Showing 54001 words to 56438 words out of 56438 words
Chapter 19 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt
kwana biyu Sumayya a sake murjewa duk wani haɗi magunguna anyiwa Sumayya da Sadiya Ummu kam Yar Sudan ta dauko dan ta gyra Sumayyah har Lubna tasa akayisa tayi kyau baki ta na kyau, Ammar kam tiri-tiri kira baya bari ta ta huta bayan Sallah karfe biyu shedu suka sheda aure Sumayyah da Ammar, Tanimu da Lubna abinci waja-waja Gidan Lubna ma ba laifi yayi kyau gida ne na zamani har da dan Gate dinsu.
Karfe huɗu aka zo ɗaukar Sumayyah kuka ta fashe dashi har da ƙanƙame Innar ta bazata tafiba, gajiya Abdullahi da Bazallah sukayi suka fita waje Ammar da ya maƙale amota yana gani su ya fito yana dogara Sandar sa.
"Ya naganku haka ina Sumayyah da yan uwansa?”
Bazallah da yazo har wuya dama shi abu kakilan ne yake tunzura shi yace.
"Wallhi Ammar bazan sake shiga gidan nan ba Yariyar nan duk ta narke ita auta wai bazata tafi ba Sai anje gobe kamar ba ita ba Haba na gaji ga matan ciki duk inda mukayi suna bin mu da kallo sai kace wasu...
Bai kai karshe ba Ammar ya bar guri cikin gidan ya shiga har ɗaki Inna ya shiga sai gani sa sukai
[2/12, 10:38 AM] OUMMU MUWADDAH: *YAR MAHAUKACIYYA*
30
*END*
DA sauri Inna ta mike saboda surukuta babu zato sai jie tayi an kama hannu ta kokari kaucewa tayi taji ya kara kamma ta,tare da kai bakin sa dai-dai kunne ta ciki raɗa ya ke mata magana.
“ Please ki tashi mu tafi itama Innar mu gobe zata koma zuwa dare sai na kaiki ki ganta”
Kai ta fara karkatawa alamu bazata ba ransa ne ya fara bacci karfi sa ya tattaro ya damoko ta ya yi samma da ita sauran matan da suke daki suka saka guda tare da dariya hannu ta ya kama suka fice daga gidan ko guri Baba bai nufa da ita.Mata biyu ne suka bishi Kanwar Baba sai makociyar su wace suke shiri da Innar Sumayyah.
Tunda suka dau hanya take kuka bai hana taba saboda mutane da suke ciki, suna isa gidan Abi part ɗin Ummu ka wuce da ita Ummu tayi mata nasiha mai ratsa zuciya tayi musu faɗa ita da Ammar, har da ita aka raka su part ɗin su dan abin yace baza su zauna a waje ba sai agida daya.
Bayan duk anyi abu da al'ada ta tanadar Ammar ya maida Sumayyah cikakiyar mace, sai dai tasha bakar wahala,ahaka ma dan Ƙafafuwan sa basu gama warkewa ba, Sumayyah ansha raki Ammar kam sai tarairaya yake, washegari Ummu ce tayi musu break fass
A gidan Malam kam Inna ta gama shiri ta tana kokarin saka hijab ɗinta sai ga Malam kamar an jefo sa Da sauri ya zube kamar wani yaro da mamaki ta dube sa murya na rawa.
“Babar Sumayyah yana ga kina ta shiri hahaha ai nazata kin dawo mana gaba ɗaya.?”
Daure fuska tayi kamar ba ita ba."Ban gane ba Malam Tom wa na ajiye anan da zan zauna dama Sumayyah ce kuma bata nan kaga zama bai kama niba”
"Dan girman Allah Rabi ki taimaka min wallahi ina sonki dama can shari sheɗan ne ki sani Sumayyah baza ta ji dadi ba duk ranar da tazo gidan bata da guri wanda zata faɗa ya kamata amanta sa komi”
Murmushi tayi sanan ta zauna nesa dashi.
