Showing 6001 words to 9000 words out of 56438 words
Chapter 3 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt
sake zaro wata leda ɗauke da bandir ɗin kuɗi, ya ajiye a gefen kujera cikin nutsuwa.
Yusuf ya ji kamar ya fasa ihu saboda farin ciki. Idonsa yana kallo tamkar ɗan akuya da aka nuna masa gyaɗa.
Malam Sule ya haɗiye miyau, zuciyarsa tana rawa.
“Alhaji Ɗan Dubai, wallahi kai mai taimako ne. Ba zan taɓa hanaka ba. Amma dai yarinyar fa, tana da mahaifiya, ko da kuwa tana da tabin hankali. Dole ne na faɗa mata ko?..”
*Dan Allah shering saboda manzo Allah kar ku manta free ne aiki ku shine Comment like*
[10/30/2025, 4:56 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
____________free book _page-4
Alhaji Ɗan Dubai ya yi dariya mai sautin makamar ta tsofafi bokaye yace."Malam, irinawannan yaran mahaukatan ai abin a tausaya musu ne?Ni dai kawai ka bani amincewa, sai in zo in ɗauke ta gobe da safe. Kuma na bar kuɗin da zai wadatar da mahaifiyar ta da dawainiyar haukan ta.”
Ya tura ledar kuɗin ɗari biyar x10- bundun miliyan biyar.Sai da Malam ya zabura kamar wanda aka haɗa masa shokin. Hannunsa ya fara rawa yana ƙoƙarin ɓoye farin cikin da ke ratsa zuciyarsa.
“Subhanallah! Alhaji Ɗan Dubai, wannan alheri ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba.ainda ka barshi ma.”Yusuf da ke gefe ya ƙaraso da sauri yana cewa,“Alhaji, wallahi kai mutum ne mai hankali. Na dade ina addu’a Allah ya kawo mana kai cikin gidanmu sai gashi kazo.”
Alhaji Musa ya yi murmushi yana shafa gemunsa.“Na gode. To kai kuma, Yusuf, zan baka aljihun ka na musamman. Kai ne zaka tabbatar ta shirya gobe da safe. Kar kowa ya sani. Kasan irin fitinar da mata suke yi sai kaji ƙananu magan ganu.”
“Na gane, Alhaji,” Yusuf ya faɗa yana kwaɓe baki cikin murmushi.Da suka fita daga falon,Yusuf ya bi Alhajin da ido kamar mai kallo aljanna.“Wannan mutum, wallahi, ba kamar sauran mutane bane,” ya ce cikin zuciyarsa. Bayan su gama tsara yadda zasu gobe har baki mota Malam ya raka Alhaji Ɗan Dubai ya raka shi yana sheƙa godiya.
Da daddare, Malam Sule ya shiga ɗakinsa hankali sa akwamce irin na wanda Aljihu sa ya cika da kuɗi. Ya ɗan gyara rawaninsa, ya ɗaga hannu sama ya ce,
“Alhamdulillah! Allah kai mai azurta bawanka ne. Idan wannan yarinya ta tafi, to wani alheri a gare ni.”
Inna ce kwance bacci ya ɗauke ta da wuri saboda abinci da ta samu taci yau Malam da kanshi ya zuba musu abinci ya basu wanda sai da Sumayyah tayi mamaki. Bacci ta ya yi nisa ta fara suru tai kamar me tabi aljanu tace."Sumayyah… za su ɗauke ki… za su ɗauke ki daga haske zuwa duhu…”Sumayya da take gefe tana cin tuwo tsari ta cire hannu ta ta fara tofa mata addu'a da haka ta daina surutai ta ci gaba da bacci ta.Washe gari da safe da wuri, Yusuf ya tashi da sassafe fada ɗaki su Sumayyah tin daga nesa yake ƙwallah mata kira a zabure ta miƙe jikin ta na rawa tunani ta tayi wani laifi ne, a ƙofar ɗaki suka haɗu, ya ɗaure fuska kamar wani boss yace.“Sumayyah, yau Malam ya ce ki shirya, akwai wani Alhaji da yake son zai taimaka miki.za ki tafi ki zauna a wajen shi lilimi zaki kyauta batare da ƙwandalar Malam ba. Ai dama Malam yana son taimaka miki ko dan hali da mahaifiyar ki take ciki damace da babu.”
Sumayyah ta ɗago kai, idonta cike da tambaya. Muryar ta na rawa tace.
“Ni kuma Yaya Yusuf? Amma Inna tafa?.”Baki ya washe.
