Showing 1 words to 3000 words out of 56438 words

Chapter 1 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

26

[10/26/2025, 6:26 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚 🌸 'YAR MAHAUKACIYYA 🌸📚*


Mallaki:
Husaina S. Abdullah (Oummu Muwaddah)
📚 © 2025 – Duk haƙƙoƙin mallaka na musamman ga marubuci.


Group din comment banda maza ko ka shiga sai ka fita👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/BXejgVglv85CWkdVCo2qUg?mode=wwt




⚠️ GARGADI ⚠️
Wannan labari ƙirƙire ne gaba ɗaya, daga tunanin marubuciya.
Bashi da alaƙa da wani mutum, gida, ko wuri na gaske.Idan wani suna,ko muhali ko abin da ya faru a cikin labarin ya yi kama da na ainihi, to hakan dai haɗuwa ce ta bazata, ba da gangan ba.Manufar marubucin ita ce nishaɗantarwa, ilmantarwa, da faɗakarwa, ba batanci ko ɓata suna ba.Duk wani hali, tunani ko ra’ayi da aka bayyana, na cikin tunanin marubuciyya ne kawai.Kar a ɗauki labarin nan da tsanani fiye da yadda marubuci ya nufa.


*SHIMFIƊA*
*Akwai wasu haihuwoyi da ke zuwa duniya da albarka, akwai kuma wasu da suke fitowa da wulakanci a gaba. Ita ce Sumayyah, ‘yar shekara ashirin, wacce duniya ta fara yiwa hukunci tun kafin ta iya magana.*
*An haifeta a A cikin wani ƙauye,cikin gidan Malam Sule Giɗaɗo, malamin soro mai mata uku. Hauwa’u, Rabi, da Zulaihat. Duk gidan nan cike yake da tsantsar kishi, nuna bambanci da ƙyamar juna. Amma mafi talaucin su ba na kudi ba ne-talaucin adalci ne.Rabi, mahaifiyar Sumayyah, ita ce suka kira “Mahaukaciya.” Tana yin magana da kanta, tana dariya a lokacin da babu wani abu mai ban dariya. Idan ta shiga kasuwa, yara sukan jefa mata duwatsu,wanda hakan jarabtace daga Allah subhanahu wata'ala.da zarar ta fita yara zasu fara kiranta da“Ga mahaukaciyar matar Malam! Ga uwar ‘yar wulaƙantacciya!”Wannan magana ce da ta yi katutu a zuciyar ‘yarta. Duk inda Sumayyah ta wuce, idanu ke binsa da raini. A makaranta, ko a wajen mata, babu wanda bai taɓa kiranta da “’Yar mahaukaciya” ba.Uban su, Malam Sule, bai taɓa tsayawa ya kare ta ba. A wurinsa, kalmar matansa biyu ne,gaskiya. Duk abin da Hauwa’u ko Zulaihat suka faɗa, shi zai amince da shi, koda kuwa zai karya ɗiyarsa .Sumayyah tana da ‘yan uwa guda biyar maza da mata, amma babu ɗaya da yake ganin ta kamar ‘yar uwa.Sadiya, ‘yar Hauwa’u-mai zafin rai, mai kishi.Lubna, ‘yar Zulaihat-mai gulma, mai mugunta.Khalid, ɗan Hauwa’u ɗan gata, mai tsanar Rabi.Yusuf, ɗan Zulaihat mai son nuna isa Baban ɗa aguri Baba Sule.Sai kuma Amina, ƙaramar yarinya mai bin umarnin uwar.Gidan Malam Sule kamar fili ne da aka shuka tsanar Sumayyah. Koda ta yi ƙoƙari ta gyara, Daga cikin ƙauyen su, babu wanda ya taɓa yi mata kallon mutum cikakke.Rayuwa ta zama masaƙiƙiyar hanya- ƙauye da ke yi mata dariya, gida da ke yi mata tsana, uba da ya zama shiru, da mahaifiya da ke cikin duniyar da ba kowa ke iya ganinta ba.Sai dai abin da duniya bata sani ba shi ne- cikin wannan yarinyar akwai asirin da zai girgiza gari, sirrin da zai bayyana gaskiyar mahaifiyarta da wautar waɗanda suka yi dariya.Wannan shi ne farkon labarin da ke tattare da hawaye, ƙiyayya, da ƙaddara.Labarin Sumayyah, ‘YAR MAHAUKACIYYA- wacce rayuwa ta ɗora wa nauyin da bai kamata ta ɗauka ba, amma ta ƙi rushewa.*



