Showing 48001 words to 51000 words out of 69262 words

Chapter 17 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1039

murmushi tayi, bata ce komai ba har ya daga,

"Hello sugar, zo ka buden qofa mutan unguwar ku kar su cinye ni da kallo,"

"Whattt ar u mad? What brings u here, dn't i tell u to wait for me, how did u even knw my home? Oh my god i am so dead"

Kashe wayar yayi ya fita cike da damuwa, yana budewa ya fizgo ta ciki, fadawa tayi jikin shi ta lafe kuwa abin ta, da sauri ya rufe gidan, nan matasan unguwa suka fara gulma, ana nuna shi, ana gulmace².

"Daga tafiyar matar shi gida har ya fara kawo arna, dan wannan ko musulma ce iyayen ta ba a gari suke ba,"

"Kai dalla kauce waya fada maka wanda iyayen su basu gari kadai ke shiga irin wannan? Na rantse da Allah wata ma uwar ta ke sai mata damammun kaya ko ta kai mata dinki wajen telan da zai fidda mata komai, kuma a gaban ta za a auna ta, ko ka manta nima tela ne?"

"Haka ne fa, Sagir, ni kai na nan abinda qanwata da babarmu keyi ai sai addu'a kun san komai ai,ko na masu wa'azi ba sa dauka, da sun ganni sai suce ga ustaz nan, gemuna kuwa yayata har ja take tana cemin dan taure tsabar sun raina sunnar Rasulullah, ai gemu ba abin zagi bane komai munin wanda ya tara shi, gemu sunnah ce, sai dai in an tara shi dan koyi da arna,yanzu dai mu bar maganar su, Allah ya shirye su, shine abinda zamu iya aikatawa, yawan zancen su zai iya sawa.muma Allah ya jarabce mu da wani sabon da ko tuba ba zamu samu damar yi ba,"

"Haka ne kuwa,"

"Sugar ina ta jiran ka baka zo ba, gashi jirgin mu ya kusan tashi, dan bana son tafiyar mota ina ta kiran ka baka dauka ba, shine na biyo ka,"

"Ba wani sugar malama,kin ko san a tashin hankalin da nake yau? Wama ya nuna maki muhallina, dubi shigar ki kin san zaki zo nan, tsakani da Allah ai sai ki gyara,"

Kallon kan ta tayi daga sama har qasa, shigar black tai matsattsun kaya sosai, shape din ta ya bayyana, hatta da jan bakin data shafa baqi ne, sai bakin tabarau, da ta manna, ga cingam tana ci cakal2, ta yi bala'in kyau, gashin nan har duwais.

"What is wrong with my outfit? Kana gani dogon wando na saka,"

"Kinga ya isa, yanzu ba ta wannan nake ba, iyaye na ina kyautata zaton yanzu suna hanya,ban san me ya tsaida su ba ma basu iso ba,.......

Sanar da ita komai yayi, tsaki ta ja mai tsaho sannan ta kunna kan ta cikin gidan, tana tafe tana magana, sai qoqarin tsaida ta yake kar ta hadu da Hadiza,

"Haka zaka shirya ka dakko jakar ka mu wuce ba zan asarar kudaden dana kashe ba hotels uku na kama mana, in min gama da wannan mu koma wancan, sannan clubs ma su zafi dik na aje mana, so ba zaka rusamin shaqatawa ta ba, lets go, go and bring ur...........wowww...... who the fuck ar u?"

"His fucking mate, don't u knw?"

Hadiza ce kwance akan doguwar kujera, ta cire kayan ta tasss, tana kwance alamar jiran Khaleefa take ya dawo su dora daga inda suka tsaya, Khaleefa sake yayi da baki, makircin Hadiza bai da na biyu, Rebecca dariya tayi, dan tafi Hadiza karuwanci, ta san in an fara ko an gama ko ana tsaka da yi, ta kuma san makirci kala2, Khaleefa ne zai mamakin hakan, Hadiza a zaton ta za ai bala'i, dan haka a shirye take, sai ta sha mamaki.

