Showing 12001 words to 15000 words out of 69262 words

Chapter 5 - KUN MAKARO BOOK COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

17 Oct 2025

1032

Baba General bane ba zata zo tarar shi ba, amma data ga yayan su ne ba zai hana ta tafi ba bata gaida shi ba,amma shine zai wulaqanta ta haka.

Hawayen baqin ciki ne ya fara zarya a kuncin ta, ta miqe ta shiga bangaren Hajja ta ma fasa shiga gaida su, Maman Khaleefan, zaune ta ga Hajja gaban mijin ta,suna zuba soyayya, suna cin abinci.

Ganin yanayin ta yasa Hajja miqewa da sauri ta yi wajen ta,

"Takwarata me ya same ki? Baki ga mijin naki ba ya dawo tin dazu, kina can kin ga dangi kin manta angon naki, wannan kwalliyar shi kk yi ma, amma kk bata ta da hawaye?"

"Zo nan amarya ta me ya faru?"

Qaqalo murmushi ta yi, ta zauna dan nesa da Kakannin nata, Hajja na zuba mata abinci, ta aje mata a gaban ta,

"Mu a qasa muke cin abinci dan yafi daɗi, ke da kk 'yar zamani, kina iya hawa can,"

"Nima anan din zan ci, Baba General Ina wuni, ka dawo lafiya? Nayi kewar ka sosai, da sosai,"

"Lafiya qloau Amarya ta, amma baki fad'an abinda ya saki kuka ba, me ya same ki?"

"Ammm baaa komai, ina shigowa ne na bige, shine na faɗi,"

Da sauri Hajja ta fara duba jikin ta ko zata ga wani ciwon suna mata sannu.

Bayan sun gama cin abinci Baba General ya umarce ta da ta je ta kira masa Khakeefa.

Gaban ta ne ya fadi ba kadan ba, amma ta dake, nan ta miqe, ta kama hanyar bangaren su Khaleefa.

Maman Khaleefa ta fara gani,  gaisawa suka yi, gaisuwar yaushe gamo, sannan ta sanar da ita me Baba General yace, sai Maman tace mata taje ciki yana nan, ta kira shi.

Gaban ta na dukan uku2, ta taka zuwa parloun shi,a qofar dakin shi ta tsaya, nimfarfashin shi take ta ji,a zaton ta ko bashi da lfy ne, ko wani abu ke damun shi.

Lokacin da Khaleefa ya wuce ta, bata san cewa a matse ya dawo ba, gashi yau ba shi da ra'ayin zuwa hotel,a gida yake son sauke buqatar shi tinda dare bai yi ba, wannan dalilin ne yasa yana komawa ya dakko laptop din shi, ya shiga sabon website da ya binciko da suke saka sabbin fina-finan banza, network ke ta bashi matsala, dan haka yayi nisa bai ji zuwan kowa ba, yana ta aikata masha'ar shi.

Cikin taraddadin bata san me zai je ya zo ba, anya ya dace ace mace ta shiga d'akin baligin namiji kamar Khaleefa ba tare da neman izini ba? Ita din ba ma'abociyar shiga waje ba tare da izi bace, amma wannan nimfashin kamar na mara lafiya ne, bari ta leqa taga meke damun shi, in wanda zata taimaka ne sai ta taimaka, in sai ta kira iyayen su ne kuma to.

Cikin rawar hannu ta bude qofar, Khaleefa ne ya saka Laptop a gaba, jikin shi babu koda mayafi, ya fita hayyacin shi, cikin tsananin firgici da tashin hankali ta zube a wajen, tare da kwalla kara.

Da sauri ya juya,ya gan ta,nan da nan ya fara diban kayan shi yana sawa,ya kife laptop din shi, ya dauke dik wani abinda bai kamata wani ya gani ba, ya nufi wajen ta...................

