Showing 39001 words to 42000 words out of 69262 words

Chapter 14 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1054

bude wani qamshi mai daɗi ya daki hancin shi, diba yayi ya fara ci, ita dai ko a wajen girki ta gama siye zuciya......

Tsayawa yayi cak da yayi wannan tinanin,

'Zuciiyar wa ta siya?inaaaa ba dai tawa ba kam, ai ni mai siyan zuciya ta sai ta shirya, a dai yi harka kawai'

Abincin shi ya gama ci, ya wuce dakin shi ya kwanta, ba sallah ba salati, wayar shi ya zaro dake silent, messages ya gani guda biyar, da no Hadiza.

"Chaii yarinyar nan akwai maita fa,dazu har wani lashe ni take kamar mayya, anyway ba laifi ta iya harka, za mu je da ita"

Dubawa yayi, messages ne na yanda yabo da nuna masa shi din gwarzo ne, abinda ko Becca bata masa,iyaka in ana harka ta fada,amma Hadiza bayan ta fada da sunayi gashi har messages ta turo masa, har yanda ya mata abubuwa sai da ta fada,ta na nuna yanda ta ji a lokacin da ya mata wani abun,Khaleefa ji yayi kamar ya koma su kwana harka, yarinyar nan ta iya sa ma mutum shauqi.

(Abinda Hadiza ta yi shi ya fi cancanta a ce matan aure na yi wa maza su, amma wasu ba su yi sai dai matan banza su yi musu shi yasa wasu ke yawo, wasu kuma rashin tsoron Allah ne kawai suna SAMUN komai har fiye da abinda suke samu a wajen,kowa dai da abinda ya ɗauka a matsayin dalilin sabon Allahn shi)

Nan take ya tura mata wasu daga cikin pictures din shi kamar yanda ta roqa,ai yana tura mata kamar jira take,nan da nan ta dinga turo masa hotunan ta da suka sa shi tashi zaune yana bi yana kalla yana kama jikin shi tsabar kwadaituwa da ita da yayi.

Khaleefa kasa jurewa yayi, ya aje wayar ya nufi dakin Aeeshaa, cikin bacci ta ji yana qoqarin shigar ta(abinda aka hana a islam) farkawa ta yi, ta tura shi gefe,

"Meye haka Yah Khaleefa? Ni na fada maka bana son irin wannan , ni matar ka ce in kana buqata ta ka tasheni ka min abu a hankali, amma sai kana nemana ina bacci,bana so,"

Khaleefa bude baki yayi yana kallon Aeeshaa,tinda suke bata taba maida masa da magana ba, daga yi hakuri sai ba zan sake ba,in bata son abu sai dai tayi ta kuka ko ta gudu, lallai yau ya tabbata ya kaita maqura,kuma ya kula tinda take da cikin nan ta fara masa haka,

"Ke wai shin ma yau cikin nan watan shi nawa?"

Nan take idon Aeeshaa yayo waje, kar dai hankalin shi ya dawo kan cikin ta,

Komawa ta yi ta zauna,ta fara qoqrin cire rigar ta, dan janye hankalin shi akan cikin,aiko tayi nasara.

Saida ya gurje ta kamar wanki, sannan yace,

"Mu dawo maganar mu, na ji rannan da Umman ki tazo tana fada tana cewa baki ko san cikin ki wata nawa bane,kina ce mata wata shida ne,haka ne?"

"Eh haka ne,

"Kuma kina zuwa asibiti ana saka kwayar nan, kina shan magani akan idona na shaida, me yasa cikin ke girma baya qasa?........."

