye ba, wanda ke son rayuwar shi da lfy a ciki bai wahala ba bai wahalar da dangi ba ya guje ta.
A zaune suke a kan kujeru suna ta hira, suna dariya, ga 'yan uwan su harda na Yola sun zo, gobe daurin aure, sai bayan an daura ne za a yi gagarumar dinner, wadda Baba General ya gayyaci manya2n qasar nan, za ayi dinner din ne mata da maza, kowa zai zo da iyalan shi dika, domin taya Baba General murna.
Aeeshaa na gefe in an abun dariya ta murmusa, abinda ke damun ta ba kaɗan bane, ga rashin Umman ta, ga miji dan iska, yanzu ace da Umman ta ta jata ajiki ai da ta sanar mata halin Khaleefah, gashi da kunya ta ce ma Hajja jikan ta babba dan iska ne, ta ina ma zata fara mata wannan bayani?
Wuce su yazo zai yi Balqis ta gaida shi, yi yayi kamar bai ji ba ya shige, bushewa da dariya 'yan uwan nata suka yi, babbar d'iyar Uncle din Aeeshaa da tazo itama Fateema ce ta dakatar dasu,
"Kuka sani ko ango ance ya kawo kud'in dinner ne account yayi qasa? Kun san fa maza da biki ya qarato da sun fara faɗa da kowa kenan "
Nan da nan kowa ya sa dariya har Bilqis data bata rai, kowa ya ci gaba da fadin albarkacin bakin shi.
"Gani," shine abinda Khaleefah ya ce bayan ya shiga babu ko gaisuwa.
Kallo Baba General ya bishi da shi, cikin takaici, sannan ya nisa yace,
"Anya mun yi wa Aeeshaa adalci in muka aura mata kai kuwa Khaleefah? Anya ba zamuyi dana sanin wanan auren ba? Daga ina kk? Jiya ina sane da baka kwana gidannan ba,na kira ka baka ga damar amsa wa ba, ba tarbiyya ka shigo min ba sallama, sannan kace min gaka, wazaka nunawa baqar zuciya? Nine fa na haifi uban ka, ka ko san ko baban ka a wajena ya gaji zuciya bare kai dorin dosano,"
"Ni fa wannan fadace2n da gore2n ne bana so, ai bani nace a haife ni a nan din ba"
Qunquni yake ta yi kuma Baba General ya ji shi tsaf, Khaleefa bai aune ba bai san daga ina hannun ya biyo ba kawai sai jin wani makakken mari a kuncin shi na hagu ya yi,gabadaya parlourn sai da ya dauka da qarar Marin, ji ya yi kunnen da na kada masa qararrawa kamar a coci,Aeeshaa kuwa da ta shigo dan komawa d'aki qamewa ta yi a inda take, jikar tsohon soja kenan, hannun ta a rufe da bakin ta,cikin ta ne ya bada wata irin qara mai sauti, da sauri ta bar wajen,ta shige daki.
"KAII KHALEEFA kar kaga ina d'aga maka qafa ina bin ka da lalama, dik wani qunci da baqin hali da rashin kunya tare da qin 'yan uwan ka da kk akan idona yake, rashin kunyar ka har ta kai ina magana kana man qunquni, kuma kana yi wato yanda zanji sabida baka da kunya ko? To ka sani daga yau sai yau, in na sake ganin rashin da'a a tare da kai ba a gabana ba ko a gaban waye sai na yi mummunan saɓa maka, tashi ka ban waje, kuma kar ka sake ka fita ko ina, gobe ne auren ka, mara mutunci kawai,"
Khaleefa wanda bakin shi yake a sake tsabar tsananin mamaki da tsoron ganin yanayi Baba General wanda tinda yake bai taba ganin bacin rai irin haka a fuskar shi ba, da saurin gaske ya zuba guiwowin shi a qasa yana bama Baba General hakuri,da kyar ya hakura dai da Hajja ta fito ta sake bashi hakuri sannan ya hakura.
Abu ɗaya ne a ran Khaleefa yanzu, wato shine ɗaukar fansar marin nan akan Aeeshaa zata fada, tinda ta ga sanda aka mare shi, kuma a sanadin auren ta da aka qaqaba masa aka mare shi, dan haka ya ma matsu a daura masu auren dan ya gana mata azabar da ko mai kalar Sunan shi ta ji an ambata sai ta suma dan tsoro............
*Mugu ta Allah ba taka ba to*
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 9:
Qarfe tara da wasu mintuna Hamdiyya ta zo da mijin ta, wanda a ranar yake son su koma in an gama d'aura aure, zuri'ar gidan Baba General cike da murna da farin ciki suke ta gudanar da harkokin bikin, wanda su kaɗai suke farin cikin su, amarya da ango zuqatan su kamar ana d'ana masu wuta suke ji.
