Showing 102001 words to 105000 words out of 114314 words

Chapter 35 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

wanda shine chamber na ruwa, sosai zaman wajen yayi mata daɗi don ji tayi kamar an cirota daga maƙabarta, ba tasan iya awannin da ta ɗauka zaune a wajen ba tana tunani iri iri, motsin zubar ruwa ta jiyo daga front din gidan, tashi tayi ta ringa bin inda motsin yake, mai gadi ne ya kunna famfon compound din yana alwala, ɗan russunawa yayi ganinta ya kashe famfon yace "ina wuni Hajiya..", Hajar ta mayar masa da gaisuwar don ta ganesa ranar da suka dawo gidan shi suka tarar, Inuwa ya duƙar da kai yace "wani abin za a amso miki hajiya...?", Hajar ta girgiza kai ta juya ta koma backyard din, ciki ta koma don yin sallah, tana idar da sallah wayarta ta fara ringing, ta ringa kallon screen ɗin wayar ganin number ke kiranta kuma bata san numbern ba har kiran ya katse wani ya sake shigowa, picking tayi ta kara a kunne ba tace komai ba, wani murmushi tayi bayan ta ɗau murya tace "Noor...", Noor tayi dariya tace "ta ya akay kika gane...?", Hajar tayi ƴar dariya tace "your voice mna", Noor tace "toh ykk ya gida...", Hajar tace "lfy lou and you..?", Noor tace "am great wllh..", Hajar tace "good, toh yaushe zaki zo..?", zaro ido Noor tayi tace "not soon..", Hajar ta marairaice murya tace "kefa kika ce zaki zo..", Noor tace "yeah zan zo amma ba yanzu ba..", Hajar tace "toh shknn sai kinxo", sun ɗan jima suna hira da Noor kafin daga karshe Noor tayi mata sallama, Hajar ta tashi ta naɗe darduman da tayi sallah, sai kace wata ƴar kurkuku haka take jin rayuwar gidan, daga ƙarshe dai ta fara gyara ɗakinta wanda babu wani datti ta masa turaren wuta wai dan duk ta ɗan ware, taje kitchen ta ciko plate da kayan garar da ta mayar abinci, da kyar ta iya hawa stairs bayan ta fito daga kitchen sbd ƙullewar da cikinta yayi, ta samu dai ta shiga ɗakinta ta zaune gefen gado ta danne cikin da yake kan murɗa mata, bayan wani lokaci cikin na murɗawa sai ta fara yin ƙalas, maiƙon Alkaki yazo ya tsaya mata a wuya har tana jin kamar za tayi amai.


★ƙarfe biyu da ƴan mintina Nurain ya fito daga office dinsa holding his briefcase, saida yayi attending kaf patient da suka zo shiyasa ya kai wnn time din, acikin doctors da suke aiki a hospital din shine me wnn halin, indai kaga kazo ganinsa bai duba ka ba toh akwai babban dalili amma duk yawan patient yana squeezing ya duba su, Ruqayyah dake zaune bakin office din over three hours tana jiran fitowarsa ta tashi da sauri tabi bayansa, tana zuwa gaf dashi tace "Dr..", dakatawa yayi da tafiyar ya jiyo yana kallonta ba tare da yace komai ba, kallon da yayi nata sai taji gaba ɗaya ɗan guntun courage dinta ya narke gami da tsiyayewa ta guiwarta, ta kasa cewa komai amma lips dinta sai ɓari suke, shi kam da yasan ma itace wllh bazai dakata ba, shi Allah ya masa wani hali na bagarar da lamari indai ya bar abu topa shknn, don yanzu idan nace muku ya manta muryarta ne shiyasa ma har ya juyo data kirasa kar kuyi mamaki, ya haɗe thick eyebrows dinsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa, Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta lumshe idanunta da suke mata zugi tsabar kukan da ta sha, da sauri ta kuma binsa sai kace mayya tace "dan