Showing 87001 words to 90000 words out of 114314 words
Chapter 30 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
ɓarayi ba zasu iya shiga ba gsky..", Abba yace "insha Allah this week zasu koma..", Hajiya ta katsesa da fadin "toh mai zai hana yau su tattara su tafi, nifa yau zan rugungunta na tafi, kamata yayi ma mu fita gidan nan tare dasu, nasan yanzu ma Umaru yana kan hanyar zuwa ɗaukata", da taushin murya Abba yace "Hajiya ku dan sake zama mana zuwa wani lokaci ko sati fa ba kiyi ba..", Hajiya ta girgiza kai tace "A'a A'a Muntari kasan dai ni adala ce, shekarata biyu a gidan nan banje gidan Salisusu ba ina nan, shima saina jingine masa shekaru biyu kafin na juyo nan idan Allah ya ara min lokacin". knocking door akay kafin aka buɗe aka shigo, Mami ta shigo da sallama, ta sanar da Hajiya cewa breakfast dinta is ready, Hajiya tace a kawo mata abincin nan anan zata ci, Mami ta juya ta fita, babu jimawa ta dawo da tray a hannunta, tayi serving Hajiya creamy groundnut pap with yummy beans cake. Mami na gama serving dinta ta tashi zata fita, Hajiya ta ajiye cup en pap tace "Khadijah...", Mami ta juyo tace "Na'am Hajiya", Hajiya tace "naga jikin ƴar taki da sauƙi toh shine nace me zai hana yau su tattara su koma gidansu..", Mami tace "Eh Alhmdllh ta samu sauqi sosai, amma dai bata gama shan drugs dinta ba, da sai nan da sati mai zuwa sai a mayar da ita ɗakinta lokacin insha Allah ta gama shan drugs en, amma yadda kika ce ai haka za ai Hajiya", Hajiya ta rausayar da kai tana cin ƙosai tace "ai shknn tinda kin kawo batun magani, shima mijin naki haka yace sai sati mai zuwa da yake bakinku ɗaya". kwanan Hajar hudu a gidansu Nurain, tin ranar da suka je wajen Hajiya bata sake fita daga part en Mami ba, everytime tana ɗakin da aka ajiyeta, tana dai fita palourn Mami ta gaisheta sai kuma ta koma ɗaki, Sosai suka saba da Noor sbd tare suke kwana, da rana kuma ta zauna ita kadai idan Noor ta tafi schl, ƙarfe biyar da minti huɗu Noor ta shiga ɗakin da Hajar take, dawowarta daga schl knn, wanka kawai tayi ta canza kaya, Noor tayi murmushi tace "masha Allah, waoh gsky kayan nan sun miki kyau", Hajar ta dubi kanta, straight skirt ne na english wears da shirt dinsa masu kyau, Noor din ce ta kawo mata su tinda daman kayanta take sawa, duk yawancin kayan da ta bata ƙanana ne amma decent, don Noor ta fi son su sbd tafi zama comfortable dasu, Noor ta ringa yaba kyan Hajar da kayan, sun fi yiwa Hajar din ma kyau don ita data saka sau ɗaya basu mata kyan haka ba, Hajar tayi murmushi tace "an dawo schl lfy?", Noor tace "lfy alhmdllh, za kici Noodles?'', Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh zan ci", daman kaɗan taci lunch da aka kawo mata, Noor tace "Ohk, let's prepare it together", Hajar tace "together?", Noor tace "yhap", ƙin yarda Hajar tayi wai ita bazata fita ba, daga ƙarshe ma tace ta ƙoshi, da kyar Noor tayi convincing dinta ta yarda, zumbulelan Hijab din da take sallah ta kirma, Noor ta bita da kallo tace "keda zaki kitchen meye kuma na saka hijab", Hajar tace "in ba dashi ba na fasa zuwa", tare suka fito main palour suka shiga huge luxury kitchen din gidan mai shegen kyau, kitchen island ma wani irin makeke, ga