Showing 36001 words to 39000 words out of 56438 words
Chapter 13 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt
kwashe² da kika saba ne yauma kika kwaso wani.”Iri kallo da Ammar ya a sake masa ne yasa Yusuf bari guri jikin sa na rawa. Sun ɗan juma a haka ya dubeta."Ko na tafi ne?”Jiki babu ƙwari ta shiga, Lumshe Ido sa yayi yana ji wata iri nutsuwa na ratsa shi tabbas Yariyar nan tana da baiwa, in har yana tare da ita takan kasa kama kansa.ita kum tun da ta zauna fargaba haɗuwar ta da Yaya Yusuf take in ta koma dan tasan wanan harara da ya masa akanta zai fanshe,Murya Ammar taji kamar daga samma"Aunty Sumayya ina Wuni tunda gaisuwar ma wahala take miki”Kunay ce tasa ta rufe fusakar ta.“Kai ai karami shine yake gaida babba ba wai yaro ba."
Dariya ya yi ya ɗauki gorar ruwa ya kurɓa sanan ya kalle ta."Tom ai naga gaba ɗaya mutane gidan nan naku nema suke su furgita min ke Allah ya kawo lokaci bari gidan nan mu huta....
[12/23/2025, 10:38 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
____________free book _page-20
Jin tayi shuru bata bashi amsa ba yasa shi juyawa ya kalleta, ganin yadda take faman wasa da yatsun hannunta cikin fargaba yasa ya kashe motar baki daya. "Sumayya, karki damu da su. Muddin ina raye, babu wanda ya isa ya cutar dake. Insha Allah nan da kwanaki kadan zan fitar dake daga wannan gidan."Wani sanyayyen murmushi tya bayyana a fuskar
Sumayya, wanda ya ƙara mata kyau da kwarjini. "Nagode Yaya Ammar, amma tsorona daya; kar Baba Zulai ta shiga tsakaninmu. Kaga yadda suka biyo ni da kallo kuwa?gashi so suke...."kenan kema kin yarda da canfi mutane ki yarda da Allah shike yin komi ba mutum ba dan haka ki manta dasu.”Shuru tayi babu ammasa hakan yasa, ya yi dariya, ya mika mata wani ƙaramin kwali mai kyau.
"Wannan turare ne da agogo, Hajiya ce tace na kawo miki. Sannan batun Baba Zulai, Allah yana tare da mu. Ke dai ki duƙufa da addu'a." Bayan sun dan taba hira,Ammar ya kalli agogo"Ranki yadade zan tafi akwai aiki agaba na zanje sai munyi waya”
Kai ta girga “Tom ai baka koya min yadda ake anfani da wayar ba”Kai ya dafe sanan ya amsa sai da ya koya mata yadda zata gane sosai sanan ta fita daga motar zuciyarta fari fes.
Bai bar anguwar ba sai da yaga tashiga cikin zaure gidan su sanan ya bar layi. tana shiga zaure gidan, gabanta ya fadi.
Yaya Yusuf ne yana tsaye jikin bango, yana huci kamar tsohon zaki jiran shigowar ta kawai yake. "Wato Sumayya har kin isa ki raina ni ko? Dan kin samu dan birni mai mota shi yasa kike kallonmu kamar wasu tsumma? Tom yau zan kade miki ƙuran da take kanki dan kutumar ub...."Baba Hauwa ce ta katse shi"Haba Yusuf wai sai yaushe yarinyar nan zata san ƙaunar 'yan uba ne dan Allah ku tausaya mata,Sumayya ba marainiya bace muddin ina numfashi. Kaje ka nemi dai²tawa da kanka, amma ba kan yarinyar nan ba.daga yau bazan sake bari kucutar da ita ba"tsaki Yusuf ya ja ya fice daga gidan yana zage-zage. Hawaye ido ta ta goge ta rusuna“Baba Hauwa nagode Allah ya saka da alheri”Ameen Tace suka shig cikin gida.
*ALHAJI ƊAN DUBAI*
A gefe guda kuma, Alhaji Ɗan Dubai ya isa gidan Alhaji Kareem Al-Labban bayan sallar magarib kamar yadda suka yi alkawari. Suna zaune a wani katafare Parlour na alfarma, Alhaji Kareem ya kalle shi cikin nutsuwa.
