Showing 51001 words to 54000 words out of 114314 words

Chapter 18 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

Zainab ta turo da steaker ta duka. murmushi Hajar tayi ta rubuta "ban jin duka, malama ki canza topic, bana son wnn zancen", Zainab ta turo "Allah ya bawa mai sonki haƙuri", Hajar ta tura mata "Ameeennnn.." sosai chatting ɗinta da Zainab ya sanyaya mata zuciya, sai bayan sallar la'asar Umma ta dawo gida, Hajar ta mata sannu da zuwa tace "ya hajiya Iyalluwa", Umma ta mata daƙuwa tace "in kinje kya kirata da Iyalluwa, me kika dafa da rana", Hajar tace "taliyar hausa da manja", Umma ta cire hijab ɗinta tace "waii wnn ba cimar malam bace, tashi ki tankaɗen gari na ɗora tuwo", mikewa Hajar tayi tace "maƙiyin Abdallah knn, ya tsani tuwo, duk ranar da akay tuwo bazai ci ba saidai a dafa masa indomie", garin tuwo dake cikin buhu ta ɗauka ta fita, saida ta hura mangal ta ɗora ruwa snn ta zauna tankaɗen, tana gama tankaɗen already ruwan ya tafasa tayi talge. Maama ta fito toilet ta ajiye butar hannunta bakin rariya, har zata shiga ɗaki sai kuma ta fasa ta tsaya akan Hajar tace "kee sbd baki da kunya da mutunci har ni zan aiki Sabra ki hanata zuwa", Hajar ta cigaba da gyara kayan miyar da za tay miya tace "ni ba hanata nayi ba", Maama ta lafto ashar ta danƙara mata tace "za kimin shiru ko saina kifa kanki a talgen tuwan nan", Hajar ta turo baki ta miƙe zata bar wajen, fuzgota Maama tayi ta daki bakin tace "nace rashin kunya zaki min kike turomin baki sai kace an mari kare", Hajar ta kalli ƙasa tana jin kamar ta kurma ihu sbd takaici, rankwashi Maama ta zuba mata a kai snn ta hankaɗeta, saura ƙiris ta faɗa kan tukunyar dake kan wuta tana zaɓalɓala da talgen tuwa, Maama tace "saina miki ƙafa ɗaya idan kika sake shiga gonata", da sauri Hajar ta shiga ɗaki sbd kukan da ya cicciyota, a ƙasa ta zube ta rushe da kuka, Umma ta kashe rediyon da take ji jikin waya tace "lfy Hajara?", Hajar dai ta kasa cewa komai kawai kuka take zuciyarta na tafarfasa, ita babban takaicinta da aka hanata ramawa, sosai hankalin Umma ya tashi tace "ciwon marar ne?", Hajar na shessheƙar kuka tace "ba waccar matar bace da ƴaƴanta", Umma ta kunna rediyonta tace "ai kam aiki ya sameki, ruwan idonki daf yake da tsiyayewa, kin gama haɗa miyar?", Hajar ta girgiza kai tace "A'a, kayan miyar fa nake gyarawa waccar matar ta takura min", Umma ta miƙe tace "bari kiga na ƙarasa kar magariba tayi ba a gama abincin dare ba" ta fita. washe gari Monday Mu'azzam ya fito tsakar gida da kuftarsa hartin da wando, agogon wayarsa ya duba yaga ƙarfe takwas harta gota, tsaki yayi ya jingina da bango, shi kam yaga ta kansa Baba ya haɗasa da ƴaƴan Maama marasa ta ido, shi ko kallo ma basu ishesa ba, ba ruwansa da su tinda ya lura ba mutunci suka cika ba, tasa ƙanwarma da suke uwa ɗaya da yaga tana shiga sabgarsu magana ya dena mata, har takwas da rabi yana tsaye wajen, ɗakin Baba ya leƙa yace "Baba har yanzu fa basu fito ba", Baba yace "har yanzu" ya tashi ya fito, ƙofar ɗakin Maama ya buga, Maama ta fito tace "A'a malam lfy?", yace "Sa'adatu da Maimuna su fito a mayar dasu makaranta", Maama ta gwalo micimicin idanunta tace "makaranta mal, wace irin makaranta ana zaune ƙalau?", yace "su fito su wuce lokacin na ƙurewa gashi kuma suna ɓatawa wnda zai kaisu lokaci", Maama ta riƙe baki tace "Eh ba