Showing 30001 words to 33000 words out of 114314 words

Chapter 11 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

da wa take waya, Anty tace "toh Allah ya basa lfy, ya sa kaffara ne" ta katse kiran tana kallon Hajar da ta kura mata na mujiya, washe gari da misalin ƙarfe 11 na safe Hajar ta fito wanka, ta shafa man da ta gani kan mirror snn ta saka doguwar rigar atamfa, tana fita palour ta ga Anty ta fito daga kitchen da basket mai ɗauke da warmers, daman tin ɗazu suka gaisa, Hajar tace "Anty me za ai?", Anty tace "ba komai Hajar, ki ɗakko gyalenki fita za muyi, za muje asibiti mu duba Baba", zuciyarta ce buga da ƙarfi tace "Baban ne bashi da lfy, dan Allah Anty me yake damunsa?", Anty tace "yafa ji sauƙi, kawai dai jininsa ne ya hau, kuma yanzu ma sallamarsa za aii", Hajar ta sauke ajiyar zuciya ta shiga ɗaki, Ghana most go ɗinta ta buɗe ta ɗakko ironed Hijab maroon, tare da wayarta da tin jiya da bata bi takanta ba, hijab ɗin ta zumbula ta fito palour ta zauna tana jiran Anty, babu jimawa saiga Antyn nan ta fito daga room ɗinta. Hajar ta miƙe da sauri, Anty ta kalleta tace "toh ɗauki abincin muje", Hajar ta ɗauki basket ɗin ta fita compound, saida Anty ta rufe ko ina snn ta fito, Anty ta rufe ƙofar gate bayan sun fito ta zuba keys ɗin a hand bag, Hajar dai ta ƙagu kafin ma Anty ta gama rufe gida harta tsare Napep. Anty ta gayawa mai Napep asibitin da zai kaisu snn ta shiga, Hajar ma ta shiga. hankalin Hajar bai kwanta ba saida taga sun iso asibitin, Anty ta kira Umma a waya tayi mata kwatancen ward ɗin da aka kwantar da Baba, Anty ce ta fara shiga ward ɗin snn Hajar dake biye da ita, gadon da yake kusa da ƙofa anan Baba yake, Umma Maama sai Nabilah ne a asibitin, Anty ko kallon direction dinda Maama take ba tayi ba ta matsa kusa da Umma da take bawa Baba Youghurt, Hajar ta ajiye basket ɗin hannunta ta isa kusa da Baba da yake jingine da allon gado, a sanyaye tace "Baba sannu, Allah ya baka lafiya", Baba ya gyaɗa mata kai yace "Ameen Hajara", Hajar ta kalli Umma tace "Umma ina kwana, ya me jiki?", keenly Umma tace "lfy, jiki da sauqi", Anty ma suka gaisa da Baba da kuma Umma, saida Anty ta zauna snn tace "sannu Rabii, ya me jiki?", Maama ta taɓe baki ta juyar da kai tana girgiza ƙafa, Anty a zuciyarta tace kinyi da ƴar halak, Umma ta kalli Hajar tace "Hajara idan kika fita ɗakin nan saiki bi hannun hagu, idan kika bi hagu saiki tambayi Nurse station, saiki tambayi Nurse ɗin wajen ya baki takardar test ki kawomin, tin ɗazu yace aje a ƙarba sbd dashi za mu ga likita anjima", Hajar ta miƙe tace "tom", walking slowly ta fita daga ward ɗin. perfectly tabi kwatance da Umma tay mata ta isa Nurse station, Sallama ta yiwa Nurse ɗin dake zaune kan white plastic chair tace "nazo amsar test ne", yace "name?", Hajar tace "Adam Muhd Gini", Nurse ɗin yace "Okay" ya buɗe wata drawer ya ciro paper ya miƙa mata, Hajar ta amshi paper snn ta juya tabar wajen da papern riƙe a hannunta.