________________free book __Page -1



A cikin Jihar Kano, tsakanin ƙananan garuruwa da ke tsakanin Bunkure da Garko, akwai wani ƙaramin ƙauye da ake kira Gidan Giɗaɗo. Ƙauye ne da yake cikin zurfin karkara, inda hayakin girki ke tashi da safe, ana jin karar sare itace da kiran Sallah daga ƙaramin masallacin.Mutanen ƙauyen su ne irin waɗanda suka dogara da noma da kiwo,rayuwarsu cike da haɗin kai da ɗan ɗabi’ar al’ada. Kowa ya san kowa, labari ba ya ɓuya. Duk abin da ya faru a gidan mutum, kafin rana ta faɗi sai ya ratsa kowane gida.Gidan Malam Sule
Giɗaɗo, malamin soro wanda ke koyar da yara karatun Alƙur’ani,da yawan Almajirai,shi ne ginshiƙin addini a ƙauyen. Ya yi suna har ma aciki birane.Gidansa ne aka haifi Sumayyah, yarinya mai kyakkyawar fuska, amma an ce tun haihuwar ta, ta fito da “baƙar sa’a” saboda wasu al’amura da suka faru a lokacin haihuwarta.Cikin Rayuwar.Wulakanci da Kaddara.

Kukan jaririya ya tsinke shiru a gidan Malam Sule Giɗaɗo-gidan da kishi da adawa suka mamaye fiye da komai. A wannan daren, sama ta yi duhu, iska tana kadawa kamar tana shaidar cewa sabuwar rayuwa da zata sauko duniya zata gamu da kalubale.Rabi tana kwance kan tabarma wace duk ta ya
galgale, jiki ta sai rawa yake saboda ciwon naƙuda da gajiya. Amma duk cikin wannan halin da take ciki babu wanda ya tsaya kusa da ita sai tsohuwar dattijuwar da ta shigo ta iske ta tana na ƙuda haka ta yaye mayafi ta ta shiga,taimaka mata kun dai san yadda haihuwar ƙauye take babu bati haihuwa a sibitia.
Daga ɗaya gefen ɗakin, Zulai ne wanda malale yake da daɓe suminti gaban ƙofar yasha fante farar wuta.muryar Zulai ce ta karaɗe ɗaki tana cewa da Hauwa’u:“Nidai Fata na kada baƙar kadarar nan ta haifa mana iri jinsin su! Dan Walhi jikina na bani wannan haihuwar sai tabi jini!.”Shewa suka yi sanan suka juya suka fita.Rabi ce ta juya idanu cikin hawaye ciki yanayi na sanbatu naƙuda ta ce.“Ya Allah, kai ne ka fi kowa sani. ka kare min 'yata!”Da haka ta rungumi jaririyar, wacce daga wannan rana duniya ta fara yiwa hukunci tun kafin ta iya magana.Sunan da Malama Sule ya sanya mata shine SUMAYYAH-bayan ta fara wayo Zulai da Hauwa'u suka fara laƙaba mata shine 'Yar mahaukaciyya hakan ya bawa samar mutane ƙauye da kiranta da wanan sunan.“Yar Mahaukaciya.”Tun tana jaririya har ta fara girma, kalmar nan ta zame mata kamar inuwar da bata rabuwa da ita.A kowanne lokaci ina ta shiga mutane ko ta wuce kasuwa, yara sukan tsayar da ita suna cewa:“Ga ‘yar mahaukaciya! Ga ‘yar Rabi wadda take tsince-tsince abola!”