shakka, toh waye wanda zai kai sun?, naga duk yayyen nasu basa gari", kai tsaye yace "Mu'azzam ne zai kaisu su fito yanzu", taɓe baki tayi tace "ai kwa dai bacci suke", Baba yace "tashe su, nan da minti biyar na gansu a waje" ya juya ya koma ɗakinsa, Maama ta hura hanci tace "toh idan ma na tashen su haka zasu tafi makarantar ciki kwalam, sai dai shi mai kaisun ya tsaya su karya kumallo nanda awa biyu ehe", da gayya ta faɗi hakan tana yiwa Mu'azzam mugun kallo ta shige ɗaki, da kyar Maama ta tashi Sa'adatu da Maimuna da suke bacci tamkar mushe, saida suka daɗe suna diminiya snn suka fito, lokacin kam har tara tayi, fuskar Mu'azzam kamar ta bujumin sa yayi hanyar soro, suka bi bayansa. ƙarfe sha ɗaya da rabi suka dawo gida, Mu'azzam ya yiwa Baba bayanin komai, Maimuna jss3 aka kaita, Sa'adatu kam dilhu dankali da makani knn daman ƙwaƙwalwar fanko ce da kyar aka barta a jss2.


★Ƙarfe takwas da rabi na safe Ruqayyah ta fito daga wanka, box ɗin kayanta da ta ɗakko jiya daga room ɗin Momy ta buɗe, daman ta kwafe a ranta bazata mayar da kayanta wardrobe ba har sai an ɗaura mata aure da dearest snn zata jera a press ɗinta ta gidan Nurain, ga kayanta ga nasa, sassanyan ƙamshinsa ya ratsa nata kayan, uniform ɗinta na Nurses ta saka, ta ɗora black Abaya a saman uniform ɗin, gaban mirror ta tsaya tana kallon fuskarta, sai kace wata taɓaɓɓiya haka ta ringa gwada yadda zata bawa Nurain haƙuri da irin kalaman da zata gaya masa, chapette mai strawberry ta shafa a pink lips ɗinta, tasa pinky finger ta kwantar da eyebrows ɗinta, ta sake gyara zaman V-shapped hijab ɗinta da kyau, perfume mai sanyin ƙamshi ta fesa sama sama, takalmi black ta sanya sandals ta ɗauki jaka ta fita palour, direct kitchen ta wuce dan ta jiyo motsin Momy a nan, ganin Momy ta kunna gas tana girki Ruqayyah tace "Momy na fa dafa breakfast, na ajiye muku a warmer...", Momy ta ajiye serving ɗin da take juya sauce tace "So, ai bance zanci ba, kinsan bana son high carbohydrate da zaki dafa doya da kwai tsura ba vegetables", Ruqayyah tace "nayi tomato sauce aii", yamutsa fuska Momy tayi tace "too much Acid knn". Ruqayyah dai ta fahimci cewa har yanxu Momyn ta bata gama hucewa ba, a ƙasan ranta tayi alƙawarin sai ta goge stain ɗin da tayi musu a zuciya, daga ta rarrashi dearest mgana ta ƙare. tace "Momy zan wuce aiki", Momy ta cigaba da aikinta tace "Ohk, kin sanar da Baban ki?", Ruqayyah tace "No, kafin na fita zan gaya masa", Momy ta taɓe baki ba tace komai ba, bayan Ruqayyah tabi da kallo tana girgiza kai tace "Allah ya baki dama kinsa ƙafa kinyi fatali da ita". Da sallama Ruqayyah ta murɗa door handle ɗin palourn Daddy, durƙusawa tayi ta gaishesa, Daddy ya amsa ba yabo ba fallasa yana duban dress ɗin jikinta, tace "Daddy zan fita aiki", his piercing eyes fixed on her yace "Okay, sai ki rubuta resignation letter ki submitting kafin ki dawo gida", a razane ta gwalo ido waje, gashi with seriousness on his voice ya fadi hakan, har ruwa ya ciko idonta tace "resignation letter?", yace "are you questioning me?", yarfe hannu tayi tace "No Daddy, i won't dare", ya daka mata tsawa yace "get lost my friend". da sauri ta miƙe ta zabga tuntuɓe da jikin kujera, saida tayi karo da bango har kanta ya sara snn ta lalubi ƙofa ta fita, tana zuwa palour ta sulale ƙasa tana yarfe hannu ta fashe da matsanancin