Showing 12001 words to 15000 words out of 114314 words
Chapter 5 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
irin rainin hankali tace "Baiwar Allah ki iya bakinki, kuma kisan a inda za kiyi zagi kici bulus, ke kin isa ki kalli mahaifina ki gaya masa magana akan idona, shiyasa na gurje bakin fitsarar da ruwan kwata, wllh kaɗan ma kika gani", waɗannan kalaman su suka dawo da Maama Sa'adatu Nabilah da Mabaruka daga duniyar daskarewa, zeenatu ta sharce kwatar da ta mamaye mata baki dake fitar da jini tana kallon Hajar cike da mamaki, Sa'adatu ta mulmulo wata ashariya tayo kan Hajar a fusace..........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{8...}
Da sauri Hajar ta tuntsurar da ruwan ɗaurayar wanke-wanken, ta ɗauki bokitin ƙarfen ta nuna Sa'adatu da ta yo kanta tace "na rantse da girman Allah kika taɓani saina rotsa miki kai", Sabra tana ganin haka ta fita a guje kiran Umma da ta shiga makwabta barka, turus Sa'adatu tayi saboda tasan tsaf zata aikata, maimakon kan Hajar da tayi nufin yi saita juya akalarta zuwa ga zeenatu da take ta faman sharce kwatar fuskarta, Mabaruka ma ta taho da sauri ta kalli fuskar zeenatu tace "chab an tsokano sama da kara", Nabilah ta shiga tafa hannaye tana faɗin "mun shiga uku yau ga ƴar daba a gida tana dabanci", Maama tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal kana ganin abinda shegiyar ƴar da kake iƙirarin takace ta aikata ko??, tafa fitarwa da ƴar mutane jini", Baba ya nuna Maama da hannunsa mai carbi yace "karki sake kiramin ƴa shegiya na gaya miki, Hajara ƴata ce", Maama ta tsaya tana kallon Baba galala tamkar wawuya sai kuma ta hura tukubar hancinta tace "wllh idan zaka shekara dubu kana kiran Hajara ƴarka saina ƙaryata", Hajar ta riƙe bokitin ƙarfen ta gam tana kallon kowa sama da ƙasa, Sa'adatu da Mabaruka suka temaki zeenatu ta wanke fuskarta da hannayenta, Mabaruka ta cire yalolon mayafin jikinta taci ɗammara ta kalli Nabilah tace "naji kin kirata da ƴar daba ko??, to ga wacca ta dameta ta shanyeta tas a iya dabanci", Baba ya ɗaga murya yace "Sa'adatu!!, ki kwashi ƙawayenki ki barmin gida", Mabaruka ta kaiwa Hajar wata damƙa, babu tausayi Hajar ta kwaɗa mata bokitin ƙarfe a hannu, azaba tasa Mabaruka durƙushewa tana yarfa hannu, da gudu Sa'adatu taje ta rarumo taɓarya zata jirga mata, Hajar ta kufce, da sauri Baba ya shiga tsakani hakan kuma yazo daidai da shigowar Umma gidan cikin sauri Sabra biye da ita, salati ta fara zabgawa ganin Hajar na huci hannunta riƙe da bokitin ƙarfe ga Sa'adatu itama da taɓarya, Maama tace "kin haifi bala'i da masifa wllh faɗima, ga shi nan shegiyar ƴarki ta kassara ƴaƴan mutane a gidan nan", Sa'adatu tsalle take tana hargowa tana ƙoƙarin bangaje Baba da ya shiga tsakaninta da Hajar faɗi take "kin san kwa su waye waɗannan, wllh yau sai kinyi nadamar zuwa gidan duniya", Hajar ta daka shewa tace "ahayye