Showing 24001 words to 27000 words out of 56438 words
Chapter 9 - Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel By Husaini S Abdullah.txt
take ɗaki, ta bayan gida ta fitar da ita ta watsar.
Cak ta tsaya gani Akwatu kayan da Hajiya ta bata an gama badali su Sadiya turmi uku Lubna turmi atamfa biyu Amina kuma Aka hada ta da Baba Hauwa turmi biyun lass ɗin da Hajiya ta bawa Sumayya a rage mata girman su, ta gano hannu Baba Zulai kala uku.
"Hauwa Amma yariyar nan ba ƙaramar makira bace, da wanan kayan gidan Ubanwa zata kaisu.”Harara Baba Hauawa ta wurgawa Sumayya."Hoho mata muguwa mai mugun hali, Dangi hauka da Aljanu”
"Babar mu don Allah,ki barmi wanan Lace ɗin Gobe naje kasuwa dashi”Cewar Sadiya da take ta faman jinjiga Baba Zulai. tsaki tayi.“Kinga fa Allah bazan baki ba, da yau da gobe duk Malam a ɗaki na yake so nake na gwangawaje lass ɗin nan ajikina ko na samu ladan Aure”Tana faɗa ta kara lass ɗin a saman ƙirjin ta.
Hawaye ne suka zubowa Sumayyah masu zafi, Zuciyar ta ta sake karaya, lokaci da ta hangi Inna ta na miƙa hannu ita ma abata, ƙoƙarin miƙewa Inna take da sauri ta Sumayya ta ƙara sa inda take ta goge Hawaye ta.
"Inna ba na hana ki riƙa miƙa hannu in kika ga abu a hannu wani ba, Ko so kike nayi kuka, ki bari zanje neman gwangwani madara in nasiyar Zan siya miki Atamfar sallah”A fili Inna ta nuna murnar ta, tana nuna jikin ta tare da alamu zata shafa hoda tayi kwalli kai Sumayya take ɗaga mata hawaye da take ƙoƙarin hana zubar sa ya sake zubo mata.maganar baba Zulai taji.
"Sadiya Dan Allah tashi ki azamin wutar nan ki zuba dadawa can Kin san Malam kamar kure yake guri nama yanzu in ya fara tsaya min aka kamar tsohon maye haka yake.”Dariya Sadiya tayi ta tashi tana waƙar Kawu ɗan sarki ta Ungollo na ciwo.
Lokaci da ake kiran sallah magari ba lokaci Farfesy Kayan ciki ya kammala, babban tire ta samo ta kasa shi kashe-kashe tare da zubawa Malam nasa a ƙaramar Samira, kowa kaso ɗaya aka bashi sai da kowa ya gama ɗauka Baba Zulai ta kwaɗawa Sumayyah kira da suke zaune Kamar kurame ita da Innar ta, Inna ce ma me yawan suru ita kaɗai.
"Sumayya..! Sumayyah..!!!”Shuru babu magana miƙewa tayi A zafafe ta tunkaro inda Sumayya take zaune tayi nisa ciki tunani rayuwa.Duka ta ɗana mata."Ke 'Yar mahaukaciya dan naga alama kinfi jin daɗi a kira da sunan ki kije ki ɗauka naki ne ke da uwar ki, naman bai yi afki ba shiyasa aka haɗa muku in kuma bakwa ci gaba takai mu”
Taji shigar dukan Sosai, jikinta na ɓari ta nufi in da nasu yake dan har Isakar tsakar gida ta tule shi da ganye maina duk ya fara tule shi da ƙura, ƙoƙarin ɗaukan faranti tayi Baba Hauwa ta daka mata tsawa."A jiye min faranti salon a zubami guba, ki kwashe a hannu ki, ki matsa ki bani guri.”
Ajiye tayi ta juya tana zuwa Inna ta fara miƙa mata hannu.“Sumayyah Zanci nama, zaki Bani Allah ina so zaki bani??”Hawaye ne ya cika Ido Sumayya tayi sauri gogewa da tafin hannuta, ta miƙa mata naman, kafin kace kwabo ta cinye shi. Jin-jiga kafaɗar Sumayyah tayi "Sumayyah ban ƙoshi ba, Allah zaki daɗa min Kinga fa yinwa nake ji kiyi Haƙuri Sumayya ki daɗami”Fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Inna.kuka take sai dai Babu ƙara ta juma ajikin ta Sanan ta ɗago kai.