cupboards da drawers suma manya wanda suka zagaye girman kitchen din, Noor ta ɗakko pot kafin ta fara harhaɗo ingredients, Hajar daga gefe ta tsaya tana kallonta, within 15mins Noor ta gama dafa wata shaɗananniyar Noodles, ga fried egg with sausage, A babban plate ta juyo musu, Noor ta buɗe fridge ta ɗakko lemon kwali da ruwa ta bawa Hajar ta riƙe musu ita kuma ta ɗakko plate en Noodles en, a Main palour suka zauna wanda Hajar ba taso hakan ba, Still Hajar tayi tana kallon Noor ganin abinda ta ajiye musu a maimakon fork, Hajar ta ringa kallon tsinkayen tace "meye kuma wnn?", Noor ta ɗauki chopsticks din ta fara ci dashi, sosai ta iya amfani da Chopsticks, saida Noor taci loma uku amma Hajar ko attempting ɗaukar sticks en ma ba tay ba, Noor tace "ya naga ba kya ci?", Hajar ta ɗauki Chopsticks en gabanta ta fara ƙoƙarin ɗebo Noodles din, daga ta ɗiba sai ta zame, Noor ta ringa mata dariya kafin ta tashi ta shiga kitchen ta ɗakko mata fork, Hajar tace "tayi daɗi sosai", Noor tace "really, da fatan dai kin riƙe recipe din cause it's one of yaya Nurain's favorite", suna gama ci Hajar ta ɗauki plate din ta shiga kitchen dashi, Noor ta juya tana kallon stairs jin footsteps, tini ta ajiye cup din lemon da take sha ta tashi da sauri ta ruga ɗakinta, tsoron haɗuwarsu take sbd wata red cancel ya turo mata akan project dinta da ta tura masa hakan yana nufin shirme tayi kenan, gashi yace sai yayi punishing dinta idan shirme tayi, shiyasa take avoiding dinsa kar ya kamata, Nurain ya ƙarasa sakkowa downstairs yana kallon ƙofar part din Mami, kitchen ya nufa da cup din Coffee da ya gama sha, yana shirin murɗa handle kawai yaji an murɗa ta ciki kafin aka buɗe ƙofar, kanta a ƙasa tana tattare ƙasan hijab dinta da yake sharar floor, ji tay tayi karo da abu, ta ja baya da sauri ta ɗago kanta, girarsa a matuƙar haɗe yake kallonta, Hajar ta zuba masa lulu eyes dinta zuciyarta na bugawa, ita tsorata ma tayi shiyasa take masa wnn kallon, da sauri ta janye idonta tabi ta gefensa zata wuce tinda akwai space sosai da yake ƙofar babba ce, ( mu bawa juna haƙuri daii ) shine abinda ya amsa a brain din Nurain within 1sec, this time around din ma junan zasu bawa haƙuri ko kuma ita zata basa, hannu yasa ya fixgota baya ya mayar da ita kitchen din, yace "kee are you mad?, dutse kika bige ne?..", Hajar ta yamutsa fuska tace "wa ya sani ko dutsen ne".......✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{41..}
Nurain was more than shocked jin abinda ta faɗa, wnn ƴar kucular yarinyar ce zata gaya masa haka, nawa take a wajensa, with hatred yake kallonta, itama Hajar da hatred din take kallonsa har wani zugii take ji a zuciyarta, da mugun sauri ta sake kewayesa zata wuce, hijab dinta ya taɗeta saura ƙiris ta baje a ƙasa tayi saurin dafa handle, a fusace Nurain ya juyo da nufi koya mata hankali, a ransa ya ji dama faɗuwar tayi ta dauje guiwa, Mami da ta fito daga part din Abba a daidai lokacin da Hajar ta taɗe snn kuma lokacin da Nurain ya juyo a fusace sai taga kamar Nurain din ne ya hankaɗota, Hajar da bata lura da presence din Mami a palour ba tayi sauri ta zagaya ta bayan kujeru ta shiga part din Mami, Mami ta bita da kallo kafin ta fara