Showing 30001 words to 33000 words out of 56438 words

Chapter 11 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt

16 Mar 2026

22

sa. bata iya buɗe motar ba sai da yazo ya buɗe mata.yau ji tayi tana jin kunyar Hajiya.Sai da suka fara taku ya kalle ta."Yau ranar farko hajiya zata ga surukar ta nasan wanan ranar tafi mata rana dubu.”Tsayawa tayi
ya kalle ta cikin mamaki.“What happened? Kika tsaya”

Murza ƙaramin yatsan ta ta fara"Kabari maganar tayi ƙwari mana sai ka sanar da ita.”Taku biyu ya ƙara zuwa inda take ya kama hannu ta."Ki sa Aranki gobe ma ana iya ɗaura mana aure Hajiya buri ta kullum taga nayi aure atunaninki yanzu bazata amince ba ko bakya Sona?”Ya bita da wani fitinan nan kallo."Har abada bazan ƙi kaba”murmushi yayi ya manna mata peck a bayan hannu, suka ci gaba da tafiya da Sallama suka shiga ƙayatace parlour.babu kowa, guri zama ya nuna mata.

Shi kuma ya taka zuwa ma dai-dai cin Fridge ya buɗe ya dauko bottle water ya ajiye kan Centar teble da ƙarami Cup Na sulba"Kisha bari na kira Hajiya”Kai ta ɗaga masa taku yake mai cike da izza da jarumta bayan sa take bi da kallo wani sanyi na ratsa duk wani san-sa na jikin ta, tana ji farin ciki da bata taɓa jiba atare dashi. Handles ya murɗa tare da sallma Umarnin shiga ta bashi tana kan prayer rug da alama lafila tayi, gefe bed ya zauna tayi addu'a suka shafa tare."Ammaru har ka dawo ko babu nisa unguwar tasu?”Kasa ya dawo kan Carpet."Hajiya Surukar ki na kawo muki ta gaida ki.”Murmushi tayi"Ammar banso zolaya Ni ba kakar ka bace dan kaga abin da nake so gani a rayuwata shine kake so ka shiga zolaya ta dashi ko.”

“Ummu By God, I won't do it to you, I won't even tell you the woman I'm going to marry, otherwise I won't do it to you.”Murmushi tayi iri nasu na manya tashiga linke prayer rug ta maida saman Badeside drower,

“Muje na gani ina wasa kake min Ammar sai na cire kunne ka”Dariya yayi yana sosa kune da Hajiya ta kama. hannu su rike da na juna suka fita parlour. Sumayyah na hanngo su ta zube kan Carpet bisu take da kallo aranta tace."Dama nima Inna ta tawarke muyi rayuwar farin ciki tare duk da nasan badamu samu daula iri tasu ba ko hira da ita ne zairage damuwa...”

“Wa nake gani kamar 'Yata Sumayya?”Ƙasa tayi da kanta“Hajiya nice Ina Wuni?”Haba Sumayyah sauri kike ne haka?”Kafin Sumayya ta bawa Hajiya Amsa Ammar ya amshe zance."Hajiya Gulma ne iri nata wai dan nace zan gabatar da ita shine ga tun awaje takeso mu juya wai kunyar ki take ji”Dariya tayi.“Ai da kabar ta ni sai naje har gidakasan 'yata ba iri ka nace.”Ummu kenan har ki fara ware Ni tun yanzu?”Ya faɗa yana kafe Sumayyah da kallo itam dagowa tayi tana mamaki yadda baya jin kunyar mahaifiyar sa.ido su ya sarƙe da na juna kowane yana zubawa ido kowa wani siri.Hajiya ce ta lura da haka ta bugi ka faɗan Ammar."Zaka bata abincin ko sai ka gama ta kura ta.”Narkewa Yayi jikin Hajiya"Ummu me kika mana yau?”dambu shikafa sai Chips salad da kunu kankama?”Miƙewa yayi ya kama hannu Sumayyah Hajiya ta cilla masa kallo da yasan ma'anar sa, Da sauri ya saki nata hannu cikin borin kunya.“A....uhu.. Hajiya dafa taya ni zata Saboda Allah taya namiji zai iya aiki mata”harara tayi masa “lokaci da kake Shiga kitchen ka dafa abin da kake so na sani sai yanzu” Shuru ya yi ya shike kitchen, Warmer mai kayu ya samu ya zuba gasansu Naman kaji ya zuba ya rufe, yaje ƙato Fridge da yake shaƙe da kayan ciye-ciye dangi drink ya kwaso bottle water guda biyu sai dogo Cup wanda yake ɗauke da daɗe lomo Kwankana sai ƙamshi Citta yake ga wata muguwar raɓa ya fito, yana 'yar waƙa, gaban Sumayyah ya ajiye ya sake juyawa babu wanda ya tanka masa hakan ne yasa shi komowa yana ƙoƙari zama Hajiya ta dubeshi."Ammar me kake ne haka babu Dambu babu Chips sai nama da Lemo ka ajiye?”