“Hmm Malam yanzu Sumayyah ai ba Yariya bace kuma duk yanayi da ta shiga abaya bai zame mata damuwa ba sai yanzu, zata saba insha Allah”
Rararafe ya fara kamar gurgu matsawa tayi ta kafe shi da kallo.“Haba Rabi mai yasa baki dauka shawara da hausa fa nake miki magana ina so ki dawo ɗakin ki shine magana”
"Uhum Malam kenan da farko ina mai baka hakuri magana ta gaskiya munyi magana da Alhaji Bashir aboki Mahaifi AMMAR ai nasan ka sanshi Tom bana so na zama karamar mace dan Allah kayi hakuri ”
Dan danan fuskar sa ta canja lokaci guda yaji kansa na juyawa yayi danasani gashi rabi ta dawo yariyar ta kamar lokaci da take budurwa farin ta ya dawo kyawu ta da yarintar ta duk ya dawo, cikin karfin hali yace.
“Shikenan Rabi ai baxan ja da mai karfi fa dama taya kina gani....
"A'a Malam kar muyi haka da kai dan Allah ka sani bani na guje kaba kaine ka fara duk kayi ƙoƙari zama dani a lokaci bani da wani anfani a guri ka na gode Allah ya kara arzikin da wata Allah ya bawa Yaya Zulai lafiya kamar yadda na samu tawa”
Kokari Magana take wani yaro ya kwaɗo sallama.
"Salamu Alaikum Wai Ace Babar Sumayyah tafito Alhaji Bashir ne yazo”
.ita kanta Inna sai da taji kunya saboda hakan kamar cin fuskane ga Malam ba zato taji yace.
“To..to... Kaje fatan kaji Yara manyan gobe sufa babu ruwan su Allah yasa dai mu dace”
Ameen ina tace tana mikewa Malam ya dauke mata Akwati bishi tayi jiki babu kwari a kofar gida suka ga Alhaji Bashi ya harɗe hannu sa Kan Ƙirji sa Mutun fari kyakyawa kana ganisa kasan Addini ya ratsa jiki sa, Bafilatani mai na gaske fusakarsa bata nuna yawan shekaru sa.
Gaisuwa sukayi ta mutunci tare da yiwa Malam ishani godiya. Da ƙamshi ya bude mata sai da tayi masa godiya sanan ta shiga motar.
Bayan Sati ɗaya yau bayan Juma'a aka daura Aure Innar Sumayyah da Alhaji Bashir wanda ya samu Halartar manyan mutane Abin ne wakili ta shikuma Kabir mahaifinsa.
Ammar ne ya shogo cikin gida Sumayyah na zaune ɗaya daga ciki kujeru Parlo goro ya jiye mata masur kyau da sauri ta dauka tana murna cikin nishaɗi ta ce.
"Beby na Kasan najima banci goro ba wallahi inaso goro”
Harara wasa ya mata tare da kama yatsar hannu ta yana murzawa.
"Beby na goro Aure Uncle Bashir ne fa.”
Kai Amma nayi murna wallahi dama tausayi yake bani Allah yasa dai wanan aure ya kawo masa shima nashi dan dan wallahi tausayi yake bani mutum har ya fara tsufa bashi da yaro ko daya, bawan Allah Mai kirki dashi”
Murmushi yayi tare da yi mata peck a bayan hannu sanan Yace.
“kika san waye Amraya”
Lumshe ido tayi tayi wa kanta masauki a jiki sa.
“sai ka fadan Ni ma ban sani ba”
Batare da wata damuwa ba yace."Innar Sarki haƙuri itace”
Da sauri ta raba jiki ta da nashi hawaye ta fara ciki mamaki yake binta da kallo gira ya daga mata.
"Lafiya me kuma aka mai ki, da ga fadi abin fari ciki sai ki kama kuka”
“Haba.beb yanzu saboda Allah taya Inna zata yarda ta aure shi wanan sai ace son kan mu yayi yawa Wallahi Ni yanzu zanje na same ta”
Daure fusaka Ammar yayi.
"Tab ɗin jan Kaji mu da yariya Tom aure dai an daura kuma tun da kika ce haka ba zaki fita ba bare kije ki daga mata hankali ko kin fiso tai ta zama babu aure, kuma Inna ai baza a sata sahu wanda zasu hakura da aure ba banda ma Rabo ai bata isa haifar kamar kiba”
Ya karasa fada yana kokari kamota da sauri ta jaye jiki sa tara hararar sa murya ya daga.
“Nafita kinsan abu namu sai inda mai ya kare”
Wuni ranar zuciyar ta babu dadi ita gani take kamar za ace kwadayi duk sun aure masu kuɗi ammar kam sai 11 ya dawo lokaci har ya fara bacci.