girman Allah Dearest kayi haƙuri, make time for us so that we can discuss about it, i will tell you all what happened...", har suka fito harabar hospital din tana biye dashi tana masa magiya, ganin ba sauraronta zaiyi ba ta tsaya a ƙofar department din gudun kar ta dizga kanta a public, Nurain yana isa parking space ya shiga motarsa, keys ya zura a ignition ya kunna motar, har lokacin girarsa a haɗe take don ba ƙaramin fama masa zuciya waccar psycho din tayi ba, he dislike the sight of her, direct gidansu ya dosa don bazai koma gidansa yaga wani abun da zai sake ɓata masa rai ba, bayan yayi parking motarsa ya shiga ciki. Mami na zaune a main palourn da wasu close friends dinta guda biyu, ya ƙarasa shiga palourn ya gaishesu duka da ladabi, Mami dai tayi mamakin ganinsa a wnn lokacin it seems like daga wajen aiki yake shine ya zarto nan a maimakon gidansa, shidai yana gama gaidasu ya wuce upstairs, Mami ta bisa da kallo, Haj Sadeeya tace "Aaa aha ashe duk munyi furfura don Allah kalli yadda yaron nan ya koma Nurainin Mami, kinga ma ban tambayesa iyalin ba don ina Canada kika gayamin zancen aurensa...", Mami tayi yaƙe tace "matarsa na nan lfy baifi kwana goma da yin auren ba..", Haj Sadeeya tace "kwana goma kuma nifa mganar almost one year nake miki..", Haj Fati tace "ni dai nasan wancan an fasa yinsa, bayan nan ma Nurain din ya koma India, toh dai wnn na kwana goman ne bansan dashi ba.." ta fadi hakan tana kallon Mami, Mami ta kallesu duka tace "wllh auren ne yazo unexpected, nima kaina saida aka ɗaurasa na sani, prof ne ya haɗasa da ƴar abokinsa, shima yaron ba sani yayi ba don lokacin ma bai dawo ƙasar ba..", Haj Sadeeya tace "duk ba labari da fasa wancan din da kuma sabon, toh in banda abinki Mami aiko baza mu zo ba ai kya gaya mana", Mami tayi ajiyar zuciya tace "duk kuyi haƙuri abin ne yazo unexpected shiyasa, ba a nitse nake ba wllh". uku da minti goma Nurain ya sakko har yayi wanka ya sauya kayan jikinsa, yana kallon Mami yace "Noory fa..", Mami tace "bata dawo schl ba..", yace "Okay" yana kallon hanyar kitchen kafin ya wuce can din, kitchen din ya shiga bayan few minutes ya fito da plate din Abinci, dining ya wuce ya zauna ya fara cin abincin, saida ya cinye tass don yunwa yake ji ba kaɗan ba tin tea da yasha da safe bai sake cin komai ba banda water, Nurain bai baro gidansu ba sai ƙarfe takwas na dare, a hakan ma sbd Mami ne dan ya lura da irin kallon da take masa ga dukkan alamu tana so ta fadi wani abun ne amma bata fada ba, yana zuwa gida daman a palourn ƙasa yayi branching, yayi powering TV kafin ya zauna kan exclusive sofa dake palourn, almost 30mins da zamansa aka buɗe ƙofar kitchen, da sauri ya kalli direction din, a hankali ta fito daga kitchen din da cup ta ciko da ruwa, ta juya ta rufe ƙofar, ƙishi ruwa ne yasata fitowa tin ɗazu, shine da tazo kitchen ɗiba ciwon cikin ya murɗa mata ta durƙushe a ƙasan kitchen din tana murƙususu har saida taji dama dama snn ta iya tashi ta ɗebi ruwan ta samu ta fito, wani irin haɗe rai Nurain yayi, wato bata ji warning din da ya mata ba knn, how dare her zata ringa masa taurin kai, who born her with her bad attitudes, dole tayi abinda yace indai tana son cigaba da zama a gidan, furiously ya tashi yace "ke ba kiji warning din da na miki ba knn..", hannunta ɗaya riƙe da cup dayan kuma ta dafe cikinta, da kyar ta iya cewa "daman nace maka naji ne.., na riga na gaya maka you can't tell me what to do malam" tana gama fadin haka ta nufi stairs, bata ankara ba taji an fixgota baya ta bige da hannun kujera.....✍️




