Showing 42001 words to 45000 words out of 56438 words

Chapter 15 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

18

kama sa take ya yi sauri ɗaga mata hannu.“Kar ki damu kizo zaku gaisa da abokaina, bana so ki yi magana bayan gaisuwa ko mai zasu ce miki”

Kai ta ɗaga ji take kamar ta rungume shi ko ta samu nutsuwa yau itace tare da wanan kyakyawam mutumin hamshaƙi mai kuɗi wallahi nasan yanzu, wata ƙila ya mallaka mini katuwar mota mai...

“Ko bakya son zuwa na tafi?”

"Uhum...Ah.... A'a ai kai nake jira ka tafi sai na bi bayan ka”

Bai sake ce mata komi ba ya wuce tana bin bayan sa har suka isa parlour, tun da suka zauna guri ya yi tsit. Wani iri kallo ya bita dashi da yi mata Alamun ta gaida su,amma ta kasa ganewa me yake nufi, sai ma bin Abokan ammar da ta sake yi da kallo, ranƙwafowa Ammar yayi ya mata rufa, ya sake kasa da Muryar sa.

“Ke me kike yine? ki gaida”

Wani iri Lumshe Ido Sadiya tayi ta saki wata iri a jiyar zuciya sanan ta kalle su, sauya salon Muryar tayi ciki yauƙi.

"Ina yini ku ya ku kaji da jama'a Allah ya huta gajiya, insha Allah in gajiyar biki ta sake mu zamu zo har gida muyi.....

“Be quiet, nobody asked yo?”cikin tsawa ya faɗa yana dalla mata harara, tsit tayi Fu'ad da dariya ta gama kama sa da sauri ya miƙe ya fice shima harara ya bishi dashi.

“nonsense”Gyaran murya Bazallah ya yi“Ammar ya kamata muyi abin da ya kawo mu”Shiru sukayi Sallama Bazallah ya sake ya fara musu wa'azi ya tunasar dasu zaman Aure da kyautatawa juna, aka yi musu addu'a suka ajiye ledoji suye baki suka mike shi ya raka su sanan ya dawo ya rufe ƙofa yana murɗa kofar Bedroom ɗin nepa ta ɗauke cike da mamaki ya zaro Phone ɗinsa da zumar ya haska sai jin saukar ƙarfe yayi ta dai-dai wuyansa kara ya saki tare da zubewa ƙasa jini ne ya fara bin ta bayan kunnen sa sai kuma haske nepa ya dawo. Sadiya ce ta ƙaraso in da ya ke a kwance ta fara kuka.kafin ta motsa mutum da ya make shi ya fito ta bayan labule kamar wasa sai ga wasu daga ciki Bratheroom kusan mutane bakawai har na waje 8 a razane Ammar ya sake ƙoƙari tashi Saurayi da ya yane fusakar sa da baƙi hirami ya take masa hannu da iri takalmin boll dinan, yar ƙara ya saki.

"Ashh” ɗaya daga ciki ya daka tsalle ya faɗa kan gado ciki zuciya da ɓaci rai Ammar ya dakawa Saurayi tsawa.

“You are crazy, you don't respect marriage.” naushi ya kaiwa Ammar a fuska har sai da baki sa ya fashe.

“Kai ɗin baza zaka zauna kana gaya min magana son ranka tom kasani baka ga komi ba aciki abin da muka zoyi dan kafi ka fara karɓar haki ka mune zamu karɓa, daga baya ka samu...

Wani iri ihu Ammar ya kurma ya nufi inda Saurayi yake ciki zafi nama matasa biyu suka fusgo Ammar ya faɗo kasan Carpet har sai da ya saki yar ƙara.

"Dama kawai muyi abin da ya kawo mu mu wuce gani mu a haka yake gani kamar zai iya damu”

Dariya wanda aka kira da Dama yayi.

"Hahaha Baushe bar shege ai na fasa sumar dashi kafi mu aikata abin da ya kawo mu dole yaga komi akan ido sa sai mu farɗe ta zamu tafi dan Ubansa”

Ritse ido yayi hawaye masu zafi suka gangaro masa,Sadiya tana taji haka ta ɗora hannu aka.

"Wayo Allah nashiga uku shike nan ni tawa ta ƙare dan Allah ku temaka kumin rai wallahi bana so kowa ya taɓa ni sai Balarabe miji.....

