Showing 51001 words to 54000 words out of 56438 words

Chapter 18 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

11

sanan Yace.

"Duk yadda Ummu taso kice Ni kike so Ni zaki aura kinji in tace mu haɗu kice tun farko dawowa na bamu haɗu ba”

Ido ta zaro waje.

"kai Yaya Ammar karya da kenan tasan fa ina zuwa kawo muku abinci.”

"Haba Sumayyah karyar ceto Ammar ne fa dan Allah kice zaki yi”

Kai ta ɗaga masa da sauri yace.

“Yawa Oya Let's go”
Fita tayi shi kuma yabi makeke gado ya kwanta yana lumshe ido akan ido Fu'at Sumayyah ta fita da sauri ya faɗa.

"Wallahi Ammar ya kusa tona mana Asiri yanzu da Ummu ta fito ta same ku fa”

“Sai kuma gashi bata fito”

Tsaki Fu'at yayi ya zauna.

Kitchen ta koma ta dauki Abinci Innar ta shiga nasu bedroom turus tayi gani Innar ta har ta gama cin nata ta idar da Sallah magarib jiki babu kwari ta zauna.

"Inna ta wai har kinyi me?”

“Ke gafara ki bani guri wai ina kika shiga ne Ummu ta turo kiran ki bakya nan”

Dariya ta ƙwakwallo.

“Wai Ummu har ta manta ta sani kwaso kaya baya shine da naji isakar guri tamin dadi na zauna”
Shuru Inna ta mata bata sake cewa komi ba.

Bayan Sallah Isha Ummu ce ta shigo ta same ta tana gyarawa Innar ta guri kwanciya tun da ta ganta Gaban ta Ya faɗi,

“Sumayya aiki kike Oya kawo Abi na Compound ina jiranki zaku tattauna”

Miƙewa Sumayyah tayi tazo gaban Ummu ta zube.

“Ummu dan Allah kiyi hakuri akan abin da Zakiji daga baki na Wallahi bazan iya aure Abi ba Ina masa kallo uba ne, Ummu ya kamata aduba iri halin da Ammar zai...

“dakata Sumayyah shi Ammar ɗin bai duba iri Halin da kika shiga ba ya auri yar uwarki dan Haka mun gama magana babu fashi gobe in Allah ya kamu za'a ɗaura aure duk wasu surutu ya ƙare.”

Ƙara Sumayyah ta gunza.

“Wayo Allah Shikenan zan mutum Dan Allah ummu an karki rabani da Ammar Ni wallahi shi nake so dan Allah ki tausaya mana”

Cak ta tsaya tana kallo iko Allah yau Sumayyah ke magana iri haka tabbatar Akwai sanya hannu ammar dan ta lura kullum yana yana saka mata dance Sumayyah tana basarwa wato shine daga ji maganar aure shine shi kuma zai yi mata tasa huɗubar.da sauri ta ajiye blanket ta fice, Inna da take zaune kam kujera tana kallo iko Allah ta mike kiran Sumayyah tayi tana zuwa ta dauke ta da mari.

Tana murɗa handles ta samesa a tsaye fitowar sa daga wanka kenan. Daure fuska tayi.

“Ammar me kace da Sumayyah, shi ka manta Maihaifinka ne yake nemana aure ta”

Sai da Ammar ya rintse ido tare da Haɗiye yawi mai ɗaci kamar bashi ya ce.

“Ummu akan me kike magana me Sumayyah tace wanda na zama abin tuhuma?”

"Wallahi Ammar zai mare ka kar kaga baka da cikakiyar lafiya Yariyar nan ta amince tun da jumawa yanzu kuma tace ba haka ba.”

Kamar yaro goye ya kamo Hannu ta.

"Haba Ummu Com down Wallahi I don't know ko Fu'at zaki tambaya ji da ita bamu magana”

Zama tayi kan kujera ta daidaita Muraya.

"Ammar dan Allah karkayi haka ne yasa kake so mai damu kannu mutane.”

Zama ya yi yadda da gaske zata yarda dashi yace.

"Ummu da kuna maganar ku dazu nasa muku baki?”kai ta girgiza."Tom me yasa baki yarda dani ba ki faɗan ita fasawa tayi?”

"Ammar na shiga Ruɗani taya za'ace Mun gama magana yanzu dakar nasa abi ɗinka yayarda zai je Compound wai dan su fuskanci juna Amma ina zuwa ta furje wai ita akwai wanda take so bashi ita Uba ta ɗauke shi.