wllh sune za suyi nadamar zuwa gidan nan, dubeki dabba jahila daƙiƙiya kin tsaya kina hura hanci da ƙoƙarin bawa hammata iska akan jakunan da suka zagi mahaifinki, asararriya mara mafaɗi da tarbiyya....", Umma ta fizgi Hajar tana ƙoƙarin dannata a ɗaki, Sa'adatu ta yunƙuro tana ɓaɓɓarkawa Hajar zagi irin na cikakkun marasa tarbiyya, Hajar da Umma ta kusan cusata a ɗaki tace "tirr da halinki Sa'adatu, ki ɗauki tsummokaran jakunan ƙawayenki daga nan ku wuce chemist, gaba ɗayansu idan suka ji zugin shanshanbale na ratsasu suka ɗanɗana azaba zasu gane inda ya kamata su nuna rashin tarbiyyarsu", Sa'adatu tace "zaki gani ne ba dai zeen da Mabruk kika taɓa ba", Hajar tace "babu abinda zan gani sai alkhairy, sara da sassaƙa basa hana gamji tofo, jaka kawai". Umma tayi nasarar danna Hajar a ɗaki ta rufe ƙofa, wani irin huci Hajar takeyi tana sauke numfashi, Umma ta kalleta cike da takaici tace "ba kya jin magana Hajara, Insha Allah gobe goben nan zaki bar gidan nan", Hajar ta koma gefen gado ta zauna tana huci zuciyarta wasai. Washe gari Umma ta haɗawa Baba karin kumallo, ɗumamen tuwa da kunun tsamiya, zama tayi har saida ya gama cin abincin sannan tace "yawwa mal daman ina so Hajara ta koma wajen iya da zama tinda zamanta anan gidan ya ƙi daɗi, idan babu damuwa ta koma gaban iya", Baba ya zuba ruwa a kofin da ya gama shan kunu ya girgije yace "faɗima ina ne gidansu Hajara?", Umma tace "nan ne", yace "yawwa, to Hajara babu inda zata agidansu zata zauna", Umma tace "amma mal...", ya ɗaga mata hannu yace "ya isa haka, kirawo min Hajarar", tace "tom" ta fita a ɗakin ta shiga nata, Hajar da take gyara gado ta kalla tace "kije inji Babanku", Hajar ta ajiye bedsheet din hannunta ta fita, ɗakin Baba ta shiga da sallama ta tsugunna tace "Baba gani", ya kalleta yace "Hajara banji daɗi da kika biyewa fitsararrun nan ba jiya, kin saɓa alƙawarin da kikai min kwanaki cewa bazaki sake shiga sabgarsu ba, yanzu jiya me kika yi..", ta buɗe baki za tay magana ya ɗaga mata hannu yace "duk nasan abinda ya faru kuma nasan me yasa kika shiga sabgar su, da kinyi haƙuri saiki samu riba, karki sake aikata hakan kinji", tace "tom Baba", yace "tashi ki tafi Allah shiryeki". ta miƙe a sanyaye ta fita, gyaran gadon da take ta ƙarasa snn ta share ɗakin. ta fito tsakar gida tana kallon Umma da ke bakin rariya, kallo ɗaya umma tayi mata ta ɗauke kai ta cigaba da wanke waken kulele da za a kai markaɗe, Umma ta ɗauki zafi fishi take da Hajar ainun yau ko gaisuwarta bata amsa ba da asuba, Hajar ta tsugunna a gabanta tace "Umma dan Allah kiyi haƙuri, nadena bazan sake ba", ba tare da ta dubeta ba tace "ai daman kin iya tuban muzuru, ki matsa min a nan wajen", idon Hajar ya ciko tace "dan Allah Ummana ki yafemin nadena bazan sake ba", Umma ta ja tsaki tace "sau nawa akai hakan Hajara, tinda dai kinƙi jin maganata ai sai kiyi abinda kika ga dama, duk