"Jini da shegiya manya yariya tom ki sani ni Dama nine ango ki na yau kuma ko macewa kika yi, yau ɗin nan sai nayi abin da aka samu”

"Nashiga Uku ni Sa...”wata muguwar Fusga Dama ya mata tare da jefa ta kan gado
Batar re da kunyar saura maza bakwai da suke guri ba haka ya hau tuɓe kayan jikin sa ya faɗa kan Sadiya, Ihu Ammar ya kurma tare da zubewa ƙasa sumame.

*Giɗaɗo*

Cikin dare A firgice Sumayyah ta farka kirjin ta yana dukan uku-uku.

“Inaalillahi wa'inaalaihi rajun Ya Allah duk A halin da Yaya Ammar da Sadiya suke Allah ka kubutar dasu Allah kaji kansu,”

Numfashi ta sauke, ta dafe dai-dai saitin zuciyar ta lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka.

“Me yasa nake ji kamar wani abu na faruwa da Yaya Ammar da Sadiya taya zan fita na sanar da Baba wanan mugun mafarki danayi??”

Wata zuciyar ta tuna mata."Sumayyah ina rabaki kada kije ace ko ba haka bane kizo kiji kunya, ki sani ba ko wane mafarki ne yakan zama gaske ba.”

Tajima tana jin bugu zuciya sanan ta miƙe ta nufi banɗaki Alwala ta ɗauro ta gabatar da Sallah raka biyu da yiwa Ammar da Sadiya zaman lafiya da Zuri'a na gari.

Sai da maza bakwai suka afkawa Sadiya kafi na takwas ɗin ne Dama ya dakatar da Shi ya ɗauki ruwa ya watsawa Ammar a furgice ya farka a kwance Ya samu Sadiya da Alamun ko numfashi bata yi, kan bed ɗin tamkar anyi ado da jini farin blacked ne amma ya koma ja. Ido sa ya rufe lokaci da ɗaya saurayi ya kwanta kan Sadiya.ido sa na zubar da hawaye me zafi ya fi Sa'a biyu sanan ya miƙe yana miƙa sai da yaran suka fita, Dama yazo gaf dashi ya miƙa masa wani gwangwani.

Kallo Ammar ya bisa dashi ɗaure fuska Dama yayi.

“Malam karɓi kasha bana so na azabtar dakai ta hanyar duka shiysa na sama poisoning kasha Hankali kwamce zaka ji komi na jikin ka ya daina aiki”

Ciki razana Ammar ya kalle shi.."Wa..wa..wa...ne yake son halakani da matata dan Allah ka sanar dani ni dai nasan bani da wata alaƙa daku?”

“Hahaha Yaro man kaza Ka sani fansa ce kuma wanda yake tare da kune ya turo mu anyi mana biyan da baka isa mu karɓi naka kuɗi ba sanan ka sani Wallahi na sake baka, baka amsa ka shaba Tom tabbas zan kira ƙarti mazan can su taka ka yadda lakar ka zata daina aiki ga kuma azaba da zaka sha”

Lumshe ido Ammar yayi tare da karɓa sai da ya shanye sanan ya yi cilli da da gwangwani, dariya Dama yayi ya ɗauke gwangwani ya fice....
[1/22, 6:16 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-26

Yana sha Ko 2 minte baiba ya zube a ƙasa jikin sa yayi sanyi, baki sa ya rufe, hawaye ne kawai yake fita daga ido sa, wani iri zafi da kishi Na Kama masa gashi bashi da damar tashi yaje inda Sadiya take kwance,yadda yaga rana haka yaga dare Sadiya kam har bayan Sallah Asuba bata farka ba haka Ammar idon da yana kan bed dinsa sadiya take kwance.

Tun guri Karfe biyu Bacci ya kauracewa Ummu tashi tayi a tsorace.

“ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil”Abi da yake gefe ne ya tashi ciki damuwa ya kama hannu ta

“Lafiya Ummu me yake faruwa ciki dare?”

"Abi Amar Wallahi wani mugun mafarki nayi tabbas Ammar yana ciki wani hali dan Allah katashi muje”

“Com dwon mana Me yasa kike haka ne rashi sabo ne kin manta yau ya shiga sabuwar rayuwa addu'a zaki masa a hankali zaki....”

