Showing 3001 words to 6000 words out of 56438 words

Chapter 2 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

9

ya lura da ita hada-hadarsu kawai suke.shawara ta yanke ta tafi ɗaki guri Innar ta Baba Hauwa ta fito daga cikin ɗaki tana washe baki kamar gonar audiga, Muryar ta har,har ɗewa take saboda sauri magana.

“Ke... tsohuwar..manya.. yanzu ..Allah kinan..? A nan naɗe kamar tsohuwar manya! Aikin banza in aka ce maka Mutum ba kanshi kallo ba. fa ka banu!”

Sumayyah ta ɗago kai cikin hawaye, ta ce cikin murya mai rauni,
“Baba Hauwa na yi kuskure ne? Ina tsaye ne ko zaku buƙaci wani abun kar ku kira kuji bana kusa”Baba
Zulai da ta biyo bayanta tana dariya, “Eh ai kin yi kuskure, kin haihu daga Rabi! Haka kawai, asalin ku kuskure,haka kawai kusa a riƙa kiran dangimu da masu cutar hauka!”

Da sauri Sumayyah ta rufe kunnenta da hannuwan ta, tana girgiza kai tace.
“Ya Allah, kai kaɗai ka isa, kai kaɗai ne mai ganin ɓoyayye.” ta sake buɗe ido ta da lokaci daya suka juya zuwa jajaye, ta ce
“Ya Allah maye laifina dan Na fito daga jikin mara lafiya?” tsaki suka buga Baba Zulai taja hannu baba Hauwa tace."Kin ga zo mu koma mar su san yana da wata 'yar baje ya lalace.

Da haka suka sake fadawa daki Malam, tana juyo muryar Alhaji musa da'awa yana cewa"Hajiya gashi kowa turmi biyu babu yawa”

Kamar Zasu kifa haka suka fara yiwa Alhaji musa godiya"Alhaji Allah ya saka ya kawo nasarori ya kaɗe hau da bala'i”Ciki isa Yake amsawa da haka suka miƙe zasu fita da sauri Baba Hauwa ta kaɗawa Yusuf ido tun da yaga ni ya gane me take nufi da sauri ya fita. A tsaye ya samu Sumayyah tana tsaye. Tsayawa ya yi daka mata tsawa “Ke tsohuwar muna fuka wato laɓe kika fara yi mana ko?” Jiki ta har rawa yake ta zube akan gwiwar ta ta fara magiya.

"Wallahi Yaya Yusuf ba laɓe nayi muku ba, ina jira ne ko”Wata iri kwarfewa ya yi mata ji kake ta faɗi ƙasa dabassss sai da jiri ya ɗauke ta balet ɗin jikin wando sa ya cire tare da jan ƙafar ta aƙasa sai da ya kaita ɗaki Baba Zulai kafi ya sakawa ƙofar sakata, dukan ta ya fara.

“Ni zaki karyata wato karya nake miki!Agaban baƙi zaki tsinka ni ko?”Kuka take tana neman agaji amma hakan bai hana Yusuf kilar taba kamar baiwa. Sai da yaga tayi lagab a ƙasa sanan ya buɗe kofar yana zuba uban gumi da kar ta miƙe ta fito atsaye ta samesu Baba Zulai ta lailayo Ashar ta maka mata"Kan bura'ubancan kayasa Mai zan gani 'Yar mahaukaciyya aciki ɗaki na Kai Yusu yanzu Dan tsiya ka rasa inda zaka kaita sai tura kar Malam?”

Baki ya cono uwa na gafiya ya fara yiwa Baba Zulai masifa“Haba Babar mu so kike na kaita wacan jujin ɗaki nasu salon kwalara ta kama ni, Ke duk abin da za'a miki ba kya
gani”Yana gama faɗa ya buga tsaki tare da cilli da bulala ya fice.tana kallon su Lubna da Safiya suna ta ɗaga kayan da aka kawo mu amma bata da damar zuwa ta gani har da lace ɗin da za'ayi yayi acikin ƙauye su wanan sallah, ɗaki Baba Hauwa suka ɗunguma tare da lissafi telan da zasu kaiwa ɗinki haka itama ta ja jikin ta da ƙar ta shiga nasu ɗaki.

Kwanan Sumayyah biyu tana kwance, jiki ta na ciwo ga mugun zazzaɓi saboda tsabar dukan da tasha guri Yusuf hakan kuma bai hana ta daina ɗaukar ruwa da wasu aiki gida ba, babu wanda ya damu da ita bare ta sa ran samu magani Ko da magani zazaɓi ne. Inna ce zaune sai kukan yinwa take, tana rera surutu na kiran abinci cikin muryar da take cike da soki burotso. Gajiya Sumayya tayi ta fashe da wani kuka, tana jin kamar zuciyarta zata fashe.