“Tom ummu ku barta mana yanzu fa ko dan da ka haifane ba'a masa dole kuma shi kanshi Abi fa cewa kikayi daƙar kinga kenan baya murna da Haɗi kawai kubuta wanda take so.”

miƙewa tayi a zafafe

"Wallahi bazai yuyu ba Sai dai na sauya mata da Fu'at dan Wanda take so har yanzu bata rashi nikaum”

"Wane ya faɗa Wallahi ummu ina sonta a kullum santa karuwa yake Please sai yanzu saki fuskanci damuwar Ɗanki Ummu”

Sai da ya faɗa kuma yaga ta gafe shi da kallo kame-kame ya fara.

“uhum..Ahhh.ummu kada fa kimin mummunar fahimta bawai yana nufi nine na zuga ta ba”

Ficewa tayi bata re da tace komi ba.

Dafe kumci ta tayi wasu waye masu zafi suka shiga gangaro mata.

“Sumayya kin manta Halaccin Ummu a gare ki,ki tari tsabar ido ta kice kin fasa so kike duniya ta zage mu so mu zama masu don kanmu, me yasa baza kokari rama halaci ba.”

Ciki kuka Sumayyah tace.

“Inna ta In har Zan kamanta Adalci da kaunar, Ammar ya kamata na nunwa yayi ɗawainiy dani ya jefar rayiwar sa ciki haɗari duk raboda Ni kisani ciwo da ya affaka da Cin zarafi da akayiwa Sadiya duk nice Sila Dan Allah Inna ta ki bari ko yaya ne na zauna da Ammar na kamanta kaunar da sadaukarwa da ya min”

Tana faɗi haka ta zube a guri ta saki kuka mai tsuma zuciya.

*BANFAI*

Alhaji Ɗan Dubai ne da shi da tawagarsa aka tsaryar dasu gefe guda kuma Asp Muntaƙa dunbulum ne aka kafa masa camara bayani ya fara.

“ Assalamu alaikum kamar yadda kuka sani suna Asp Muntaƙa dunbulum mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jahara kano wa ɗan nan mutane da kuke gani ana zarginsu da aikata manyan laifika karkashi sashi na ɗari uku da goma shabi..gamar yadda kuke gani sun shiga gidan mata da miji ta sun aika fade tare da zubawa miji poisoning wanda sukayi kokari hallaka mijin a karshe matar tarasa ranta”

Juyara da Canada akayi kan Dama.

“Kai zaka iya fada mana yadda akayi kuka shiga gidan da dalili zuwanku kuma me yasa kuka aikata hakan?”

“Ni Alhaji Ɗan Dubai ne ya bamu kuɗi shi ya kaimu gidan ma tare da kashe mana wutar gidan sanan muka shiga shi ya faɗa mana yadda zamu in mushiga mu bamu tunani shi Namiji zai rayu ba”

Akayi daga kan Dama aka maida kan Alhaji Ahmed Ɗan Dubai nan ya bada labari duk abin da ya faru da dalili yi musu haka.

Bayan sati biyu kotu ta yanke musu ɗauri rai da rai sanan kutu ta bada umarni ake gidan da ya ke aikata haramci sa arushe gidan a gina kato masallaci.Soaai Alhaji Ɗan Dubai ya shiga tashi hankali atunani sa bazai jima ba zai fito sai gashi babu wanda ya nemeshi gudu kar sunan su ya baci.

Ta jima tana kuka hakan ya sa Inna ta jin babu dadi, a hankali ta jata jikin ta ta fara rarashi ta, cikin shasheƙar kuka tace.

“Inna dan Allah karki rabani da Ya Ammar wallahi har yanzu son shi bai dishashe a cikin zuciya taba, Ban taba Kallo Abi a matsayi Wanda zan Aura ba sai Uba Agare ni taya zan iya rayuwa da mahaifina matsayin miji”

“Shikenan naji Allah yasa hakan ya zama alkairi gobe In Allah ya kaimu zan koma Giɗaɗo zan nemi mahaifin ku da ya sauwaƙe min dan Bazan iya zama dashi ba in Allah ya kaimu zan nemi haya ko wanko ne na rika yi”

Sai da Sumayyah ya buga lokaci da ta furta rabuwa duk da tasan babu zama a tsakani ta da mahaifi nata.nisawa tayi tace.