"Ab...Abi dan Allah ka tsaya ka fahimce Ni Wallahi wanan ba rashi sabone ko wani abu ba tabbas jiki na Yana bani Ammar yana ciki wani hali dan Allah me yasa baza ka tsaya ka duba magana taba”

Sosai ya sassauta murya ya fara kwantar mata da hankali ciki nutsuwa har ta rage tsoro da fargabar da take, Bathroom ta faɗa Alwala ta dauro tayi sallah raka'a biyu ta jima tana addu'a da kai jikanta guri mai duka akan Ammar da matar sa. Sallah Asuba ita ta tashe ta bayan tayi Sallah Kitchen ta shiga dan haɗawa Ammar break fass shida Amarya sa. Sai 8 ta fito lokaci Fu'at yazo bayan tasa A cikin Vaskeet ta miƙa masa yana ammasa zai juya ta dakatar dashi.

"Fu'at ka jira tare zamu”

Cikin dariya ya fara zolayar ta.

"Haba Ummi ki bari rana ta ɗaga sai kije Wai tun yau har kin fara kewar Ammar ɗin?”

“Fu'at ba zance ne na kewa ba ko zumuɗi kawai inaso naga yadda...

"Babu inda Zata Fu'at maza ka wuce kace wa AMMAR ya kira tsohuwar nan ta kasa samu salama saboda baya gidan”

Abi na faɗi haka Fu'at ya fice yana dariya Da sauti Ummu ta shige Kitchen dan Ita da gaske gidan Ammar zata shiga.

Tun asuba da Sumayyah ta tashi tayi Sallah bata koma ba jiki ta duk asanyaye yake Allah-Allah take gari ya waye taji kiran Sadiya ko hankalin ta ya kwanta.

Tun da Fu'at yaje baki gate yake Aiki Horn amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa tsaki ya doka gani mai gadi yaki zuwa ya buɗe masa gate da kansa ya buɗe dan yaga da alamu a buɗe ƙofar take yana buɗewa ya koma cikin motar ya shiga yana isa parking space ya gara parking baya ya bude ya dauki Vaskeet din ya fita ciki isa ya tunkari ƙofar parlo da mamaki sa sai ya tarar da buɗe sallama ya fara jin shuru kuka gaba daya hankali sa ya kasa nutsuwa yasa ya danna kansa cikin parlo hankali sane ya sake tashi ganin kowace kofa abude kuma kamar ba dai-dai komi yake ba da sauri ya tunkari bedroom Ammar ya fara karo dashi kamar gawa ido sa ya kai kan Amayar Ammar da sari ya kwalla ihu tare da ja da baya ido sa ya kaɗa ya yi full.

Parlour ya dawo yana jan Kafa da kar wayar sa ya janyo yana ƙoƙarin kiran Ummu kiran ta ya shigo hannu sa na rawa ya ɗauka.

“Hallo Fu'at na jira Ammar Bai dauka ba ka karasa ka bashi waya.?”

“Hallo Fu'at kana jina kuwa.?”

Wani miyau ya haɗiye mai ɗaci Muryar sa na rawa.

"Ummu... Ummu kina... Ummu dan Allah ki taho ke da Abi ki yanzu.”

Yana faɗi haka ya katse kiran.

A gigice Ummu ta hausa samma a hanyar fitowa suka haɗu da Abi jikin ta na rawa da sauri ya kama ta gani tana niyar faɗuwa.

"Me kuma ya faru?”

"Abi Dama sai da nagaya maka Akwai Matsala yanzu Fu'at ya kira ni yace mu taho akwai matsala”

Duk da yashiga matsanancin tashi hankali amma baibari ta gane ba ciki dabara yace.

"Tom bara na kira shi Fu'at din kije Parlour ina zuwa”

Da sauri ta ɗauki mayafin ta da Handbag ta fice Wayar sa ya fido ya kira Fu'at 2 miss Call sanan ya ya picking.

"Hello Fu'at me yake faruwa ne?”

“Abi dan Allah kuyi sauri kuɗi Yanzu haka na kira police station suna kan hanyar zuwa ina tunani wasu ɓata gari sun shiga gidan Ammar Anyi repin dim matar sa”

“ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil”yana faɗin haka ko katse kiran baiba ya fito a firgice bai samu Ummu a Parlour kasa ba yana fita Compound ya same ta sai Safa da marwa take bai yarda ta gane halin da ya ke ciki ba guri Mansur drive yaje ya sanar dashi yaje gidan surukan Ammar ya ɗauko mahaifiyar ta da mahaifinta, suna fita Mansur ya fice.

