Showing 54001 words to 57000 words out of 69262 words
Chapter 19 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx
maki nasiha kiji tsoron Allah, ki kiyaye dokokin Allah,Allah sai ya kiyaye ki,Allah ya baki rai, ya baki lfy, ya baki arziqi na wajen zama da ruwa kina iya diban ruwa kiyi wanka ki fice yawon tazubar amma alwala da ba zaki wahala bama tana maki wahala, kina iya kwantawa kiyi awa biyar kina chatting amma ki ware minti biyar kiyi sallah yana maki wahala,kina iya yin rawa wai dan motsa jiki ki ta zufa,amma sallah na maki wahala, lallai Hadiza imani kk rasa, da kinyi imani da Allah kin kuma san yana kallon ki a dikkan abinda kk, numfashin ki daya baya fita face da sanin Allah, qifatawar idon ki daya baya kasantuwa face Allah ya gani, Hadiza da kina da imani da kin san hakan, da kin gyara rayuwar ki kin maida sallah abin so,kuma da kina yin ta da nishadi da shauqi, inace nan kk satar jiki ki tafi wajen dik wani qato da kk so? Ashe Allah ne baki so? Tinda ga dama har gida, har dakin ki da zaki gana da ubangijin ki abin son kowane abin halitta, amma ke baki damu ba, sallah fa tsakanin bawa da Ubangijin shi ne suke magana,bawa ya kira, Allah ya amsa masa, bawa ya roqa Allah ya biya masa, bawa yayi godiya Allah ya mushi rahama, Hadiza wadannan ne baki so? Na saka ki islamiyya kin gudu, gani kk kin girmi islamiyya, amma shi iskanci baki girme shi ba, ke wai Hadiza ke ce zaki budema namijin da ba muharramin ki ba qafa ya gama zina ZINA fa Hadiza dake, ki tashi ki kade jiki ki dawon cikin gida ba kunya ba tsoron Allah na ganin dikkan abinda kukai inni ban gani ba, Hadiza kin cutar dani, kin cutar dani iya cutarwa,"
Hadiza kuka take harda majina mai yawa, ta ma rasa inda zata saka kan ta saboda tinawa da tarin zunuban ta, istigifari kawai take yi iyakar iyawar ta, tin tana yi a zuci sai da ta fara a bayyane, har wani shessheqar shidewa take, Goggo kam ta tabbata kalaman ta sun shigi diyar ta ta, hamdala ta yi a zuciyar ta sannan ta kama hadizan ta rungume, da qarfi ta qanqame ta, tare da sake fashewa da kuka mai qarfi, tinowa take da yanda take zama ta biyawa kan ta buqata da hannayen ta, da zuwa wajen samari da masu aure dan kawai tayi zina, kuka take sosai,
"Goggooo kkkkkiii yaaafee minnn,"
"Na yafe maki,Allah ya yafe mana dika, tashi kije ki fara gyara rayuwar ki tin yanzu,"
Da sauri ta miqe dan zuwa tai wanka,sai take jin jikin ta najasa ne gaba daya, Goggo sai magana take mata, akan ba sai tayi wanka ba, kada kai tayi kawai ta wuce, ita kadai tasan qazantar da take ji a jikin ta, wankan ne zai sa zuciyar ta ta nutsu, kafin ta riqe ibada kamar yau aka haife ta.
Goggo har dariya tayi dan jin daɗi, ba abinda yafi magana a nitse, domin a fahimci juna, bayani shike kawowa a fahimce ka da iya tsara kalamai, amma hayaniya da tashin hankali sai dai a sake rincaba al'amari ba wanda zai fahimci wani
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 25
Aeeshaa da Umma ba qaramin shaquwa sukai ba dan zaman da sukai na wata daya a gidan Hajja, in ka gan su suna hira kamar qawaye, Umma wataran har qurawa Aeeshaa ido take hawaye ya dinga zubo mata, saboda tinawa da irin gallazawa diyar cikin ta da ta dinga yi, ta nemi yafiya har ba adadi, Aeeshaa sai ta tsokane ta tace
"Sai kin sai min ice cream"
Sai suyi dariya tace,
"Dan wannan, shirya yanzu ma muje shan ice cream,"
Hajja bata barin fita, musamman da Aeeshaa, sai dai a kawo masu har gida, su cika parlour ana sha ana hira, har da su Hassana.