Da yamma Baba Hauwa ta shiga ɗakin inda Sumayyah ke kwance, gani har yanzu bata fito tayi sharar yamma ba,ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta tare da doka mata uwar harara babu tausayawa a cikin idon ta. “Ke Sumayyah..!wane iri sakarci ne ya hana ki fitowa kiyi mana shara kina kallo duk gyanye ya zubo ko dalili a fita ana zagi matan Malam ana mana kudi goro ana kiran mu da mahaukata gaba ɗaya?banda tugu da iya muna furci wanan ɗan dukan shi zai sa ki sharɓe wai baki da lafiya.”Sumayyah ta yi shiru. kamar yadda ta saba, bata mayar da martani ba. Haka Baba Hauwa ta ƙari faɗan ta ta tusa ƙeyar ta, har tsakar gida ta share gidan har da waje guri zanam karatu Almajirai wanda Malam yace Almajirai su daina duk Sumayyah ce zata riƙa yi.Da dare, bayan kowa ya kwanta, ta fito da ƙyar ta tsaya bakin ƙofar ɗaki. Tana sauraron irin maganganun da Inna ke yi tana dariya ita kaɗai.Sai kuma taji muryar Innar ta na cewa.

“Sumayyah, kar ki ji tsoro. Wata rana za ki san gaskiya. Wata rana haske zai shigo cikin duhu. Kuma ranar, zasu gane ke ba ‘yar hauka bace…”da sauri ta waiga ɗaki ta kallon Innar ta kafin ta sake motsi Inna ta sake buɗe baki ta cikin bacci ta ce.

“Ki kula da duk wanda zai zo miki da taimako, kar ki yi gaggawa. Ba kowa ke da zuciya tsarkakakkiya ba. Amma akwai wanda Allah ya rubuta zai zo ya goge miki hawaye.”da Bango Sumayyah ta jingina kanta na mata wani iri sarawa hawaye na gangaro mata a hankali, tana jin kalaman Inna kamar ana shigar da su cikin ranta ne da wuta.
Washe gari, tana zaune gefe guda a fili makaranta, Malama Ruqayya ta lura da tabon da ke gefen hannunta. Ta kira ta gefe. Guda inda Babu yara sosai tace.

“Sumayyah, wannan ciwon fa? Me ya same ki?”Sumayyah tayi ƙasa da idon ta, ta girgiza kai. “Ban sani ba Malama. Nima kawai gani sa nayi.”Malama Ruqayya ta jinjina kai, tana kallonta cikin tausayawa.“Ki sani, ko da duniya ta yi miki hukunci, Allah ba zai taɓa mantawa da ke ba. Idan akwai gaskiya a rayuwarki, zata bayyana-ko da bayan shekaru.”Sumayyah ta amsa da “Amin Malama,”Cikin murya mai sanyi. Amma zuciyar ta tana ta bugawa.

Ranar Asabar ta kama babu makaranta haka kuma lokaci tashi yayi daga makarantar allo fita tayi samo gwangwani madara saboda tana fafe su ta kai gidan masu Alala su bata kuɗi hakan ne ya faru da hanzari ta fita kofar gida, wata ƙatuwar mota ce ta tunkaro kofar gidan Malam Giɗaɗo baƙa kana gani kasan atajirai ne aciki.
Wasu mutanene su uku aciki, suna neman gidan Malam Sule Giɗaɗo. Kallon farko da Sumayyah ta yi musu, ta ji zuciyarta ta rikice, hankali ta bai kwanta da na gaban ba, Gashi baƙi ga muni tsiya tunda ya kafe ta da kallo ya kasa ɗauke idon sa akan ta,sanye yake da farar shadda, kana gani sa zaka san bashi da imani sai kato ciki kamar an kifa ƙwarya. Gani Sumayya tana ƙoƙarin wuce su ya washe baki tare da ɗaga mata gira ya yafito ta da hannu.“ 'Yan mata ina kuma zaki zo mana muna da tambaya ne”Sai da gabanta ya fadi dan Muryar sa ko daɗi sauraro babu. Jikinta na rawa ta matsa baki motar turo kai ya yi kamar zasu haɗa Fusakar kana jin tashi turare sa kasan na 'yan Duniya ne, muryar sa ta sake ji"Da alama sauri kike? in baza ki damu ba Gidan Malam Sule Giɗaɗo muke tambaya”