💛 HAJAR 💛
na Nafeesah Yusuf Nagoda
A.K.A Feenerh feeche

{46..}
Nurain was extremely angry at that moment, yana mata wani kallon barazana yace "maimaita abinda kika ce..", ta ja da baya zuciyarta na lugude tace "bazan maimaita din ba, idan baka ji ba kai ka sani...", da sauri ta durƙushe ƙasa ta ajiye cup din ruwan ta damƙe cikinta tana murƙususu, fashewa tayi da kuka tana yarfe hannu tace "na shiga uku cikina", tsuke idanunsa yayi ya matsa daga kusa da ita yana kallonta, after looking at her for few seconds yace "hey get up..", banza tayi dashi ta cigaba da kukanta a hankali, folding hands dinsa yayi yace "ke tashi daga nan...", duk da irin azabar da take ji hakan bai hanata ɗaga kai ta zabga masa harara ba, ya koma kan kujera ya zauna gami da ɗaukan remove ya ƙure volume din Tv don baya son ya cigaba da jin sautin kukanta, saida cikin ya lafa mata bayan kamar minti goma ta tashi tana goge fuskarta, ta ɗauki kofin ruwan ta haura sama tana tafiya a hankali, bayanta yabi da kallo bai san lokacin da wani tsaki ya kufce masa ba, ya tashi ya kashe Tvn gaba ɗaya, kitchen ya shiga yana ƙare masa kallo, ya buɗe store ya duba ko ina, yadda ya ajiye foodstuffs haka ya gansu ba a taɓa ba, carton din Noodles kawai ya gani a bude kuma shima pack ɗaya aka ɗauka, ya fito daga storen ya buɗe fridge shima dai babu abinda aka taɓa, ganin bottle water shima ko ɗaya ba'a taɓa ba murya ƙasan maƙoshi yace "what.. toh wane ruwa take sha..", bottle water ya ɗauka ya rufe fridge din snn ya bar kitchen din, upstairs ya haura zuwa part dinsa, direct bedroom ya shiga ya kunna lights, yayi drawing bedside drawer ya ɗauki wani satchet na drug, tashi yayi ya fito daga bedroom din snn ya fita daga part din, tsaye yayi a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta, after standing for few seconds ya haɗe gira ya murɗa handle din ƙofar ya shiga, ƙasa ƙasa yayi sallama wanda ta tsaya iya lips, kwance ya ganta kan carpet ta rufa da duvet har ka, ya ƙarasa cikin ɗakin bayan yabar door a wangale, controlling ɓacin ran dake taso masa yayi, chest of drawers ya bubbuga yace "hey", ta yaye rufar da tayi ta tashi zaune, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta, fuskarsa a haɗe ya ƙara four steps towards her, dungurar da bottle water din yayi a gabanta, ta juyo ta kalli ruwan ta ɗaga kai ta kallesa, ya ajiye satchet din drug din yace "take it..", ta haɗe gira tace "bazan sha ba...", one step ya kara getting even more closer to her, tayi sauri ta muskuta ta bada space a tsakaninsu, taɓe baki yayi yace "an gaya miki nayi hakan ne sbd ke, hmm you don't worth it ba dan ke nayi ba, darajar Abba kika ci, tinda an riga an liƙa min ke babu yadda zan iya and now we are living in the same roof, so listen tinda kema kin nace kina son auren nan toh ga fili ga mai doki, zaki zauna anan amma kuma bazaki jamin matsala ba, na fita haƙƙina na ajiye miki foodstuffs, you are free ki shiga kitchen ki dafa abinda za kici idan