Tun Sumayyah na yin kuka har ta koyi yin shiru. Sai-dai shiru nata ya fi kuka nauyi.Idan ta shiga makaranta, malamai sukan nuna ban-banci tsakani ta dasu Sadiya da lubna; idan ta dawo gida, Baba Hauwa’u da Baba Zulai sukan nuna ƙyama.
Uban ta, Malam Sule wanda ake kira “Malam Giɗaɗo”saboda darajarsa a gari- bai taɓa tsaiwa ya kareta ba.A wurinsa, kalmar matansa biyu ce gaskiya.
Idan suka ce Rabi ta yi kuskure, to, ko da,da gaskiya ce, sai ya hukunta ta.Sai dai duniya bata san sirrin da ke cikin wannan yarinya ba.Sirrin da zai girgiza gida Malam Giɗaɗo,da kuma ƙauye, har ma da mutanen da suka sha dariya a kanta.

Rayuwar Sumayyah ce za ta zama littafi mai ɗauke da hawaye, ƙiyayya, da ƙaddara
amma daga ƙarshe, gaskiya ce za ta yi nasara.Tunanin da yaro ke yi na farin ciki da nishaɗi idan aka ambaci makaranta, bai taɓa zama cikin zuciyar Sumayyah ba. A wurinta, makaranta ba wurin koyon karatu ba ne- wurin ƙuntatawa ne, wuri ne da ake tuna mata da laifin da bata aikata ba.Da safe, tana tashi kafin kowa. Sai ta wanke kayan Innar ta, ta share ɗaki, sannan ta kama hanyar makaranta da littafinta guda ɗaya wanda ya ci wahalar duniya. Duk lokacin da zo wucewa ta ƙofar ɗaki Baba Hauwa’u domin fita ta kofar baya Saboda zaman Almajirai, Sadiya sai tayi mata tsaki tana sukar ta da kalamai marasa daɗi ta ce.“Ke ‘yar mahaukaciya, kar ki yi amfani da kofar nan, ki bi ta babbar ƙofa. Ba nason ganin fuskarki tana gilmawa kamar hadari fuska sai muni tsiya baƙi kamar na zunubi.” haka Sumayyah zata yi shiru ta ratse ta wuce.ta san idan ta yi magana, Baba Hauwa za ta ce tana raina manya.ko ta tsine mata tass ƙarshe ta zuga Malam ya buge ta.Koda ta yi kuka,haka Baba Zulai za ta hauta da laba'i tace ta isheta da kuka.Saboda haka tayi mata shuru ko ta ƙara mata.

Haka rayiwar ta ta ci gaba.A makaranta kuwa, labarin ba ya canjawa.
Lokacin da malamai suka kira sunan ta cikin lissafin ɗalibai, wasu yara sukan fara dariya wasu yara da suke kusa da ita suka tun tsire da dariya ɗaya daga ciki tace:“Gaskiya Malam, wannan ai ba ta da hankali. ‘Yar mahaukaciya ce fa.” lokaci da kalmar ta fito daga baki dayar shaida Sumayyah ta rintse ido tare da zubar da hawaye masu zafi.malamai suna fita sauran ɗaliban suka hau waƙa suna dukan benci,suna cewa:“Summah mahaukaciya! Ki yi rawa mana!”koda ta kai kara karshe laifi kanta ya koma haka aka hukunta ta. Bayan da ta koma gida kamar kullum haka ta kaiwa mahaifinta ƙara,Sai dai Malam Sule bai taɓa zuwa makarantar ya tambayi halin ‘yarsa ba.ko ya kai ƙara akan korafi da take kai masa ba,Shi kawai yana ganin duk abin da ake faɗa a kanta gaskiya ne. Yau ta kama Jum'a karfe goma aka tashe shi daga makaranta tun a hanya Sadiya da Lubna suke mata waƙa har suka isa baban Zaure gidan inda suka samu Malam Sule yana gani ta ya daure fuska ya fara masifar"Tom daga an ganki an ga 'yar sarki marasa haƙuri yau kuma da me kika zo?” Ciki kuka mai cin rai tace"Baba Sadiya Da Lubna ce suke tsona ta wai ni...“Tsawa ya daka mata tare da nuna ta da hannu ciki muryar sa ta Malaman Soro ya ce“ Karya sukayi!Nace karya sukayi Sumayyah ba daga Rabi kika fito ba? Kenan baki da maraba da mahau...” bata jira ya karasa ba ta kwasa cikin gida a guje Sadiya da Lubna kuwa toshe baki sukayi suna dariya.