★ƙarfe tara da rabi Nurain ya fito daga room ɗinsa, car key da briefcase ne riƙe a hannunsa, down stairs ya sauka, Noor ya tarar a kan dining tana breakfast, ta yi shirin fita schl shine ta tsaya yin breakfast, Noor ta kallesa tace "good morning", yace "morning lil sis", tace "ga breakfast", yace "enjoy it alone, idan kin gama help me with a cup of coffee", tace "Tom", yace "zan shiga wajen Abba, make it kafin na dawo", ya ajiye briefcase ɗin hannunsa a kan kujera snn ya wuce part ɗin Abbansa, da sallama Nurain ya murɗa tsadadden handle ɗin ƙofar palourn kana ya shiga, ya ji daɗin ganin Mami itama a palourn tare da Abba, kan carpet ya zauna ya gaishesu, Abba ya amsa yana nuna masa kujara yace "sit", Nurain ya koma kan kujera ya zauna yana shafa kansa, a zuciyarsa addu'a yake Allah yasa parent ɗinsa su yarda da maganar da yazo musu da ita yanzu, Abba yace "is there any problem Uthman?", Nurain yace "yeah, but it is not a problem", Abba yace "then?", Mami ta ringa kallon Nurain tana jiran taji abinda zai ce, Calmly Nurain ya fara magana yace "Akan maganar course ɗin da 1yr back nace zanyi a India sai kuma na canza decision, yanzu kuma am ready to take it if i get your approval", Abba yace "for how long?", Nurain yace "six to eight months", da wani expression Mami ta kalli Nurain sai kuma ta girgiza kai tace "No", Abba ya kalleta yace "why ?", Mami tace "sai ya bar aikinsa da business ɗinsa da ya fara kafasa yanzu ya tafi wani karatu, gaskiya nidae bada yawuna ba", Abba yace "wnn ma ai zaiyi boosting qualifications ɗinsa snn kuma he need a rest, kinsan da hakan ko?", Mami ta kalli Nurain tace "tom shknn Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, nagode Mami", Abba yace "saika fara shirye-shirye", Nurain yace "yeah, idan komai ya tafi normal ina jin ma ranar Friday zan tafi", Mami tace "this Friday?", Nurain yace "yeah", Abba yace "Ohk, Allah ya bada sa'a", Nurain yace "Ameen, yanzu ma zan wuce hospital nayi signing". Abba ya gyaɗa kai, Nurain yayi musu sallama ya fita. Main palour ya koma, a lokacin Noor ta fito da Mug ɗin coffeen da ta haɗa masa, tace "in time?" ta miƙa masa, ya karɓa yace "thank you" ya zauna kan kujera kusa da briefcase ɗinsa ya fara sipping, Noor ta rataya jakarta zata fita dan already driver na jiranta, yace "muga wayarki", tayi sak sai kuma ta zuge bag ɗinta ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, jujjuyata kawai yayi bai kunna ba ya mayar mata da kayarta. ta mayar da ita bag snn tayi masa sallama ta fita. saida ya gama shan coffeen snn ya ɗauki car key da briefcase ɗinsa ya fita compound, parking space ya nufa ya buɗe motarsa, bayan yayi warming ya fita daga compound ɗin ya hau kwaltar street ɗin gidansu dake a mulmule, with a minimum speed ya isa Hospital, wajen da aka tanada dominsa na parking anan ya paka motarsa, ya kashe motar ya fito hannunsa riƙe da briefcase, Majestically yake tafiya har yaje office ɗinsa, secretaryn sa Halima ta miƙe cike da girmamawa tace "welcome Dr, good morning", yace "Morning" ya wuce katafaren office ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke yana ƙarewa Office ɗin kallo sai kuma ya buɗe briefcase ɗin da ya shigo da ita ya ɗakko wani file, da file ɗin a hannunsa ya fito, Haleema ta miƙe da sauri tace "Sir aike ne?", yace "No, continue what you're doing", ya fita. wani corridor yabi yana shan kwana sukay karo da juna, kanta ya bugu da ƙirjinsa ta shaƙi ƙamshisa, hannunta kuma mai riƙe da papern da ta kwarɓo wajen Nurse ya bige file ɗin hannunsa, a take takardun file ɗin suka baje a ƙasa, itama takardar hannunta ta faɗa cikin takardun, Hajar ta ɗago da nufin basa haƙuri amma suna yin ido huɗu saita murtuke fuska taja da baya..........✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{17..}