*Tambaya wa zai amsawa khaleefa na mamajo?*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 17

Aeeshaa dai bata da anmsar bashi dan haka kwantawa kawai tayi a kusa da shi ta yi shiru,

"Ina miki magana kin yi min shiru, wannan ai raini ne,"

"Yah Khaleefa nima ban sani ba, tinda yace mu jira wata biyar mu gani mu jira mana, me ne ne abin saurin a ciki, muka jira watannin baya sai na gaba ne zai mana wahala? Dika2 wata nawa ne ya rage yanzu, dan girman Allah kayi hakuri bacci nake ji,"

Whaaaatttt? Did u hear that? Aeeshaan ku fa ta fara zama babbar mace😅

Khaleefa bai samu bakin magana ba, shiru yayi yana nazarin a wanne yanayi wai take maganar nan ne? Fada ta masa ko fada masa fact din take kawai? Yana wanan tinanin har bacci ya dauke shi a dakin Aeeshaa, yau ne rana ta farko daya kwana a d'akin, da sai dai lalurar shi ta kai shi da farkon dare ya tafi ko ya je mata da tsakiyar dare ko kuma da asssuba kamar maye🙊

Ana kiran asuba Aeeshaa ta tashi domin gabatar da sallah, ji tai an qanqame ta, kamar za a kwace ta, d'aga kai ta yi taga yanda ya ɗora kan shi daf da nata, hannayen shi na kan qirjin ta, haka ma qafafun shi suna maqale da nata.

Hade ran ta tayi, shi baida aiki sai hakan,a karon banza ba zai mata wannan riqon na so da tausayawa ba.

Janye hannayen shi tayi daga kan qirjin ta, aikuwa kamar yaron da aka kwacewa alawa, ya qara rarumar ta ya matse a jikin shi,

"Wasssshhh Allah na"

Bude ido yayi ya ga kwanciyar da yayi, da sauri ya sake ta yayi baya yana zaro idon shi, rufe jikin shi yayi ya tashi, ya sanyakayan shi ya bar dakin, da kallo tabi bayan shi, daga baya ta tashi ta je dan tai wanka tayi sallah.

Yau Khaleefa ko karyawa bai ba ya je wani babban shago da suke saida wayoyi, ya siyo ma Aeeshaa waya mai kyau, ya had'o da yan abubuwan motsa baki, ya nufi gida, sanda yaje ta gama haɗa abin karyawa, ta saka doguwar riga baqa mai ratsin blue, ta daura mayafin, gwanin sha'awa, lips din ta sai walqiya yake, gashin ta ya kwanta a bayan ta,ga qamshi mai kwantar da hankali dake fita daga kowanne sassa na jikin ta, cikin ya matuqar amsar ta ya mata kyau sosai.

Ya na shiga ta tashi tana masa sannu da zuwa, yau ce rana ta farko da Khaleefa ya mata magana ba fada ba hantara ba zagi,

"Yauwa, kin gama abinci? Yuuunnwaaa nake ji,"

"Na gama, bismillah,"

Aje mata ledar kayan yayi ya wuce ya fara durawa tumbin shi abinci, yana ci yana kallon ta,ta aje kayan a gefe inda daya gama zai dauka ya wuce dakin shi.

"Ki duba mana,"

Kallon shi tayi kafin ta fara buda ledar farko, kayan marmarin da take so ne, murmushi ne ya subuce mata, dan ta samu abun karyawa, dama yunwa take ji ta kasa cin abincin.

Dayar ledar ta bude ta ci karo da waya mai mugun kyau da tsada, da sauri2 ta qarasa zaro ta tana washe baki, Khaleefa ma murmushin gefen baki yayi, ya qura mata ido, wayar shi ce tayi qara, yana dubawa yaga Hadiza ce ta ke kiran shi, bai dauka ba, amma zai so ya dauka ɗin, da ta ji bai dauka ba ta turo masa message,

_Duba_ _whatsapp_ _dinka_ __love_

Da sauri kamar wanda aka mintsina ya tashi yana murmushi,

"Ki sata a caji kan ki fara amfani da ita,ban da kiran qawaye, kuma inna kama ki kina abinda bai dace ba daga ranar zan amshe ta,"

"Na gode Allah ya qara budi, Allah ya sanya ka farin ciki,"

Garammm ta ji qarar qofa, juyawa tayi taga ya shige daki,

'Mai hali ai bai fasawa'

Bude whatsapp din shi yayi ya ga hotunan Hadiza, ta sha gayu da qananan kaya dik qirjin ta a bayyane, riga ce shara2, yan mitsi2n n****wanta a waje a tsaitsaye, Khaleefa kiran ta yayi suka hau hirar su ta rashin da'a.