"Inna kin manta da akwai samu akwai rashi? kinsan yanayi da muke ciki a gidan nan me yasa baza ki haƙuri da abin da kika samu ba”Turɓine fusaka Inna tayi wai itama tasan faɗa gani za tayi fushi yasa ta cewa.
"Gobe in na fita nayi aiki Sosai Nama zan fara sai miki kafi mu samu kuɗi ɗinki”kai ta hau kaɗawa tana murna da haka Malam ya shigo ya kora su ɗaki suna daga ciki suna jin hirar su har da su Sadiya da Iyaye su. Ciki farin ciki suke hira.
*Alhaji Ɗan Dubai*
Ko da ya tafi bai koma Lagos ba dan Business ɗunsa na safar mata ne yake kai shi Lagos ko aiki da da uban gidan sa ya tura sa. Safa da marwa yake ciki makeke Bedroom ɗinsa, Hajiya Fatiha matar sa ce da take kwance ta bisa da kallo."Alhaji lafiya naga tun da ka shigo banga walwalar kaba.?”Zama ya yi gefe Bed din kafin ya furzar da iska mai zafi“Kibari kawai Hajiya Fatiha Ban taɓa asara kamar na wanan Lokaci ba, Riba mai yawa ta tunkaro ni sai dai tsinane yaro nan Ammar ya lalata komai”
Tashi tayi daga kwanciyar da tayi ta dawo jikin sa."Ammar wane fa?”Ammar mana yaro Alhaji nawa”kafe shi da kallo ta yi.“kamar ya ban gane ba kamin bayani”kwashe komi ya yi ya faɗa mata. Ajiyar Zuciya ta sauke."Kenan yana da Alaƙa da ita kome?”
"Bana ce ba Amma wallahi sai na lalata rayuwar sa ba'a cin bashi na a zauna Lafiya sai na ɗai-ɗai ta shege Uban nan nata, dan shine kwallo shege,
Sai dai naga A-lamar tana so Ammar zanyi anfani da son da take masa na ruguza farin ciki ta, ban taɓa samu naƙasu aciki Kasuwanci na ba sai akan yariyar nan, naci buri a akanta Amma yaro nan har da min baraza nar Sallama daga guri aiki.”
Dariya Hajiya Fatiha tayi "Wanan me sauƙine, mu fara raba alaƙar Ammar ɗin da ita sanan musa duniya ta juya mata baya ta rasa madafa kaga dole ta neme mu. Kuma bariki da bata so tayi dole sai tayi shi”Dariya Alhaji Ɗan Dubai ya yi mai sauti"Bana bukatar ta,a yanzu bayanta kawai nake so gani”Yana faɗi haka ya fita.
*Nasarawa*
Tunda suka shiga mota babu mai magana dama haka tafiya da Ammar take da wuya kaji shi yana yawan surutu, sai ma in da Hajiyar sa ne ko kuma Abin sa suke tafiya.suna isa Airport ɗin Malam Aminu Kano driver ya nemi guri packing din mota yagyra packing ciki nutsuwa suka fita, Ammar ya kama hannu hajiya suka fara tafiya sai da su kayi nisa sanan ya kalle ta.
"Hajiya Gobe aiki zai miki yawa nasa a kawo kan sa zaki gyra zan kaiwa Innar Sumayya”
"Allah yasa zamu gani Ammar sai dai ina so naji halin da yariyar nan take ciki da Mahaifiyar ta.”peck ya mata a goshi sanan yace.
“Ummu zan kai ki ma sai ki ganta, yanzu taya zan baki labari nida ba ɗan Jarida ba ko marubuci labarai ”kunnesa ta kama“Ba sai ka kai ni ba zansa drive ya kaini”
Suna gurin a tsaye Abi ya fitowa har da Manager da P.A ɗinsa da suri Ammar Ya faɗa jiki Balarabe mutun wanda shekaru ne kawai ya ban-banta shi da Ammar.
“Abi, ahla wa daula....kif kéinit l-tari’? Kteer mshta’lak.”
“Abi,Sannu da zuwa..Ya hanya? Na yi matuƙar kewark.”Bayan sa ya shafa tare da peck ɗinsa a hannu ciki lafazi yaran Labanis.
“Ya Ammar! hibib Albi..ana kaman mshta’lak.
El-hamdellah ‘a Saléme.”