tafiya towards Nurain daya daskare a tsaye, tace "daman ka na gidan nan Nurain..?", don gaba ɗaya ya ƙauracewa part dinta, kwana biyar knn bai shiga part en ba, saidai ya gaisheta a main palour ko kuma part en Abba idan sun haɗu a can, Nurain yace "yeah, shirye shiryen kowama work nake so am busy in my room.." da haka ya shige kitchen, Mami ta bisa cikin kitchen din, ya ajiye cup din dake hannunsa a sink yana sauke ajiyar zuciya, Mami tace "i saw what you did Nurain", ya juyo ya zuba mata idanunsa da kana gani kasan ransa a ɓace yake ba tare da yace komai ba don bai fahimci me take nufi ba, tace "why did you pushed her..?", Nurain was confused don brain dinsa ma ta kasa basa hadin kai yayi thinking, bai ma san me zai ce ba sbd bai gane me take cewa ba, da kyar ya samu kansa da cewa "Mami i don't get you", sosai ran Mami ya fara ɓaci kawai ta juya tabar kitchen din. Hajar na shiga ɗakin da take ta kafa goshinta a bango tana jin suya a ƙahon zuciyarta, hawaye ne suka fara bin cheeks dinta kafin ta fashe da kuka gaba ɗaya, a haka Mami ta shigo ɗakin ta tarar da ita, har harɗewa ƙafafuwan Mami suke ta iso wajenta ta riƙe both shoulders dinta tana tambayarta me ya faru, Hajar ta girgiza kai alamar ba komai tana ƙoƙarin danne kukan, Mami da hankalin ta ya tashi sosai tace "talk to me my dear what happened..?", kawai girgiza kai Hajar take taƙi tace komai, gashi kuma ta kasa haɗiye kukan sbd zuciyarta a raunane take, da kyar Mami tayi consoling dinta duk da taƙi gaya mata damuwarta. Hajar ta shiga toilet ta wanke fuska ta fito, wani irin fige hijab ɗin jikinta tayi sbd ƙamshin Nurain da ta fahimci akwai ajiki, kodai hancinta ne ke jin hakan, tayi wurgi da hijab ɗin a tsakar ɗakin, ta juyar da kanta gefe tana kallon damtsenta inda ya rutsa ya fuzgota baya, cike da takaici tayi kwafa tace "Allah ya saka min da ka taɓa ni..."
★Maama ta saki tsintsiya da abin kwasar sharar da ta sharo uban dattin dakinta wanda ke ɗauke da mushen kuɗin cizo da aka zubawa piya piya daren jiya tana kallon ƙattin da suke shigowa da buhunhunan shinkafa, da catoon na spaghetti Macaroni da Indomie, ga kuma manya mayan jarkokin Mai biyu, Baba ne ya shigo yana nuna musu inda zasu ajiye kayan, har suka gama shigar da kayan ɗakin Baba Maama bata dena kallonsu ba, Nabilah ma dake zaune gaban murhu tana jefa ɗan wake sakin baki tay tana bin kayan abincin da ido, har kumfar ɗan waken da ta zuba a tukunya ta fara zuba bata sani ba, Baba ya sallami yaran da suka shigo da kayan kafin ya ja ƙofar ɗakin nasa ya saka mata kwaɗo, Maama ta washe yalayen haƙoranta tace "sannu da ƙoƙari mal, wnn irin uban kayan abinci haka, ai ma shekara muna ci wllh, Allah ya biya buƙatu ya bunƙasa hanyar nema, shine nace dama ba ɗakinka aka kai ba ga kitchen nan da ba a amfani dashi sai a ciro shirgin ciki a kai bola a zuba kayan abincin anan, kaga ba a ringa takura maka ba idan zamu ɗiba, wllh tllh dama a kitchen aka ajiye...", Baba dai kawai jinta yake, ta sake cewa "idan ka yarda yanzu sai na ci ɗammara na fara fiddo shirgin kitchen din, ina da ma piya piya saina feshe sa da shi gudun ƙananan ƙwari..", direct Baba yace "Ai ba namu bane garar Hajara ce", Maama ta zaro mici micin