Sai da ta yatsina fuska kafi tace“Eh... Ga gidan kunzo”dogo hannu ta yabi da kallo wanda chocolate ne duk jirwaye ruwa ya kama hannu, gargasar hannu ta ita ta luluɓe datti hannuta. Ƙoƙarin buɗe motar Yake tare da cewa“Da dai zaki ƙarasa ladan ki ki mana Sallama da shi”Ji tayi kamar ta ɗora hannu ta fasa ƙara.“Subhanallah…” ta furta a hankali, tana ja da baya.Sai dai kafin ta sake magana, Yusuf ya fito da sauri, ya ƙaraso gare su yana zabbga mata harararta.“Ke wai wace iri shasahar yariya ce,anya ba baƙin ciki kikewa Babanmu ba?In ba haka ba tun ɗazu bayin Allah nan suke tsaye suna tambayar ki kina ya ƙuna su sai kace 'Yar wata cikakiyar mai hankali” Bakin Yusuf har wata kumfar masifa yake,Shikam Alhaji ɗan gambo wanda yake ji tamkar ya kamo Sumayya ya mana a ƙurjin sa ko ya samu sauƙi haka yake ji, wani abu ya raya acikin ransa sanan ya juyo cikin nutsuwa da ya aro wa kansa, ya kalli Yusuf.

“Ka bari ta tafi, ɗan uwa maibi uzuri ta mai ƙarfi ne,” ya faɗa cikin murya mai taushi, kamar na Allah.dariya ya yi tare da tsara kalamomin da zai ɓata Sumayyah guri wanna hamshaki mai kuɗi.

"Ranka yadade Uzuri ta na banza, ai kufi uzuri nata daraja jakar banza sai wari tsiya ka ganta nan sai ta kwashe mako huɗu ba tare da ruwa yaga jikin ta ba....







*Up up up azo Amin comments da Shering da like Yan amanna akwai abubuwan nishadi fadakarwa dakuma tausayi acikin rayiwar Yar mahaukaciyya*
[10/29/2025, 7:19 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a



*📚 🌸 'YAR MAHAUKACIYYA 🌸📚*


Mallaki:
Husaina S. Abdullah (Oummu Muwaddah)
📚 © 2025 – Duk haƙƙoƙin mallaka na musamman ga marubuci.




_______________free book __Page -3



Alhaji Sa'idu (Alhaji Dubai) ya yi murmushi mai cike da kwarewa ta 'yan duniya, yana kallon Sumayyah da idanuwan da Na cikakken ɗan bariki San nan ya juya ga Yusuf cikin murya iri ta mutane ƙwaraiya ce.

“Yaro, ka kira min Malam Sule, ka ce Alhaji Ɗan Dubai ne ne yazo. Ina son ganinsa.” tun da Yufus yaji sunan da yayi fice a Lagos ya haɗiye miyau.jikin sa ya hau ɓari “To Alhaji, yanzu nan,” ya amsa cikin rawar jiki.gudu da sauri ya haɗa kamar wanda yake ɗauke da saƙo daga sarki.Yana isa Baban zaure sallamar baki, ya tarar da Malam yana karanta wani hatimi,Yusuf ya tsaya daga ɗan baya yana huci saboda gudun da ya yi, ya ce,“Malam... Malam! Yau da kayi baban Kani Alhaji Ɗan Dubai ne yazo... yana waje!”Kafin Malam ya maida
numfashi, hannunsa ya fara rawa. Hatimin dake hannunsa ya faɗi ƙasa, ya ɗago cikin tashin hankali. Da wata iri murna yace."Ka tabbata Yusufa ko dai idon kane Alhaji Ɗan Dubai da na lagos?”Baki Yusuf ya sake wage wa ya ce“
Allah Baba Alhaji Ɗan Dubai dai wanda kasani ɗin nan na Legas! Motar sa ma tana nan a waje, har da mutane biyu tare da shi.”

Malam Sule ya miƙe da sauri, jikinsa na rawa kamar wanda aka tsikara da wuta. Ya fara tafa hannaye yana bulin-bulun da babbar riga tare da ambaton “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” cikin muryar farin cikin kamar ya cashe da rawa.

Ko da Sumayyah ta tafi ta samu gwangwani madarar ba sai yara da suka kusa tura ta su maida ita mahaukaciya da gudu ta shiga gida ta kofar baya har da Masu jifan ta.