“Ammar! Masoyin zuciyata...ni ma nayi kewara.”P.A da Manager da suke tare da Abi ne suka rusina suka gaida Hajiya. kallo Ammar suka yi shima suka gaida shi hannu ya ɗaga musu dan bai cika so yana magana da iyaye sa ana katse shi ba Abin ya dube shi.
"Jeet men America deghri ‘a Nigeria...‘anjad eshta’telkon kelkon.” Peck ya masa ba tare da ya sake ce masa komi ba.Abi ya ƙaraso waje Hajiya.
"kin kara kyau Kamar ba Ummu Ammaru ba gaskiya budurwa nan tana jin daɗi”Duka ta kai masa a ƙirji“Wallahi kasa naji kunya Ammar da P.A ɗinka suna guri baka ji nauyi sai?”
Hannu ta ya kama yasan dama sai ta sako zance Ammar yana guri,kullum bata son Abin da zai sa ta jin kunya Agaban yaro ta. Mota suka shiga Ammar ya zauna a for seat driver ya ɗauki hanya.
Yau yajima bai yi hira iri haka ba Bacci ne ya fara ɗaukar sa ajiki Abinsa kira ya shigo masa ƙaramin tsaki ya saki.sanan ya picking call ɗi.
“Hello Fu'ad”Banji mai aka ce a ɗaya ɓangare ba sai tashi da yayi daga jikin abin."Ok ka shigo dashi ina Parlour Hajiya”Katse kiran ya yi babu jimawa Fu'ad ya shigo yaro ne matashin baza su wuce sa'anni ba,Sai dai daga gani yaro Ammar ne gaisawa yayi da Abi ya gaida Hajiya Sannan ya ajiya Leda biyu ta viva.“Ranka ya dade duk an gyra sai dai a ƙara wanke wa”
“Oky Hajiya gashi ya kawo.Fu'ad kai shi cikin Freigd”Yana kaiwa Ammar Ya miƙe suka fita da Fu'ad.
Washe gari Tin da Hajiya tayi Sallah bata koma Bacci ba, tana kitchen tana aiki,
Aiki biyu ta haɗa dana Ammar dana Mahaifinsa Sosai aiki ya kacame mata Deluwa 'Yar aiki ta bata gari taje gani gida shikuma kuku tin da aka kamasa yana zuba musu guba aka kai shi virus bata sake naiman wani kuku ba, tace ta haƙura da mai girki duk wahalar aiki tace zata iya kayanta. Sai 11 Ammar ya fito cikim shiri sa yadi ne light Blue yasa, iri aikin hannu nan da hula zanna bukar ya yi kyau sosai, ƙamshi kawai yake zubawa.ɓurintu Hajiya ya ji a kitchen da sauri ya faɗa ta baya ya rungume ta.
“Sorry Hajiya ta na saki aiki Sorry”Kan sa ta shafa aiki ya zame mana jiki karka damu ɗana kayi break fast aiki ka ya kammala”Godiya ya mata ya koma parlo Tea ya sha sai chips ya goge bakin sa da Tissues sanan ya koma kitchen.
“Wow Hajiya wanan flask ɗinan ya yi min kyau”
"kayi addu'a matar ka tazo ma da iri sa,Ammar zo ka tafi time na ƙurewa Ban so dare a yayi maka a hanya”Godiya ya yi ya kira Madu mai gadi ya dauka masa Flask ya saka a cikin but ya mata sallama tare da cewa ta gaida Abi in ya fito ba zai jira ya fitowar saba.Tun da ya ɗauki hanya yake jin wani iri farin ciki na ratsa zuciyar sa yanayi Fusakar Sumayya da tafiyar da suka yi jiya yake tunawa, sa'i² ya saki murmurshi.
******
******
Tinda aka fito masallaci Sumaiyya ta fita daga ɗaki tsunma tasa ta ɗaure ƙofar gudu Inna kar ta fita bata ganta ba tayi wani guri.Bola bola take bi ko zata samu gwangwani madara sai dai yau kamar baki ta gaza samu har goma da rabi gwagwani uku ta samu bakin ta duk ya bushe har jiri take ji gashi takalmi ta da tazo dashi Sadiya ta ƙwace sai wani haɗu bauta tasa, shima saboda tsabar yawo da tayi ya tsinke leda tasa ta ɗaure dashi.Sha ɗaya da rabi ta taki sa'a ciki wata bola da take gefe rami gwagwanaye ne birjuk da Alamu ba'a juma da zubar da su ba kasa boye farin ciki ta tayi.