idanunta tamkar an kwantali ɗata tace "kam bala'i da masifa, me kake nufi mal, wai kanaso kace min wnn uban kayan Hajara za a kaiwa da sunan gara?", yace "Eh Rabii, kayan garar Hajara ne", Maama tayi wani murmushin takaici tace "wasa ma knn, nan da kake gani na ba karen hauka ne ya cijeni da zan zauna inaji ina gani a ɗebi kayan nan akaiwa Hajara ba, idan kai da matarka kun makance to ni garau nake, muna fama da yar Hausa Mai da yaji da tuwan dawa shine za a kwaso yar gwamnati da abincin kwali a kaiwa yar so ko, ni ban taɓa ganin inda ake haka ba wllh, ai wnn ƙarawa mai kuɗi ƙarfi ne, ce muku akay babu abinci a gidan nata ne, koda yake ashe baku je kunga gidan ƴan yankan kan ba..", Baba yace "sai kuma kiyi, gara dai sai an kai mata, babu ruwana da cewar masu kuɗi ne, mutuncin ƴata zan kare..", Maama ta fara fyace majina tana sharar kwalla don sosai maganar tayi mata ciwo tace "wllh Allah sai ya saka min nida ƴaƴana yadda ake mana cin kashi a gidan nan...", Baba ya haɗe rai yace "Da Hajara da su Maimuna duk ɗaya suke a wajena, idan kina ganin rashin adalci nake yi akan su to kwa kin yaudari kanki, dukka abinda na yiwa Hajara insha Allah irinsa zan maimaita idan Allah ya kawo lokacin auren su Maimuna" da haka ya barta a wajen ya matsa kusa da ɗakin Umma ya kirata, Umma ta amsa ta fito tace "gani mal", duk tana jin abinda ya faru daga ɗaki, Baba yace "Jamilah ce zata amso kayan zaƙin ko?", Umma tace "Eh, in Allah ya yarda ranar juma'a za a kawo", yace "yawwa gobe knn, zuwa ranar asabar ko lahadi sai a kai mata garar ta", Umma tace "toh Allah ya nuna mana da rai da lfy, Allah ya saka da alkhairy", yace "Ameen" ya fita daga gidan, Nabilah da take jefa ɗan wake ta ɗago kai ta dubi Maama tace "dan Allah Maama ki ringa ragawa Babanmu, nifa yanzu na zama ƴar ba ruwana wllh, idan ma bai mana irin na Hajara ba ai Allah na gani..", Maama ta rausayar da kai tace "idan bai muku ba ni zan muku da yardar Allah, kuma sai Allah ya kawo muku mazaje wanda suka kere dan yankan kan da waccar shegiyar ta aura, ai tin yanzu ma na fara gani tinda Alhaj ɗin Maimuna a Habuja yake, kinga kuwa ai yanada kuɗi". Umma na komawa ɗaki tayi dialing numbern Anty Jamilah, tana ɗagawa bayan sun gaisa Umma tace "Jamilah ya maganar mai dubulan da alkakin nan ne..?, da ƙarfe nawa zata bayar goben..?", Anty Jamilah tace "da safe tace wajen ƙarfe goma", Umma tace "tom, ga su shinkafa da taliyar har an kawo, kin san mal da karfin hali tinda yaji cewa ba a jerawa Hajara kayan ɗaki ba ya dage akan sai an mata gara, yace bazai bari mutumcin ƴarsa ya zube ba ace ba a kaita da ko tsinke ba, kuɗin kayan ɗakinta da aka siyar dasu yayi amfani wajen siyayyar garar snn kuma yace ragowar nata ne", Anty Jamilah tace "Alhmdllh, Allah ya saka da alkhairy, ai hakan shine dai dai wllh", Umma tace "wai ya ƴar taki kuwa? ni kam bana samun wayarta...", Anty Jamilah tace "nima haka Adda, ashe ma tana gidan su mijin, da naji bana samunta a waya shine na kira numbern wacca nake zaton kwanwar mother in law dinta ce wacca na amsa a wajenki ranar da muka dubota a hospital, shine fa take gayamin cewa ai Hajar na gidan surkanta", Umma tace "tofa ashe haka akay", daga haka sukay sallama.