Tamakar yaro ƙarami me shiri kuka ya kalleta."Hajiya babu wanda yace sannu da aiki kuma kuna kallo na sha wuya”Kauna iri ta ɗa da mahaifi yasa ta mitso inda yake tsaye“Haka iyaye suke shan fama saboda ku da iyaye ku, nasan baza ka iya ba zauna naje na haɗa muku”Murmushi ya mata."Ummu kawai ke da ita kuce min sannu zan karasa lada na”Kafin Hajiya tayi magana Sumayyah tace."Sannu Yaya Ammar ka huta mana”dariya Hajiya tayi tana girgiza kai.Shikam Gogan naka da sauri ya miƙe “Yawa dama haka nake so ji.”Bai jima ba ya fito, tsakiya ya dire ya dauko Pillow guda uku na kujeru."Hajiya ga naki kema ga naki”Ya faɗa yana nuna musu inda zasu zauna, babu musu kowa ya zauna, Bayan su fara cin Abinci Ammar ya kalli Hajiya.“Hajiya Ki danar da Abi Yaro ki ya girma 2 Week nake so asa dan Allah Hajiya kisa suje gobe su neman aure kinji”

"Wallahi Ammar baka da kunya mu ba haka muka yiwa namu Iyaye ba, wai ina rashi maganar ka ya tafi ne yau kan bai fara ciwo ba.”Shuru yayi ya fara sosa kansa, daga haka bai sake magana ba, Sumayya kam Tamkar ruwa ya cinye ta haka tayi shuru sai juya Shoop take da hannu.badan ta koshi ba ta cire hannu, bata taɓa jin dambu mai daɗi wanna ba su gidan su na gero ake babu zogale sai rama, babu mai arziƙi sai dai ka haɗa da ruwa a haka ma yana shaƙe ka.

Bayan su kammala Sumayya ce ta wuce kitchen ta wanke kwanikan kafi ta fito Ammar baya parlour kuma baza ta iya tambayar Hajiya ba.

“Sumayya Ammaru yace ga kayan naki kije ɗaki ki na sama ki sanka sai kisa zai fito ya maida ki gida”Godiya tayi sanna ta haura samma ɗaki yana nan kamar akwai mai kwana aciki a gyra komi, Bratheroom ta shiga ta wanke jiki ta tas taji daɗi wanka, rabonta da wanka tun anan gidan. Fatar ta ta sake kyau duk da ba fara bace amma baƙi ta yafi na wasu fafare mata ɗaukar hankali abinda da kyakyawan mace ga hanci ga ido ga tsayeye baki.Ta jima tana mulkawa jikin ta Cram masu tsada da sa laushi skin sanan ta gayar tuzaze gashita da yake da tsoho kitso sai a yau taji tana son gura Kanta kitso da yafi wata biyu babu gyara. Kayan tasa Pink colour n da ratsin white a jiki wando ne falazo da riga iya gwiwa sun mata kyau, Jaysey Veil shima white yane kanta tayi kamar tasan yadda ake yafa shi, da sabo plate din takalmin tayi kyau taku ta fara har ta sauka ƙasa, tana ƙoƙarin zama Ammar ya shigo Three quarter wando na jeans yasa sai t-shirt light Blue colour ta kama ƙirji sa ta fitar da ainihi surar sa Sandal din takalmin yasa kalar rigar yana ganita ya karaso da sauri.

“Wait wace ke me kika zo yi gidan?”Kallo sa tayi taga babu alamu dariya ko alamu ya santa muryar ta na rawa tace."Yaya Ammar nice fa Sumayyah.”Tsaki ya saki ƙaramin.“Wace Kuma Sumayya Ni ban sanki ba wane ya baki izini zuwa gidan mu”dan danan hawaye ya fara kawowa fusakar ziyara badai ya kawo gidan sune dan ya wulakanta taba.....
[12/2/2025, 12:18 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*



Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.