Ranar bai fita office da wuri ba.

Da rana Umma tazo da su Ameena, Ameena da Aeeshaa sunyi murnar ganin juna sosai, Abdul ba laifi harda gaisuwa.

Bayan sun gaisa da Umma, Umma ta debo kayayyakin da take tarawa ta ba Aeeshaa,

"Saura naji kin fada ma wani ni na kawo,"

Dariyar qasan maqoshi Aeeshaa tayi, kwana biyu Umma ta daina nuna matsananciyar kunyar nan, da alama anayi da wannan jikan ko da ita ba a yi da ita.

Godiya ta yi sosai, ta nuna ma Umman wayar ta sabuwa da aka siyo mata da safe.

Kar ba tayi ta kalla, ta miqa mata,

"Allah ya tsare, aji tsoron Allah wajen amfani da waya, dan yanzu waya ta zama makamin kai da damar mutane wuta, an sauqaqa zina da dikkan wani mugun abu, yanzu har bokanci ana yi ta waya, dan haka ki ji tsoron Allah akan waya, dik abinda zaki kiyi kina tinawa yatsa daya in kin dora akan screen Allah yana ganin me kk danna, mala'iku na rubuta abinda kk aikata,"

"Inshaa Allahu Ummana zan kiyaye, na kuma gode,"

Tana son ta dakko masu abin tabawa tana tinani tasan halin Umma, tinda take ko ruwa bata taba sha a gidan ba, tashi tai a hakan dai bari ta kawo.

Fruits ta wanko ta kawo masu da juice, da snaks, Ameenaa da Abdul kuwa sun ci, amma Umma sai azalzalar su take akan suyi sauro su tafi, ko ta wuceta barsu,

"Umma ki barmu anan,"

"Abarki dai,"

"Ohhh Abdul Allah ya nunamin sanda zaka daina qina,"

Jikin su je yayi sanyi dika har Umman, a ran ta tana son aje kunyar nan amma abun yabi jikin ta, hakan ne ma yasa take zuwa akai2 kwana biyu, amma har yau Khaleefa bai san tana zuwa ba sai sau guda da sukai kacibus da shi ta riga ta zo shi ma ya dawo dole suka shiga ba ɗan ta so ba, Hajja ma a tinanin ta bata taba zuwa ba har yau, har fada ta mata,amma tai shiru ita dai bazata ce mata taje ba.

"Kawo na sa maki whatsapp a wayar ki, na buɗe maki facebook,instagram, na sa maki snapchat"

"Nan kafi kauri,"

Abdul karba yayi ya saka mata through Xender, daga wayar Umman su, nan da nan ya bude ya koya mata yanda akeyi, Instagram ne yafi daukan hanakalin ta, da facebook, tinda Whatsapp bata da no kowa, Abdul ne ya sa mata no Umman su, data Hajja.

Tayi murna sosai,aje wayar tayi, ta bama Umman ta lokacin ta, Umman ta ji daɗin hakan, amma sai ta ce bari su tafi, kafin wannan dan rainin wayon ya dawo, dik da ba wani jituwa suke ba amma Aeeshaa bata son Umman ta na fadan hakan.

***********************

Cikin Aeesshaa ya kai wata bakwai, ya shiga farko2n na takwas,Hajja ce ta zo da yamma liqis, cike da fara'a,dan so take ta wuce da Aeeshaa,

"Hajja na haɗa komai da kk ce, amma ai zamu jira ya dawo ko?"

"Ahhh dole ai, na dauke masa mata bai sani ba? Ke dai gama shiryawa kawai, ina nan ina jiran shi, na tambaye ki yafi sau shurin masaqi lafy kuke kince lfy kuke, ana zaune lafiya ace mace bata da lambar wayar mijin ta waya tayi wata,tabbas akwai wata a qasa da ba a son na sani, kuma in Allah ya so sai na gano ko me ne, ai ita qarya fure take bata 'ya'ya"

"Kaiiii Hajja ba kyau mita,tsufa take sawa,"

"Uwaki, ni din da wace ce? Ai kowa ya ganni ya san dama tsohuwace ni,ko dan kinga ban takwarkwashe ba?"

