Showing 39001 words to 42000 words out of 56438 words

Chapter 14 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

16

mata tuwo basu sani ba sai da suka lafa sanan Baba Hauwa ta matso ta mikawa Inna tuwo, duk yadda ta juya amma Inna taki ci sai kwauda kai da ta riƙa yi Kamar tasan me ya faru. A na cikin haka Suka ji maganar Baba Zulai tana faɗa.

"Dan Allah ku kwashe kwanikan tuwo nan ga suruki nanan zai shigo,ke Suwaiba ɗauke yaro nan naki daga kan 4 shi kullum cikin kashi yake,yara sai shege cin tsiya ba dole su ta Kashi ba”. Hayaniyar maza daga ji su Ammar ne haka kuwa akayi daga wasu maza biyu sai AMMAR da Abdullah suna zuwa kofar ɗaki Inna Ammar ya zame babu zato Baba Hauwa da Sumayyah suka ganshi a tsaye a kansu suna haɗa ido da Sumayyah ya yi sauri ɗauke kansa gaban Inna yaje kamar bazai magana ba suka ji murya sa.

"Inna kici abinci, ko kinaso na baki da kaina?....
[1/8, 10:56 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channehttps://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a


*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-23

Kauda kai Inna tayi ya sake maida kansa inda take zata sake kauda kai ya sauri kamo hannuta ciki saunyi murya yace.

"Ki yafe min Inna nasan Uwa bazata taɓa fushi da Dan taba ko zakiyi fushi dani?”Kallo sa tayi hawaye na zubo mata babu magana hankici ya ciro daga aljihu sa ya fara goge mata hawaye, sai da ya goge mata ya saka hannu sa aciki robar tuwo da kansa ya riƙa bata. Sumayyah kam ta kafe shi da kallo amma ko kallo inda take ba yayi sai da yaga ta fara kauda kai sanan ya cire hannu sa ruwa ya miƙa mata na hannusa ta karɓa tasha, ya miƙe ba tare da yace musu komi ba ya fita. Kuka zata guza Baba hauwa ta yi sauri da katar da ita.

"Haba Sumayyah sai kace ba yariyar da nasani ba Nasan akwai ciwo amma ki daure karki bawa maƙiyi damar ya miki dariya yanzu akwai takalmin da Lubna ta suyo a ciki zan ɗako miki ɗaya kisa, kinuna baki damu da aure nasu ba hakan zaisa suji kunya kiji”

Kai kawai ta iya ɗaga mata ta fita. Bata juma ba ta dawo har da powder da jan baki da kwali kwaliya tayi sama-sama tayi kyau abinka da Black Beauty har madarar turarer ta saka mata sanan ta kama hannu ta suka fita suna fita lokaci an gama hoto da ango da amarya zunzo zasu fita suma Su Sumayyah suka fito, wan nan ne haɗa ido su na biyu a yau a wanan karo shine ya kasa ɗauke ido sa daga kanta ita kuwa kamar bata san da tsaiwar sa aguri ba Sai da Abdullah ya bugi kafaɗar sa sanan ya dawo hayyaci sa sai da suka fita sanan Sumayyah ta samu guri nesa da ƙawaye Sadiya ta zauna tun da suka lura da ita suka fara dasa baƙaƙe maganganun in tayi kamar ta bar guri Baba Hauwa tayi mata alamu da ido karta tashi haka ta daure har lokaci sallah Azahar tayi alwala ta shige daki su.

'Yan ɗauri aure na komawa kan fara hada-hada Ummi babu abin da ta sani haka kuma Abin ya gargadi kowa akan kada asanar da kowa halin da ake ciki iya wanda suke guri su haƙa su binne saboda gudu surutun mutane. Da yake magana ce ta wanda in ya faɗa ake ji kamar bayi wani abu aguri ɗauri aure ba. Kasa zaune abi yayi ya kasa tsaye ƙarshe wayar Ummi ya kira ya sanar da ita yana parlo. Da ƙar ta iya ya kice baƙi ta haura sama tun da ta ganshi gaban ta ya fara dukan uku² tasan ba lafiya ba.