Can gidan Umman Aeeshaa ita da qawayen ta suna can suna na su bikin,amma nunawa take ita kam ba wani hidimar biki da zata yi, Hajja kuwa na riqe da jin takaicin ta ,ta dau alwashin itama sai ta d'and'ana mata ta ji yanda Aeeshaa ke ji, Allah ya kaimu a gama bikin lfy, ai in fillanci take ji ta fita zama bafulatana tinda ita ta haife ta.
Qarfe 11:00am daidai aka d'aura auren Khaleefa da Aeeshaa akan sadaki dubu ɗari ,aure ne daya halarci manyan masu hannu da shuni daga kan manyan 'yan siyasa zuwa 'yan kasuwa.
Kowa ka gani cikin farin ciki yake amm banda Ango,shi ko dan yaqen nan ma yaqi yi,Sabeer ke ta gaisawa da mutane sai ka rantse shine angon ma, amma cikin zuciyar shi shi kaɗai yasan me yake ji, babu wanda ya kula ya zame ya bar wajen, mota ya faɗa ya kife kan shi ya na sauke numfashi mai nauyi da zafi, shikenan, shikenan Khaleefa ke da sa'a ba shi ba, Khaleefa ya fishi sa'a a rayuwa, ina zai saka kan shi yau, Aeeshaa ta zama mallakin wani, numfashin shi ne ya fara barazanar dauke masa, da sauri ya kunna motar ya bude window ya tada ta a guje ya bar wajen, iska na ratsa shi amma ji yake kamar a cikin rana yake.
Bai tsaya a ko ina ba sai gidan Umma, yana zuwa ya shige dakin shi, ya kulle,kuka mai sauti ya sake, bai damu ba kowa ye zai ji shi ba zai iya riqe wannan baqin cikin ba, kuka yake kamar wani qaramin yaro yana birgima a gadon shi, hannun shi riqe da saitin zuciyar shi ya manna pillow a qirjin shi lokaci zuwa lokaci ya na danna pillown a fuskar shi, ji yake kamar zuciyar shi zata fashe dan kumburin da ya ji qirjin shi ya yi masa, ga wani maqaqin d'auri a wuyan shi ya qi shigewa yaqi ficewa.
Kwankwasa qofar dakin aka yi, hakan bai sa ya daina kukan ba, da qarfi take kwankwasawa, dan taga wucewar shi, cikin kukan da yake son ya danne ya miqe yana layi ya bude mata qofar, juya baya yayi, zai koma ya kwanta ta dora hannun ta akan kafadar shi,cikin muryar lallashi da tausayawa ta ce,
"Haba yaron Umma? Komai yayi zafi maganin shi addu'a ga Allah ya yaye ma bawa damuwar sa, ina hankalin ka ya tafi zaka manta da Allah a wannan yanayin da kake ciki, ka yi hakuri ka ɗauki qaddarar da ta zo maka,ni kaina ba yanda zanyi ne da ban bari an yi wannan auren ba,"
Da sauri ya katse ta, cikin d'aga mata hannu, idon shi sun yi jawur saboda kuka.
"Umma baki taɓa min laifi ba a duniya domin ke uwata ce, amma a wannan karon bana ganin laifin kowa sai naki, ke ce silar yi ma Aeeshaa auren dole, da kin ja ta a jiki ba ki nuna mata tsana da wai itan 'yar fari bace da ta zayyana maki me take so, meye bata so, sannan da kin cire kunya sanda akai had'in nan,da kin tsaya mata kin ce bai maki ba, da kin kwatar ma diyar ki 'yancin ta da aka danne mata.....
Da qarfi ya tafi zai faɗi sakamakon marin daya ziyarci fuskar shi ba tare da zato ko tsammani ba.
Cikin kuka Umma ke magana itama.
"Kana da hankali kuwa? Baba General ya yanke hukunci nace baimin ba? Yau ko ni na kawo rashin kunya a duniya Ubana yayi wa d'iya ta miji da babban jikan shi sannan na qi amincewa? Inaaa ai bazan musa ba Sabeer, kenan kana nufin na yi ma mahaifana rashin kunya akan abinda suke da iko akai, dani da ita dik mallakin su ne, ba zan taba musanta masu ba, .....my boy, ka kwantar da hankalin ka, kayi hakuri ka nemi wata, Allah zai baka wadda ta fi ta na san kana son ta, kana qaunar ta, amma ya zama dole ka yi hakuri da son ta, ka yafeni akan abinda na aikata wanda bai maka daidai ba,"
Juyawa ta yi zata fita, dan zuciyar ta ta mata nauyi, bata taɓa zaton tana son Aeeshaa irin haka ba, ashe dik abinda take mata aikin banza ne,son nan da take qin nuna mata yana nan danqare a ran ta,kuka take buqatar yi itama,dan sai yanzu ta ke hangowa diyar ta ta zaman quncin da za ta yi da Khaleefa, a halin shi da suka sani shi ɗin ba wanda zai yi laushi bane ba tare da an ci baqar kwakwa ba.