*After 10 month*
Parlour sai tashi hayani kasa kasa Parlo ya gaji da haduwa gana gani kasan an kashe kuɗi Ammar ne sai Ummu a gefe da Sanan Fu'at da Matar sa Jamila sai Inna Yara ne jarirai ne ɗaya Hannu Ummu ɗaya hannu Sumayyah kyawawa ne masha Allah Inna ce ta ke saukowa ita Da Alhaji Bashi daga samma ciki kauna suna zuwa Alhaji Bashi ciki wasa yace.
“Ranki ya dade Amarya Alhaji Kareem Allah ya ja kwana da sutura daga ke babu kari”
Dariya tayi.
"Yaran ka dai na jinka kai baka gajiya da zolaya kuma waye ya hana ku kari aure aini na jima da yarjewa dan-dai aboki naka kamar tsoro mata yake”
Ammar da Ya saba da jin iri wanan wasan nasu tsamma ya tashi ya koma kusa da Sumayyah peck ya manna mata ita da jariri sanan ya mannawa kato ciki ta.
“Beby niƙan bazan yi iri ta Abi ba kina haihu zan sake aure so nake gidana ya cika da yara.”
Naushi ta kai masa a ciki ya saki kara.
“Ashhhh Ummu Yariyar nan zata kashe ni”
Harara Ummu ta masa.
“Ammar Akwai abin da kamata da bata maka ba”
Baki ya bude zai fadi abin da suke da sauri fara rufe masa baki dariya yake yana cewa."Ummu wai dan nace Ni da wuri zanyi wani aure shine da zata illa ta miki Auta”
Kunya ce ta kama Sumayyah tayi kasa da kanta Bayan Alhaji Bashir ya fita taho da kani sa wanda rabon sa da Nigeria Shekara goma sha uku yau yake dawowa saboda yayansa ya samu karuwa wanda tsayi rayuwa da shekara siti da biyar bai samu raboba har Allah ya amshi ran matar sa wanda tsayi shekara goma bai sake aure ba Sai yanzu da ya auri Inna ta haifa masa yara biyu duk maza.
Bayan fitar da babu jimawa Ammar ya dawo kusa da Sumayyah.
"Beby na tashi mu tafi gobe kya dawo”
Narkewa tayi.
"Beb inaso gani Uncle Sagir da Aunty Rahama yanzu fa zaka gansu dan Allah”
Kusa da ita ya koma"No Beby na gaskiya yau nazo har wuya Wallahi bazan iya jira ba,in kuma zakiwa Inna magana sai ta bamu daki shi....
"Duka ta kai masa da sauri ya kauce matsowa ya sake zata murɗa masa hannu yakai ya dauke jariri Jamila ya mikawa ya koma zai dauki Sumayyah tana gani haka ta mike tana mita Fu'at da Jamila dariya suka rika musu Da haka suka yi musu Salama.
Suna fita ko 30 minute basu da tafiya ba Sai ga Abba da Uncle Sagir sai Matar sa Maryam da yaranta, Sagir.na matsawa Fusakar, Maryam ta fito Da sauri Inna ta mike Itama Maryam jikin ta na rawa tace.
"Ya...ya..Ra..bi”
Inna kam kuka ta fashe dashi." Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun da gaske ne ba mafarki nake Ba Maryam ɗinta ce tabbas itace ashe zan sake gani iri dangi na A duniya”
Da gudu Maryam ta faɗa jiki ta ta saki kuka mai tsuma zuciya kallo su suka fara da son sani inna tasan Maryam Ummu kam cewa take badai Inna ita yar gari su Maryam bace sai da suka juna sanan suka samu nutsuwa ciki dashashiyar Murya Inna tace.
"Maryam ya akayi kika kubuta bayan kaf yan ƙauye mu babu wanda ya kubuta ke ya akayi kika kubuta bayan gobarar da akayi?”