“Kar ki damu, an ce za a kula da ita sosai. Wannan dama ce babba, Sumayyah. Ki tafi, ki ga duniya duniya ta ganki.”
Cikin ranta wani abu ya fara yi mata yayo“Ki kula da duk wanda zai zo miki da taimako, ba kowa ke da zuciya tsarkakakkiya ba…”kalmar Inna kenan da ta faɗa a daren da ya gabata.Zuciyarta ta fara bugawa da karfi.
Ta ɗan dafa ƙirji, ta ce cikin murya mai rauni:
“Amma Yaya Yusuf Sadiya da Lubna suma zasu… me yasa bana jin daɗin wannan tafiya?kuma...” wani iri lafiyaye mari ya kifa mata tare da nuna ta da yatsa."Zanci Ubanki yanzu ance miki zuwa nayi na lalaɓa ki tom kisani ko kiji kwanciyar hankali ki kar kiji tafiya babu fashi”kunci ta dafe hawaye na sauka a hankali kan kumci ta Baba Zulai da Baba Hauwa kam shewa suka yi kamar a gidan biki baba Zulai ta ce."Yo Allah na tuba dama ai sai dai temako dan iri wanna 'ya'yan mahaukatan ko mijin aure basa samu.Sadiya da Lubna suka ƙyal ƙyale da dariya.
Bayan gari ya daɗa haske, ƙauyen ya yi shiru.sai kukan tsuntsaye suna tashi daga kan bishiyoyi, sai kuma iska mai sanyi tana kaɗawa tana ɗauke da ƙamshin ruwan sama.
Sumayyah ta zauna a bakin ƙofa tana kallon hanya, cikin zuciyarta tana jin wani irin nauyi kamar an ɗaura dutse a kirji. Ta ɗaura hijabinta na tsoho tayabo da Inna ta daɗe tana amfani da shi, saboda babu wanda ya ba ta sabo.
A gefe, Yusuf na ta faman cika da batsewa ya ce:"Ki gaggauta mana Sumayyah, Alhaji bai cika son jira ba. Kuma ki daina wannan yanayin kamar wacce aka tura ta dole. Ke fa za ki samu rayuwa mai kyau a Legas.”wata muguwar faɗiwar gaba taji duk da bata san nisan Lagos ba amma tana ji masu zuwa neman kudi na cewa kwana biyu ake a hanya batare da anje ba, share hawayen idon ta tayi da gefe hijab ɗinta. Ta Kasafi inda Yusuf yake tace.
“Amma Yaya Yusuf… Inna bata san zan tafi ba. Kuma jiya nayi mafarki… ina ganin kamar ana ɗaukata da ƙarfi, Inna tana kuka tana cewa ‘kar ki tafi! Dan Allah Ni ku barni guri Inna ta”
Yusuf haka wani dogon tsaki tare da buga mata harare.“Ke ki tsaya da mafarki ki, dama 'Yar mahaukaciyya ana rabata da mafarki hauka ne? Ke baki san wani lokaci Allah yana ɓoye alheri cikin abin da kike jin tsoro ba. Ki tashi mu tafi kafin Malam ya fito.”
Tana miƙewa suka ji ƙarar mota daga nesa, ta ƙaraso cikin ƙofar gidan, Mota ce fara mai gilashin baki ba iri ta jiya ba. Tana tsayawa, Alhaji Sa'idu Dan Dubai ya fito cikin riga mai tsada da hula ja.
Hannu ta ya kama har ƙofar gida Yusuf: na gani sa ya zube ya gaida Alhaji Ɗan Dubai, shikuma Alhaji Ɗan dubai ya bashi hannu tare da cewa.“Madalla! Itace yariyar”a zumat bai gane ta ba.Yusuf ya ce, “Eh Alhaji, ta shirya kamar yadda ka ce.”
Alhaji Ɗan Dubai ya kalli Sumayyah daga ƙasa zuwa sama, sai ya ɗan ɗaga kai yana murmushi.“Kin fi yadda na zata. Kar ki damu, za ki ga rayuwa mai kyau. Ki shige mota mu tafi.”
Sumayyah ta tsaya, ta kalli ƙofar shiga gida. Da sauri ta maida kallo ta kan yusuf tace
“Inna ta… bari in ce mata sai na dawo.”tana ƙoƙarin juyawa Yusuf ya riƙe hannunta.“Ke karki damu, Innarki ba ta cikin hayyacinta yanzu. Alhaji na jiranki fa!”turjewa ta fara tana kuka.ciki zafi rai Yusuf ya kira ƙani da Khalid,Cikin ƙanƙanin lokaci, suka tura ta cikin motar. Alhaji Ɗan Dubai ya shiga mazaunin gaba, sai direba ya tayar da mota.