"Allahmdllhi Allah na gode maka Allah yasa kaltu mai Alala ta siya kan naira ashirin na samu kuɗi siya wa Inna ta Nama”
Ciki sauri ta fara zuba gwangwani ciki buhu ta wasu yara ne da aka musu break daga makarantar boko suna hango Sumayya, suka tsayar dariya ɗaya yayi dutse wuta ya ɗauka ya saita bayan Sumayya ba zato taji saukar dutse tasss a gadon bayan ta miƙewa tayi tare da gantsare wa hawaye masu zafi suka sulalo mata. Dariya yaran suka sa.“'Yar mahaukaciya Uwarki kema kin fara haukar ne naga kin fara bin bola kinaci leda”Ihu suka fara suna mata waƙa ga mahaukaciya 'Yar macukule, gani yaran sun fara ihu suna tula mata ƙasa, ya sata haƙura da kwashe ragowar gwangwani tabar guri duk da haka wasu sai da suka raka ta da gudu.
Tafiya take ido ta A rufe ji take kamar zata yanke jiki ta faɗi har Allah yasa ya sa ta ƙaraso gida, Ammar da yake waje jikin motar sa, gefe ɗaya motar da ta kawo kayan ɗaki ne da kayan abinci da ta riga shi yo gaba a gefe.Tana ƙoƙarin tashi babu wanda ta kula dashi sai kiran sunann ta da taji, muraya da bata taɓa zato sunan ta na da daɗi furta wa ba.
“Sumayyah....! ” Da ƙyar ta iya ɗaga Ido ta kalleshi, hannu sa da suke kan ƙirjin sa ya saki tsoro furgici ya cika shi iya jiya da ya Barta bata da maraba da mahaukaciya ciki ransa yace Anya Sumayyah da na bari jiya ce ko kuma wata da ban?”Jin bashi da amasa ya sake ɗagowa ya dube ta ido sune ya sarƙe da na juna wani iri yanayi ya shi ga,ya kasa tantace ainihi abu da yake ji akanta. Taku ya yi kusa da ita.
“Wannan duk na maye, Maye wanna ajikin ki,I na kuma kika je yanzu da safiyar nan??”Hawaye ta fara Numfashi ta yana ƙoƙarin ɗaukewa kasa jurewa ya yi ya fusgo ta ta faɗo jikin sa kuka ta fashe dashi, ba tare da tsantsamin ƙazantar da take jikin taba ya sake yi mata masauki akan kirjin sa yana shafa bayan ta alamu rarrashi.........
[11/23/2025, 4:27 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a
*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*
Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.
____________free book _page-13
Ga nin yadda kuka ta ke ƙara tsananta ne ya sa Ammar lumshe ido, zuciyarsa na kai komo tamkar ana murɗa ta. Wani irin tausayinta ya sake shigar sa, ya ji tamkar ya ɓoye ta a cikin kirjinsa har abada. Sai da ya jira kuka ya lafa kaɗan kafin ya matsar da ita gefe, ya kalli fuskarta a hankali.
“Sumayyah… me ya faru? Waye ya miki haka?”
Kallon da ta yi masa ba irin kallo bane na yau da Kullu ji take kamar ana daɗa Ƙawata mata fusakar sa Sai dai tasan Ya mata nisan da bata isa tasa a ran ta zai so ta ko ya ƙaunace taba.
Da sauri ta kauda kai tana share hawayen da ya ƙi tsayawa.
“Ba komai… kawai na gaji ne.”
Ammar ya girgiza kai, idosa ya ƙanƙance suka sauya.launi izuwa ja.
"Har tsawon yaushe zaki juri yi min karya? Sumayyah...! Ni ban zo nan don ki rikita ni ba ko Na zama silar shiga tsakani ki da dangi kiba. Ki sani duk abinda yake damunki, na san akwai wanda ya haddasa hakan kuma bazan iya shuru Na zuba miki ido ba ki duba jikin ki jiya ba haka Na barki ba.”yana Faɗi ya kafeta da Sihirtatu idanunsa.
Shiru ta yi,ta kama kallon ƙasa. Sai bayan wasu sakanni tayi ƙoƙarin raba jikinta daga nashi.