Abayan Sallah Isha'i Sumayya ta rufe musu kofa wanda Doka ce da Malam ya kafa wa iya Sumayyah da mahaifiyar ta, bayan bacci ya fara ɗaukar tana kwance gefen mahaifiyarta, kallo Innar ta tayi tana kallon Yadda take yin magana da kanta cikin bacci, tare da kaiwa jikin ta yakushi da cizo.karshe ta fashe da kuka, tana cewa:
“Sule, ka yi min adalci… Ka tuna da alkawarin aure!”da haka kuma tayi shuru kamar ba ita ba,Wannan kalmomi ne yasa Sumayyah tashi ta rafka ta gumi kalmomin suka fara yi mata yawo cikin kunnen ta har ta rufe idanuta a fili ta furta.“Wane ne mahaifina a gaske? Me ya sa yake shiru? Me ya faru da mahaifiyata?”Lumshe ido ta tayi cikin hawaye.tace
“Duniya ta ƙi fahimtar ta..”





*Zuciyarta ta cika da tambayoyi da za su zama asalin labarinta.
Saboda a cikin shiru, akwai sirri.A cikin hawaye, akwai gaskiya.
Kuma a cikin wannan yarinya da ake kira “’Yar Mahaukaciya”, akwai ƙarfin da zai girgiza duniya.




*Comment lik da Shering shine zai karfafa min gwiwa dan Allah a Amin kara free Book ne amma nace ba kullum zan rika Update ba*
[10/28/2025, 1:15 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a


*📚 🌸 ‘YAR MAHAUKACIYYA🌸📚*


Mallaki:
Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah)
📚©2025 -haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


________________free book __page-2



Sai da tayi 'yan Addu'o'in da tasani,kafin ta kwanta.Rana ta tashi kamar yadda take tasowa kullum, amma ga Sumayyah, kowace rana sabuwar jarabawa ce. Haske bai taɓa zama alamar farin ciki a gare ta ba, sai dai tunasar da ita cewa ta sake tsallake wata rana cikin
wulakanci da rashin tausayi.

Da safe ta tashi da kyar, jiki babu ƙarfi, idanu wanta sun kumbura saboda kuka. Ta ɗauki bokitin ruwa ta nufi rijiya da take nesa da gidan su,tafiya take da kyar da dama jiya bawani abinci kirki ta ci ba. Hanyar rijiya ba mai nisa ba ce, amma a gare ta kamar tafiya cikin duhun da babu haske take. Ji take tamakar anayi mata yasa acikin ta, tun da ta doshi guri yaran da suke wasa,wasu na wucewa, suka fara tsaiwa suna kallonta suna dariya.“Yar mahaukaciya, ki kawo mana ruwa mu sha, kar ki yi dariya ki haukace mana, Aguri nan!”

Ta tsaya, ta ɗan kalli ƙasa, hawaye suka gangaro mata. Ta yi shiru, ta juya ta ci gaba da tafiya.lokaci da ta isa ta samu wasu matan ƙauye suna hira. Tana isowa, hirar ta tsaya. Kowa ya juyo yana kallonta da murmushin raini hankali.