Motar tana fara tafiya, suka ji muryar Inna daga cikin gida-da sautin da ya fi kowane tsoro ɗan Adam tana cewa.
“Sumayyahhhh! Kar ki tafi!! Kar ki tafi da su! Ba alheri bane! Za su ɗauke ki daga haske zuwa duhu! Sumayyahhhh!!!” duk iri riƙo da Malam da Baba Zulai suka mata sai da ta girgizar dasu.
Ta fito da gudu gashi kanta duk ya dik-dige saboda cigar sa da take da hannu, idanu ta suka yi jajaye, tana gudu kamar wacce wuta ke bint. turus tayi gani motar ta ɓace tana tada ƙura.Ta fāɗi ƙasa tana ihu tana bubbuga ƙirjinta tare da ɗiban gari kasa tana afawa a bakin ta.
“Ina kuka kai ta? Ku dawo da ‘yata! Ku dawo da ita! Ku mauhakata ne.”Dariya Amina ƙaramar 'yar Malam ta ƙyal ƙyale da ita tace."Rabi ai kece mahaukaciyar ba wasu ba kaji aiki Hauka”
Da ƙuwa Malam yayi mata tare da kaɗasu gida.
Har Inna sai da ya kaɗa su cikin gid. Malam Sule ya tsaya daga nesa yana kallo hanya, zuciyarsa na karyewa da abin da ya ji, amma sha’awar kuɗi ta rufe komai.
Ya shiga gida yana faɗin,
“Allah ne yasan alheri.da ke tattarai da yariyar nan yar kusu ƙa.”Inna ta sake fitowa daga ɗaki da tashiga,ta ɗago kai cikin zufa da ƙura, ta kalli sama tana kuka:
“kune kuka ɗauke ta daina kama ku na kaiku an kama ku” Kara Malam ya ɗako da gudu ta faɗa ɗaki tana ran taɓa ihu Baba Hauwa tace.“Au ashe haukata banza kike da ki tsaya mana”
***----***
A cikin mota kuwa, Sumayyah jikinta ya yi sanyi. Ta jingina a jikin gilashi tana kallo hanyar ƙauyensu da ke ƙara nisa. A cikin zuciyarta wani irin tsoro ne ya fara girma- tsoro wanda ba ta san dalilinsa ba.Ta ɗan kalli Alhaji Ɗan Dubai da ke gaba yana waya cikin dariya:
“Eh, na ɗauke ta yanzu. Ta yi kyau fiye da yadda nake tsammani. Ku shirya wajen kamar yadda na faɗa.”Zuciyarta ta sake bugawa!
Ta kalli Yusuf da ke gefe yana lumshe ido saboda zasu rage masa hanya zuwa ciki gari, ta ce cikin murya mai rauni:
“Yaya Yusuf… wannan tafiya… me take nufi da ‘ku shirya wajen’?”Yusuf bai ce komai ba, kawai ya ƙara sunkuyar da kai yana wasa da wayarsa da Alhaji Ɗan Dubai ya kawo masa sabuwa fill a kwali.Zuciyarta ta fara bugu da ƙarfi, sai ta runtse ido tana ambaton “Hasbunallahu wa ni‘mal wakeel...” bayan su shigo cikin ƙwayar birni kano aka sauke Yusuf Sannan motar ta ɗauki hanyar da bata san inda take kaiwa ba.
Kwanan su biyu ba tare da ta rintsa ba marar ta taga ɗaure wa da fitsari dan baza ta iya cewa zata yi ba, duk abin da aka bata bata iya ci dan gani take ƙarshe ta yazo.
Cinkus daki tsuma, yanayi iska da ta sauya kaɗai ta isa kasan ka shiga Lagos bayan su dan huce gurare da baza ta iya cewa gasunan unguwar ba.Motar ta tsaya a gaban wata babbar ƙofa da aka rubuta da manyan haruffa:“Cibiyar Ilimi ta Mata-Alheri Foundation.”
Sumayyah ta kalli rubutun, zuciyarta tana rawa. Amma ta lura da wani abu -duk da sunan da ke ƙofar, babu wata alama ta makaranta a wurin. Babu yara, babu murya, sai shiru mai nauyi da ƙamshin turaren da ya haɗu da wari-iri na bariki.