Hajja ta amincewa da Umma ta koma gida, in yaso in Aeeshaa ta gama Idda sai ta koma can, Umma taji daɗin zama da diyar ta, dan haka ta tafi cikin kewa.
Wataranar juma'a da safe, Aeeshaa na whatsapp, sai taga Haermeebraer, (me😆) ta sa status, abinda ta rubuta ya bawa Aeesha sha'awa, nan take ta yi replying, da "Nice one" ba yan wasu mintuna, Haermeebraerh ta amsa mata da "Thank u🥰"
Daga nan hira ta fara, Aeeshaa ta sanar da ita dik matsalar da take faruwa a gidan su, iya abinda ta sani, a lokacin, including rashin lafiyar Sabeer, sai dai har a lokacin Aeeshaa bata da masaniyar son da Sabeer ke mata.
Amma Haermeebraerh ta gano hakan a labarin Aeeshaa, dan haka a cikin shawarwarin da ta bata, har da yanda zata qirmama Sabeer, tayi hakuri da halin shi da take gani, a gaba zata fahimci komai, Aeeshaa taji daɗin shawarwarin da ta samu, musamman na yanda zata gyara lamarin rayuwar ta, da yanda zata zama very romantic kusan shi ne matsalar ta, dan ba laifi ta ko ina aka taba ta ta san me take.
Bayan ta gama hira da Haermeebraerh ta koma IG, sai taji kawai tana son taga wace wainar Hadiza ke soyawa, tana shiga taga ta sauke hotunan Khaleefa da ta saka, musamman wanda ta nuna zasuyi aure, ta maye gurbin su da wasu na addu'o'i da neman gafarar Allah akan abubuwan da tayi a baya, murmushi Aeeshaa tayi, ta danna masu heart, sannan ta kashe data ta sauka.
Ameerah da ta fara zama sosai, da rarrafe,ta yi bacci, addu'a ta yi mata ta shafe mata jikin ta da shi, sannan ta fita dan zuwa wajen Hassana, dan yanzu In Hajja na kula da dan tsohon mijin ta bata kula ta, sai tayi ta hira Hajja na tashi ta shiga daki tace tana zuwa, a haka ta sake gane yanda ake kula da miji, mannewa miji sosai kan sa yaji ya gaji yana buqatar a bashi space, sannan sake miji sakaka, ba body contact nan ma yana sa miji ya nemi inda za a rab'a shi, so ki zama mai daidaita lamarin gidan ki, da tarayyar ki da mijin ki.
"Maman Ameerah,"
Cike da kunya tace,
"Ahhh ni kam Adda Hassana ba diya ta bace, diyar ku ce, rainon ta nake maku, Adda ina Ammar?"
"Aeeshaa qaniyar ki, yaushe na fara wasa dake,"
"Addaaaaaa, just tell me, do u love him?"
"Hummm kind of,..... he is cute, gentle, ke komai ya hada, i think i am so in love with him,"
"And i love u more, i can't wait to marry u, will u marry me Hassana?"
Gaba dayan su juyawa suka yi suka gan shi jingine da qofar dakin Sabeer, ya dad'e yana tsaye basu sani ba, har zai magana ya ji Aeeshaa ta sako maganar shi sai yayi shiru.
Hassana kunya ce ta kama ta, ta tashi da sauri dan ta gudu, sai da taje daf da shi ta sauke hannayen ta sannan ta masa kallon qasa2, kallon da ya matuqar ratsa kowacce gaba ta jikin Ammar.