____________free book _page-16

Tana kokarin juya baya domin barin falon taji ya riko hannun ta gam.Dariya Ammar ya fashe da ita har da dafe ciki, yana kallon yadda jikinta ke rawa. "Haba My Sumayya, wasa nake miki fa. Yanzu ke har kin yarda zan iya manta kyakkyawar surar ki saboda kin canza kaya? Ai ko cikin duhu na ganki zan gane ki bare yanzu da kika zama tamkar Hurul-a'in.Tsayawa tayi Cak batare da ta juyo ta kalle shi ba, da sauri ya koma inda take ido sa ya sarke cikin nata,wanda suka rine saboda kukan da ya taso mata."Wasa?" ta furta a hankali muryar ta na rawa.

"Wasa nake miki mana. Kin yi kyau dayawa Sumayya, wallahi har na kasa gaskata cewa kece a gabana. Kin ga yadda kayan nan suka karbe ki kuwa? Kamar a jikin ki aka dinka su." Ya faɗa yana mata wani irin kallo mai narkar da zuciya yana zagaye ta.Hajiya dake tsaye abakin kofa tana kallon ikon Allah ta saki murmushi. "Kyale shi Sumayya, halin Ammar sai shi. Banda Ni da Abi banga wace yakewa iri wanan wasan ba,ka sani in ka tsokano tsuliyar dodo tace ta fasa maga Yadda zakai.”Juyawa tayi ta kalli Sumayya “Masha Allah, tabarakallah, gaskiya kin yi kyau sosai 'yata. Allah ya yi muku albarka."Sunkuyar da kai ta cike da kunya,“Nagode Hajiya."Agogon hannun shi ya kallah."Hajiya bari mu tafi kar dare ya yi, kinsan gidan su akwai 'yan sa ido."Sai da ta ɗan sansauta fara fusakar ta ce.“Ammar Iyali tane kuma surukinsu zaka zama kar kayi ɓatanci a kan su.kuje Allah ya tsara ka tuƙa motar a hankali, Sumayya ki gaida min da mahaifiyar taki kin ji? Idan mun zo neman auren zan shigo har ciki mu gaisa."

Wani iri sanyi taji a ranta. Ita da ake kira 'yar mahaukaciyya, yau gata a gidan da ko a mafarki bata taba tunanin shiga ba, ana girmama ta. "Zata ji Hajiya, nagode sosai."Sallama tayi mata ta fita ta basu guri peck ya yiwa Hajiya a goshi sanan yabi Sumayya.

A jikin motar ya sameta, ya bude mata mota ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver. Motar ta danyi kara kadan sannan ta silale ta bar harabar gidan.Suna tafiya a mota, kamshin turaren da ya fesa mata da sanyin AC ya sa ta lumshe ido. Ammar ya kalle ta ta gefe ido. "Hope dai baki yi fushi da ni ba ko?"

Girgiza kai tayi, "A'a Yaya Ammar, kawai na zata dagaske baka gane ni bane."

Murmushi ya yi, ya sa hannu ya dauko wata leda mai kyau a gidan baya ya mika mata. "Karbi wannan, waya ce a ciki da ɗan kudin kashewa. Bana so kina wahala kafin na aure ki. Kuma maganar da na gaya wa Hajiya da gaske nake, nan da sati biyu nake so a daura mana aure, so ki shirya."

Gabanta ne ya fadi, ba don tsoro ba sai don fargabar su Inna da Baba Zulai.Taya zata bar Innar ta a gaban su Baba Zulai ahaka ma bata tsira ba bare babu kowa nata.Muryata na rawa ta ce"Yaya Ammar, Inna fa?"Murmushi yayi wanda haƙorar da suka ɗan bayyana kaɗan"Ki bar komi a hannu na. Ni zan san yadda zan yi Inna. Ke dai kawai ki kula min da kanki."Suna shiga Giɗaɗo,Kallo ya koma kansu. Motar Ammar mai tsada da kyalli ta ja hankalin Almajirai Malam har da dattawa da suke taya Malam zama suna zaune akan karoni wasu kuma kan buzu wasu kuma kan ice ana hira.Bai tsaya Saitar inda suke ba, sai da ya je Ya tsaya dai-dai kofar gidan, ya fito ya zagaya ya bude mata kofa.