“Inna dama...Fa..Uhum. Babanmu tun lokaci Bikin Sadiya Baba Zulai tasa ya sauwake miki yanzu babu sauran zama atsakani ku baki ga bai taɓa zuwa duba ki ba”

Ta faɗa ido ta na cukowa fall da hawaye, Murmushi tayi ta shafa bayan ta.

“Auta Karki damu Allah yasa hakan ya zame min alkairi Amma duk da Haka gobe zan koma can na nemi gidan na zauna kafi ta Allah ta kasan....

“Dan Allah Inna ta ki daina faɗi haka in kika barni dawa Zan Rayu? bani da kowa faɗi duniyar nan sai ke?”

"Haba Sumayyah ki dan Mutuwa dole ce ko mu dade ko mujima dole wataran sai mu tafi”

"Insha Allah Inna ta Bayanzu ba Sai na tara kudi na biya miki Aiki Hajji ki ga iri 'ya'yayana”

Duk hirar da suke Ammar yana ji su lokaci ya fito ɗauka abu A parlour da yake manne da Ɗakinsu.

Washegari Ummu ce da Ammar sai Fu'at zaune A parlour magana suke duk da babu wanda yasan me suke tautaunawa guri suka nema suka zaunar Sumayyah ta gaida Ummu Ammar da Fu'at suka gaida Inna.Duk yadda ya kafe Sumayyah da kallo amma taki kallo sa, bayan jim kadan Inna ta kalli Ummu tace.

"Hajiya dama yanzu nake cewa zan koma ƙauye mu saboda zama na bazai yuyu anan ba ga shiri biki Sumayyah”

Murmurshi Ummu tayi

“Inna in kin koma wa kike dashi Acan sanan Nasan da Ku rabu da Malam ammar kuma ɗaki ya mallaka miki gida Anan Tarauni dan Haka yanzu Fu'at zai kaiku ku gano babu wani gyara da Za'a masa sai dai abu da ba'a rasa ba Yau kuma Abi ya tafi shi da Abokan wa dan neman Aure Sumayyah.”

Inna taso ta nuna rashi Amincewa ta wai dakwai kyar tayi yawa Sai Da Ammar ya marairaice kamar zaiyi mata kuka sanan ta Amince.

Gidan Ba wai Babba bane sosai sai dai Ya mutukar haduwa komi a kwai aciki ɗakuna Uku ne Sai Kitchen duk wani Kayan more rayuwa akwai aciki kayan sawa ne babu, Godiya ta rikawa Fu'at kamar shine Ammar ɗin Sumayyah kam fita tayi tayi kukan ta ta more ta goge ta dawo suka wuce gida.

*ƘAUYE GIƊAƊO*

Lamarin Baba Zulai ya dada ta'azara dan Har duka take kaiwa almau hauka ya bayyana sosai banda Kashi da fitsari da take a kwance gashi kanta kam duk ta tsige shi da Hannu Malam kam komi ya tsaya Sai ya kwana uku huɗu babu mutumin da yazo bare ya samu abin rufa wa kai asiri, komai na duniya ya jagule masa, Yusuf kam Yau ya faɗa wani gida ya garƙama Sata sai da suka masa lulus sanan suka yasar da shi abayan gari bayan wasu kwana lalura ta bayanna ciwo kafa ne ya kama shi duka kafa biyu (Bone cancer) wace take zaizaye masa kafa duk yadda yaso Malam ya kai shi asibiti amma furr yaƙi yace ba ciwo Asibiti bane.

Bayan wata Uku malam yana zaune Almajirai sa duk sun gudu sun koma wasu garuruwa ya zubar tagumi masu zama ma duk sun daina yafa gani baƙi motoci har uku baisa ran guri sa aka zoba dan atunai sa Alhaji Namadi ne Makocirda yake tashe yanzu ya yi baki, gani motar ta tsaya kusa dashi da sauri ya mike gani Abi, Abi na fitowa ya karaso yana masa sannu da zuwa ciki baban Zaure aka musu shimfida suka zauna bayan sun tattauna Abi yazo da bukatar neman Aure Sumayyah akan Ammar bai isa yace A'a ba dan yanzu yayi nadama gashi baisan ida zai samu Sumayyah ba bare mahaifiyar ta yanemi yafiyarta duk ya iske labari Alhaji Namadi yace ya taba gani ta A yankaba su je siyan kayan miyya da Sumayya da wani yaro sai dai baiyi tunani a gidan su Ammar take zaune ba nunfasawa yayi yace.