kinga dama, don babu wanda zai miki gage, secondly you see this room da downstairs palour and kitchen are the only places da kike da damar shiga daga su kar kiyi gigin shiga wani wajen, and if you need anything bance kimin magana ba, ki nemi pen da jotter ki ajiye duk sanda kike buƙatar wani abu ki rubuta ki ajiye kan center table a palour, i will give that idan baki da shi, am done with you...." da haka ya isa gaban mirror ya ɗauki cup din da ta ajiye, girgiza kai yayi yana kallon ruwan kafin ya juyo ya dubeta yace "for your own heath tap water ba shine ruwan sha a nan ba...", ƙofa ya nufa zai fita yaji tace "malam ka gama, dawo ka ɗauki tarkacen da ka zube min a nan who are you to give me drug, kai tinda aka kawoni wnn ƙaddararran gidan na taɓa mka magana ne da farko da kake cewa wani kar na maka mgana, kaga malam nifa ba mara galihu bace da zaka ringa giggillamin sharuɗa sai kace wata ƴarka, ni nan na fika tsanar wnn jarababben auren wllh, da zaka sauwaƙe mna da ka huta..." ta ƙarashe tana murguɗa baki gami da hura siririn hancinta, bai motsa daga inda yake tsaye yana kallonta ba, tana lura da reaction din fuskarsa zuciyarta ta buga da ƙarfi, tayi sauri ta yaye duvet din da ta lulluɓe jikinta ta miƙe tsaye fuskarta a haɗe, lokaci guda ta dubi kanta, kayan bacci ne a jikinta riga da wando, ai kam da sauri ta durƙusa ta yayibi duvet din ta rufe jikinta, kamar me ƙirga takunsa haka ya fara walking towards her, ganin haka yasa ta fara tafiya da baya tana banka masa harara, da gudu ta shige bathroom tana taɗewa da duvet din, tayi sauri ta saka lock tana sauke numfashi, Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana bin ƙofar bathroom din da kallo kafin ya juya ya fita daga ɗakin, jingina Hajar tayi da jikin ƙofa, ta hura hanci tace "Wllh ka gayamin ajali sai na gaya mka mutuwa, haka kurum ba zaka danƙaramin magana nayi shiru na kyaleka ba zuciyata ta buga, kai da kanka zaka koma wajen wnda ya ƙulla wnn jarababben auren ya kunce sa ehe, dan billahillazi la'ilaha illa huwa yanxu na fara musguna maka a gidan nan, kai ka isa ka aureni kai asuwa...", ita kaɗai ta ringa huci sai kace wata kububuwa, bayan kamar minti goma ta buɗe ƙofar a hankali, ta gama surveying ɗakin da idanunta kafin ta fito, tsaki tayi taje ta rufe ƙofarta, tasa ƙafa tayi fatali da bottle water da satchet din maganin dake kan carpet, ta sake yin wani tsakin tayi kwanciyarta, tsakar dare ciki yace ba sai kiyi baccin na gani ba, duk da sanyin AC gumi ne ya ringa tsattsafo mata a goshi, ganin alamar dai cikin nan ba lafa mata zaiyi ba ta tashi zaune, a gigice ta fara laluben maganin tana rarrafe, taci sa'a kam ta hango sa a karkashin mirror, ta ƙarasa bakin ƙofa ta ɗauki ruwan da ta wurga can, da sauri ta buɗe bottle din ta ɓalli 2tablets ta afa a baki ta bisa da ruwa, within minutes Allah ya taimaketa cikin ya lafa, ta ringa kallon satchet din maganin kafin ta tashi ta ajiye bisa mirror ta koma ta kwanta. washe gari wajen ƙarfe takwas da rabi Hajar ta fito daga ɗakinta bayan tayi wanka ta shirya, downstairs ta sauka zuwa kitchen, tana buɗe ƙofar kitchen sukay ido huɗu da Nurain da ke making coffee, da sauri ta rufe ƙofar ta haura sama, Nurain ya kashe coffee makern bayan ya gama haɗawa, zai ɗau cup din Coffeen