Alhaji Ɗan Dubai ya fito daga mota, ya gyara rigarsa tare da ɗaga mata gira ya ce:"Gashi munzo! nan ne, ‘yar albarka. Nan za ki zauna. Karki damu, komai zai gyaru nan gaba.” wata mace da ke tsaye a ƙofa cikin kaya masu fidda tsirai. Ya kalla yana kashe mata ido yace “Saffy chic ga sabuwar yariya ce,Ki gyara ta sosai.”Saffy Chic ta kalli Sumayyah a gadarance tare da binta da up and down . Ta ɗauke kai cikin raini, ta ce:“Zo ki bi ni.”
Sumayyah ta bi ta a hankali, zuciyarta na harbawa. Suna shiga tsoro ya daɗa kamata, ta ga matan da yawa, wasu suna zaune cikin kayan masu bayyana tsiraici, wasu suna dariya suna shan abin da ta kasa gane ko menene.
Gashi ji take kamar ana kallonta da ido masu cike da ta’addanci da yaɗa alfasha.
Saffy Chic ta ja hannunta ta shiga da ita ɗaki guda. A ciki akwai kaya masu kyau duk da kowane kasa sai tsun bayyana suran bawa- iri su riga da siket, da turare da takalma haka bangare ƙananu kaya kowane kala akawai.
Saffy Chic ta jefe ta da wasu kayan, ta ce:“Alhaji ya ce ki sa wannan.
Bayan kin gama, za ki ci abinci kiyi wanka. Ki sa su yanzu.”
Sumayyah ta tsaya cak, hawaye suka taru a idonta.“Ina makarantar da Alhaji ya ce zai kawo ni?Wannan wane irin wuri ne?”Saffy Chic tayi dariya iri ta matan duniya ta yi ta ce:“Ke yarinya,makaranta ce… ta rayuwa.”tana faɗi haka ta juya ta fita ta rufe ƙofa.A nan Sumayyah ta zauna, jikinta na rawa. Ta tuna muryar Inna a ƙauye tana cewa “Kar ki tafi da su! Ba alheri bane!”
Ta sa hannu ta rufe fuskarta, tana kuka cikin rauni.“Ya Allah…” ta ce cikin kuka, “Ka fitar dani daga kaddara… idan wannan wuri ba alheri bane, ka fitar da ni kafin zuciyata ta mutu.kafi Sheɗe ya yi galaba akaina.”
Bayan wani duk da haka bata ɗago ba tana kan dumdumemiyar katifa ta kifa kanta tana kuka, aka buga ƙofar da ƙarfi muryar Saffy Chic ta sake fitowa"Ki fito yanzu! Alhaji na jiranki a ɗaki”A lokacin ne zuciyarta ta fara sanin cewa ta shiga ƙofar da ba a komawa daga cikinta.Rikon ta ta fara da ta barta ta huta zazzaɓi ne ajikin ta tsaki Saffy Chic tayi ta rufe mata kofa ta fice.
[11/2/2025, 5:38 AM] OUMMU MUWADDAH: Follow the Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah) WhatsApp Channel. channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
________free book _page-5
Babu wanda ya sake shigowa inda Samayya take har dare, hakan ya yi mata daɗi.Saffy ce ta murɗa kofa ta dawo ciki wata iri shiga mara kyau gani, ciki fashashiyar muryar ta iri ta 'yan shaye-shaye mai cike da umarni a ciki ta ce.“Ki shirya. Alhaji na son ganinki yanzu. Kar ki sake min tambaya,ki sani in kika bi umarnin to rayuwarki za ta canza.”Sumayyah ta kalle ta cikin tsoro.
“Amma… me zan je in yi wurin Alhaji da dare haka?”Saffy ta yi murmushi.“Zaki ga komai da idonki. Ki taho kada ki tsaya tambaya.”
Cikin fargaba, Sumayyah ta bi ta har suka shiga babban wani ɗaki me cike da kayan alatu.
An cika wurin da kayan alatu- kujeru masu sirdi, ƙamshin turare mai nauyi, da sautin dariyar maza da mata.
A can tsakiyar ɗakin, ta hango Alhaji Ɗan Dubai zaune a kan kujera mai faɗi, yana dariya da wasu manyan mutane masu kuɗi-wasu da babban ciki, wasu da farin gemu.gefe su duk yaran 'Yan mata masu ƙananu, a tskiyar parlour wata yarinya ce mai kyawu gaske,tana ta rawar banza cikin night gown duk ta kama jikin ta. Sumayyah tana shiga, duk suka juya,
Idanu suka zuba mata kamar yadda karnuka ke kallon nama mai ƙamshi.
Wani daga cikin manyan ya ɗaga kofi lemo yana dariya:“Alhaji, wannan sabuwar ce? Kai, kai! Ka ce kaya sun sauka!”