abinda haƙuri bai samar ba rashinsa bazai yi ba", Hajar tace "wllh Umma nifa bana shiga harkarsu tinda kikai min magana, sau nawa suna takalata bana kulasu, jiya ma fa ƙawayen Sa'adatu ne suka yiwa Baba rashin ɗa'a", Umma tace "uhmm ai kina ganinsu kinsan basu da tarbiyya dan me yasa zaki tanka masu", Hajar tace "bazan sake ba", Umma tace "da ya fi dai". Maimuna ce ta fito daga ɗakin Maama tana rangwaɗa, ta saka wasu matsattsun kaya riga da skirt na atamfa, saboda ɗamewar da skirt ɗin yayi mata har shatin panties ɗinta ana gani, itama ta tsiri fita yanzu kuma bata dawowa gida sai dare da ƴan ledojinta na kwaɗayi mabuɗin wahala, ko kallon inda take Umma da Hajar ba suyi ba tazo ta gama barbaɗesu da Harara kana ta fita. Hajar tace "umma dan Allah da yamma zanje gidansu zainab muyi karatu", Umma tace "toh shknn Allah ya kaimu". Bayan Sallahr la'asar Hajar tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa, ta kashe maiƙon fuskarta da farar huda ta murza lipstick a lips ɗinta, ta saka hijab da ya zarce mata guiwa, tayi kyau sosai sai kace wacca ta caɓa kwalliya, wani flat shoe ta ɗakko ta saka ta yiwa Umma sallama ta ƙara gaba, da yake gidansu Zainab ɗin akwai ƴar tazara daga gidansu, ta tsaya a bakin gate tana knocking a hankali, Zainab ce ta buɗe ƙofar ta haɗe rai tace "haba Hajar tin ɗazu fa nake jiranki amma sai yanzu zaki zo", Hajar tace "ke dalla malama Umma na taya aikin kulele", Zainab ta matsa gefe tace "Shigo mana", a ɗan matsakaicin compound ɗin gidan suka tsaya, Hajar ta kalleta da kyau tace "ke kuma ina zuwa??, naga kinyi shiga sai kace mai shirin fita", Zainab ta gyara yafen mayafinta tace "fita zanyi mana, tinda Allah ya kawoki saiki rakani Ummi ce ta aiken", Hajar tace "ban tambayi Umma ba iya nan kawai nace mata zanzo", Zainab tace "muje ki gaisa da Ummi saina kira Umma a waya mu tambayeta ko?", Hajar tace "Eh hakan dai yafi". cikin gidan suka shiga, Mamansu Zainab tana zaune a palour, Hajar ta tsugunna tace "Ummi ina wuni", Ummi tace "ina gajiya, ya Maman taku", Hajar tace "lafiya alhmdllh", Ummi tace "masha Allah", Zainab tace "Ummi ɗan aramin wayarki plxx", Ummi ta lalubi gefe da gefenta taji wayam tace "duba ɗakina", Zainab ta shiga ɗakin Ummi ta fito da wayar a hannunta ta kalli Hajar tace "taso muje", ɗakinsu Zainab suka shiga, Zainab ta miƙawa Hajar wayar tace "saka numbern Umma", bayan Hajar ta ɗura numbern tayi dialing, anayin picking Hajar taji muryar Sabra, Hajar tace "game kike mata ko?, maza ki kay mata wayarta", tana jiyo muryar Sabra tana cewa Adda ta bugo waya, Umma tayi sallama ta kara wayar a kunne, Hajar tace "Umma nice". da kyar Umma ta amince kuma tace mata kar ta kai magariba. bakin titi suka fito suka tari napep, unguwar da suka je ta masu hali ce haka ma gidan da suka amso saƙo wajen ƙawar Ummi, a clean and silent street ɗin suka tsaya suna jiran abin hawa.