Takalman sa Yasa hagu da dama tare da cewa.
“Allah ya kawo wannan rana! Kai Yusuf, zo muje mu tarbe shi! Kai yi tsaf ka gyara rigar ka, kasan masu damar nan basa so ƙazanta. Wannan mutum ne da idan ya taɓa mutum, sai ka ce alheri ne yake zubowa daga sama!”

Yusuf ya gyara rigarsa da wandon sa da sauri, yana kallon Malam da murmushi mai cike da yaudara. “Malam, Allah ya kawo lokacin ka kenan amma ya kamata amin baban Kasafi?. Wannan Alhaji Ɗan dubai ɗin fa mutum ne mai alheri sosai dan cewa akayi kyautar mota da gida aguri da ba abu ne mai Wahala ba,sanan naji ana cewa yana taimaka wa malamai. Sosai Bari ma in buƙatun sa suka biya” Dariya
Malam Sule yiyi ya shafi fari gemu sa, ya gyara rawani kansa, ya ɗauki misbaharsa da ƙamshi mai ƙarfi ajiki.suka fita Kofar gida.

Saboda ya nuna isa da cewa shiga malam ne na gaske sanan ya yi wa Su Alhaji Ɗan Dubai bazara yasa shi cokewa ya bawa Yusuf izini yaje ya taho dasu,yana zuwa Yusuf ya yi musu jagora, ya durƙusa gaban Alhaji Ɗan Dubai har ƙasa abin da ko malam baya yiwa ya ce.“Ga shi can Malam ɗin.”Alhaji Ɗan Dubai ya miƙe daga jikin motar da tulu ciki sa, ya ɗan gyara igar sa tare da cewa abokan cin mushe sa.“Alhaji Dollar, Alhaji Iri bisimillah”suna Isa gaban sa Alhaji Ɗan Dubai har da cire takalma kamar su haɗa baki suka ce“Assalamu alaikum Alaranma barka da warhaka!” ya tamkar mutumin ƙwarai.hannu Malam ya miƙa ciki Murya manya yace.“Wa alaikumus salam warahmatullah!”cike da nutsuwa, amma jikinsa har yanzu bai daina rawa ba“Wallahi Alhaji Ɗan Dubai nake gani tsaye a gaba na! Na dade ina addu’a Allah ya haɗa mu, yau kuma ga shi ya cika!”Sai da Alhaji Ɗan Dubai ya saba ƙato tubisa kamar me tsohon ciki kafi yace.“Alhamdulillah, Malam yau gashi Allah ya haɗa”

Hannu Kalma ta sake bashi "A...Almajiri malam dai ai nasha gani ziyarar da kake kaiwa Manyan Malama iri su Malami buzu da sauran su wane mu” Dariya Alhaji Ɗan dubai ya yi ya kiftawa Alhaji Dollar ido sanna yace.

"Allah gafarta Malam na zo ne da saƙo daga gwamati te makawa malamai wanda ake kaiwa gari gari dan inganta masallatai shine mukayi tambaya akace ai guri ka zamu zo.”wani iri Farin ciki ne ya kama Malam giɗaɗo yasan zai ci kuɗi afili kuma gemu sa ya shafa yana furta"Masha Allah, Allah ya yi albarka ai inda zamu riƙa samu mutane iri ku da duniya ta zauna lafiya 'yan Aljana iri ku basu da yawa.” kai suka jinji Alhaji Ɗan Dubai ya sake cewa.

"Allah gafarta Malam Amma kuma, akwai wata magana ta daban da nake son muyi a sirri.”
Malam giɗaɗo ya haɗiye miyau, ya ɗan sunkuyar da kai. “A’a, babu matsala, za mu iya shiga ciki.” a tunani sa wani mugun hasafi zai sake masa asiri saboda idon mutane ya bukaci su kebe guri guda.
Yusuf ya sa a gaba yana nuna musu hanya, yana ta murmushi saboda yasan wannan ce damar da zai kashi rabon sa.
Suna shiga, Alhaji Ɗan Dubai ya zauna a kan babbar kujera, yana dube-dube da ido irin na mashuran masu kuɗi.Ya ɗan ja numfashi, Malm yana zuwa kan wani kato buzu ya zauna tare da tankwashe kafafu sa.ya yi gyran murya da matsar da tawada da alkaliman da suke bahe akan buzu.