Haka sukai ta hira suna kumawa, Hajja na sane taqi kiran shi so take taga yaushe zai dawo, ta san lokacin tashin shi yanzu yayi, me ya hana shi dawowa har anyi magrib yanzun.

Abinci Aeeshaa tayi mai sauqi suka ci, ta aje ma Khaleefa ma, tana nan zaune suna taba hira da Hajja Hadiza ta shigo, ta sha kwalliya kamar mai zuwa gasar zaɓen sarauniyar kyau,

"Amarya ina ta kiran wayar ki baki daga ba, dama na ji mai gidan na nan ko baya nan dan na shigo, kar mu hadu ya hau fadan nan nashi,"

Aeeshaa sai kyafta mata ido take kwata2 bata kula da Hajja ba sai da ta zagayo ta zauna,

"Yi hakuri Ina wuni,ban kula ba,"

Hajja haka nan ta ji Hadiza bata mata ba, dan haka cikin daure fuska ta amsa da

"Lfy ke kuma wace ce kk tambayar me gida na nan ko baya nan?"

Kamar an gama sanin sirrin ta haka Hadiza ta ji,cike da daburcewa ta amsa,

"Maaammmmaqota muke, suna na Hadiza,"

"Ohhhh, to fita zamuyi yanzu,"

"Ok to sai anjima, Amarya sai munyi waya,"

"To na gode ki gaida Goggo,"

Bayan ta tafi, Hajja tace

"Wannan kullum take zuwa?"

"Eh, da farko Yah khaleefa baya son kowa ya shigo, daga baya kuma ya bar ta tana zuwa, in bata zo bama zai ce na kira ta ta yani zama, na kula bai son na zauna ni daya ne,"

"Ummm"

"Tsakanin ki da Allah yaushe yake dawowa gida?"

Jimmm tayi kafin ta amsa,

"Gaskiya wataran yana kai 1 ko biyu ma, kin san yanayin aikin shine hakan,"

Hajja kad'a kai kawai tayi akwai matsala, aikin shi bai kaiwa haka, tabbas wani wajen yake zuwa, amma zata gyara komai, in ma matsalar daga wajen Aeeshan ne zata gyara, in daga wajen shi ne zata gyra inshaa Allahu.

"Tashi mu tafi,"

"Hajja baya nan fa,"

"Nace muje, uban daya sa shi a dad'e shi zai sa ya dawo yaga baki nan,"

Driver ne ya shiga yayi ta diban kaya yana kaiwa mota, Hajja ta danna wayar khaleefa,

"In ka dawo daga yawon naka mun wuce gida da ita,"

Ta kashe wayar ta, Khaleefa kira yayi tayi bata dauka ba, ashe sanda Hadiza ta shigo, tana fita suka haɗu,ya dauke ta suka wuce wajen da suke haduwa,

"Mu je gida,"

"Habaa yanzu fa muka zo, kasan ina tsananin buqatar ka,plss ko minti sha biyar mu dan yi sai mu tafi"

Bai ko gama jin me zata ce ba ya fara tuqa motar zuwa gida.

Hajja na tayi ma Aeeshaa faɗa dan ta kula so take ya dawo kan su wuce, ita Aeeshaa tana ganin haramun ne ta tafi ba tare da izinin shi ba, shiyasa take jan lokaci, a dole haka suka tafi ba tare daya isko su ba.

Sanda Khaleefa suka iso bakin layin su, ya tsaya Hadiza ta bude motar ta fita ranta bace,da sauri ya ja motar ya nufi gida,yana zuwa ya ga ba kowa, sun wuce kenan gaskiya Hajja na masa abinda taso, ranshi bace ya fita rufe gate,Hadiza ya hango bata qarasa shiga gida ba, wani tinani ne ya fado masa a ran shi.........