"Yes i will marry u, saboda ina son ka fiye da yanda kk so na"
Da sauri ta shige nata dakin, ya bude baki da qarfi yace
"Ai kuwa ban yar da ba, ke kin san yanda nake son ki kuwa? Lallai ina bin ki bashin yi maki bayanin yanda soyayyata take a ran ki,"
Leqo da kan ta tayi tace,
"Can't wait,"
Aeeshaa tayi sakaqeee da baki da hanci da kunne sai zabga murmushi take tana kallon yanda ake zuba soyayya.
Sabeer ne ya fito ya zauna kusa da ita yace,
"Hajiya Aeeshaa rufe bakin kafin qaton quda ya faɗa, ina babyna take?"
Rufe baki tai idon ta sai walqiya yake saboda farin ciki, soyayya akwai daɗi, ko zata samu hakan a rayuwar ta ta gaba oho? Allah shine mafi sani.
"Yah Sabeer wato soyayya akwai daɗi, kana ganin yanda su Yah Ammar ke zuba ta, Babyn ka tayi bacci,"
"Ummmm Aeeshaa ban yarda dake ba, soyayya mugun ciwo ne mai matuqar wahalar warkewa,yanda kk zaton zaka iya hakuri ka rufe ido ka ji ka warke baka samun hakan, a kullum kashe ka take tana qarawa, har sai ka samu abinda kk so, in ba haka ba, haka zaka mutu cikin rashin walwalar zuci kamar kowa,ke soyayya ba a iya bayanin yanda take, wanda yake yin ta shi kadai yake ji a jikin shi, daɗin ta ko wahalar ta, duk shi ya sani"
Ba qaramin nutsuwa Aeeshaa tayi ba da take sauraron bayanin Sabeer.
Ammar ya yi matuqar tausaya ma abokin shi kuma qanin shi to be.
Dafa shi kawai yayi ya dan bubbuga kafadar shi sannan ya fita, Sabeer sauri yayi ya goge 'yar kwallar da ke idan shi,
"Yah Sabeer lallai kana da babban experience akan soyayya dik yanda akai, ko zaka iya sanar dani wace ce wannan mai sa'ar?"
"Lokaci ne Aeeshaa, akwai lokacin da zaki gan ta ma da idon ki, so mu bar maganar nan, je ki dan debon ruwa na sha,"
Tashi tayi tana fatan ganin ranar da zata ga budurwar Yah Sabeer.
Binta yayi da kallo, yana fatan Allah ya mallaka masa ita, dan in ba ita ba baya jin zai aure, ko da zai aure sai dai yayi kawai amma ba dan soyayya ba.
Kawo masa ruwan tayi, Ammar ya dawo,
"Qanwar mu samin Number Addan ki pls,"
Amsa tayi ta saka mashi no Hassana, ta bashi tana dariya,
"Yah Ammar ya kamata su Baba General su san wannan lamarin fa, dan na matsu ayi bikin ku, ban taba attending biki ba, ko na su Adda Bilqis ban samu zuwa ba, na zauna a gida kar a bar gidan ba kowa,"
"Ina son faɗa Aeeshaa ina jin nauyin tinkarar su da wannan maganar,"
"Lallai indai yanda Yah Sabeer yayi bayanin so kana jin haka ai ba zaka san sanda zaka fada ba din, just go and let them knw how u feel about her, saboda in ba haka ba wani zai riga ka, dan naji tana zancen wani rannan"
Ta qarasa tana dariya,tare da kashewa Sabeer ido daya, wani numfashi Sabeer ya sake, tare da rintse ido, yarinyar nan zata kashe shi.
Ammar kam bai dauka da wasa ba, dan haka ya qudurta ana sakkowa daga sallar Juma'a zai sanar ma da Baba General, in yaso daga nan sai ya koma Yola, ya sanar da iyayen shi ya samu mata, kullum fatan su kenan dama.
"Yah Sabeer kazo mu koma gida, tinda Baba General ya yi kutun2n an dawo da kai Kano, gobe zan koma gida, gobe zan gama idda, kamar yanda musulunci ya tsara,"
"Haba dan Allah, gobe zaki gama? Alhamdu lilLAAH,🙊kinga bari muje mu fara shiri, lokaci zai qure, naji ma kamar Ameerah na kuka ko? Je ki duba,"
Da sauri mamakin Hamdalar shi ya kau mata, ta yi bangaren Hajja saboda ta gani ko Ameerah ta tashi.