Tana fitowa, guri ya ɗau shiru ido ne kawai yake binsu. Wasu na zaton wata bakuwa ce aka kawo, sai da ta juya ta kalli Ammar tana murmushi.Nagode Yaya Ammar. Allah ya kai kai gida lafiya."

"Amin Gimbiya ta. gobe zan turo Driver ya kawo kayan lefe da sauran su abubuwa. I love you."ido ta zaro.“Kai yaya Ammar mune zamu aure da kanmu
babu,magabata?”Dariya Yayi."No wasa nake, but kar ki sanar zamu zo naiman aure ki kawai Abi da wasu nashi zasu zo, wanan kayan ki bawa 'yan uwanki”Amsa tayi
Kafin ta bashi amsa,Baba Zulai ta fito daga gida tana gyra ɗauri zani, tana masifa. "Wace shegiyar ce take mana horn a kofar gida haka kamar tsohuwar kila..." Maganar ta ta makale a makogwaro lokacin da idonta ya sauka kan Sumayya, da yadda taga canji ta lokaci guda.

baba Zulai ta waro ido, ta kalli motar, ta kalli Ammar, sannan ta kalli Sumayya daga sama har kasa. "Sumayya? Kece ko kuwa idona ne yake min gizo?"Sumayya ta gyara tsayuwar ta, wani kwarin gwiwa ya zo mata wanda bata taba ji ba. "Nice Baba. Yaya Ammar ne Sila gashi wanan na Sadiya da Lubna."Baba Hauwa ce itama ta zuro kai tana leƙowa kofar gida, tana ganin Ammar ta saki baki. "Ikon Allah!Nidai naga ta yadda buri Yaya zulai zai cika? Lallai Yaya Zulai ta kade har ganyen ta."

Ammar bai ko kalli inda suke ba, ya shige motar sa ya ja ya bar su da kura da kuma bin motar da kallo.Taski Baba Hauwa tayi"Yaya gaskiya surukin nan naki ba ƙaramin kallo bane.”harara take mata tana yafitar ta da hannu tayi shuru.Gajiya Sumayya tayi da tsaiwa ta ɗauki ledar ta, ta shige gida tana taku ɗai-ɗai, ta bar Baba Zulai da Baba Hauwa baki bude, zuciyoyin su na tafasa kamar zasu kone kurmus.

Baba Zulai ta bi bayan ta da gudu, "Ke Sumayya! Zo nan! Daga ina kike? Wa ya baki wadannan kayan na alfarma? Kar dai kin fara bi..."

Sumayya ta juyo, fuskarta dauke da murmushin da ya kara tunzura Baba. "Baba lokaci ya yi da zaku daina wahalar da ni. Yaya Ammar aure na zai yi, kuma ba mai hana wa da yardar Allah.In ma kuna tunani wani abu Tom wallahi tun wuri ku daina.”Ta shige dakin mahaifiyarta ta bar Baba tsaye tana salati tana tafa hannu. "Lallai yarinyar nan ta raina mu! Hauwa! Hauwa! Zo kiga tashin hankali ido buɗe zai afkawa gidanmu..."ke dai Yaya aini bani ba shiga tashi hankali daga Ni har yara na Wallahi leda malam sai ku sake sabo shiri”

Tana faɗi haka ta juya nata ɗaki dan gani take in ta zauna ɓata lokaci zasu aguri.Sumayya na shiga ta iske Inna duk ta fita hayyacinta.har da fitsarinta da ta makaka akan sabuwar ledar tsakar ɗaki gashi goshinta a kumbura saboda jifan da Yusuf yamata.

Gaba ɗaya farin cikin da ta shigo dashi ya mutu warwas, ya koma baƙin ciki da takaici marar misaltuwa. Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, tana jin yadda zuciyarta ke mata zafi saboda cin zarafi da gallazawa. Ya zata bar Innar ta a hannun mutanen nan? Wannan zafin ne ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa kan cewa shawarar Ammar ita ce mafita, kuma dole ne ta riƙe shi da hannu biyu.Da sauri ta shafe hawayenta, ta fara aiki. Ta ɗauki Inna a hankali ta zaunar da ita gefe, tana ta maimaita mata “Sannu Inna ta, sannu.” Daga nan ta yayafa ruwa, ta fara share ledar tsakar ɗaki. Ta wanke tabarmar da omo har sai da ta tabbatar ba wari. Bayan ta gama tsabtace ɗakin, ta dawo kan Inna. A hankali ta cire mata datti da fitsarin da ya ɓata mata jiki. Ta ɗaura mata sabon zani mai tsabta. Ta duba kumburin goshinta, ta shafa mata man shafawa mai sanyi don rage radadi.Bayan ta kammala komai, ta gyara Inna a kan sabun gado da Ammar yaKawo musu. ta zaunar da ita gefen ta rungume ta.