"Allah ya temake ka ina ango ne ko ka fara kewa ne tun yanzu”

Hannu ta ya kama.“Ummu Ammar akwai matsala fa”

Rass kirji ta ya shiga bugu ciki rawar murya tace."Abi wace iri matsala badai fasa bashi aure kayi ba ina shi Ammar ɗin ya tsaya??”Gaba ɗaya ta rikice hannu ta ya kama ya zaunar da ita gefe bed."Colm down An ɗaura aure dai² lokaci da aka sai Sai dai Ammar ya furje shi yar uwar ita yariyar yake so wai ba ita ba duk yadda naso na ganar dashi ilar yin haka amma ya kafe yana ta wani iri sambatu....


“ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakili.Abu Ammar ina Sumayyah ina Shi Ammar ɗin?”

“Ki kwatar da hankali ki mun baro su shi da su Abdullah zasu shiga ya gaida surukansa amma...

Mikewa Ummu tayi da sauri Abi zanje naga Sumayyah dole tana bukatar kulawa dan Allah kabarni naje”kai ya kada mata."Bana so mutane Su san hali da ake ciki fitar ki zai iya jan hankali al'umma ki bari zuwa gobe”Wallahi Abin bazan iya jira ba dan Allah ka temaka min yariyar nan bata da kowa sai Ammar amma yanzu ya yi mata haka shikenan ya raba alakar shi da ita me yake damu sa ne?”

Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa"Shikenan ki tashi zan sa Aminu ya yi driving ɗinki”mikewa tayi handbag dinta ta ɗauka sai mayafi ta fita ta kofar kitchen tana isa Parking space motar su Ammar na tsaiwa, ciki taƙama ya fito yana baza Babar riga tun da ya hango Ummu kirji sa ke bugu tara-tara tun karar ta yayi da zumar suyi magana kafi ya ƙaraso ta shige cikin mota jikin sane yayi sanyi gaban sa ya tsanan ta faduwa yana kallo ta fice haka yaja kafa suka shiga parlo nan aka fara zolayar sa yaƙe kawai yake bawai dan hakali sa akwance ba.

*Gidan Malam*
Tun da Sumayyah ta shiga bata sha'awar sake fitowa tana ji ana ihu masu DJ sunzo za afara kida hakan yasa ta miƙe da zumar ta kare musu ƙofa dan wasu har keƙe su suke wai suna san gani Inna da Sumayyah kokari tura kofar take Kaf ido ya ya sarke da fusakr Ummu cike da fargaba da Mammaki ta fara hada magana.

"Ummu...kece..yanzu Ina Yan....

"Ya Isa Sumayyah mushiga daga ciki”Karfin Hali faɗaɗa fara'a tayi tare da bata hanya Ummi ta wuce, tana shiga guri ta nema ta zauna tana bin Sumayyah da kallo wace ko motsin kirki ta kasa.

"Sumayyah zo ki zauna”Jiki babu kwari ta zauna kasan kewar tsakar ɗaki."Ummu ina Wuni ya taro”Hawaye Ummu ta fara.

“Sumayyah ki yafewa Ammar ki kuma yafemi Wallahi nasanr Ammar baya ciki hayyaci sa”

"Ummu Ya Ammar bai taɓa min kimiyya ba Wallahi hasali mi Ni taimako na yayi daga muguwar rayiwar da naso na faɗa ko iya haka Ummu ya temake Aure kuma nufi ne na Allah bawa bai isa ya canja ƙaddara da tazo masa ba dama Wanan aure Rubuttace Al'amarin daga Allah waye ya isa ya canja zane ƙaddara mu”Sosai Ummu ta ji dadi furici Sumayyah mikewa tayi tsaye ta kafe Inna da kallo wace Bacci ya mata dadi saboda maganin bacci da Sumayyah ta ba sanan ta saki ajiyar zuciya.

“Sumayyah Akaro na biyu nazo da ƙoƙon bara ta A gare ku Dan Allah ina fata zaki amma kuma baza ki bani kunya ba.”batare da Sumayyah ta ɗago ba tace.

“Ummu bana fata ranar da zaki roƙi abu aguri na nakasa yi miki wallahi komaye na aminci matukar bai saɓa Addini da shari'ar Muslunci ba”
Kusa da Sumayyah ta dawo.