Nutsuwa Alhaji Ɗan Dubai ya yi shida amini sa sannan ya ce cikin ladabi da sai ka rantse mutumin kirki ne.
“Allah ya ja kwana, wannan yarinya da na gani a waje nan, wacce Yusuf ya ce ‘yar gidan ku ce…? Ta kace itama?”
Malam ya ɗan karkata kai, tare da tafiya dan nazari Alhaji Ɗan Dubai ya katse masa tunani da cewa.“Naji kamar kamar ya ce Sumayya ko sakeena.!!”Ya fada yana satar kallo Malam. Hannu Malma ya tafa“O..O.. Sumaiyya kenan itama yariyar Guri nace sai dai mahaifiyar bata da hankali zargi da muke itama abin ya shafe ta har tayi suna ma dan Wani sa'ilu sai kace gidan su 'Yar mahaukaciyya zava kawo kanan.”farin ciki ne ya cika zuciyar Alhaji Ɗan Dubai fall da da alamu bazai sha wahala ba guri samu abu da yake so. ya lumshe ido, ya dan jinjina kai yana murmushi.“Toh… jinƙai kenan,” ya ce, yana duban Malam da wani murmushi mai ma’ana.
“Allah sarki Allah gafarta,na lura akwai wani abu a cikin idonta… sai naga kamar tana ɗauke da wata hikima da ba kowace mace ke da ita ba.” ya tsaigata dan yaga yadda zasu ɗauki maganar tasa.Malam ya yi dariya kadan.“To ai duk hauka tana da nata hikimar, Alhaji. Amma dai ka bar wannan, meye saƙon da kake tafe da shi?”Alhaji Ɗan Dubai ya zaro wata envelope daga aljihun rigarsa. Ya ajiye a gaban Malam Sule, yana murmushi da ladabi.

“Wannan kuɗi ne na godiya, saboda addu’o’inku da taimakon ku da kuke yiwa malamai da almajirai. Kuma akwai wata ƙaramar bukata… amma sai in ka amince kuma akawai tari alkairi aciki.”
Malam Sule ya yi saurin ɗaga envelope ɗin da hannunsa yana dariya. “Subhanallah! Alhaji, kai fa mutum ne da Allah ya albarkace! Bana jin akawai abin da zaka roƙa baka damu ba..!”
Yusuf da yake gefe ya kalli envelope ɗin da idanu ji yake kamar ya fusgo ta da ido, yana taɗe harshensa.Alhaji Ɗan Dubai ya lumshe ido ya dan ɗaga kai. “Akwai wata ƙaramar magana da nake son mu yi game da waccan yarinya da ke waje…”
Ya ɗan ja numfashi ya ce cikin murya mai sanyi amma cike da mugunta: sai da gaban Malam da na Yusuf ya buga fatan su kar yace zai haɗa ta aure da iyali da gasu Lubna da Sadiya can a gida., kafi suyi dogo tunani sake jin muryar Alhaji Ɗan Dubai.
“Malam, ina son ka bar ni in ɗauke ta na duba ta a Legas. Akwai wata dama da nake ganin zata taimaka mata... kuma kai ma za ka amfana.”Malam Sule ya tsaya cak. Kalmar “ina son ka bar ni in ɗauke ta” ta ɗan girgiza shi a farko. Ya ɗan gyara zamansa yana duban Alhaji Ɗan Dubai, sai kuma ya saki murmushi fari ciki da yaji ba batu aure bane.
“Alhaji, ɗauka kuma? Kana nufin taimako kenan ko ya.....?”
Alhaji Ɗan Dubai ya yi murmushi irin na mutumin da ya saba wasa da hankali mutane.“Eh, taimako mana, Malam. Kamar yadda na faɗa maka- yarinyar tana da wata alama ta hankali da hikima, amma a karkashin hauka da talauci. Ina da wata makaranta ce ta matan marasa gata a Legas. Ina so in ɗauke komi Ni zan ɗau nauyi ta a can, zata samu kulawa, ta koya ilimi, kuma ta taimaka ma kanta. Ba komai bane illa taimako sanan kaima zaka samu sauƙi ci da iyali.”
Malam ya ɗan yi shiru. A ransa ya fara hasashen kuɗi, kuma idanunsa sun rufe da abin duniya. Ya kalli envelope ɗin da yake a gabansa.ko makaho yasan kuɗi ne ba nawasa ba acikin envelope dinnan.
Alhaji Ɗan Dubai ya ɗora da cewa.“Ka kwantar da hankalinka, Malam. Ba tare da wani matsala ba, zan ajiye maka abin da zai taimaka wajen kula da sauran yaran ka da kuma makarantar ka ta, tsangaya sannan zan turo wasu kudade daban don kula da da mahaifiyar ta wace kace tana da matsalar kwakwalwa.” sai Yanzu Malama ya samu damar
zaro ido gani Alhaji Ɗan Dubai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login