“O Allah ya rabamu da hauka koda bana tiburan bane?” wata ta faɗa cikin dariya.Wata mai ɗauri ƙirji ta bigawa Sumayyah harara tare da cilla guga cikin rijiya tace., “Eh ai ita ce ‘yar da bata da uba. Ai Malam Sule ma yana gudunta bare mu kuma mutane gari,yo hauka yake zai sake bari tsatson sa ya biyu ta guri
mahaukaciya.”Da sauri
Sumayyah ta jingina da rijiyar, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma ta yi haƙuri. Ta hanana zuciyar ta shiga damuwa, cikin ranta taji wata zuciyar na ce mata “Ki yi haƙuri Sumayyah, rayuwa ba ta tsaya kan baƙin rana ba sai dai tana koyar da juriya.”

Bata iya ƙarasawa guri su ba har sai da suka gama nasu jan ruwan kafi ta janyo nata.Da ta koma gida, ta iske Baba Hauwa zaune tana ɗinki. Tana zuwa zata wuce ta ce.

“Ke kuma, wane irin jinkiri ne haka? Ko kin tsaya kina tattaunawa da mahaukata irin mahaifiyarki? Yo in ba hauka ba ina dalilin zama haka!”Sumayyah ta sunkuyar da kai, ta mika mata bokitin ruwa.Baba Zulai da take aikatau ɗin awara ta ce
“Allah ya ƙyauta, amma irin su wanan yaran ba su da albarka. Haka uwar, haka ‘ya.”babu wand ta tankawa bare su samu abin kai wa Malam ƙara.Da ta gaji ma ɗaki ta shiga abinta guri mahaifiyar ta.

Da yamma bayan ta gama ɗora wa Baba Zulai sanwa tuwo dare, ɗakin mahaifiyarta.Inna ta shiga tana zaune tana kallon sama, tana murmushi kamar tana magana da wanda ba kowa ke gani sa ba.“Inna ta..!,”Sumayyah ta ce cikin rauni.Inn ta juyo, ta ƙyalkyale da dariya, sannan ta kama hannunta.“Sumayyah, su sun manta, amma Allah bai manta ba kizo nayi maki wanka na goyaki na kaiki baki rami.”
Hawaye ta goge da bayan hannu takafi ta ce.

“Inna ta! me suke nufi idan suna cewa ba ni da uba? Ina ce Malam Giɗaɗo shine mahaifina?”Inna Sai da ta ƙarewa Sumayyah kallo kafin ta Ƙyal ƙyale da dariya tace“Sule Saurayi nane ya sai min kajal da janbaki kina so Na ara miki?"Inna ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta lumshe idanu.ta ɗora da cewa“Ki girma, ki sani da kanki. Gaskiya ba ta ɓoye har abada. Amma ki sani, wanda yake da gaskiya, sai ya sha wuya kafin ta bayyana.” kuka Sumayyah ta fashe da shi tare da cewa."Inna ta, na kasa gane wa,yau zaki magana da kyau ajima akasi ta Allah ka kawo sauƙi cikin rayiwar mahaifiyya ta ko nasan suwaye dangi ta.”

Tun daga wannan rana, tambayar “Wacece ita?” ta zama abin da ke damunta fiye da komai.
Ta daina jin zafi daga kalmar “’Yar mahaukaciya.”
Yanzu tana jin cewa wata rana, zata nuna musu cewa hauka bata gajiya bace, hauka na iya zama hikima da duniya ta kasa ganewa.

Da dare, lokacin da kowa ya kwanta,kasa bacci tayi a hankula ta buɗe ƙofar su ta fito ta zauna ƙarƙashin tsohuwar wata bishiyar kuka dake bayan gida ɗakin su.ta zauna ta ɗaga kanta samma Tana kallon sama wani siriri hawaye ne suka shiga gangaro mata cikin kasan zuciyar ta tace.