Kamo hannun ta Sabeer yayi yana kuka, ya durqusa.
"Umma ki yafe min ba zan sake abinda na aikata maki ba yanzu, amma ina neman izini zan koma bakin aikina a yau, ba zan iya ci gaba da zama ba, zuciyata kamar zata fashe haka nake ji,"
Cikin tsananin tausayin shi ta ke shafa kan shi, tana hawaye,
"Na amince maka ka koma bakin aikin ka d'ana, amma ka bari sai gobe, yanzu zaka yi dare idan ka tafi, Allah ya maka albarka, ya sauqaqa maka abinda ke damun ka a zuciyar ka, Allah ya sanya ka a cikin bayin shi masu hakuri,"
"Ameen Ummana,"
"Zauna na kawo maka abinci kaci,"
"Umma bana son cin komai, ki dai hadan tea ya isheni, shima magani nake son nasha ko na rage jin zogin da kaina yake min,"
Bata musanta masa ba ta fice tana gyara fuskar ta, amma qawayen ta sai da suka gane ta yi kuka, nan suka hau tambayar ta me ya same shi ya shige kamar wanda aka koro? Murmushi kawai tayi tace bashi d lafiya ne, nan suka hau jinjina shaquwar dake tsakanin su, dan baida lfy take kuka itama.
Sai da ta dafa masa ruwan tea din da kayan qamshi ta haɗa masa mai kauri da maganin ciwon kai ta dora a tray, inda kayan gara yake ta nufa da plate, ta zuba masa dibilan da cincin da dai sauran abin bikin a plate ta nufi dakin nashi, shiru ta ji dakin gashi bata ga alamar kayan Sabeer ba, ajewa tayi ta hau duba dakin, tsaf har toilete ta duba baya nan, zama ta yi a bakin gadon zuciyar ta cike da baqin cikin abinda Sabeer yayi, ashe ba zai ji maganar ta ba yanzu, ya hakura zuwa gobe.
"Allah ya kiyaye hanya,Allah ya kare min yarona dik inda yake, ya Allah ka sauqaqa masa wannan qunci da yake ciki"
Ɗauke kayan ta yi ta fita da su, haka sika yi wunin bikin da qawayen ta ba wani kwari a jikin ta, tausayin Aeeshaa da Sabeer ke dawainiya da ita, gashi ko a qawayen ta ba wadda ta sakewa sike dan maganar Aeeshaa da ita balle ta yi masu maganar ko za ta ji dan sanyi a ran ta (sai ko maganar ta cinye ki tinda ke kk jawo, kunya kamar a rugga)
***********************
"Dan Allah General a kai yarinya dakin mijin ta ba sai an yi wani yawace2 ba,ina ce nan yarinyar nan ta zo a yi biki gaba ɗaya anan qi tai, abu tuwona mai na, sannan naga ba wai ta damu da yarinyar nan bane, da za a bi tawa da kai ta kawai akai"
"Hajja tawa kenan, ke in banda abinki ya za a kai yarinya d'akin miji ba tare da mahaifiya ta ta sa mata albarka ba? Tana raye ba a mace ba? Habaaa kar ki sa wannan a ranki, whatever it is mahaifiyar ta ce, and in banda abinki ai can ma mutane zasu je,ina ga shine dalilin ta na qin zuwa, ai tana da qawaye, kuma ga wasu daga 'yan uwa ma musamman dangin mahaifin yarinyar ai sun je can bayan an gama anan, dik dai ba sauqin mu bane da kuma samun wajen kwana, canfa shine asalin yarinya nan ne gidan iyayen ta, nan gidan kakannin ta ne, so ki cire komai a ran ki ku kai ta can, daga nan sai a wuce da ita gidan mijin ta, Allah ya muku albarka ya baku zaman lfy, Allah ya kare ku daga dikkan sharrin mutum da aljan,"
Aeeshaa da take riqe jikin Hamdiyya Sai kuka take, kewar mahaifin ta ya dame ta, ga uwa tana da ita amma kamar bata da ita,jin ta take kamar marainiya, ga miji mara halin