"Alhaji Ahmed (Ɗan Dubai), kasan amana dake tsakaninmu. Ina son wannan bikin na Ammar ya zama abin alfahari shikadai ne yaro na daga shi bani da wani magaji inaso akyakyautawa ma'aikata”
Alhaji Ɗan Dubai ya gyara zaman sa, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake dakin. "Ranka ya dade, za ayi komi cikin tsari kamar yadda ka buƙata?sai dai ni ina gani kamar Yarinya ce ’yar talakawa,kamar bata dace da yaro mu ammar ba?"
Alhaji Kareem ya kura masa ido dan bai tsamaci haka daga guri Alhaji Ahmed ba.nisawa ya yi ya daki Murmushi iri na manyan mutane.
"Ina ga wanan ba abin daga hakali bane daga Ni har kai babu wanda zai zauna masa da ita so bamu da damuwa da haka”Ɗan Dubai ya gyada kai,badan ranshi yaso ba soyayi zugar da tayi tasiri tun anan, sai dai ko hakan bai damu ba Akwai tanadi da yayiwa ammar da shegiyar yariyar da ta jamasa asara.
*GIDAN MALAM*
Tun kafi ketowar alfijir Baba Zulai da Sadiya sun gama shiryawa tsaf. "Sadiya, shirya bana so mufita akan ido jama'a tun kafin asuba zamu kama hanyar Rafin Malam. Dole ne mu raba wannan zaren tun kafin a kai ga saka shi" Sadiya ta yi dariyar mugunta, "Ina tare dake Babarmu gara mu raba su yanzu kafin ta je can birni tana mana takama da feleƙe Dan Wallahi Babar mu in naje gidan sa Har Uwar tashi sai naci ubanta tunda ta nuna tana son Sumayya."dariya Baba Zulai tayi suka ci gaba da shiri su ciki sirri.
Alhaji Ɗan Dubai ya fito daga gidan Alhaji Kareem yana goge gumin fuskarsa. Wani mugun murmushi ya subuce masa yayin da yake tada motarsa. "Alhaji Kareem, kana tunanin zanyi abin da zai faranta maka ko wanan shege ɗan naka? To zan tsara maka abin da zai raba danka da wannan yarinyar har abada.Dole ne na shirya tarkon da zai sa Alhaji Kareem ya tsani Sumayya, shi kuma Ammar ya ga laifinta. Zan hada su da babban laifi, wanda ko Ammar ba zai iya kare ta ba," ya fada a fili yana bankawa motar sa wuta.
Washegari tun kafin assalatu, Baba Zulai da Sadiya suka sace hanya suka nufi dajin Rafin Malam. Tafiyar kusan sa'a biyu ce a kan a kafa kafin su isa bukar Malam Mai yatsa ɗaya. Wurin yana da kyan gani amma cike da kwaramniyar tsuntsaye daji da hayakin turaren da ke fita daga kogon dutse.
Suna isa, suka tarar da Malam zaune, idanunsa sun yi jawur. "Zulaiha! Kun zo neman rugujawar katangar da kuka kasa hawa ko?" Ya fada cikin muryar mai cike da kuwa mara daɗi sauraro.
Baba Zulai ta zube tana tana masa wani kirari"Haka ne Malam. Wannan yarinyar Sumayya tana neman fi karfinmu. Muna so a raba wannan auren, a sanya kiyayya tsakaninta da Ammar, sannan a sanya Ammar din ya koma son Sadiya. Har aure ya koma kanta"
Malam Mai yatsa ɗaya ya buga kasa, wata irin tsawa ta daka a dajin.hoto ammar ya bayyana yana kwance sai da ya nuna musu hoto sa sanan ya hoto ya bace ya kalli Baba Zulai."Abin da kuka nema yana da tsada. Domin yarinyar nan da shi kanshi suna da tsari na addu'a. Amma zan baku wani magani da zaku binne a kofar dakin Innarta. Duk ranar da kafar Sumayya ta taka wurin, duk abin da Ammar zai gani a jikinta zai zama kaskanci da maita bazai taba gani farin ta ba sai baƙin ta. Amma ku sani, idan asirin ya karye, kanku zai dawo!"