Da wani irin expression Nurain ya kalli Hajar da ta wani murtuke fuska, ya kalli file ɗin da papers ɗin ciki suka baje a ƙasa, Hajar ta yamutsa fuska sbd scent ɗinsa da ya gama bulale corridorn, ta tsugunna ta fara laluben papern ta, tana ɗaukar papern ta miƙe ta zagayesa zata wuce, yayi mata side look yace "rashin sanin darajar mutanen naki har ya kai haka?, ki bige mutum kuma bazaki basa haƙuri ba", Hajar tayi jim sai kuma ta juyo ta kallesa da lulu eyes ɗinta, ta nunasa da papern hannunta tace "mu bawa juna haƙuri daii", ta juya ta cigaba da tafiya, taku uku tayi taji anyi sama da papern hannunta, kafin ta waigo har ya sunkuya ya fara packing papers ɗinsa, ya zubasu a file ɗin ya miƙe, ta haɗe gira tace "ka bani takarda ta", ko dubanta beyi ba yayi wucewarsa bayan ya saka papern tata a pocket, galala tabi bayansa da kallo kafin ta fara tafiya da sauri following him, zumbulelen hijab ɗinta har taɗeta yake, tana zuwa kusa dashi ta rage speed amma duk da hka sauri take following him tace "ka bani paper na", idan corridorn da suke bi yayi magana to tabbas Nurain ya tanka, he was just walking Majestically without minding her, ta naɗe hijab ɗinta tayi blocking front ɗinsa tace "bani paper na", wani kallo da yayi mata and how huge he is in front of her yasa tayi gefe tana juya lulu eyes ɗinta, yayi gaba abunsa, ta tsaya tana daidaita heart racing ɗinta kafin brain ɗinta tayi booting on, yanzu fa result ɗin gwajin Baba ya tafi dashi, toh taya Baba zaiga Doctor babu test ɗin, juyowa tayi taga har ya ɓace mata, yama fita daga block ɗin, a guje ta kwasa ta fito daga block ɗin itama, ta ringa kalle-kalle da waige-waige a compound ɗin asibitin sai kace mara gaskiya, a fili tace "wai nida lantarki", wani worker ta gani yana watering flowers ta isa gabansa tace "Assalamu alaikum, Malam barka dai", ya ajiye watering can ɗin yace "wa'alaykissam, yawwa barka", duk a daburce take tace "dan Allah kaga wani mutum da ya fito yanzun nan?", yace "ai mutane da yawa ke shige da fice ta ƙofar nan, gaskiya bazan iya tantancesa ba, amma ko zaki fasalta minshi wataƙila na ganesa", Hajar ba ta da wani option than to describe him, wani ƙulluto ne ya tsaya mata a wuya, how can she describe him?, toh tace me?, workern ganin ba tace komai ba yace "ko baki sansa bane?", ta gyaɗa kai tace "Eh bansan sa ba, amma dogo ne, shi ba fari ba kuma ba baƙi ba", worker ya ƙanƙance ido yace "topa", tace "gashin kansa me nannaɗewa kuma yana sanye da ƙananan kaya" ta runtse idonta sai kace wacca ta faɗi wani mugun abu, yace "Au Dakta wai?", Hajar tayi wani tunani tace "Eh shi", ya nuna mata wani direction yace "nan yayi", ta kalli direction ɗin tace "nagode", ta nufi direction ɗin da sauri, tsayawa tayi tana ƙarewa wajen kallo, ga wani entrance nan yana facing ɗinta, direct ta shiga entrance ɗin, wani sanyin AC ya daki fuskarta, gashi wajen so quiet and calm, few mutanen wajen ta tambaya, kuma amsa ɗaya suka bata wai bai shigo ba, ta fito duk guiwa babu ƙwari, ta ringa