*hummmmmmm wata sabuwa*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 18

Suna hada ido ta qunshe baki, dan ta ga fitar su Aeeshaa, ta san kuma yau a hannu yake, yanda ya wulaqanta ta sai ta rama itama, dariya ta hau yi, daga baya ta hade fuska kamar bata taba dariya ba, daf da shi ta je ta fara magana,

"Khaleefa mijin Aeeshaa kenan, ina Aeeshar ta tafi ta barka da tsohon daren nan? Hhhhhhhhh👏🏼har roqon ka nake amma kana wani min walaqanci kai me mata ko? Nima ai a gaban uwata na ke amma na bika, sai kaje yanzu ka kwana da pillo ko kuma ka yi ta....... kanka yau dai ka rasa, ba wan ba qanin karatun dan kama😅😅😅"

Wani taku take da ka gani kaga kwararriyar yar duniya.

Gidan su ta buda qofa ta shige, tana tsananin son kasancewa da shi amma ba yanda za tai, dole ta dan ja ajin ta itama.

Khaleefa ba shi da wani option daya wuce ya kira Rebecca ya ji in tana gari dan a gaskiya baya jin zai iya zama haka sammm.

Ya kira yafi sau biyar bata d'aga ba, ana shida ya qudirta in bata dauka ba ya hakura, sai da ya kusa katsewa ta daga.

"Hello sugar ya kk?"

"Lfy na ke,kina gida ne?"

"Eh sugar ina nan, amma ina da baqo, sabon Alhajin nan da nai ne ya zo yau ma, sai ruwan nera yake min, yaushe zaka shigo?"

Tsaki yayi ya katse wayar ya qarasa rufe gate din ya shige gida, zama yayi a kujera, qamshin Aeeshaa ne yake dukan hancin shi, ido ya lumshe yana hango surar ta mai kyau, wani irin shauqin son kasancewa da ita ne ya kama shi, no ta ya fara dubawa a wayar shi, ko saving bata samu  arziqin a mata ba, nan take yayi saving da

"Ayshaa"

Sannan ya danna dan kiran ta,har ya fara shiga ya katse me zai ce mata?

Aeeshaa na zaune da Hajja da Baba General suna hira, ta ga flashing, dubawa tai taga no ne kawai, ajewa tayi,

"Wa ke kiran ki?da daren nan, 11 ta kusa fa,"

"Hajja ban san no ba flashing ne ma ba kira ba,"

"K ki kira ki ji ko qaye mana, baki san me kiran ba ko yana da uziri amma ba kati,"

"K Hajja, bari na kira,"

Kiran no tayi, Hajja da Baba General suka ci gaba da hirar su.

Tayi ringing na farko Khaleefa ya na tinanin dauka ko bari, har ta katse bai tantance ba, kira ne ya sake shiga, dagawa yayi tare da amsa sallamar ta,

"Wato dan kin raina ni shine zaki fita daga gidannan ba da izini na ba ko? Wake da iko da ke daya wuce ni? Umarnin wa ya kamata ki bi tsakanin ni da Hajja?"

"Naka,"

Tashi tayi idon hajja akan ta, tana nazarin ta, nan take ta gano Khaleefa ne ya kira,murmushi tayi.

"Abinda ya faru shine na yi iya qoqarina Hajja ta bari ka dawo taqi, ni kuma bani da no ka, shi yasa, Hajja kuma taqi kiran ka tace sai ka dawo da kan ka,"

"Amma ai kome za ai ya kamata a fara sanar dani, ko dan an auramin ke sai aka ce banda iko ko 'yancin sawa da hanawa?"

Aeeshaa na jin ikon Allah yau, abinda ba ita ta aikata laifi ba da izinin magabatan su ta fita amma an tsare ta da fada, shiru ta masa ya gama fadan shi da surutun shi bata ce masa komai ba,sai hakuri datake ta jera bashi, sai da ya gama fadan sannan ya fara sakkowa,

"Ya cikin? Yana dai fita a hankali ko? Kina ganin alamar zubar shi ko?"

"Eh kullum yana fita kadan2,"

Cikin murmushi take amsa masa.

"Murmushin me kk?"

Kaiii gano ta yake?nan da nan ta kama inda2,

"Dama naji daɗi da ka kira ne kawai🙊🙉"

Rintse idon ta tayi, daga ina wannan maganar ta fito,....dan murmushi yayi shima,

"Koh?"

"Eh"

'Wayyoo meke damuna ne?.... ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login