kuka, Momy ta fito kitchen ta ringa kallonta cike da mamaki, har ƙoƙarin birgima Ruqayyah take sbd raɗaɗin da zuciyarta ke mata, Momy ta haɗe gira tace "meye haka?", Ruqayyah ta taso da gudu ta rumgumeta ta cigaba da kuka, Momy tace "ba tambayarki nake ba", Ruqayyah ta ɗago kanta daga shoulder ɗin Momy tace "Daddy ne yace nayi resigning from work..", Momy ta buɗe baki tace "ban gane ki bar aikinki ba", Ruqayyah na shessheƙar kuka tace "haka yace idan naje aiki yau sai na rubuta resignation letter na kai, na shiga uku Momyyy, wllh i love my job", Momy ta zameta daga jikinta ta shiga wajen Daddy, malamala Ruqayyah tayi a ƙasa tana hawaye, after 10mins Momy ta fito fuskarta a haɗe, Ruqayyah ta ɗago idanunta da suka rine tana kallonta, Momy tace "tashi ki tafi, ki rubuta resignation lettern ki dawo gida da ita", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tace "tom, kar nayi submitting?", Momy tayi tsaki tace "ai kinji me nace" ta nufi room ɗinta. saida Ruqayyah ta koma ɗakinta ta wanke fuska snn ta fita daga gidan, har ta isa Hospital tunani kawai take, ai abun sai yayi mata yawa ga rashin dearest ga kuma rashin aiki, tsaf zuciyarta za tayi bombing idan ta rasa these two valuable things. a hankali take tafiya cikin babban compound din, wajen da ake parking motoci ta tsaya tana kallo, idonta ya sauka a parking space din thoracic surgeon Dr Uthman, babu mota a parking space din nasa, tayi murmushin ƙarfin hali tace "dearest bai ƙaraso ba". Nurse station ta wuce, gaisawa sukay da colleague ɗin nata su biyu dake zaune wajen, Ruqayyah tace "ina Jiddah?", ɗaya daga cikin Nurses din tace "ai kam ina jin ta tafi gida da yake jiya night tayi", Ruqayyah tace "Ohk". wani room da suke ajiye ƴan kayansu na Nurses ta shiga, kettle ɗin ruwan zafi ta nufa ta kunna, ta buɗe locker dinta ta ɗakko mug da coffee powder, coffee mai rai da lafiya ta haɗa snn ta fito daga room ɗin. barin Nurse station ɗin tayi ta wuce Office ɗin Dr Uthman zuciyarta na harbawa, a garƙame ta tarar da office ɗin, kan silver chair da ke wajen Office ɗin inda patient ke jira ta zauna, almost 1hour babu alamar wnda take jira zai zo, har secretarynsa ma bata zo ba, Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya deeply in thoughts ta dubi Mug ɗin hannunta da coffeen ciki ya gama hucewa, ta duba agogon dake wrist dinta taga har 11am ta wuce, murya can ƙasan maƙoshi tace "Dearest". ta ciro wayarta daga pocket ta shiga kiran layinsa, saida ta kira sau goma amma switched off, hankalinta ne ya kuma tashi, Sha daya da rabi na cika ta tashi ta nufi Office din Dr Marwan, patient ta tarar yana dubawa don haka ta samu space ta zauna, Dr Marwan ya gyara zaman glasses dinsa yana rubutu jikin card, patient din ya miƙawa card ɗin yace "sai next week", patient ta amshi card ɗinta snn ta fita, Ruqayyah da hankalinta ba a jikinta yake ba tace "barka da safiya Dr", Dr Marwan da ke mata wani weird look yace "yawwa A Nurse", tace "ya aikin?", yace "Alhmdllh, wai ina kika shiga ne A Nurse?, har mun fara samun matsala wajen anesthesia", murmushin yaƙe Ruqayyah tayi tace "Egypt naje, yanxu kam ba ku da matsala tinda na dawo", yace "great, Khaleel ma ya gama complain ɗinsa", tace "yau ba ku da surgery ne naga Dr baizo ba har yanzu?", file ɗin dake kan table ya shiga buɗewa like he don't care yace "Boss yana India, this Friday ya tafi". tamkar wata statue in human form haka ta ringa kallonsa, shirun da yaji tayi ne yasa ya ɗago idanunsa ya kalleta, kallonsa yaga tana yi yace "A Nurse, kinyi shiru?".......✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{26..}