Wani kuma ya da gefe yace:
“Wannan fa ba irin tamu bace Ga ga duk kan alama sabuwa ce, ba ta saba da irin wannan rayuwa ba.”Alhaji Ɗan Dubai ya yi Murmushi yana kallon Sumayyah.
“Eh, sabuwa ce.. kuma tana da kyau. Ku bari in koya mata yadda ake zama ‘yar gari mai sanan sai ta fara kawo muku ziyara.”Yana rufe baki dariya ta cika ɗakin.
Sumayyah ta tsaya cak, jikinta ya mutu gaba ɗaya.
Hannu ta soma rawa, idanunta suka cika da hawaye.Ta tuna Innar ta, da maganarta ta ƙarshe, zuciyarta ta soma dukan uku-uku.Ta juya da ƙarfi za ta gudu,Saffy ta rufe ƙofar ta tsaya a bayanta tana murmushi.“Kin riga kin shigo,kaddarar ki ta fara daga yau.”A wannan lokacin ne Sumayyah ta gane cewa duk wanda ya shiga wannan gida- ko dai ya lalace.kifa kanta tayi tsakani tsinyar ta tana kuka, tana ambaton:“Ya Allah, ka bani ƙarfi. Kada in zama ɗaya daga cikin su…”
*****
*Tuna baya*
Rabi yarinya ce mai kawaici da kunya.A lokacin baya,Malam Sule Giɗaɗo yaro ne matashin ankawo shi almajiranta Bunkure, ya taso da ƙazo kuma shine Baban yaro aciki Almajirai Malam Idi hakan ya sa duk saure almajiran Malama idi suke shaka sa acikin wanan hali Ya hadu da Zulai ya aure ta haihuwar ta daya ya sake aure Hauwa, yana da haka ɗauka kaka ta tazo masa acikin ƙauye su,ya shahara, guri yiwa mutane kauye Giɗaɗo wa’azi, ya zama mai jama’a, wanda kowa yake girmamawa.lokaci Da ya sake zuwa gaida Malam Idi, ba don neman aure ya zo ba, sai don neman gaida Malami sa, wato mahaifin Rabi. Bayan su gauisa da nutsuwa Malam ya Kali Sule yace. “Sule ga yarinya ta Rabi,na baka ita a matsayin sadaka domin Allah.”Sai da gaban Sule ya buga dan Shi rabi bata taɓa burge shi ba Gasali na Matan sa biyu sun isheshe rayuwa.Rabi da tazo kawo masa ruwa ta tsaya cak. Kallon mahaifinta kawai take yi, idanunta suka cika da hawaye.
Ta so ta ce a’a, amma kalmar “na baka ita sadaka” ta rufe mata baki. Haka Nauyi Malam idi da kuma kwarjinin da yasa shi amincew da zumar washe gari zaizo da shedu a daure masa aure. Haka kuwa akan yi washegari Malam Sule ya dawo da magabatan aka ɗaura musu aure wanda a take a lokaci ya tafi da Rabi. Bayan kwana biyar da faruwar haka, cikl dare gobara ta tashi babu gidan da bata shigaba wanda yasa iyaeye Rabi konewa musru, hakan ya jefa Rabi ciki tashin hakali da damu wanda hakan shi kuma Yayi wa Malam Sule daɗi ga samu hanyar ƙuntata ma har ta gaji ta bar masa gidan.
Daga wannan rana, rayuwarta ta sauya gaba ɗaya.a gidan Malam Sule, Rabi ta tarar da matan sa biyu- Zulai da Hauwa.Su biyun sun haɗu gaba ɗaya wajen wulakantarta.A wurin cin abinci, haka zasu fara yaɓa mata magana ciki waka ko wasa tauna kamar kullum suna zama Zulai ta kalleta ta ce.“Ke fa matar sadaka ce, ba ‘yar gida ba. Me kike nema anan?” haka ta zame hannu ta ta barsu, shewa sukayi suka ci gaba da cin tuwo su. haka rayuwar ta taita guda na acikin gidan Malam Sule.Idan ta yi ƙoƙarin shiga cikin su, sai su zage ta, su kwace mata abin hannunta.
Malam Sule kuwa, ko da ya ga hakan, bai ce komai ba.A idonsa, Rabi ba komai bace face kyautar da aka bashi-a matsayi matar sadaka.Kullum tana kuka cikin sirri, tana roƙon Allah:
“Ya Allah, ka bani haƙuri, ko da kuwa zuciyata zata tarwatse.”Haka rayuwarta ta koma kamar ta bawa a cikin gida,ana