"Sumayyah Inaso ki Wuri Abi Mijina Wallahi nasan baza kiyi nadama duk da Nasan Mijina ya kwana biyu kuma yara basa don Aure me shekaru da yawa”

Wata iri firgita Sumayyah tayi tare da miƙewa jikin ta na tsuma."Ummu wallahi kaina ya kulle ban gane abin da kike don ce...."Murmushi Ummu tayi ta dafa kafaɗar Sumayyah."Sumayyah nasan kin san me nake nufi amma bara na sake mai-maita miki Inaso in har kin Amince ki aure mijina Sheikh Kareem Al-Labbani Mahaifi Ammar Kuma mijina Wannan shine kadai roƙo da nake mi....

Sulalayewa Sumayyah tayi ƙasa Sumayyah....
[1/9, 3:40 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73


*Ayi hakuri Babu Editing dan Allah*


*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-24

Ciki tashin hankali Ummu ta ƙasa inda take sunan ta ta fara kira."Sumayyah..! Sumayyah..!dan Allah ki tashi...“ Inaalillahi wa'inaalaihi rajun mai zan gani baiwar Allah wace ke me kikayiwa Sumayyah??”Baba Hauwa da ta shigo ta bawa Sumayyah kayam Lubna ta sauya saboda yini biki,kallo ta Ummu tayi murya a sanyaye."Wallhi baiwar Allah babu abin da na mata hasali ma nice mahaifiyar Ammar maso naga halin da take ciki ne.”Sake daure Fusakar Baba Hauwa tayi tare da zama kusa da Sumayyah ta ɗora ta kan ciyar ta."Allah sarki ai da yake Sumayyah tamu mai tawali'u ce Babu komi Allah yasa haka ya zame mata Alkairi kuma mungode da kulawar ki”Muushi Ummu tayi dan yasan Baba Hauwa a matuƙar hasale take, miƙewa tayi ta bude randar gwauro bayan kaure ta ɗauko ruwa mai sanyi ta mikawa Baba Hauwa."Ki sa mata suma tayi da Alamu maganar da na gaya mata itace ta firgita ta...

"Haba Baiwar Allah ya tana ciki wani hali zaki sake jefata kubar ta da iya wanda kuka sata Cuta ce dai an riga acuci marainiya Allah sai dai Allah ya saka mata da gan-gawa.”Ajiyar zuciyar Ummi tayi."Ki kwantar da hankali ki Bazan taɓa cutar da Sumayya ba inaji ta Araina tamkar Ammar kuma maganar da nazo da ita a nawa tunani zai rage mata radaɗi abu da yake damu ta.”Baba Hauwa bata sake magana ba sai ruwa da ta fara yayafawa Sumayyah bayan tsayi mintes goma ta farfado ido biyu tayi da Baba Hauwa ciki sanyi halitta ta furta."Dama nasan mafarki ne Bazai taɓa zama gaske ba taya ma zan Auri Abi wanan ba gaskiya....

“Gaskiya ne Sumayyah babu mafarki aciki kuma zan tsaya kai da fata dan naga wanan al'amarin ya yu fata na ki amice kuma zaki ga alfano da abin da na gaya miki”Kalli Baba Hauwa take bisu,su dukka biyu ta kasa gane me maganar su take nufi karfi hali tayi ta sake kallo Ummu."Baiwar Allah kusa ni cikin duhu dan Allah ku warware Ni daga ciki wanan lamari”

Murmushi Ummu tayi.

“Hajiya kar ki fa wani damu Sumayyah ce kadai take so ta maida lamari babba, nazo nemawa mijina aure ta wato mahaifin Ammar tunda shi ammar ɗin yaƙi ba sai ayi tuwo na maina ba mu baza mu taɓa gujewa Sumayyah ba sukuma wanda suka raba wannan alaƙa a hankali Gaskiya zata yi halinta insha Allah”

Sosai Baba Hauwa abin ya razana ta amma domi ta nuna su Baba Zulai Allah mai iko ne kuma suma da arziƙin ta take tafe, zata yi fatan Wanan al'amari ya tabba dan hakan sai ya fi girgiza su mai arziki kacokan Sumayyah zata aura.fara'ata ta faɗaɗa.“Kai wai da wanan abin ne Amma Sumayyah har da suma wallahi nafi kowa farin ciki idan har haka ta kasance sai dai wani hanzari ba gudu ba bana so kowa yasan maganar nan har sai ranar da aka tsara ta daura aure gudu sheɗanu mutane”