knn wayarsa ta fara vibrate, da asuba ya dakkota daga mota bayan ya dawo masallaci, ya duba yaga babu wani missed call kuma luckily wacca tasa ya tsani wayar bata kira ba kuma bata turo message ba, ya ciro wayar daga pocket yayi picking ganin Dr Marwan, fita yayi daga kitchen din still yana wayar, Nurain yace "alright send it now..", Dr Marwan yace "Okay", Nurain yace "when is it going to start..?", Dr Marwan yace "12noon insha Allah...", Nurain yace "Neh, i will be there before then..", Dr Marwan yace "thank you Dr..", Nurain ya katse wayar ya haura sama ya shiga part dinsa, Laptop dinsa dake jone a charge ya ciro ya zauna yayi switching dinta on, tana gama booting ya buɗe WiFi, it connected automatically with the house router, ai kam sai ga mail daga Dr Marwan, Nurain ya bude mail din yana duba hoton jiki, almost 30mins yana examining picturen, it is a human chest diagram, a zuciyarsa wondering yake who is this patient with a damage lungs. Hajar ta sake sakkowa ƙasa don yunwa take ji sosai, plain Noodles ta dafa ta juye a plate, tinda ta shigo kitchen din take kallon Cup din dake cike da Coffee, bayan ta gama tafasa tea ta juye a cup ta zuba sugar da lipton, har zata fita da shayi da Noodles dinta a hannu sai kuma ta dawo da baya, ta ajiyesu kan kitchen island, store ta shiga ta ɗakko ledar gishiri ta fito, farke ledar tayi ta ɗauki spoon ta matsa wajen Coffeen, ta zuba cokali biyar cikakku na gishiri a Coffeen tana murmushi, ta mayar da gishirin store ta fito tana kakkaɓe hannunta tace "Asha shayii lfy.. counting from today..." kafin ta ɗauki plate din Noodles da kofin shayinta ta fita. Nurain ya shigo kitchen din bayan fitar Hajar da minti biyu, direct Coffeen sa ya ɗauka, ya ringa kallon coffeen ganin kamar ya ƙara yawa, gashi kuma it is not hot but warm, tinda it is warm he can take it, Sipping yayi domin yaji temp din dai a bakinsa, guntse wanda ya kurɓa yayi ya yamutsa fuska, lokaci guda ya isa gaban sink ya zubar ya kunna tap ya wanke bakinsa, har lokacin wani irin taste yake ji a bakinsa wanda ya kasa gane masa, ya ringa kallon Coffeen kafin ya sheƙar dashi ya bar kitchen din, yana zuwa ɗakinsa ya wuce bathroom ya shiga wanke bakinsa da mouth wash har saida yaji taste din ya ragu sosai.


★Tin daga soro Sa'adatu ta fara zabga sallama harta shiga cikin gida, wani kallon hadarin kaji ta watsawa Umma dake zaune kan ƙaramar kujera tana shafa manja jikin gwangwanaye, ɗakin Maama ta shiga, Maimuna dake zaune kan gado ta bita da kallo tace "kin dawo..?", Sa'adatu ta saki baki tana kallon Maimuna kafin ta yakice hijab din da ta zumbula a jikinta, wasu irin matsattsun kaya ne jikinta wanda ya bayyana shape din bom bom dinta da ƙirjinta, ta zauna kusa da Maimuna ta sake ƙare mata kallo tace "ke kuma wa ya mayar dake wnn mummunar halittar, babur ne ya bigeki...?", Maimuna ta shafa goshinta tace "idan na gaya miki Allah yasa ki yarda.., wai fa Mu'azzam ne yamin haka..", Sa'adatu ta hangame baki tace "Mu'azzam din ne ya miki haka...?", Maimuna da takaici ya kuma maƙureta tace "shifa..", Sa'adatu tace "chaɓɗi jamm, wato har dasu kaza acin danƙo, ke me ya haɗani da wnn jakin har yayi miki haka...?", Maimuna ta kwashe kaf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login