Sadiya ta gyaɗa kai cike da zumudi, "Malam ko mene ne mu shirya mude. Burinmu dai mu ga Sumayya tana kuka, muna dariya.na mallaki wanan atajiri dan birni"dariya ya bushe da ita ya hada musu laya da wani ruwa da zasu hada su binne tare, basu bar guri malam mai yatsa ɗaya ba sai da Baba Zulai ta tafe masa dubu talatin sanan suka masa sallama.A lokacin da suka dawo gida, Sumayya tana zaune tana hira da Innarta, zuciyarta cike da farin cikin tunanin kiran da Ammar ya yi mata dazu ya dabaibaye zuciyar ta da ƙaunar da mara misaltuwa. Ba ta sani ba cewa makirci yana kewaye da ita ta kowane bangare ga Alhaji Ɗan Dubai daga birni, ga kuma su Baba Zulai a gida.
Sumayyah tana gani su ta miƙe tana masu sannu da zuwa ko kallo inda take basu ba suka shige ɗaki ransu fari ƙal.sunazama Sadiya ta ran gaɗa guɗa"Yanzu aka fara wasan, Sumayya. Ke da kike jin kun sani guri mutuwar ki ta kusa, kwanan nan zaki zama abar kyama a idon kowa.har shi wanda kika dogara dashi."baki Baba Zulai ta bige mata."Wanan shege baki naki sai ya tuna mana asiri gari azarɓaɓinki.”Dariya ta Ƙyal ƙyale da ita."Tom Babar mu na daina...”
[1/6, 9:29 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
____________free book _page-21
Da haka suka shiga abin da yake gaban su. Cikin dare misali biyu da rabi Baba Zulai ta mike Sadiya na kwance ta daka mata duba.murginawa ta sake zata koma bacci."Sadiya Dan Ubanki tashi waye yace miki ana bori da sanyi jiki,yanzu ne lokaci aiki mu dan haka tashi muyi abin da ya dace duk kafi lokaci ya ƙure mana”Miƙewa tayi azabure tana murje indo ciki sanɗa suka bude ƙofar , suka fita basu samu kowa ba, Baba ce ta kurkusa a baki kofar su Sumayyah, karamar wuka ta zamu ta fara haka kofar sai da tayi zurfi sanan ta karbi layu ta saka maida ta rufe ta yayafa ruwa sanan ta saka basasar ƙasa,da hanzarin suka koma ɗaki suna maida nufashi.
Kiran Sallah Asuba shine yasa Sumayyah fitowa tana wuce ta dauro alwala ta koma daki ido Su Baba Zulai yana kai tana wuce suka kwashe da dariya tare da tafawa.sumayyah na idar da Sallah wani azababe ciwon kai ya kama ta dakar ta iya rashi ta nemi guri ta kwanta kusa da Inna ta. Har gari ya yi haske bata fito ba.baba Zulai ce ta yaye musu labule kofar ɗaki a kwance ta same ta.
"Sumayya yau kuma wani sabo iskanci ne bazaki fito tsakar gida kiyi aiki ba sai kibi gado ki kwanta ai sai ki bari sai anyi aure naki ki fara nunawa mutane isa dallah ki tashi ko naje na sanar da Malam”
Da ƙar ta iya miƙewa tana dafa bango ta kalli Baba Zulai."Ba Wallahi kaina ke ciwo dakar nake iya daga ido kiyi hakuri bawai kin fitowa nayi ba”
"Matseeeee karyar banza ayi dai mu gani”Da haka baba zulai ta fice.
Kwaci tashi yau tsayi sati guda Baba Ammar babu kiran sa haka kuma in ta kira sai dai taitaji wani iri turanci.Shirye-Shirye biki ya kankama saura kwana uku yau ne aka kawo laife set bakwai an zuba kaya sosai, duk yadda Sumayya taso taga kayan nan haka Baba Zulai ta kafe tace ta bari in taje gidan ta ta kare musu kallo hata ɗinkaku ciki bata bar sumayya ta dauka ba Ƙarshe ciki sirri ta bawa Sadiya takai aka mai dasu dai-dai sawar ta.
*AMMAR*
Tin da bikin ya motso ya rasa mai yake masa dadi ,gashi fusakar Sadiya yake gani duk yadda yaso ya tuna Sumayyah ya kasa ko kira ta ya tafi zaiyi sai ya nemi number ya rasa, ya kasa sanarwa da kowa, matsalar da take damu sa.har biki ya rage kwana uku aka kai lefe.