*KUN MAKARO*

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 6:

A duqe take kan guiwowin ta, idon ta a rufe, bakin ta na rawa, hawaye face2 a fuskar ta, dik wanda ya gan ta zai zaci gamo tayi d fatalwa, ko aljanu, tsabar tsoron dake kan fuskar ta, babu wanda bai san iskanci ba, tabbas Khaleefa kura ce a cikin fatar rago, ba qaramin dan basaja bane, a zaton da take masa, tsabar nagartar shi da kirkin shine yasa baya son hayaniya, tsoron Allah ne yasa baya son kula matan da ba muharraman shi ba, sannan yana tsoron Allah ne akan kalaman shi kar ya fadi sabon Allah shi yake hana shi yawan magana, ashe yana boye mugayen halayen shi ne.

Gani tayi ya goge hannun shi da tissue ya tako inda take, d sauri ta fara qoqarin tashi ta gudu, amma santsin qasan wajen da yanayin rigar da tasa mai santsi sai ya sa ta zame, Allah2 take wani ya shigo saboda ihun da tai,amma shiru, matsalar irin gidajen nan masu manyan qofofi kenan,Maman su na can parlour, zai wahala taji tinda babban parlour ne, qara zata sake saki, kafin ta kwalla ya damqe mata baki.

Magana yake son yayi, amma bai ma san ta ina zai fara ba, cikin zare ido, da tsoratar da ita ya fara magana,

"Abinda kk gani ya tsaya a tsakanin mu,in kuma kina ganin ba zai tsaya a tsakanin mu ba sai kin fada ma wani,ni ba zan hana ki ba, tinda ba tare dake nake yawo ba, amma ki kuka da kan ki, dik abinda ya same ki, da mahaifiyar ki da qannen ki, je ki zaki iya tafiya, ba zan iya dogon surutu ba ni,"

Tsoron shi ne mai tsanani a tare da ita, kuma shima ya fuskanci hakan, dan haka ya qara daure fuska, ya nuna mata bai damu ba, in ta ga zata iya risking rayuwar ahalin ta ta je ta faɗa,cikin sauri ta qoqarta miqewa ta fita, da sauri ya bi bayan ta ya sake fizgo ta,

"Me ma ya kawo ki waje na, bayan kin gaishe ni ban amsa ba shine dan naci sai kin biyo ni,"

Bakin ta na rawa sosai ta furta,

"Baaabbbaa Geeegggeneral keee kiran ka,"

"Shit ! Me zan yiwa tsohon nan ne? Ya qaqaban auren da ban so, ya sani zullumi da zancen nake kwana nake tashi, kiran na meye yanzu kuma, me kk ji yana magana akai?"

"Baan san ni ba nima,"

"To goge idon ki, kuma ki nutsu, kafin ki jawon magana wajen tsohon can, dan na kula bai haɗa son ki da kowa ba, "

Da saurin ta kuwa ta fara gyara fuskar ta, da dikkan wani abu da ke buqatar gyara a jikin ta, ya ji daɗin yanda take tsoron shi, hakan zai bashi damar yin abinda ya so kenan, da kyau.

Komawa ciki yayi, dan bai isa fita a haka ba, dole sai ya dan watsa ruwa, ita kuwa data fita a parlourn shi, bata ga kowa ba, ta godewa Allah, dan bata son wani ya tambaye ta me ya faru.

Tap din flowers ta nufa,ta kunna tana ta watsawa fuskar ta ruwa, tana koka me ta gani, wannan abu ba zai taba barin kan ta ya huta ba, bata san sanda zata daina hango wannan mummunan gamon ba,wataqila sai bayan ran ta, bai kula da ita ba sanda ya wuce, tana ganin shi ta manne jikin queen of the night dake shuke a kusa da wajen da take saye, har sai da ya wuce, qamshin turaren shi mai sanyi da daɗi ta shaqa, dazu kafin suyi mummuna gamon nan, ta yaba da qamshin, amma yanzu qarni da wari yake mata, da sauri ta sake splashing ruwa a fuskar ta, ta shaqi iskar wajen, idon ta rufe, sai da taji hankalin ta ya kwanta sannan ta fara qoqarin komawa ciki,ta na shiga ta ji Khaleefah na fad'in,