Kau da kai Becca tayi, ta zauna, qafa daya kan daya,

"I am waiting, go inside and bring ur bags out,"

Kamar raqumi da akala,haka yaje ya dakko jakar shi, Becca ta miqe Khaleefa na gaba,Hadiza na bin su cikin tashin hankali, in khaleefa ya wuce ya barta da cikin nan ya zatai,bata san ranar dawowar ta ba, har gate ta bi su, Becca cikin dariya ta ce.

"Baiwar Allah, Hadiza ko? Kar ki mamaki, na sha ganin cheep chats din ku ke da shi, so na san ki sarai, qaramar karuwa, karuwar gida, ki koma ki saka kayan ki, kafin gyatuma ta fito ta gan ki tsirara gidan maqota, ta yanke jiki ta faɗi, ni nan da kk ganni karuwanci na da ajin shi da kuma sa albarkar iyaye, ke da iyaye basu sani ba shine ya maida ke qaramar karuwa komai zaki ba zaki ya nawa ba, yanzu zani neman kuɗi, kuma na shaqata da mijin wata kuma kwarton ki, inna samu kudi na ikawa iyaye na ke fa? In kin samu sai dai ki boye ki kashe da dari da dari biyu,"

Wata dariya ta sake, ta shige mota, Khaleefa ya wurgawa Hadiza Keys din gidan, yace ta ce ma Goggo yayi tafiya, ya barta ta kular masu da gida,

Wasu hawayen bala'i da masifa ne suka sukar mata, ita aka ci wa mutunci haka.

Da gudu ta koma ciki ta saka kayan ta ta kira wayar Khaleefa yaqi dagawa, message ta tura masa, akan zata je gidan iyayen shi ta nuna masu cikin jikin ta.

Har ya kidime Becca ta amshe wayar, ta aika mata message, akan in taje ta tabbatar sun gano na shi ne, shi yayi gaba.

Hadiza kuka ta fashe da shi kamar zata shide, tana son Khaleefa da abinda ya mallaka, bata taba sanin akwai wata ba bayan ita,ta zaci kawai gidan karuwai yake dan leqawa ya samu wadda ta masa kawai ya gama ya dawo, ashe yana da ajajjiya kuma kwararriyar karuwa haka? A zaton ta da Aeeshaa kawai zata buga kishi,kuka ta saka sosai, ta qudir ta sai ta bata shi wajen Aeeshaa kuwa.

Rufe gidan tayi ta kai ma Goggo makulli ta shige daki, Goggo sai magana take mata akan me ya same ta tai kuka,bata amsa ba ta shige ta kwanta, ta ci gaba da kukan ta, har daki ta bita amma ta mata rashin kunya ta kore ta, fita tayi tare da yi mata addu'a, dik abinda ke damun ta Allah ya yaye mata, ya kawo mata sauqi, Allah kuma ya shirya mata ita.

***********************

Hajja tin da ta ga yanayin Muhammad bata sake tambayar shi me ya faru ba, dan ta san Khaleefa ne ya qunsa masa wani baqin cikin shima,ga shi suna asibiti so bata sake magana ba, bari har su gama jinyar Sabeer ta sa a dakko mata shi ko a ka ne, ta ci mai uwa.

Sabeer yayi sati biyu a asibiti kafin ya ji sauqi a sallame shi, Aeeshaa na nan na shayar da Ameerah wadda tayi qiba sosai, Aeeshaa ma haka, sun yi kyau kamar ka dauke ka aje gaban ka kai ta kallo.

Tinda ya samu sauqi yaqi yarda ya kula Aeeshaa, wani irin zafi yake ji a qirjin shi saboda kasancewar ta a gaban shi amma baida iko akan ta, kuma ba zai iya cewa ta dena zuwa duba shi ba.

Aeeshaa ta kula da hakan, tin kowa na ganin zafin ciwo ne, sai ya zamana kowa ya ga ita ɗaya yakewa hakan, to ko akwai abin da ta masa ne? Iyayen sun ɗauke ki bakan a tsakanin su ne sun daidai ta kan su, sun fi kusa.