*ALHAJI ƊAN DUBAI*
ya riga ya gama tsara komi, dan har sabo gidan Ammar ya sani dashi ake shirya komi dan Sani lokaci abin da za Asama Alhaji Ɗan Dubai ya sani Ammar bai sani wai duk dan ayi masa bazata kayan daki kuwa tuni suka ce sunyafe Ummi ce zata yiwa Sumayya. Bayan su fito daga gidan Alhaji Ɗan Dubai ya kalli Mustapha yaro sa da suka fito daga gidan Ammar kai wasu kujeri ya tun tsireeda dariya yace.“ Mustapha Wallahi yaro nan har ya fara bani tausayi domi iri muguntar da na shirya masa bai isa ya tsallake ba”Wanan Haka yake Alhaji Allah yaro baisan wuta ba sai ya taka, baisan ba'a taɓaka azauna lafiya ba”Dariya suka yi suka tafa sanan Mustapha ya tuƙa suka bar layi.
*3 Day*
Kofar gidan Malam Sule Gidaɗo damƙar yake da Malam zaure da almajira ana ta yawo da tuwo mutane kowa yana zuba ido zuwan ango da iyaye sa domi kuwa labari ya iske su atajiri Sumayyah zata aura.Ciki gida kuwa Sadiya ce ta fito da wata arniyar shadda kana gani kasan ta manya ce dan Bazum ce tasha aiki ajiki da mayafi da takalmin duk aciki lefe ta dauka Sumayya kuwa da ƙar Baba Zulai ta dauko atamfa mai tsada ce sosai sai takalmin wanka da mayafi ta bata, kallo ta bita dashi ta wirga mata harara.
"Kimga saboda baki duniya na dauka miki wanan inkuma so kike baki ya miki yawa sai na kwaso miki tsiyar ki kije can ki ƙarata duk abin da ake muku bakwa gani yaran yanzu”
Shuru Sumayya tayi hawaye na zuba a kan fusakar ya, daki Inna ta tace ta zube kayan tasha layi kafi ta samu ta shiga wanka, ko da ta fito dangwali yaɓa ta shafa ko arzikin hoda bata samu ba tayi kuka kamar ranta zaifita babu mai rarashi ta taji lokaci da Sadiya ta fito wasu dangi Baba Zulai na zolayar ta.
"Sadiya Yar Baba wallahi sai kace kece Amarya wanan ango da yasan dake da baikai kanshi guri hauka ba.”budar baki Sadiya tace."Ku kuke abin ku dama ai nice Amarya ba wata ba kuma zaku gani lokaci zai nuna kansa ”Shewa suka sa."Shegiya Sadiya kar kisa Sumayyah ta hadiyi zuciya ta Mutum saboda baƙi ciki”
Har suka gama surutun su, tana ji haka kuma bata yi karan bani fitowa tsakar gida ba dan ko ta fito bamda kyara da hantara babu abin da zata sha, a guri dangi mahaifin nata dana matan baban ta.11 dai-dai ɓangare aungo sukazo sai dai Babu Alhaji Ɗan Dubai dan shi ance ya zauna ta kula dama su zuwa daga baya yana salmar su.
Waliye Sumayyah dana Ammar su Halara a masallaci shedu ake gabatarwa wandda addini ya tana da.ammar suna gefe shi da wasu abokasa, zuciyar sa ta fara masa hudu da kuma tilas tashi akan abin da tun dare jiya yake jin haka shine daidai. Ciki sauri ya tunkari masallaci, da sauri Abdullah aboki da ya tare sa
"Kai bana so shirme iyaye mune a ciki mai zaka yi kuma indai Sumayyah ce nan da 'yan daƙiƙu zata zama taka.”Da sauri ya dago ƙirjina wata iri bugawa.
"Abdullah hakan ne bana so Sadiya nake so aure shiyasa nake sauri kar amin ba dai-dai ba wanda hakan zai iya zama barazana da rayiwata gaba ɗaya.”