Sabunta Sumayyah Tayi ta bar jiki Baba Hauwa.hawaye na bin fusakar ta."Baba Wallahi Bazan iya zama da Abi ba, shine fa Mahaifi Ammaru, kuma mijin Ummu wanan ai cin Ammana ne kuma Ammar bazai taɓa yafe min ba”

"Haba Sumayyah meye abin cin Ammana aciki Sunnha maiki Sallallahu alaihi Wasallama cefa kuma In ma cin amana ne waye ya fara bashi ba ,Forget Ammar and what the world will say, be his wife and I agree with you.dan Allah karki kawaye baya”. Saidai take kuka ita tama rasa ya zatayi haɗuwa su kayi Ummu da Baba Hauwa suna ta kawo mata kauli da ba'adi har kunyar Ummu ta shige kai kwai ta iya ɗaga wa Hammadallah sukayi 100k Ummu ta ciro cikin Handbags ɗinta ta ɗora kan ciyar Baba Hauwa.

“Dan Allah ayi hakuri da wanan kafu Abi yazo da kansa....“Kai Sumayya ta fara girgiza wa Ummu."Dan Allah Ummu kar yazo wallahi bazan iya haɗa ido dashi ba wanne roƙo mafi girma da zan iya miki dan Allah ”

"Haba Sumayyah in baizo ba taya zaku saba zama ne fa na din-din....

“Hauwa wai me kike a ɗaki yariyar nan nafa kasa gane miki tun da al'amari....”Sauran maganar ne ya tsaya mata gani Ummu duk da ba sani ta tayi ba taga Ammar ajiki ta saki fuskar ta tayi.

“Wa nake gani kamar Hajiya gajiyar Al'uma bata hana ki fitowa ba Hala makawa kikayi ai can ne ɗaki nawa??”Cewar Baba Zulai da take ta yaƙe baki kamar ganar audiga”

Dakar Ummu ta ita tataro ragowar Murmushi fusakata tayiwa Baba Zulai.“Wallahi kam na fara zuwa naga ɗiyata kafin sai na ga ita surukar tawa”tana fadi haka ta miƙe Baba Hauwa ta rufa mata baya jiki Baba Zulai na rawa ta busu suna fita tsakar gida ta dubi Baba Zulai."Kinga kuma gashi an fara kira na shida inaga in tazo kawai na ganta a kula min da ita kafi tazo”Godoya Baba Zulai tayi tana ƙokarin fita Sadiya na turo kai da ƙaruwar 'yan fi a kanta sai kayan da ta cire, ruwan Ash'ari yake makawa yaran da suke bin bayanta.

" Yara sai kace Tumakai 'ya'Yan jara Alkur'ani duk wanda yasake bi mu zanci gato...”Asha Auzubiallahi wanne wace iri Yariyar ce baiwar Allah Ai yara Rahama ce dasu ki daina iri haka ke uwa ce mai bada tarbiya in kina iri wanan zagi taya zaki bada tarbiyya?”

Baki Sadiya ta taɓe.“Kujimu da mata ke kuma daga ina dan Ban sanki a dangi Malam ko na Babarmu ba”Murmushi Ummu tayi zata yi magana suka ji maganar Baba Zulai.

"Ubanki Sadiya nace Ubanki, Surukar kice Babar Ammar Shasha mahaukaciyar banza”Wuri-wuri Sadiya tayi tana kifta ido.da sauri ta zube zata kama ƙafar Ummu, Ummu tayi sauri janyew."Karki samu Allah ya miki Albaka”bata jira me zasu ce ba ta fice tabar dadɗan turare ta.Ajiyar zuciya ta sauke.“Nashiga Uku wanan 'Yan bura...make mata Baki Baba Zulai tayi."Wato zagi dai baza ki fasa ba har abada”

Tun da Ummu tabar gidan take tausawa Ammar iri matar da ya kwaso wa kansa dole ne ta tashi tsaye in ba haka ba Ammar zai faɗa mugun halin da bai taɓa tunani ba,haka ta koma gida jiki babu ƙwari.


*After 6:00pm*

Bayan an gama kidan DJ har su tashi motocin suka fara jerin gwano na daukar Amarya Habaici da ihu babu kalar wanda Sumayyah bata shaba karshe rufe musu ƙofar su tayi ta kwanta. Lifaya Sadiya tasa babu ƙarya tayi kyau dan Ance amarya ko ta buzuzu ce kyau take sabuwar Motar Ammar aka saka.Sai karfe takwas suka isa gidan Ummu duk wata tarɓa da akewa Amarya Ummu ta sa anyi mata kuma da kayan daukar Amarya surutu kam ansha da yiwa Sadiya murna ta samu daula.