"Ranku yadade ban tari numfashi kuba Saidai A halin da Ake ciki Bansan Inda Sumayyah da mahaifiyar ta suke ba Tun da akazo aka dauke mahaifiyar ta Itakam Sumayyah tun da akayi Sadakar Sadiya banasn inda tayi ba.”

Jinjina kai Abi yayi.

"Tom Ahalin Yanzu Sumayyah da mahaifiyar ya duk suna cikin ƙoshi lafiya sai da yardar su ma muka samu zuwa nanan”

Fashewa ya yi da kuka.

“Allah sarki Sumayyah Allah sarki na cutar da ita da mahaifiyar dan Allah ka kaini na roƙi yafiyarta Wallahi nasan Haki ta ke wahalar dani Komi ya cakuɗe kumi ya lalace yanzu Gidan Malami kamar Ni Ace sai mufi sati Uku batare da An ɗora ko an sauke ba”

Hakuri Abi ya bashi sosai kuma yaga nadama a fuskar sa a take a guri ya kira Fu'at ya sanar dashi ya kawo kayan abinci gidan su Sumayya, suna kokari an tsaida Ranar aure Sati mai zuwa saboda Abi yace ba sai ya yi komi ba shima Uba ne ga Sumayyah zaiyi komi, suna ƙoƙari tashi Kani Mahaifi Tanimu da na mahaifiyar sa suka zo dan neman Aure lubna soyaya su tayi karfi Kuma Tanimu yana da Nasibi a kasuwanci wanda Ammar ne aboye ya bashi Jari yace karya sanar wa da kowa hakan, albarka ta shiga cikin Neman sa a yanzu haka shago sa na kayan masarufi uku wadda yake makil da kaya, Hana su Abi yayi tafiya dama ya rasa wanda zasu zo su amshi kudi yar tasa wai mugun halin sa yasa kowa ya guje shi tare dasu Abi aka amshi kuɗi Lubna da sa rana wata shida abi ya yi magana.

"Ban tari nufashi kuba Amma zanso Ace an haɗa aure ta dana yar uwarta dan Allah amin wanan alfarma”

Kanin Mahaifin Tanimu ne yace.

"Alhaji Kasan shi yaro maraya ne Allah nema ya duba shi wani Yaro Ammar suruki Shi Malam Sule saboda temako da yayiwa Mahaifiyar Sumayya ya dauki Makudan kudi ya bashi Allah yasa masa albarka shine yake gini abin da yasa muka nemi wata Shida lokacin yayi dai-dai da gama Gidan sa da Yake kasan Abinka da Maraya babu matallafi Sai Allah”

Ya ƙare Maganar yana dariya.

"Nuna ko dan Saboda Abin da zanyiwa Ita Lubna dole sai nayi ɗan bige-bige zan so Bar nata wata shidan”

“Alhaji Bashir ne Ya tare zance.

“Insha Allah na daina nayi kayan daki yariyar duk wani abu da zava bukata na dauki nauyi”

Zubewa ya yi har kasa yana godiya,Abi yace.

“Kar ka damu shi kuma Yaro zan Sa Yaro na Fu'at yazo yaji abin da ba akarasa ba sai ayi insha Allah duk bazai gagara ba”

Godiya sukayi zasu tashi Yusufa ya fito yana jan gindi ihu yake tun ƙarfi sa Azabar ciwo na cin sa har ya dangana ga Baban Zaure.

“Babanmu kamin rai wallahi gara a yanke kafar nan da wanan Azabar”

Surutu yake yana kaiwa kafar yakushi duk da Ɗumamewar da guri yayi da wari amma Abi baiji tsantsamin saba haka ya kama sa ya sa Wasu mata sa da suka leko zaure kallo Yusufa su kama shi amota aka sashi zasu wuce dashi Asibiti Khalid aka kira daga guri leburanci da yake ya shiga ya riƙe Yusufa.

Basu tsaya ko ina ba sai Cikin Hospital dan-danan dashi wani ɗaki bayan wani lokaci doctor ya fito Abi ya sanar sai dai fa Acire kafafu dan duk sun tashi daga aiki, Malam yasa Khalid ya kira dan neman Amincewar sa, batare da shawara ba ya Amince, Abi ne da Khalid suka sa Hannu aka shiga dashi Tiyata.

Sai da Aka shafe awa biyu aka fito da Yusuf kafafuwan sa duk sun koma dungulmi ita guwar sa zuwa ciyarsa ne kawai bata taɓu ba, sosai Khalid ya dada mika lamurran sa ga Buwayi gagara misali, tare da Tasbihi.