Sororo Abdullah ya yi dan gano yake zaki aure ne yake damusa ba tare da wata damuwa ya bashi hanya ya wuce.ciki ya kutsa kansa duk wanda ya gansa sai ya bashi hanya dan yasan ango ne, ko kaci da ake kokari daura aure ya sauri karasa wa.
"Dan Allah ku da kata Ni Sadiya nake so ba Sumayyah dan Allah.....
[1/7, 9:01 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
____________free book _page-22
Babu wanda bai kalli Ammar ba, Abi ne ya mike da sauri ya kama Ammar kasa yayi da murya Ammar.
"Ammar lafiya kake? Sumayyah ce fa yariyar da ka kawo mana ita,Me ya shigi kanka ne?”
Lokaci ɗaya jijoyoyi kansa suka tashi Ya fashe da kuka kamar yaro ƙarami tare da fadawa kan Abi.
"Abi wallahi nima ban sani ba amma haka kawai nake ji kamar in na aureta shine silar bari na duniya Abi dan Allah in dai kana sona kawai ka yarda na Auri Sadiya kaga itace muka san Asali....”
Da sauri ya rufe masa baki"Amma Ammar ina jiye maka tsoro ranar ladama dan Allah yaro na kayi tunani me yasa zaka yiwa yariyar nan haka, ita fa tamkar marainiya....”Tafiya Ammar ya yi lu'ulu'u kamar zai fadi da sauri Abin ya kamo sa.
"Ammar Lafiya baka da lafiya??”
“Abi ko sunan ta naji an abanta kaina sara min yake jinake nufashi na yana so ɗaukewa, Abi a kan wata zaka so ƙarasa rayiwar naka yaro?”Kai ya girgiza zuciyar sa nayi masa ciwo, kama sa yayi ya zaunar dashi, sanan ya koma kusa da manyan mutane ya sanar dasu a sauya aure daga kan Sumayyah zuwa kan Sadiya fara'a Malam da Yusuf kasa boyuwa tayi ciki zumi ɗin aka daura auren akan sadaki naira dubu dari uku.shedu suka sheda,Yusuf har da gudu sa ya ƙarasa ciki gida ya sheda musu na aka hau tsalala guda. Maganar Sa'ade da taje jikin Window su Sumayyah ce ta doki dodo kunne Sumayyah.
“Allah mai kyauta da ƙari Kaji kudirar Allah An taho da zumar Aure Sumayyah ya koma ka Sadiya dama Allah bai rubuta Sumayya itace matar tasa ba Yariya Allah yasa ki shigar A Sa'a dama kin fi kala da matar many...
Sulalayewa Sumayyah tayi sumamiya babu wanda yasan ta suma dan a tsakar gida bidiri kawai ake Baba Hauwa ce ta nufo daki Da gudu tana zuwa ta samu Sumayyah a sanƙame hawaye ta fara.
"Sumayyah..! Sumayyah ki tashi kada ki bari wanan abu ya ɗaga miki hankalin kin ga jarabawa da tafi wanan insha Allah Allah zai misanya miki da mafi alkairi Kisani kina zaune Gaskiya, zata yi halinta kuma ƙarya fure take bata 'Ya'ya wallahi”Duk surutu da Baba Hauwa take Sumayyah bata san tana yiba ruwa ta dauka ta yayafa mata da Sallati ta farka suna haɗa ido da Baba Hauwa komi ya dawowa mata sabo hawaye ido ta ta goge ciki karyewar zuciya tace.
"Baba Hauwa da gaske Ammar bani ya aura ba Sadiya ce matar sa bani ba?”Hawaye itama Baba Hauwa ta fara gegewa.
"Sumayyah ki daure nasan akwai ciwo amma dan Allah karki bari sheɗe ya yi galaba akanki Wallahi Allah dama ya riga ya rubuta can dama bake ce matar Ammar ba, ki Sani ko Ba Sadiya ba dole zai auri wata kiyi musu addu'a kiyiwa kanki addu'a Allah yasa hakan ya ame miki alkairi kina zaune zaki ga sakaiya domin Allah baya bacci ”Kai ta gigiza kukan Inna suka ji da take bacci tun dare jiya bata farka ba sai yanzu, da sauri Sumayya ta fada jikin ta kuka ta saki mai kara tana sake ƙankame Innar ta sai da suka shafe 30 minute sanan Ta tsaigata har Baba Hauwa ta fita ta dauko