"Tinda gata ta zo kawai ku fara komai na shirye2n bikin, ni me zance, yarinyar da na ninka shekarun ta amma wai ita kuke son haɗa ni da ita, in ma nace bana so ba ji za ku yi ba, ko ra'yin ta akai na na tabbata baku ji ba, shekara nawa a tsakani, tin tana aji biyar baku nemi ra'ayina ba sai yanzu da lokaci ya qure,"

"Bamu kira ka dan ka mana rashin kunya ba tijararre, tinda kai ba a fara abin arziqi da kai bai koma na tsiya ba, da kai da Aeeshaa dika mallakin mune, zamu iya zaba maku wanda muka so, ko sisin ka bamu buqata, zamu aura maka ita, za kuma akai ma ka ita gidan baban ka na kabuga, in kaga dama in an kaita kar kaje gidan, kace ba ka auren, tashi ka bar mana nan dan iskan yaro kawai,"

Hajja ke shafa hannun General a hankali, saboda yanda ta kula ranshi ya baci matuqa, cikin rashin kunya ya miqe zai fice, Aeeshaa da ta ji dik abinda ke faruwa ce ta shigo, idon ta na tsiyayar da hawaye, ta durqusa a gaban General da ke cikin matsanancin fushi.

"Baba General ka taimaka min kar ku auramin wannan fasiqin, kar ku hada aurena da shi yafi qarfina ba zan iya auren shi ba, dan Allah kar ku jefa rayuwata cikin halaka, na sani tin tasowa ta ba wanda ya damu dani, ba wanda yake jin me nake so, ko meye bana so, dik abinda aka so yankewa ake akaina, na tabbata in mahaifina na nan zai tsaya min, dan.....

Wani gigitaccen mari ta ji ya sauka a kuncin ta, tana juyawa ta ga Umman ta tsaye,

"Lallai wuyan ki yayi kaurin da har zaki sa iyayena a gaba kina aibata jikan su a gaban idon su, wato tarbiyyar da na maki kk son nuna masu ko? Sai ki bi mahaifin naki shi da ya fimu son ki ya tafi ya barki bai tafi da ke ba,mara mutunci, durqusa ki basu hakuri,har Khaleefa din,"

Khaleefa na jin haka ya sa kai ya fice, dan shi wannan drama ba da shi ba, sun dad'e basu aura masa itan ba, ko kuma sun dad'e ba su fasa bashi ita ba, dik ɗaya ne a wajen shi, bakin ta na rawa ta fara bawa kakannin nata hakurin abinda ta aikata, zuciyar ta kamar ta fito waje, ji take da ta san inda Yayan mahaifin ta yake a Katsina can zata gudu.

"Khadeeja bai kamata ki yi saurin dukan ta ba, ra'ayin ta take faɗa, amma Aeeshaa ina son ki gane, ita mace budurwa iyayen ta ke zaba mata mijin aure, bazawara ita ke da 'yancin zabar miji, dan haka ki yi hakuri da zabin General, inshaa Allahu ba za ki yi dana sani ba, maza jeki, ki yi alwala magrib tayi, Allah ya sanya maku albarka,ya kare dikkan abin qi,"

Cikin rangaji irin na mayen damuwa take takawa zuwa daki, Umman ta ta bita da kallon tausayawa a cikin zuciyar ta, ta sani bata kyauta ba,amma ba zata iya jayayya da mahaifan ta ba,ba su mata wannan tarbiyyar ba,dole ne diyar ta itama ta zama mai biyayya.

General ne ya tashi dan zuwa masjid, yau Khaleefa bai je ba, Sabeer kawai ya gani, ya kada kai, wato dan an masa fada shi yasa yayi fushi har da sallar ma,Allah ya shirya.

Har Umma ta tafi bata nemi ganin Aeeshaa ba, dama Aeeshan ta san za ai hakan, bata sa a ka ba, dan haka tana idar da sallah ta haye gado ta nade cikin bargo, saboda ciwon kan dake damun ta, Hajja ce ta shigo dauke da mug, ta hada mata shayi mai kauri, da kuma plate dauke da faten dankalin turawa, wanda ya sha kayan lambu, da kayan ciki.