Har bayan Sallah magariba Sumayyah dasu Inna basu dawo ba, Abi kam ya dawo ya sanar da Ummu halin da Yusuf yake ciki ya sanar ayi musu abinci a kai musu,ita ma Ummu ta tausayawa Yusuf bayan Abi ya haura sama Ammar ya kira Fu'at.

"Malam kana ina wai har yanzu baka dawo da Sumayyah ba”

"Gani nan zan shigo Parlour sai na gaya maka yadda mukai”

Zai sake magana sai ga Fu'at ya shigo da kallo tuhuma ya bishi ya gane me yake nufi amma sai ya share.

"Ummu sannu da gida”

Yawa Fu'at ya gajiyar ka Allah ya saka da Alkairi.”

"Ameen Ummu”

Zama ya yi yana kokari daukar romot ya dallah masa Harara.

"Ina Sumayyah kazo kake wani basarwa”

"Tana Gidan su mana kasan dai zamanta anan ai ya kare sai dai akawo ta Matsayi mata.”

"Me sarai kasan fa ba cikakiyar lafiya gare niba kuma sai ka barta acan taya zan rika zuwa hira kafin Sati”

Dariya fu'at yayi.

“Wallahi guy ɗin nan kana lokaci 1 week baza ka jira ba, sai ka tashi ka koma can da zama kasan Ummu baza ta lamuci haka ba Yawa gobe zanje gidan su Sumayyah zan kai musu abu sanan zanje guri yaro da zai aure yar uwarta ya bani sako,So Bazallah zai zo ya zauna dakai.”

Baki ya tabe ya ɗauki sandar sa ya haura sama,washe gari da wuri Fu'at ya shirya dai kai sako Abi dana Uncle Bashir murna guri Malam har da kuka, Tanimu ma da Innar da harda kuka basu san Wace iri godiya zasu yiwa wanan bayi Allah ba wanea ta silar Sumayyah da innar ta aka musu duk wannan alkairi.

Bayan kwana uku Aka Sallmi Yusufa an haɗa shi da Keke guragu da mashi Wanda yake an fani da na'ura godiya da neman yafi babu iri wanda Yusuf baiba Ana i kwana Biyu biki Ammar yasa aka gyra ɗaki Inna na Giɗaɗo har sabo feti akayi Shida Fu'at suka kaisu suna zuwa kofar cida Malam da Khalid suka kwashi kayan Inna dana Sumayyah suka shiga dasu ciki dandano mutane suka cika ana kallo Innar Sumayyah farin ta ya fito tayi kyau ta zama babbar mace.
Har Sumayyah zata fita Ammar ya yi sauri rufe kofar da sauri ta daugo ta kalle shi.Kafe ta yayi da kallo.

"Ina zaki ke ko iri kewar nan tawa baki ba kuma kina sani ki gudu ko?”

Ido ta fara kif-kiftawa zata magana cikin shagwaba ya dakatar da ita da cewa.

"Gobe masu Henna zasu zo da masu Mek up Sai kuma me kike buƙata?”

Lumshe ido tayi ta bude ciki shagwaba tace.

"Sai kai kaine bana so ka sake kubuce”

Hannu ya kawo zai kamata ta zame.

"Maye haka”

"Kome zaka faɗa ka faɗa amma banda taba ni”

Laɓe ƙasa ya cije sanan ya sake lumshe ido.

"Ammar naki ne har abada Insha Allah kamar yadda Sai mutuwa zata raba Abi da Ummu na nima ina fatan haka”

Zai sake magana ta fice tare da tura masa peck ta hannu, Murmushi yayi ya sa hannu kamar ya amsa ya manna dai-dai saitin zuciyar sa tare da kwanciya kan kujeran.

Tana sakar kafarta Baba Zulai ta fito ko zani kirki babu a jikin ta farce duk yayi zaƙo-zaƙo jikin ta kuwa duk sawu farata zube wa tayi tana kama Sumayyah.

"Mune muka muki asiri Ni da Sadiya ta muka aurawa Sadiya mijiki kiyafe mana nice Mahaukaciya me kashi a kwace, Ita Sadiya da ka take cin Abinci, Hauwa tana dariya da kafarta”

Gani Baba Zulai bata Hayacin ta yasa tayi mata dabar ta zame ta wuce Amina kuma ta kamata ta maida ɗaki Sumayyah kam har kuka tayi ta tausayawa Baba Zulai halin da take ciki.

Bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login