Aeeshaa abun na mata ciwo sosai, ita kullum tana tinanin ya yake, ya lafiyar shi amma shi bama ya son ganin ta, yau dai har bangaren su zata sai taji me ne ne ta masa.

Ta shirya Ameerah sai qamshi take, itama ta shirya cikin doguwar rigar lace, mai kyau, ta yafa mayafi a kafadar ta, amma ta rufe wuyan ta, ta dau wayar ta ta nufi bangaren su Sabeer, har zatayi sallama taji maganar Sabeer,

"Ammar ba zaka gane ba, faɗa mata bashi da amfani, tayi aure, kan tinanin ina musulmi zan samu matar wani nace mata wance ina son ki, to me kenan? Ta bar mijin ta ta dawo min kk nifi? Ai ba zai yu ba, sai na sa mata tinani a banza, ko ta fara so na kuma da auren ta, ko muyi ta aikata sabo ni da ita, ko zan mutu ba zan taba fadan abinda ke raina ba, na riga da NA MAKARO, akan son ta, an riga ni,"

Wani irin tausayin Yayan nata ne ya makama ta, hawaye ta share, ko wace ce wannan yake so bai samu ba, har yake ciwo? Lallai she is so lucky to be loved by Yah Sabeer.

Kuka irin na yara Ameerah tai, ai kawai Aeeshaa sai ta sa kai, kamar zuwan su kenan,

Da sallama ta zauna, dan nesa da su, ta gaida Ammar, ya amsa cikin sakewa da kare mata kallo, lallai dole Sabeer ya kidime akan wannan halitta,

"Yah Sabeer ya jiki? Allah ya qara maka lfy, ya sa kaffara ne, As'alallahal azeem, rabbul arshil azeem, an yashfika Yayana,

Bari na koma, dama na shigo na ga jikin ka ne, dik da baka son yi min magana, Allah ya baka hakuri akan dikkan abinda na maka ba da sani na ba, ko da sani na,"

Tana kaiwa qarshe hawaye masu zafi suka sauka mata, rintse ido yayi, saukar hawayen ta kamar wuta aka sa masa a qirjin shi Ammar fita yayi dan ya basu waje.

"Aeeshaa ki daina damun kan ki, kin sani a da mun shaqu, amma a yanzu ke matar aure ce, ko kinga ina wasa da su Bilqis ne? Dik da yayuna ne su dole akwai tsakani, su din ba muharramai na bane, su Hassana da Hussaina sune zan iya sakewa sosai, ina fatan yanzu kin gane dalili na? Ki daina damun kan ki kin ji qanwata?"

D'aga kai tayi tana murmushin jin daɗi, Yah Sabeer daban ne a cikin maza, ya san dokokin Allah, kuma yana kare su, ina ma haka Yah khaleefa yake, nan da nan ta tina shi, qirjin ta sai da ya buga dan faduwar gaba, tinowa tai da Hoton su da ta gani shi da Hadiza, Hadiza na nuna shi a matsayin mijin da zata aura a IG, suna cikin motar shi, ga ice cream gaban su, yana bata a baki sukai hoton.

Da sauri ta dauki Ameerah zasu fita, fuskar ta ba walwala sam

"Lafiya Ayshaa?"

"Ba komai Yah Sabeer"

Da Ammar ta haɗu, ta wuce shi, Ammar shigo wa yayi yana kallon Sabeer da bacin rai,

"Wai kai yaushe zaka daina wannan halin kafiyar? Ance maka ka faɗa mata ko ka sassauta mata ku koma normal, ji yanda ka bata mata rai, yarinya kamila,"

"Nifa ba ni bane, kawai mun gama magana naga ta tashi kamar ta tina abu ta fita, mun gama magana mun fahimci juna, kawai naga ta hade fuska ta fita cikin sauri, na tambaya tace ba komai, me kk so nayi,"

Har Ammar zai magana Hassana ta shigo dauke da magani da abincin su, ajewa ta yi,ta masa sannu, Ammar kallon ta kawai yake, har sai da Sabeer ya taba shi,

"Ka fa kiyaye, yaya ta ce,"

"So? Ni ban girme ka ba? Ko dan ina abota da kai? Shin in ma sa'o'i muke da kai mace ai ba ta yi wa namiji kadan sai dai in bai balaga ba,"

"Da gaske kk yi kana son ta?"