Wannan time ɗin ma dai Ruqayyah a ciki ta ji bugun zuciyarta, har wani darkness ne ya rufe mata sight, sama sama taji muryar Dr Marwan, a firgice tace "Dr, kamar dai banji me kace ba..", yace "i said kinyi shiru..." da sauri ta katsesa tace "No ba wnn ba", kallonta ya ringa yi ganin she isn't herself yace "ohk, which one?", tace "you said something like Boss yana India, this Friday ya tafi", he can't help it dole yayi blushing yace "Ohh you heard it, am jet serious baya nan, sai nanda 8months insha Allah zamu gansa", ƙirjinta ta dafe tace "8months..", katseta yayi yace "A Nurse i thought you are here for something serious, but i have patients waiting outside", tamkar wacca aka zarewa spine haka ta miƙe tace "Alright, thank you for the little time" da haka ta nufi door ta buɗe ta fita, da kyar ta isa Nurse station cause har yanzu darkness ɗin da yayi mending sight ɗinta bai gama fading ba. room ɗin dake station ɗin ta shiga, tsaye tayi tamkar wata statue, a tare ƙafafuwanta da hannayenta suka fara karkarwa sai kace wnda aka jona musu shocking machine, ta dubi Mug ɗin hannunta mai ɗauke da coffeen da ya zama tap water tsabar hucewar da yayi, tasss Cup din ya faɗi ya tawarwatse, two seconds da faɗuwarsa itama ta bisa ƙasan. kuka take son yi amma ta kasa, tears sun ƙafe a idanunta, kawai mgnar Dr Marwan ce take amsa ƙuwwa a kwanyarta, she spent 15 good minutes durƙushe tana kukan zuci, ta lumshe idonta da ƙarfi, she wish this is nothing but a nightmare, ita kanta tasan she was just fooling herself babu wani nightmare. wata colleague ɗinta ce ta shigo, kallonta ta tsaya yi kafin ta dubi broken cup ɗin dake ƙasa tace "Ruqayyah are you okay", Ruqayyah ta miƙe tana murje idonta wanda take fatan hawaye ya cikosa tace "partially, kai na ke ciwo Amina", Amina tace "ohh sorry bari na kawo miki drug", tsugunnawa Ruqayyah tayi ta fara picking pieces ɗin broken cup ɗin tace "don't burder I'm going home", Amina tace "Okay lemmi help you", Ruqayyah ta tashi ta dafe kanta tace "thank you", tarkacenta ta ɗauka ta bar asibitin da ya zame mata one living hell, a wani book shop ta tsaya ta siyi plain sheet da envelope snn ta fito ta tari Napep ta wuce gida, kafin taje gida ciwon kan da ta kirawa kanta ya lulluɓeta, a ɗan madaidaicin compound ɗin gidan nasu ta tsaya, ta zauna akan dakalin shiga main building ɗin, jakarta ta buɗe ta ɗakko pen da plain sheet ɗin da ta siya ta ɗora akan jotter, tana ɗora pen kan papern hannunta ya ringa rawa, da kyar ta gama rubuta umarnin da Daddy ya bata, tayi folding papern ta saka cikin envelope amma bata liƙe ba, tashi tayi ta shiga ciki da sallama, Momy dake zaune palour ta amsa, Ruqayyah da kanta ya fara juya mata tace "Momy barka da gida, na dawo", Momy ta kalli agogon dake palourn tace "da wuri haka", Ruqayyah ba tace komai ba, Momy ta taɓe baki tace "ina resignation lettern?", Ruqayyah ta miƙe mata white envelope dake hannunta, amsa Momy tayi ta ajiye hannun kujera, Ruqayyah tace "Momy na shiga ciki" ta wuce room ɗinta, da ido Momy ta bita ganin yadda ta dawo odd, she looks