"Tashi kici wannan ki sha magani sai ki kwanta, kin yi sallar isha'i ko?"

D'aga kai ta yi,sannan ta fara sauka,ta daukar wa kan ta alqawari bazata sake ma kowa musu ba har qarshen rayuwar ta,sai dai in abin da ya sab'awa Allah ne, shi kaɗai ne ba zatai ba, ta kula rayuwar ta bata da amfani a cikin iyalin ta,abinda suke so shi suke mata, koda kuwa shine abu na qarshe da ta tsana a rayuwar ta, ba ruwan su.

Abinci ta fara ci, Hajja na kallon ta da tausayawa, bayan ta gama ta sha maganin ta koma zata kwanta, Hajja ta riqo ta, ta jingina ta da jikin ta.

"My dear, ki sanar dani me ke ranki game da Yayan ki, in baki son shi ko kina da dalilin da yasa kk kira shi fasiqi ki sanar dani, ni na fara sha'awar haɗa ku, saboda ke ta gari ce, shi kuma halin shi bamu da tabbas akan shi, muna saka ran, ko me yake aikatawa mara kyau zaki zama sanadin shiryuwar shi, wannan dalilin yasa na sanar da General ra'ayina da tinani na, amma a yau in kk ce baki so,ga dalili kwakkwara, zan warware maganar nan, kin dai fi kowa sanin dik abinda nake so, shi General ke so,so tell me, i am here for u my dear,"

Hajja na magana tana tinani, tabbas tinda suka ce suna saka ran ta sauya shi, is either suna da masaniyar mugayen halayen shi,ko kuma suna zargin yana da mugayen halayen ne, dan haka is of no use ta tsaya masu bayani, dan haka kawai ta amince, Allah ya bata ikon zama da shi da amana, kar ta cutar da shi, kar ya cutar da ita, kuma zata miqawa Allah zabin rayuwar ta, dik abinda yake alkhairi Allah ya mata, ya kare ta daga sharri.

"Kinyi shiru baki ce komai ba,"

"Na amince da zabin ku, Allah ya shige mana gaba,"

Rungume ta Hajja tayi sannan ta mata kiss a goshi,

"Allah ya miki albarka,"

Nan ta dinga bata labarin zuwan su England, da su America, da sauran qasashen waje, da irin qauyancin da ta yi kan ta waye ta saba,just to cheer her up, tin Aeeshaa bata dariya har ta fara, sai da ta kula tana jin bacci ta miqe tace ta gudu wajen dan tsohon mijin ta.

Tana fita,Aeeshaa ta shiga sabon shafin tinanin yanda rayuwar aure zata kasance mata da Yah khaleefa.

*********************

Da safe Sabeer ya ji labarin amincewar Aeeshaa, hankalin shi ya qara tashi, lallai yana son maso wani, tinda ta amince shi me ya rage masa ya zauna anan, da hanzari ya wuce office, yana neman transfer ko kudu ne a hankada shi, inda ba zai sake ganin ta ba sai ya so.

Aeeshaa ta so su haɗu da shi, dan ta koka masa dik abinda ke zuciyar ta, ko hakuri ya bata ai ta samu sauqi, sai dai kash Sabeer ya danna layar zana.

*******************

Hajja da kan ta take saka driver ya kai su shagon HUMKAM dan a yi wa Aeeshaa dilka da halawa tare da dukkan na amare, ana gyaran jikin amare a shagon har ma da na uwayen gida suna saida kayayyaki na gyaran jiki koda mutum na so ya yi a gida da kan shi, ga kuma ingantattun kayan mata masu kyau da inganci, turarukan wuta da Shu'umar Khumra mai kyau,hummm abun dai ba a cewa komai sai wanda ya gani kawai, sai kuma wanda ya je shagon kawai, ga sauqin kuɗi ba sa tsawwalawa a kud'in kayayyakin su,(mai son kayan Humkam ya min magana ta pc) daga nan suka yi order ɗin sabulan gyaran jiki na HAMIBRAH BEAUTY PALACE, bayan sabulu har da man kitson ta sai da suka siya saboda ya qara gyara kan Aeeshaar,ga body scrub da skin oil, Hajja ta ce a sai breast cream da ke gyara nono amma Aeeshaa ta qi saboda kunya take ji,ba yanda Hajja ta iya dole ta kyale ta.