Gudu yake cikin 20 minute sai gasu a gidan ammar,Ummu bata jira Abi ya gama parking ba ta ficewa A tsakiyar Parlo Ummu ta iske Fu'at ƙoƙarin shigewa Tayi Fu'at ya sauri rike ta ido sa na fitar da hawaye.

"No..! Ummu dan Allah kar ki shiga yanzu 'yan sanda zasu zo suyi aiki....

Tsawa ta daka masa

“Me yasa Fu'at Ammar ne fa da matar sa sun kashe min shi ko Nasan ya mutu Inaalillahi wa Inna ilahi...

"Dan Allah Ummu kiyu shuru bana tunani Sun mutun sai dai Halin da suke ciki ne ya yi....

Tura shi tayi da ƙarfin ta.

"Matsa ka bani guri dole naje magana Ammar ko a wane iri hali yake”

Bata sake tsawa saurare saba lokaci Abin ya shigo tare da D.P.O da sauran ta wagar sa tana shiga ɗaki kan Ammar ta fara kai ido ta tafi zata jiniga shi ta hango Sadiya ƙara ta ƙwalla zata zame ta faɗi Abi ya tare ta ta faɗa jikin sa, Nuna sadiya ta fada.

“Abi Kalli ruwaye waɗan nan?wane mara tausayi ne Me yariyar nan tayi musu...?”



*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-27

Bai kula taba sai kamo ta da ya yi suka fice daga ɗaki Mata ne 'yan sanda suka shiga bince kafi suka rufe Al'aura Sadiya Ammar kuma maza biyu ne suka saka shi amota gaba tare da Sadiya suna ƙoƙari fita Malam da Baba Zulai sai Yusuf suka iso ciki kaɗuwa ta fara tambaya ko sadiya ta mutum ne Tsakani Ummu da Abi Babu wanda ya iya bata Amma sai Mace 'Yan sada ta ce.

"Baiwar Allah har yanzu tana raye sai dai zamu je Asibi domin likitoci suyi nasu bincike dan Allah ki kwantar da hankali ki kinji”

Kai ta girgiza tana matse kwallah da baki zani ta A motar da Aka kawo su a motar suka nufi asibiti.Tun da suka isa aka fara dukufa kan bince Saka mako Safiya ne ya fara fito. Doctor ya kira iyaye Sadiya da Na Ammar sanan D.P.O

Bayan su zauna ya gyaran murya ciki kwantar da Hankali yace.

“Da farko ina mai baku haƙuri bisa wanan iftila'i da ya afku Labarin mara daɗi, a bincike da mukayi Ba iya mutun ɗaya ne ya keta hadin taɓa Mutane ɗai² har bakwai zuwa takwas wanda hakan zai iya je fata....

Kwaran Da Baba Zulai ta ƙwalla ce ta zube ƙasa tana wasu iri surutai yasa Doctor dakatar da bayani da yanke da Alamu Baba Zulai Aljanu take Yusuf ne Da Baba Malam suka fitar da ita aka bata ɗaki gudu. Ummu kuwa banda sunan Allah babu abin da take an bato, komi ya tsaya mata suwaye suke san Hallaka yaro ta da matar sa Adare su na farko waye yake son gani bayansu..?”tambayar da bata da Ammsa take Sallmar wata Nurses ce ta dawo da hankali kowa kanshi Sakamakon Ammar ne ya fito ammasa ya yi sai da ya maida Fari Glass ɗinsa ya duba takardar da take ɗauke da bayani sanan ya ajiye Ummu ya kallah yaga shi take kallo tausayi ta yasa ke kama ta ya sani tun Ammar yana yaro shine Doctor su zabbaɓi comment in AMMAR yana yi Hankali ta sai ya tashi na wani ma ya tashi, bare taji abin da ya samo yaro ta. Gyaran murya ya yi.

“ehamm A Gajiya Dan Allah ko zaki bamu guri sabo...

"Doctor Mutuwar Ammar ɗin ce baza ka iya sanarwa agaba na ba sai na fita?” yadda tayi furci ciki karaya yasa shi girgiza kai.