"Yaya Rabi kafin gobarar ta tashi kinsan yadda nake da ammaki bayan na fito naje nayi fitsari da haka na fita saboda babu ƙyaure a kofar shiga gidan mu hakan yasa nayi tafi naje gidan maina na kwanta babu jimawa gobara ta fara cin gidaje wanda han guri da nake kwance saboda karan da aka ajiye saman soro sai da ya kama ciki iko Allah na farka da na ina tari ina gudu har nabar ciki gari ban samu kaina ako ina sai a baban titi daga haka ban sake sani inda kaina yake ba sai aguri Uncle Bashir wanda ya kaini Asibiti bayan farfaɗo wa ta yake sanar dani babu wanda ya rage aciki kauye, nayi kuka kamar bazan sake samu wani farin ciki arayiwa taba amma silar da ya mai dani tamkar yar da ya sani makarantar masu kuɗi ya inganta rayiwa ta bayan na isa muzali aure ya aura wa kani sa saboda baya so wasu su tozar tani”
Babu wanda bai tausayawa Maryam ba da dada jadada godiyar Alhaji bashir da karamci iri nasa, sun jima kowane yana bada labari yadda rayiwa ta zame masa, addu'a babu kalara wace basu yiwa Alhaji Bashir ba.
Tun adare Inna ta bawa Sumayyah labari Maryam yar kani mahaifi tace uwa daya uba daya wanda suka taso gida ɗaya, murna sosai Sumayyah tayi tasamu abokiyat shawara tun Asuba Sumayyah bata koma bacci ba dan so take taje taga Aunty Maryam.aji Ammar ya rika ha mata wanda sai da yaga ranta ya fara bacci sanan ya shirya suka tafi.
.bayan sati ɗaya anyi sunan yara sunci suna Baban Inna da Maihaifin Abba (Alhaji Bashir) ana kiransu da Waleed da Walidi.
Bayan wata uku Sumayya ta haifi yariya mace wace taci sunan Sadiya An kashe kudi bayan wata Uku Baba Zulai Allah ya mata rasuwa, Yusuf kam abu ya gagara sai zaman daki yake, Lubna ta haihu ta haifi yaro namiji yaci sunn mahaifi Tanimu, Ammar ya hudewa Malam shago sai dai bayan wata shida shago ya kama da wuta komi ya kone.
Bayan Shekara Uku Inna ta sake samu mace Taci runan Mahaifiyar ta, Sumayya kuma ta samu yaro na miji wanda aka sa sunan Abin, Rayuwa ta juya Sumayyah ta sahi daga Yar mahaukaciya ta zamar abar so da mutane kauye Gidaɗo har fata suke suga Sumayyah yar mahaukaciya saboda tari alkairi da takawo kaye Gidaɗo har Titi Abi yasa gwammna ya musu an kawo musu ruwan sha da wutar lantarki cigaba sosai suka Yar mahaukaciya ta a kawo musu.
Bayan shekaru goma sha biyar Kasan da Husaini sun zama samari Sadiya ma ta zama budurwa kamar yar shekara Ashiri a nutse take Haka kani ta Fadil Ammar an zama uba zaune suke a Falo Fadil na rokon Ammar ya siya masa mashi, da haka Sumayyah ta shigo da tsoho cikin ta da sauri Fadil ya koma jikin ta.
"Please Mom dan Allah kice Dady ya siya min Mashi Allah bazan yi gudu ba”
"Wallahi Daddy karka siya so yake suyi riƙa hauka dasu Uncle Hussain”
"Mom ki rabani da Yaya Sadiya ciwo hassada ta ya motsa”
Ya tsina fusaka tayi saboda ciwo da yake tsinkina ta.
"Abban Sadiya Dan Allah ka sai masa na huta da matsa jiki da yake”
Mikewa Ammar ya yi ya zo inda take.
“Mai kyau lafiya kike?”
Kafi tayi magana marar ta ta riƙe da sauri ta riƙe shi Kuka Sadiya zata yi ya hanna ta Da sauri Fadil ya fita ya bude mota Ammar kuma ya yi samma da Sumayyah ta yana zuwa ya aka ta aciki Hospital suka wuce babu jumawa ta haifi yara biyu duk mata murna babu kalar wace Ammar baiba haka Inna da Ummu.Ranar suna sunci sunan Ummu da Inna.
*Tammat bihammdulla Ina me nemann yafiya da Afuwar duk wani kuskure da kuka gani na ciki litattafi yar mahaukaciya domi dan Adam ajazi ne,Ina rokon Allah ya yafe kuskure da nayi abin da yake na dai-dai Allah ya bamu lada baki daya Ina mai bada hakuri na rashi Editing na wanan book gaba daya zaku ga littafin ba anutse na yi shiba*
*Idan mai Albashi da Wanda suka biya kudi book ɗin gidan Baba Jibo in sha Allah biyu ga ramadan zaku samu dacomments din book ɗi*
~Nagode Nagode nice taku har kullum Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah)~