“Dan Allah ka barni… Zan je in duba Inna tun kafi Asuba Na fita nasan yanzu Yinwa take ji. Kuma In yaya Yusuf Ko Baba ya ganni da kai a haka Sai ya dake ni ya min faɗa…”
Zai yi magana,malam ya yi Sallama daga cikin, idon sa ya ci Farin kwalli, sauya sallon magana ya yi kamar ta tsofaffin waliye."To...to Ammar Ke tafe kuma kaƙi shiga ciki Ke Mai yasa bakya rabo da sakarci”Magana zata yi Ammar ya dakatar da ita.“Ni ne ban shiga ba, kayan nan na Mamar Sumayya ne ina so a naimo wanda zasu saka Na biya su”
Gaba ɗaya jikin Malam ya hau tsuma kamar tsoho ɗan tauri.“Haba Akwai tiƙa-tiƙan mata har biyu aciki bara naje sai suyi abiya su, Mudai babu abin da zamu ce dakai sai Godiya”Tamkar kurma haka Ammar ya masa da Sauri Malam ya afka cikin gida. suna tsakar gida anyi baje baje da kayan kari kumalo, ya faɗo tafa hannu ya fara"Tom..tom ki tashi arziƙi ya sake Sallama agidan ku wannan MAHAUKACIYYA aka kawo wa kayan Saiti in kuka saka za'a biya ku da kuɗi mai tsoka”Wanni banzo kallo Suka bishi dashi."Malam yaushe ka fara tausayi ta da sonta har zaka bari asa mata kayan ɗaki muku ma mana zaune ko ledar tsakar ɗaki bani da ita”
“Matseeee ke dai Hauwaila har abada baza ki daina shiririta da sakarci ba,yo ko kare hauka ne ya cijeni zan yi asara kuɗi na sai wa wanna Mahaukaciyar kaya ne sai dai in baki iyaye ne ke ɗawainiya dani.”ya faɗa yana zaro ido kamar baƙin kure. Baba Zulai ce ta miƙe.“Ai kuwa ko wanne asarare ne ya siya Wallhi yana tafiya zan fido su, su dawo ɗaki na dan nice uwar gida a ɗaki na ya kamata a saka su.”
“Jita da Allah figai-gai dake Zulai tom surukin kine kina yin sake dama zata kwace miki,na dai gaya miki sharɗi kar gi rawar kai wallahi dan babu wani taimako da zan sake miki ki kayi wasa da wanan damar”tin da Malam ya fara suba-ɗaɗar sa Baba Zulai taken kifta masa ido yayi shuru kada Baba Hauwa taji shirin su akan Ammar haka ya miƙe ya fice.
Malam na shiga cikin gida ya juya ya dako Baban Vasket ya dawo ya tsaya agaban ta, ya kalla ta.“Ki shiga ki zaunar da Inna.Zan shigo yanzu?”Kai kawai ta ɗaga kamar yarinya ƙarama.Ta shiga gida a hankali.Ammar ya tsaya na tsayi sakanni biyu yana kallon ƙofar, zuciyarsa na bugawa a hankali ya furta.
“Wallahi idan wani ya kuma taba min ke… Zan lalata masa rayuwa, zan nuna masa ke mai gata ce”ya furta cikin ɓacin rai. flask ya ɗauka da jaka, ya nufi ƙofar cikin nutsuwa.
ACIKIN GIDA
Inna Sumayya na zaune cikin ɗaki gefe guda ta takure jikin ta, tun tana kukan yinwa har ta haƙura, Sumayya ta taɓuɗe ƙofar da sauri ta kama hannu ta, ta zaunar da ita tana goge mata fuska da ruwan ɗumi.basu juma da zama ba Ammar ya shigo, ya durƙusa gaban Inna.
“Inna, sannu. Na kawo muki abin da za ki ci.”Kallo sa tayi,ta dan saki murmushi.
“Naman… kakawo min zaka sai min powder nayi kwalliya?”
Ammar ya yi murmushi kaɗan,ya kama hannu ta
Ya dubi Sumayya, a tare zuciyar su ta buga wani baƙo al'amari ya ziyarce su da kar ya iya kauda kai.
“Ki samo plate ki zuba mata”Ya furta,Sumayya tana ƙoƙarin mikewa Inna ta riƙe mata hannu “Sumayya kar ki tafi Yusuf zai sake duka na”
Ido suka haɗa da Ammar da sauri ta kauda kanta dan ta kasa jure kallo da yake mata.cire hannu Inna ya yi