"Kwarai da gaske in dai zata so ni, a shirye nake na aure ta, kana ganin a iri na gidan ku akwai mummuna ne ko mai mummunan hali?"

Shiru Sabeer yayi, shi dai iya sanin shi babu, amma yana zargin khaleefa bai da halin kirki, dik da ba zai nuna hannu akan wani laifin shi ba amma dai bai da halin kirki haka yake zargi,

"Gaskiya babu, a iya sani na,"

"Then zan saka kai kawai Alhaji,"

Tafawa sukai, Ammar na qara jin labarai akan Hassana.

***********************

Aeeshaa na komawa ta samu Hajja,ta kunna Data, dan ta nuna wa Hajja abinda ta gani, saboda qarin aure ba da sanin su ba babban abu ne,kuma Hadiza yake son aura for that matter.

Hajja ke waya,

"K, aiko min da su gida kamar wancan, kuma ka ci gaba da sa masa ido,"

Kashe wayar tai ta kalli Aeeshaa cikin tausayawa.

"Hajja akwai abinda nake son na nuna maki game da Yah Khaleefa,"

"Bana buqata, sai yanzu? Yanzu kk ga damar ki sanar dani ko ki nuna min wani abu game da mijin ki? Tin yaushe nake bin kan ki akan hakan? Kin nuna min? Riqe abin ki, nima na riqe abinda na sani akan shi, har a dawo daga dik gidan uwar daya tafi"

"Tafiya Hajja?"

Banza Hajja ta mata ta shige kitchen, tare da kwalla mata kira akan ta je suyi aikin abinci.........

*Team Sabeer me kuke gani game da shirun Hajja akan wannan lamari?.... Team Khaleefa me mutumin ku ke aikatawa a ABJ ne a bamu mu sha...😅*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 22

"Hadiza ni fa ban gane maki ba kwana biyu, kwata2 kin rage walwala, sannan yanayin jikin ki ma kin sauya, anya Hadiza? Kar ki sa na dinga maki zargin da ba haka bane, abinda nake zargin ki da shi bai kamata ace kina tare da shi ba duba da ke din bazawara ce"

"Goggo ki fito fili kice ciki ne da ni, yes ciki ne da ni, kuma cikin Khaleefa ne mijin Amarya,"

"Ya Allah, Ya kareem, Ya mannan, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wayyo Allah na,ya Allah ka sa mummunan mafarki nake yi kar ka tabbatar da wannan lamarin a zahiri,"

Kuka Hadiza ta fashe da shi, sai yanzu abun ke bata takaici, ta bata wayon ta, da tarbiyyar da Goggo ke bata a kullum, albasa batai halin ruwa ba.

Goggo ce a harzuqe ta nufe ta,

"Kukan me zaki? Ashe dik tarbiyyar da nake baki a banza? Dama tin da naga fitar ki ta yi yawa addu'a ta Allah ya kiyaye mu kar ki dakkon magana, ashe ba zaki riqe maraicin ki ba da zawarcin ki har Allah ya kawo maki miji na gari, bayan kin san yanzu 'yan matan ma ba mijin suka samu ba, kowacce mace ta qanqame mijin ta bata son kishiya, koda kuwa mijin mai ra'ayin qara aure ne kin ban kunya, da ke da dikkan zawarawa masu aikata zina suna fakewa da zawarci suna aikata zina,tir da halin ki, tir da ke Hadiza,"

Goggo fada kawai take yi ji take kamar ta rufe ta da duka, ba dan ta kai zuciya nesa ba da har ciwo sai ta jiwa Hadizan mummunan ciwo kuwa, dan a rayuwar duniya ba abinda ta tsana irin zina, ga shi Allah ya jarabci zuri'ar ta da ita, wannan mummunan labari in ya yaɗu a dangin su daga na uba har nata ai sun shiga uku, qara nesanta za ai da su, kuma ga mutan unguwa za su shiga bakin su, ohhh Hadiza ta dakko mata magana.