★Da daddare da misalin tara da rabi, da ɗan sauri Nurain yake sakkowa daga stairs ya zura right hand dinsa a pocket na dark brown sweat pant dake jikinsa, left hand din kuma yana shafa tsakiyar cikakkiyar sumar kansa, hanyar part din Abba ya nufa, ya murɗa door handle na great room din kafin ya shiga da sallama, ya cire soft room slippers dinsa ya ƙarasa ciki, har zai zauna kan carpet Abba ya nuna masa sofa don haka ya zauna a sofar, Mami ta gama zubawa Abba Moringa tea ta miƙa masa, ya amsa yana murmushi yace "thank you..", tace "ur welcome dear..", Mami ta ɗago sukay ido huɗu da Nurain, ɗauke kanta tayi ta tashi ta shiga bedroom din Abba, Abba ya ɗauki tean yayi sipping, sip uku yayi snn ya ajiye Mug din, ya rage volume din TV, Abba ya dubi Nurain da yake jiran kiran da ake masa yace "ya project din Mamana tace ta turo maka zaka duba mata...?", Nurain yace "Yeah she try", Abba ya gyaɗa kai yace "good", after like 5secs Abba ya nisa yace "Uthmaan kasan me yasa na kiraka nan..?", Nurain dai kawai kallon Abba yake ya girgiza kai yace "A'a..", Abba yace "lokacin da Allah ya yiwa first wife dina rasuwa the mother of Sakeena, Sakeena was just 3months old lokacin da mamanta ta rasu, duk wanda yaga Sakeena sai yaji tausayinta sosai, dangin mahaifiyarta sun so su amsheta su riƙeta ni kuma nace bazan basu ba sbd tana ɗebemin kewar mahaifiyarta, a koda yaushe Sakeena na wajena sai idan zan fita aiki ne nake kaita wajen Hajiya idan na taso kuma na ɗakkota mu koma gida, Hajiya tayi min mgna akan na ƙara aure amma ni kuma sam aure ya fita a raina, a haka har Sakeena ta cika wata bakwai a lokacin ne kuma na tafi Abuja wani aiki", Abba yayi murmushin manya snn ya cigaba da magana yace "ai sai dawowa nayi daga Abuja na tarar da gidana a buɗe an kawo min mata, aikin Hajiya ne, itace ta shiga ta fita ta haɗa aurena da Maminku tinda ƴar Aminiyarta ce, Hajiya tayi kicin kicin ta ɗaure fuska da ta ganni kawai warkajaminta take, ban kai ga mata magana ba tace min ai Uwa ta yiwa Sakeena, ai kam dai Hajiya gave Sakeena the best Mother ever domin kuwa hannu bibbiyu Mami ta riƙeta tamkar ƴar cikinta, ni kuma Allah ya musanya min ita da Marigayiyar mata ta, sosai na samu peace of mind wllh, your Mother is a good woman..", Abba ya dakata yana sauke ajiyar zuciya yace "kaga biyayyar da nayi ma Hajiya a tashar da ta ajiyeni, nine na kasance a farin ciki da kwanciyar hankali, don good wife ita ke riƙon gida ba kuɗi da kyale kyale ba, kasan me yasa na baka brief storyn nan??", Nurain yace "No Father", Abba yace "sbd kaima ka shiga irin halin da na shiga Son, saidai nawa da naka akwai bambancin amma kuma suna kamanceceniya, hankalinka da nutsuwarka da sanin kai din waye da kuma iko yasa na aura maka yarinyar nan", nan Abba ya shiga labarta masa yadda komai ya wanzu har ya aura masa Hajar, Abba yayi sipping tea yace "ina da babban hope akanka Son shiyasa na tafi kai tsaye na amso maka auren yarinyar nan, amma look at what happened you are trying to do something da ban taɓa tsammani ba, Uthmaan wllh da nasan za kace sakin yarinyar nan za kai bazan aura maka ita ba, wai ni nan gata na gwada maka snn kuma na haɗa da taimako, ranar nan da Hajiya tace a bar maganar saki kawai shiru nayi