Aeeshaa kunya ta dinga ji saboda yanda Hajja  ke gyara ta ciki da waje kamar ta san wajen wanda za ta kai jikar tata,ita ko Hajja ko a jikin ta, haka ta dinga yi ma HUMKAM da HAMIBRAH bayanin aurar da jikar ta za ta yi, tana son a had'a mata kayan mata masu kyau da zasu gyara ta, nan kuwa suka dinga haɗa mata duk abinda ya dace, sai da suka tabbatar sun saka komai, suka buga lissafi, suka basu kaya suka tafi.

A zaton Aeeshaa kayan nan da ta gani za ai ta dirka mata tasha, sai taga Hajja ta adana su,ta boye.

"Kk zaro ido kamar an wurga mage sama, ba wai baki zan yanzu ba, sai an kai ki naga kamun ludayin mijin naki zan fara baki su, yanzu gyara zamu fara namu na gargajiya, natural gyara wanda ba zai lalata maki budurci ba,sai dai ya qara inganta shi, dan ba komai ake yi wa budurwa ba da sunan gyara kin gane?".

Kan Aeeshaa na qasa dan kunya, ga ajiyar zuciyar kwanciyar hankalin da ya shige ta sanda ta ji ba ita za a dirkawa wannan kayayyakin ba yanzu.

Aikin girki suka fara, hajja na son ta sake koyar da ita abincin gargajiya masu gina jiki, tinda ba laifi ta iya na zamani sosai, dan wasu ma Hajja agunta take gani.

Daga girki kuma sai  Hajja ta daina barin ta cin kowanne abinci, sai mai gina jiki, da zai qara mata ni'ima,kamar ganyayyaki. Farfesun da yaji kayan qamshi,shayin da yasha kayan qamshi da minannas kadan, sannan tana mata kwadon zogale, da alayyahu, tare da tumatur mai yawa, da albasa.

Gashi kusan koda yaushe tana markade mata cucumber da carrot, tana hadawa da sugar, zuma da dan gishiri kadan ta sa ta shafe mata jikin ta da shi, bayan ta gama ta jiqa lalle ta tace ruwan ta sa ta wanke jikin ta da ruwan, tin Aeeshaa bata so, ita kan ta sai ta ji tana so, fatar ta ta sauya, kyaun da tai ko ba kwalliya in ka kalle ta  sai ka qara.

Cikin wata daya, Aeesha ta sauya, harda girma sai da ta qara,ga shi ta cika sosai hips ɗin ta da dik inda ya kamata ajikin ta sai da  dik su ka ciko, saboda had'in ganyayyakin da ake bata, kunya take ji ta zauna ba Hijab, dan haka kullum cikin doguwar riga da Hijab take.

Sabeer dai har yanzu basu haɗu da Aeeshaa ba,wata rana ta na zaune a kujerun farfajiyar gidan ta hango shi zai fita da mota daga gidan,ashe a ranar ne zai koma aiki can Ibadan, ya yi kyau abin shi ya yi 'yar qiba tare da aje saje,Aeeshaa ce ta miqe da sauri ta bi bayan shi sai d'aga masa hannu take yi amma bai tsaya ba, ya ganta ko bai gan ta ba, daga shi sai Allah suka san hakan.

Cikin bacin rai, da rashin jin daɗi ta juya zata koma ciki,ta na d'aga qafa ta juya zata koma cikin gida cikin rashin sani ta sauke qafar ta a kan qafar Khaleefah, ita ba ta san ma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login