"Na kusa kwafsawa fa baba,"
"Sauran qiris sunan wani film,"
Dariya sukai, tare da shigewa ciki dan shirya kan su, zuwa masjid.
*********************
"Dan Allah ku fitar dani, na gaji, ni ba barawo ba, ni ba dan fashi ba, kun bi kun aje ni anan, wata da watanni."
Banza sukai da shi, Khaleefa har abota ya so ya qulla da su amma sun maida shi dan iska, ko magana yayi suna hira dai su sauya hira, in daya zai fita to zai bar daya, tin da aka daure shi ba su kwance shi ba, sai dai sun sassauta mashi daurin, Khaleefa tinani ya masa yawa na me yasa ya saki Aeeshaa? Ga shi ya kwana biyu yana matuqar son kasancewa da mace, dik wani qoqarin shi na ko da kan shi ne ya yi sana'ar daya saba ta biya ma kai buqata ya gagara, saboda daurin da aka masa, in fitsari zashi sai su daure masa ta gaba, sannan suna bakin qofa, yayi ya gama a sake maida masa hannu a daure, hatta da qafar shi a daure take.
'Inama wayata na nan, ko Becca na kira da kwarewar ta sai na samu nishadi yanda nake so, ko Hadiza ma ba baya ba wajen iya.....'
Zaro ido yayi daya tino da Hadiza da kuma abinda take dauke da shi, bala'i, yanzu da gaske Hadiza za a aura masa? Wani abu ne mai.maqaqi da daci ya tokare masa wiyan shi.
Ihu ya fara sosai, yana buga kan shi,yana burgima, tasowa sukai, a zaton su wani iskancin ne,
Gani sukai abu yaqi qarewa, da sauri suka bude qofa, suka kunce shi, suka daga shi sama, zuwa mota, John ne ya bude qofa yana fadin,
"Karya yake yi fa ba wani abu dake damun shi, kar mu bari ya kufce mana,"
"Baka da hankali, ko mai zaman mu masu amana, muka bar masu da ya mutu sai sun tsane mu, mu kaishi asibiti sai mu kira su,"
Sun gama musun su kenan sai su ka juya wajen mota, suka nemi Khaleefa suka rasa................
KUN MAKARO
WRITTEN BY HAERMEEBRAER
PAGE 26
Khaleefa ya san in gudu za ai tini zasu kama shi, takun shi da nasu ba ɗaya bane,wani shago dake ya ke kusa da su ya fada, su John ba uniform ne ba a jikin su, balle a gane sojoji ke biye da shi,mai shagon ne ya ga an fado masa ba zato ba tsammani, a rikice ya durgusa dan kare kan shi daga koma meye ya zo masa a bazata haka.
"Malam lfy? Zaka shiga min waje kamar an jefo ka?"
"Ba gwanda wanda aka jefo ba, ina cikin matsala, wasu yan fashi ne suka biyo ni tin daga wajen gari har nan,rayuwa ta suke so, ka taimaka kayi ceton rai, kar su kama ni,"
"Shigo ta nan, shige ciki, bari na tsaya bakin shagona,dukiya ta nake ji,"
Da jarumta mai shago ya leqa, ya tsaya a bakin shago, ganin su John dik ya zare masa lakar jikin shi, komawa yayi kamar dan tsakon da ruwa ya mai duka, a bakin shagon suka tsaya suna tinanin inda za su gn shi, Auwal ne ya kama John yace,
"Muje kawai mu fada masu gaskiya,"
"Haka za ai,"
Komawar su mota suka sauya shawara, dan gano inda Khaleefa zai fara nufa.
Raba qafa sikai daya ya tafi gidan Khaleefa a adaidaita sahu, daya ya wice gidan Rebecca,suna jiran zuwan shi.