"Goggo dan Allah ki zauna ki ji,ki daina daga hankalin ki, abinda ya faru ya faru,"

Dik daurewar Goggo sai da ta zabga mata magigicin mari wanda ya sa ta daina ganin haske na wasu mintina.

"Hadiza kar ki kaini maqura na maki abinda bana fata,dan uwar ki har kina da abin fada? Har ni zaki kalla ki ce kar na daga hankali na? Kin dagan shi tsaye ya zan ya kwanta yanzu, baki son na damu kk dau matakin wulaqanta ni, bani da buri wanda ya wuce na sama mana abinda zamu kai bakin mu, amma ke burin ki bai wice na ki watsar min da mutumci na ba ko? Allah ya shirya ki Hadiza?"

Hadiza ce ta fara magana cikin kuka sosai,

"Dan Allah Goggo ki yi hakuri, ki yafe min,inshaa Allahu wannan abun daya faru ba zai rusa komai ba indai kin ban hadin kai, so nake na aure shi, kinga shikenan mun samu surukin da zai dauke mana wahalhalin da muke ciki ko?"

"Ke yanzu kina ganin har kina da darajar da wani zai aura kuma? Me kk tanada da zaki ba namiji? Na farko dai na hana ki shafe2n mayukan nan na zamani kin kafe, fari banaki ba kowa ya gani ya san ba naki bane,dik yanda mai shafa mai ya so boyewa kar a gane wallahi sai an gane, kin zubda mutuncin ki a wajen mutane dan zasu gan ki baki waye ba, ke din ba ki da tarbiyya,ke mai sabon Allah ce kin sauya halittar da ya maki, kin raina Allah wa'iyazu billah, kina nuna masa bai iya halitta ba, ke ce kk iya, subhanallah,Hadiza baki iya girki ba, nayi2 ki koya kin qi, Hadiza baki da tsafta, da girman ki komai sai na maki in ban ba gidannan ya rub'e dan qazanta ke ba abinda ya dame ki bane,Hadiza ibada bata dame ki ba dik da damun ki da nake na saki gaba dan ki yi amma inaaa, Hadiza kwata2 ke ba yariyar kirki bace, kan wani ya fadamin na sani da kaina shi yasa na rage bacci nake tsaya wa tsayin daka dan na yi maki addu'a,wannan abinda ya faru ma na San jarabawa ce daga wajen Allah dan jarabta imani na"

"Goggo.....kiiikiiii....yaaafeeminnn, inshaa Allahu na daina dikkan abinda kk ce, na tuba Goggo, daga yau na daina aikata dik abinda Allah yace a bari, bana son na shiga wuta goggo, wayyooo Allah na, Allah ka yafe min, ya Allah kai me gafara ne kana son masu tuba Allah ka yafe min,"

Hadiza fa da gaske take kukan nan, kamar zata shide, gane cewa da gaske take neman gafarar Allah ne yasa Goggo ta rungume ta,tana lallashin ta, tare da kwantar mata da hankali.

"Goggo yanzu zubar da cikin za ai? Wata biyu ne da kwanaki, na je asibiti an tabbatar min da hakan,"

"Sam ba zamu zubar ba,yanda kk dakko sai kin haife shi,ina tausaya wa wannan mata yanda zata ji cin amanar da kk aikata mata,"

"Goggo na fiki tausaya mata yanzu, a da ina ganin itace babbar maqiyyiya ta,amma yanzu na fuskanci ni ce maqiyyiyar ta,kuma na cuci kaina,dan yanzu haka shi baya nan, ya tafi shaqatawa da wata karuwar shi,"

"Karuwar shi?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login