Sai yanzu ta tuna da wayar da Ammar ya bata jiki a sanyaye ta bude ledar wayar, ta ciro wayar kirar iPhone mai kyau da kyalli. Tana riƙe da wayar, sai taji kamar tana wata duniyar daban."Sati biyu?" ta furta a zuci. "Aure nan da sati biyu? Ammar ya ce shi zai san yadda zai yi da su." Tunanin Hajiya da kalaman ta sun sake dawo mata, sun tabbatar mata da cewa wannan gida ne na mutunci, kuma Allah ya fitar da ita daga wahala. "Godiya ta tabbata ga Allah."Wata murya mai zafi ta katse tunaninta. Baba Zulai ce ta dawo har bakin ƙofa, fuskar ta kamar wanda aka daka mata barkono. "Ke! Tunda kika dawo dan iskanci kin ki zuwa ki faɗa mana inda kikaje da gardi ƙato?kizo ki mana bayani dan Malam bai shirya ammsar abin kunyaba.tin da yaro nan yanzo gare ki shikenan ki ɗorawa kanki girman kank tsiya? Wallahi Tallahi, wannan aure da kika ƙulafincimn kina tunani zai aure ki,Tom ki sani mudun Zulai Baba kandala na raye ba zai taɓa yiwuwa ba! Sai na rufuzashi kuma na faɗawa duniya Mahaukaciyar Uwar taki, zan gaya musu ke ƴar mahaukaciyya ce, dan kada su aurea a haifa musu mahaukata!" ta faɗa tana huci da nuna ta da yatsa.Sumayya ta miƙe tsaye, tsayin ta ya kusan kai na Baba. Ta kalle ta cikin idanuwa, ba tare da tsoro ko fargaba ba. A yanzu ba Sumayyar jiya bace. “Baba, ku daina. Kun riga kun cutar da ni fiye da yadda zan iya jurewa. Duk abin da kuke so ku faɗa, ku faɗa. Ammar ya san komai. Kuma insha Allahu zan bar wannan gida nan da sati biyu. Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya zalunce ni a nan! Ko mahaifiya ta”Ta fada cikin kwarin gwiwa wanda ya firgita Baba Zulai.Baba Zulai ta kifa hannu a baki, tana salati, haushi da kishi sun cika mata zuciya. Ta kasa magana, sai numfashi take sama-sama. “Yarinya ta raina ni! Wannan yarinya ta raina ni! Hauwa! Hauwa! Zo ki gani! Zo ki gani!” ta juya tana kiran Baba Hauwa da niyyar ta hada kai suyi wata shawarar ta wulakanta Sumayyah.Bata yi aune ba taji muryar Baba Hauwa ta dawo mata da martani.

“Yaya aini bani ba shiga tashi hankali daga Ni har yara na Wallahi zunubi da muka kwasa na baya na ya ishe ni.”tana faɗi haka ta maida kanta cikin ɗaki ta ta gyara zaman labile ta,.Duk abin da suke cewa Sumayya bata ce Inda ba sai da taga Baba Zulai ta matsa zuge musu labule duk da ƙurjinta yana bugawa tasan yau sai ta sha duka guri Yaya Yusufa.Tana zama ta kalli mahaifiyar ta dake kwance cikin kwanciyar hankali. Ta rungume wayar hannunta sosai. Mafarkinta na cikawa. Nan take ta kunna wayar, hasken allon ya haskaka fuskarta. Bata san ya ake nemo lamba ba bare ma tasan da layi aciki ko ababu zubawa wayar ido tayi, tana dai gani waya a hannu su sadiya amma ki da wasa bata taɓa karanbani cewa su bata ta ɗana ba.Bata juma ba kira ya ya shigo ruɗewa ce tasa ta danne wayar gudu karwani yaji, bata san kashe wayar tayi ba baki ɗaya.....
[12/6/2025,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login