“Ya Allah, kai ka halicce ni, kai ka san dalilin da yasa ka saka ni cikin wannan gida. Idan akwai gaskiya, ka bayyana ta. Idan ni ba yar wulaƙanci bace, ka nuna min haske.”Sai da taji anna kiran Sallah ta maza ta faɗa ɗaki dan tasan yanzu Malam zai bi ɗaki-ɗaki yana tashi saboda sallah asuba.

Bayan kwana biyu yau ta kama ranar Litinin, duk yadda taso ta tafi makaranta akan lokaci bata tafi ba Sadiya da Lubna kuwa tun tuni su jima acan sai da ta gama gyara gidan da kwashe karan da Almajirai suke karatu dare kafi ta isa makaranta.

Suna zaune cikim aji Sabuwar malama ta shigo, sabuwar malamar da aka kawo daga birni,Malama Ruqayya, tun da ta shigo ta lura da yanayin Sumayyah. Tashi farko taji yariyar ta shiga ranta, kiran ta tayi bayan kowa ya fita break ta ce.

“Sumayyah, me yasa nake ganin kina da zafin zuciya amma kina ɓoyewa?”Sumayyah ta yi shiru, hawaye suka cika idonta.Malama Ruqayya ta sake magana cikin tausayawa.“Na san kaddara tana iya zama nauyi, amma Allah baya rubuta ciwo sai da magani. Ki ƙarfafa zuciyarki.”kai ta girgiza tare da aminta da maganar ta.sannan ta sallameta.Tunda tabar guru.Kalmar nan ta zama abin da Sumayyah ke maimaitawa a ranta kullum.

“Allah baya rubuta ciwo sai da magani.”
Sai dai tana tambayar kanta-a ina maganin nata yake?”haka suka koma ciki aji, duk da a kaso tamani bisa ɗari babu abin da Sumayyah take fuskanta a ciki karatun da ake musu.

Rana ta sake tashi a gidan da kalmar “adalci” ta dade da mutuwa.
Gidan da dariya ta wasu, ke nufin hawaye ga wasu.

A yau, an shirya babban liyafa a gidan Malam Sule.wanda bisa addu'a da Malam Sule ya yiwa wani Alhaji Musa mai da'awa kan wata kwangila da yake so ya samu buri sa ya cika shine ya haɗa musu Babbar liyafa.kowa ya shirya Sadiya da Lubna kamar sun shiga kanti ɗan kurma saboda tsabar ƙamshi, kwaliya kam har da su barbaɗa kumatu.
Ana jiran Alhaji Musa mai da'awa ya ƙaraso har da iyalin sa.

Baba Hauwa da Baba Zulai jikin su sai rawa yake burin sun bai wuce ko Sadiya da Lubna zasu dace ba guri yaran Alhaji musa mai da'awa.Ko tsinke ne ya faɗi sai su sa Sumayyah ta ɗauke, ko wanka sun hana tayi wai bazata yi wanka ba kar wani yace yana so. Itama bata damu ba dan bata jin za'a barta taje guri walima bare har ta ga wani yace yana sonta hasalima ita bata sha'awar aure wani me kuɗi.

Inna kuwa, Malam ne ya kulle ta da kanshi aɗaki wai kar ta zo ta kashe musu guri da wari, Hankali ta kwance jikinta yayi busu-busu da ƙasa tana waƙar da babu wanda ke fahimta.

Sumayyah tana ta hidima, tana ɗaukar abinci tana kaiwa Babbar falo Malam wanda sai ka ɗauka ba acikin gidan yake ba saboda tsabar haɗuwar da har da sol.Ba kowa yake shiga ɗaki ba sai Manyan mutane masu zuwa temako guri sa. Bayan ta kammala lokaci da take ƙoƙarin zama motar su ta ƙaraso babu wanda ya bi ta kanta guri tarbar Alhaji Musa mai da'awa da matar sa da samari yaran da guda uku, Baba Zulai da Baba Hauwa har da zubewa har ƙasa suna yiwa yaran ciki gaisuwa su kuma suna fusgewa waisu 'ya'yan manya.


Ko da ta gaji da jira, babu wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login