kallon makeken compound ɗin asibitin da mutanen da suke ta hada-hada, daga ƙarshe dai da ta gaji da dubansa ga rana sai kashe mata ido take kawai ta nufi hanyar ward ɗin da Baba yake, babu abinda zuciyarta take sai tafarfasa, sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga ward ɗin, sukay ido huɗu da Umma dake zaune kan darduma tana cin abincin da suka zo dashi, daga ita sai Anty Jamila, Maama da Nabilah sun tafi daman ba wani daɗewa sukay ba. Hajar ta ƙarasa gefen gado ta zaune kusa da ƙafar Baba da yake bacci, Umma tace "da baki gane wajen ba ai sai ki dawo, ba kije kiyi ta bulayi ba", Anty tace "yana ganki duk wani iri ne?", Hajar tace "takardar ce fa ta ɓata", Umma ta ajiye spoon ɗin hannunta tace "kamar ya ta ɓata?", Hajar ta fara jan fingers ɗinta tace "dana karɓo takardar a wajen Nurse kamar yadda kika gayamin shine a hanyar dawowa na kasa ganewa, shine na fita waje, a wajen ne iska ta ɗauke takardar ta shiga cikin silap ɗin kwata", Umma ta taɓe baki ta ɗauki spoon ta cigaba da cin abincinta ba tace komai ba, Anty tace "amma shine baki dawo da wuri kin sanar ba", Umma ta ɗago ta kalli Hajar tace "ƙarya take yi, da ita dai za a duba mahaifinki, idan kin salwantar da ita ke kika sani", wani takaici ya sake balbale Hajar kamar ta fashe da kuka haka take ji, Anty tace "Hajar da gaske kike ?", Hajar ta gyaɗa kai da sauri, wata matron ce ta shigo ta sanar da kowa ya fita za a bayar da magani, Anty tace "toh Adda Allah ya basa lfy, ni dai idan na fita wucewa zanyi", Umma tace "toh Jamila nagode, ku gaida gida", Anty tace "saina bar miki Hajar anan ko sbd wani temakon", Umma tace "A'a karki barmin ita, nima bazan daɗe ba zan koma gida, Naseer da Mu'azzam suna zuwa zan tafi", Anty tace "toh shknn, sune suke kwana dashi?", Umma tace "Eh", Anty ta ɗauki handbag ɗinta ta miƙe tana kallon Hajar tace "tashi mu tafi", Hajar ta tashi tace "Umma sai gobe, Allah ya basa lfy", Umma bata dubeta ba tace "Ameen". da suka fita farfajiyar asibitin Hajar ba abinda take sai faman baza idanu, ko kallon gabanta ma bayi take sosai ba, wani me motorbike ne ya kusan bigeta, Anty ta janyota gefe tace "ki kalli gabanki mana, kalle-kallen me kike haka?", sai a sannan Hajar ta maida hankalinta ga tafiyar da take. suna komawa gida Hajar ta shiga kichen ta fara preparing lunch, jollof rice ta dafa wacca taji attaruhu, a hankali take yanka cabbage ɗin gabanta a kan chopping board bayan ta gama goga carrots, time to time saita ja dogon tsaki tace "lallai ma mutumin nan", ƙarfe ɗaya da minti hamsin ta gama abinda za tay ta wuce ɗakinsu Hafsa, ta shiga toilet tayo alwala ta fito, darduma ta shimfiɗa tayi sallar azahar, tana idarwa ta miƙe ta linke darduman ta ajiye gefe, wayarta ta ɗauka taga missed call da two messages from Nura, karantawa tayi tana murmushi kafin ta shiga tura masa reply, tana tura masa message ɗin babu jimawa sai gashi yana kira, taɓe baki tayi ta kara wayar a kunne bayan ta ɗaga, Calmly tace "Salamu alayyykumm", Nura yayi slight voice smile yace "wa'alay kumussalam babe", tayi shiru ba tace komai ba, yace "ina kika saka wayarki tin jiya ina nemanki?", Hajar ta turo baki kamar tana gabansa tace "toh aii banida chaji", yace "toh yanzu kam anyi chajin ko?", tace "Eh", yace "gobe zanzo, kinga jiya ban samu nazo ba, gashi yauma inada appointment", tace "tom", yayi ƙasa da murya yace "saina tambaya ko?", tace "me?", yace "me yake damunki?, ki faɗa min?", Hajar taji kamar ta fashe da kuka daman tin ɗazu take cijewa, ga Umma na fishi da ita har yanzu bata huce ba, ga Baba ba lafiya, ga kuma baƙin cikin abinda wnn mutumin yayi mata, sosai ya ƙona mata rai, ko mene nashi na tafiya da papern oho, a hankali tace "Baba ne bashi da lafiya, an kwantar dashi a asibiti...", sai kuma ta fara kuka a hankali, Nura yayi ajiyar zuciya yace "me yake damunsa", tace "BP ɗinsa ne yayi high", yace "ki dena kuka kinji, zai samu lafiya Insha Allah", ta goge hawayen da ya zubo mata tace "tom", ta ɗago idanunta da suka fara canza launi ta kalli ƙofa, Hafsa ce ta shigo wacca ta dawo daga schl, Hafsa ta ajiye schl bag ɗin ta tana kallon Hajar, Hajar da waya kare a kunnenta tace "kun dawo?", Hafsa tace "yess, naga ana tsinkar flowers ai", Hajar ta harareta ta kwanta a gado tana sauraron abinda Nura yake faɗa mata. Hafsa tace "Eh lallai" ta fara cire uniform ɗinta ta ɗaura towel ta shiga toilet. harta fito daga wanka Hajar na maƙale da waya, ta buɗe press ta ɗauki kayan da zata saka tana satar kallon Hajar, Hafsa ta zauna akan stool tana rubbing lotion a fatarta. Hajar ta ajiye wayarta tana sauke ajiyar zuciya, ta miƙe zaune tana kallon Hafsa tace "wai har kin fito wanka?", Hafsa tace "Eh mana", Hajar tace "nida jiƙa-jiƙa", Hafsa ta cigaba da rubbing lotion tace "ai dole kice haka sbd lokaci ya miki ƙaranci na tsinkar flowers". Hajar tace "ke kika sani, ina Humaira?", Hafsa tace "tayi wajen Anty", Hajar ta gyaɗa kai ba tace komai ba. Hafsa ta ɗauki kayanta ta saka, ta kalli Ghana most gon kayan Hajar tace "Au baki shirya kayan a wardrobe ɗin ba", Hajar tace "nida ba daɗewa zanyi ba", Hafsa tace "oho miki, Anty ce dai tace na baki space, don haka muci abinci saina temaka miki ki shirya kayan a press".


★Nurain bai baro hospital ba saida ya gama komai da ya dace, ya ajiye aikinsa na good 8months, yayi submitting komai da ya dace, Office ɗinsa ya koma after that, ya tsaya wajen secretary Haleema yace ta kira masa Dr Marwan, Khaleel da sauran team members ɗinsa, with due respect tace "okay sir", Nurain ya wuce cikin Office ɗin, A kan kujera ya zauna wasu moments suna dawo masa a brain, ya kalli kujerar da Ruqayyah take zama, ya ɗauke idonsa daga wajen cause he don't want to think about her, lumshe idonsa yayi yana juyi kan kujerar da yake kai, a bazata yaji zuciyarsa ta sarƙe da tunaninta, a hankali yace "stubborn girl, ashe dai tana tsoro", ya zura hannunsa a pocket ya ciro papern, ya ringa kallon papern da take folded, yanayin papern ne yasa yayi unfolding ɗinta a hankali, kasancewar result ɗin dake rubuce a papern is inside his field ya fahimci komai, ya mayar da papern yadda take bayan ya linketa. Khaleel ne ya fara shigowa ya zauna kan soft sofas da suke hakimce gefe guda a Office ɗin, Khaleel yace "Gani Boss", Nurain na kallon wani makaken picturen heart dake office ɗin yace "Ohk, bari su Marwan su ƙaraso", Khaleel yace "Neh", few minutes kam Office ɗin ya cika da well trained team members of thoracic surgeon Dr Uthman, Nurain ya ringa kallonsu kafin yace "zanyi tafiya na 8 months, so i have to tell you this sbd we work together, kamar yadda idan wani uzirin ya kamani nake barin Dr Marwan incharge, to this time around ma shine, follow by Khaleel, i wish you people all the best",

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login