Khaleefa na fita yayi wa mai shago godiya, ya fita yana leqe, gidan Rebecca kuwa ya dau ki hanyar zuwa.
Rebecca na zaune ido ya mata zuru2, sakamakon warning din da ta sha.
"Sugar taimaka min nayi wanka, ki ji me ya samen,"
"Wace sugar? Wanne wanka? Kuma a ina? Fitar min a gida ba zaka ja min masifa ba, dik connection danake da shi kafin a kawon dauki sun lahantan jiki, ba zan risking jikina ba kuwa ka fi kowa sanin hakan,so get out,"
"Me kk nufi ne,"
Daya daga cikin dakin ta ne ya bude, already John ya yi ma abokin shi waya ya sanar da shi inda Khaleefa yake, dan haka yana gab da isowa, Khaleefa na ganin John, wani kuka ya xo masa, ya san in ya kama shi kashin shi ya bushe,
"Wai ku nawa aka baku ne kuke azabtar dani haka? Sai kace tsohon barawo,"
"Kudin kula da cin ka da shan ka da kuma na haya da muka kama, sai wanda zamuci abinci, kana da matsala da hakan ne,"
"A'a ba wai matsala nake da ita ba, kun matsa min, kun takurawa rayuwa ta, dan Allah ku barni ko kwana daya nayi anan na yarda ku maida ni,ko shekara zan,"
"Ba a bamu wannan umarnin barin ka zuwa gidan karuwai ba,wuce muje,"
"Yana ina?"
Yana qarasa shiga sukai ido hudu da Khaleefa da Auwal, Auwal ya debe shi da mari, sai da ya hantsila, ya qara kifa masa mari, Rebecca sai ihu take, sai da ya masa duka sosai sannan suka kama shi suka maida shi,
"Da ga yau ba zaka sake fita ba ko fitsari kk ji kayi a wajen, kai da sake fita sai dai kashi kashin ma sai mun amince da gaske shi kk ji za a bude ka, in banda abinka a lissafina sauran watanni biyu ka fita, lokacin za a haife maka shegen dan ka, ko 'yar ka, da an kwana biyu a daura maku aure da karuwar taka Ango"
Tinda Khaleefa yake basu taba masa magana har haka ba, balle su yi masa dariya, nan fa suka kafa tsokanar shi, shi dukan da suka masa ba shine ya sashi kuka ba, kiran shi ango da suke ne ya sashi kuka, dariya kuwa haka ya dinga shan ta a wajen su.
Kwana goma sha takwas Khaleefa ya qara a daure a wajen, Hajja ta sa a maida shi gida, a bangaren shi na da, no TV, no laptop, no phone, dik wani abu mai sa nishadi ba shi, daga redio da aka sawa kaset na karatun qur'ani ba komai a dakin, tin Khaleefa baya son sauraran karatun har ya fara hakura, watarana sai ya tashi da sha'awa yana son aikata tsiyar tashi ta biyawa kai buqata, sai yaji nauyi da kunyar yin hakan ga qur'ani na playing, haka yake hakura, lokacin sallah na yi Hajja da kan ta take zuwa ta sa shi gaba sai yayi ta, in ya kuskure a wani wajen in ya idar ta gyara masa, Hajja ke kai masa abinci, da dik wani abu daya ke buqata, ko sau daya ta hana shi ganin iyayen shi, ta hana su zuwa ko da da dare ne kuwa, dan da dare Auwal ko John ke zama bakin qofar shi.
Ba qaramin matakan tsaro da na gyara Hajja ta sawa Khaleefa ba, a ganin ta haqqin ta ne ta gyara shi, da ran ta da lfyr ta ba zata bar zuri'ar ta ta lalace ba, sai dai in bata numfashi, in iyayen da mijin ta ba zasu iya ba ita za ta iya, Allah bai tauye ta da komai ba, na lfy, da arziqi, ba zata qi bauta masa, kuma ba zata bari a zuri'ar ta a samu kafur kafur ba.
Khaleefa ya samu nutsuwar zuciya, har ya samu damar roqon Hajja a maida