"No Ajiya, Amma ina gani kika fita..

"Doctor kayi bayani ka Babu abin da Zai faru na riga falwalawa Allah al'amura na”

“Masha Allah Alhaji Haƙikani Gaskiya ko suwaye sun su bawa Ammar Poisoning ma'ana (Guba) wace takan iya shafar gabobi da dama a jikin ɗan Adam,gwargwado irin gubar, da Adadin ta da hanyar da ta shiga jikin.”

“ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun”Abi yake ta maimaitawa Ummu kam hawaye kawai take maganar ma ta kasa, maganar Doctor ce ta katse kowane daga iri tunani da yake.

“Sai da Muce Allahmmdullilah saboda shi a bince da mukayi bai samu rikicewar ƙwaƙwalwa ma'ana(Brain) ko rikicewa tunani, Ana shi bincike da muka samu Ammar ba zai iya motsin ba sai an dage guri kula da lafiyar sa sanan ida nusa sun riga sun juya su tsaya guri ɗaya amma duk abin da za'a ce xauki damar magana ce kawai babh sanan zaku ci gaba da taya shi da addu'a dan A halin da ake ciki addu'ar kuce kaɗai mafita.

“ Allahuma ajirni fil'musibati wakilni khairai minha”

Cewat Ummu da take ta mase hawaye, Abi ne yayi ƙarfi halin cewa.

“ Doctor zamu iya shiga mu ganshi shi da matar tashi”

"Yariyar dai Yanzu ana kan yi mata ɗinki da ƙara mata ruwa zuwa ajima zaku shiga”

Godiya suka masa suka fita lokaci da suka fita aka fito da Ammar daga room ɗin gashi da aka shigar dashi ɗaki hutu aka kai shi.

Ɗakin hutu suka shiga gaba ɗaya, kowa zuciyarsa cike da raɗaɗi. Ammar yana kwance a kan gadon asibiti, na’urar numfashi na amsa aikinta, idanuwansa a akafe, fuskarsa ta rame fiye da yadda aka saba ganinsa. Ummu ta durƙusa gefen gadon, ta kama hannunsa duk biyu tana shafa shi tamkar.

“Ya Allah… Ammar ɗana, ka bashi iko cin wanan jarabawa” ta faɗa cikin kuka mai karya zuciya.
Abi kuwa yana tsaye gefe guda, idanuwansa sun cika da hawaye, gani Ammar kwace babu inda yake motsi aikin sa,amma da yake namiji ne dole ya riƙe kansa. Ya ɗora hannusa kan kafadar Ummu.
“Ki yi haƙuri Ummu, komai daga Allah yake, kina daɗa ɗaga masa hankali.”

A ɗakin daban kuma Sadiya tana kwance, ruwan drip na shiga jikinta a hankali. Baba Zulai zaune a gefenta tana karanta Ayatul Kursiyyu tare da face majina da baki hijab ɗinta, Yusuf kuwa yana yawo a ɗaki ya kai mari ya kai gwaro.

“Wannan wane irin jarabawa ne Wallahi Babar mu nafi tunanu wanan Yar Mahaukaciyar da sa hannu ta aciki ture ne wanana baza mu yarda ba” Yusuf ya faɗa yana girgiza kai. Baki Malam na kufa saboda Azabar yinwar da yake ji ya fito tun farar sabiya bai karya ba tasar cewa.

"Yusuf Fatana Kada Sadiya ta mutu duk wani buri na Ya dori akan yaro nan Allah yasa yaro nan ya riga ta tafiya ko masa mu gado”
Da Sauri Yusuf yace.

“Ameen dai Baban mu, Amma ban taɓa gani masifa iri wanan ba daren aurenta?”

Bayan wasu mintuna Nurse ta shigo ɗakin da Ammar yake kwance.
“Dan Allah lokaci ya yi, zamu kai shi ICU domin kulawa ta musamman.”

Miƙewa Ummu tayi ta riƙe hannun Ammar da ƙarfi kamar za a ƙwace mata shi.
“Allah Ya duba ka ya baka kafiya Don Allah ku kula min da shi, shi kaɗai nake da shi.”

Kai Nurse ta girgiza cike da tausayi.
“In sha Allahu, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu.”

Suka tura gadon Ammar zuwa ICU, Ummu da Abi suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login