Sai bayan tara Ammar ya shigo shida tawagar abokan sa shi kaɗai ya haura sama a zaune ya same Ummu baki gado, da alamu tayi nisa ciki tunani Muryar Ammar ce ta doki dodo kunne sa."Ummu kina zauna”Da kallo ta bushi har ya yiwa kansa mazauni ƙasan Carpet ɗin da yake gaban gado.saki fuska tayi "Ammar kain?”Kasa ya yi da kansa ya gaida ta sanan yace "Ummu ki yafe nazo nayi...”Kasa karsawa ya yi ya fashe da matsanancin kuka ya juma yanayi sanan ta ɗauki ruwan miƙa masa ai da yasha ya samu Nutsuwa ta kama hannu ta kira sunan sa.

“Ammar, yau ka zama miji. Ka bar yarinta a bayanka, ka rungumi nauyin da Allah Ya ɗora maka.”Ammarbya sake sun kunyar da kai yana goge hawaye da ya gangaro masa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ta kara da cewa. “Matar da ka aura ba baƙuwa ba ce. Amana ce da Allah Ya ba ka. Idan ka ji tana yin kuskure, ka tuna kai ma ba cikakke ba ne. Ka rufa mata asiri, ka gyara ta da haƙuri, ba da tsawa ba.Ka kula da harshenka, domin kalma ɗaya na iya gina gida ko ta rusa shi. Ka rika yi mata magana da taushi, domin mace zuciya ce kafin ta zama jiki.Idan ka samu saɓani, ka zaɓi sulhu. Kada ka bar fushi ya zama shugabanka. Ka zama maigida da ake girmamawa saboda adalci, ba don tsoro ba”Ta sauke nufashi ta kama hannu sa.

"Ammar Ka nemi halal ka ciyar da iyalinka, ka yawaita addu’a. Aure ba ya ɗorewa da ƙarfi, sai da tausayi da tsoron Allah.”kai kawai yake iya girgiza masa jiyake kamar ta hana shi tafiya sai tsinkawo muryata yayi tana cewa “Tashi kaje Allah ya maka Albarka ya baku zaman lafiya..”
[1/12, 12:22 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-25

Mikewa yayi jiki babu ƙwari kamar an kwara masa ruwan sanyi ji yanke yau duniyar tayi masa zafi. Har ya sauka parlour ƙasa baya jin sa a dai-dai, tsaki Abdullah ya buga.

“Mastwww Wallhi Ammar kana da matsala kai iri rawar kan nan ma na an gwaye banga kana yi ba kazo muyi mu kai ka, mu wuce gida kasan kusan muna da matan mu kuma mu suke jira”

“Abdullah nace ku tsaya ne,Abdullah you know I don't like this kind of nonsense.in baza ka tsaya ba, zan iya tafiya ba tare da kowa ba”

Yana fadi haka bai sake jiran me Abdullah zai ce ba ya fice, binsa suka yi Sunayi masa dariya har suka isa parking space.
Tun kafin su ƙarasa, ya shiga sabuwar motar sa Abdullah ne ya zauna kusa dashi Fu'ad ya musu driving sunyi tafiya bawai mai nisa sosai ba suka isa bayan Asibitin Nasarawa.gidan Ya haɗu sosai dan har yafi na Abi girma, ƙamshi ya riga ya gama cika Parlour sallama sukai shuru babu kowa guri Suka nema suka zauna,cikin ɗaure fuska Ammar ya kalle su.

"Bara na fito da ita, sai muyi abin da ya dace ku wuce ko?”

“Dama Ammar ai bamu ce zama muka zoba”

“Bazallah bar shege Kar ka bata mana rai sai muce anan zamu zauna har muga yadda zata...”

“Matseeewww Abdullah Wallahi kai banza ne har abada baza ka girma ba”

Yana faɗi haka ya shiga Bedroom yana sallama gaban sa ya faɗi wani iri jiri ya ɗauke shi da sauri ya dafa bango.Sadiya da Ido ta yake kan shi tun Sallamar sa tayi sauri dirowa daka kan gado nufosa tayi.

"Subahallah lafiya baka da lafiya?”

Ƙoƙarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login