disturb and weak. wunin yau Ruqayyah bata ji daɗinsa ba, tama rasa meke damunta, gaba ɗaya ta kasa figuring out what is happening to her, abinci ma saida Momy ta kirata tace mata taci snn taci kaɗan, that was bayan sallar la'asar, tinda taci ta koma ɗakinta har akay sallar magrib da isha bata fito ba, tana kwance kan tiles tana juye juye Momy ta shigo, kallonta ta ringa yi kafin tace "ke me yake damunki ne waii?", zaune Ruqayyah ta miƙe tace "ba komai Momy", ai ko karen hauka ne ya cijeta bazata iya faɗin damuwarta ba, daman Momy ba haƙura ta gama yi ba tasan tsaf za tace mata Allah shi ƙara or something that will add salt to her fresh wound. Momy tace "ki sameni a palourn Daddy yanxun nan, kuma in kinje karki ce komai haquri kawai zaki basa", Ruqayyah ta gyaɗa kai, Momy ta juya ta fita. Ruqayyah ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta saka ta fita, zuciyarta na lugude ta shiga palourn Daddy, rakuɓewa tayi gefe saman carpet ta zauna, Daddy ya ɗauki envelope da ke gefensa ya wurga mata yace "ni zaki kawowa ko ni na baki aikin?", Ruqayyah dai kanta a ƙasa tace "sorry Daddy, dan girman Allah kayi haƙuri, wllh i learn my mistakes", keenly yace "wane mistake?", kuka ta ringa yi kamar ranta zai fita tace "kayi haƙuri dan Allah..", wani ɓoyayyen ajiyar zuciya yayi baice komai ba, sai a lokacin Momy dake zaune palour itama tace "ayi mata afuwa Alhaji, wnn shine first time da tayi wronging namu amma kuma she won't go free ayi mata wani hukuncin dan Allah", shiru Daddy yayi na wani lokaci kafin yace "da farko ma dai ina yarinyar taje?", Momy ta kalli Ruqayyah tace "talk", Ruqayyah ta sharce hawayen idonta tace "Egypt naje", baki buɗe Momy tace "Ruqayyah me ya kaiki Egypt?", Ruqayyah tace "kuyi haƙuri dan Allah..", wani tsawa Momy ta daka mata tace "wnn ba zancen haƙuri bane magana za kiyi malama", Ruqayyah ta kwantar da murya tana shessheƙa tace "wani aiki naje nema amma ban samu ba...", Momy tace "karki bari na sake tambayarki Ruqayyah, I'm giving you this last warning, ki gaya min komai", Ruqayyah ta share zufar dake keto mata tace "few months kafin a kawo kuɗin aurena na cike wani form online na wani aiki da ƙasar Egypt take bayarwa na waɗan da suke da karatu a fannin lafiya, aikine na shekara ɗaya mai kyau, bayan na tura musu form ɗin suka turomin da saƙon cewa zasu nemeni domin yin interview, ban sake samun wani message ba har sai ranar wata alhamis ranar mother's eve ɗina, tsakar dare na ga message cewa anyi hiring ɗina don haka kafin ranar Monday na kasance a garin Cairo, ban tafi haka ba saida na ajiye muku latter ai kuma shima Nurain na tura masa saƙon cewa ya jirani zan dawo, ranar juma'a na hau jirgi zuwa Abuja kamar yadda suka ce nan ne meeting point ɗin da zamu taru kafin mu wuce Egypt, A Cairo Monday ta riskeni, akay mana interview amma ni banci ba, don haka suka ce na ƙara gaba baza a ɗaukeni ba, da kyar na samu aikin da nayi na samu kuɗin ticket din jirgi na dawo Nigeria, Momy Daddy wnn shine gaskiyar dan Allah kuyi haƙuri na ɓoye muku da nayi, ina tsoron ku hanani shiyasa ban gaya muku ba...", Daddy ya jinjina kai ya kalli Momy yace "barin aikin shine hukuncin da ya dace da ita...", Momy dai tayi tagumi takaicin ƴarta ta ya gama cikata, ajiyar zuciya tayi tace "get

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login