★Noor na zaune a main palour tare da Khausar da yau kwananta biyu a gidan, wata spicy noodle mai shegen daɗi suke ci, gaba ɗaya hankalin Noor yana ga TV da ake haska wani Kdrama, Khausar ta ajiye fork ɗin hannunta tace "Noor what is the name of the drama??", ba tare da ta kalleta ba tace "Alchemy of souls", Khausar ta taɓe baki tace "ni kam nafi kallon Cdrama, ina yaya Nurain ne?", Noor bata amsata ba her mind was fully on screen, Khausar ta ɗala mata duka a cinya tace "hey I'm talking to you", Noor ta zabura tace "ouchh kadan ba saina rama ba" ta mayar da idonta Tv, Khausar tace "wai bazaki ci ba saita sandare", Noor idonta ƙur kan Tv tace "kashe AC", Khausar ta janyo wayarta tace "I'm not your servant". atmosphere ɗin living room ɗin ce ta fara canzawa zuwa wani breath taking scent mai daɗi, Khausar ta ɗago kanta suka haɗa ido da Nurain, murmushi yayi mata ya kalli Noor da bata ma san da shigowarsa ba yace "Noor.. Noor.. Noor.." ya kirata sau uku, saida Khausar ta zungureta sannan ta juya tace "what, wai mene??", da ido Khausar tayi mata nuni da Nurain tace "yaya na magana", yace "juicy fruit salad zaki hada min", Noor tace "ohk, amma babu fruit fa, apple and berries ne kawai ya rage", juyawa yayi ya fita daga palourn Khausar ta bisa da kallo, compound ya fita yana neman Garba ya bashi ya siyo masa fruits ɗin amma ya tarar baya nan, lallausar sumarsa ya shafa yace "shittt", ya shafa pocket ɗin wandonsa yaji key ɗin motarsa yace "good", motarsa ya dosa dake parking lot ya buɗe bayan ya gama warming ya mirgina ya bar compound ɗin, a hankali yake murza steering ɗin motar amma kuma ya take accelerator. Almost 20mis Hajar da Zainab na jiran napep, wasu yara su uku suna wasa da ball daga cikin wani ɗan fili, guda ɗaya ne ya buga ball ɗin da ƙarfi tayo kan road, da gudu yaron ya biyota a lokacin kuma wata dunƙulalliyar mota ta yanko cikin street ɗin with minimum speed, saura ƙiris motar ta bige yaron taci wani uban burki ƙiiii ta tsaya gaf da yaron da tsoro yasa ya ƙame, Hajar ta runtse idonta tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", Zainab kam juya baya tayi ta toshe kunnuwanta da hannayenta, a hankali Hajar ta buɗe idonta ta dubi yaron da ya zama froze a gaban motar, da sauri ta isa gabansa ta fara shafa kansa a hankali tace "wake up kiddo babu abinda ya sameka", ajiyar zuciya yaron ya sauke. Tinda ya tabbatar bai bige yaron ba ya kifa kansa ga steering, calming kansa yake yana addu'a a zuci, ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago kansa a hankali, ta front glass yake kallon yaron da kuma ƴar budurwar da take tare dashi wacca tayi backing dinsa bega face ɗinta ba. tamkar wacca aka umarta haka ta juya ta kalli glass ɗin motar da wani irin yanayi, in one sight ƙwaƙwalwarsa tayi booting on ya gane wannan fuskar, one thing came to his mind which is ƴar gidan gini.........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{9...}
Da yake glass din motar tint ne yasa Hajar bata ga drivern ciki ba. hannun yaron ta riƙe still dai tana kallon glass din motar, kawai jira take drivern ciki ya fito, few seconds passed amma babu alamar wanda yaso aikata ta'asar zai fito, Zainab da ta toshe kunnuwanta har tayi jarumtar juyowa ta hango Hajar tsakiyar titi tare da yaron, Hajar taja hannun yaron ta tsaya bakin ƙofar driver ta shiga knocking glass, a hankali glass din yayi ƙasa ya zuge gaba ɗaya, wani sanyi da ƙamshi suka fara sirnanowa suna dukan fuskar Hajar da ta yaron. ta haɗe gira tana kallonsa tace "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba", Zainab ce ta tsallako kan titin itama tace "zo mu tafi ai Allah ya kiyaye tinda dai bai bigesa ba", Hajar tace "ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai fa yadda Allah yayi", shi kam Nurain mamaki da firgicin da ya ziyarcesa ne ya hanasa magana, Hajar ta sake kallon cikin motar tace "Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar ɗan Adam", Zainab ta zaro ido tace "Hajar mene haka?", Hajar taja hannun yaron ta tsallar dashi titi tace "maza gida kaji", yaron ya kyalla da gudu ƴan uwansa suka take masa baya. wajen da suke jiran napep ta koma ta tsaya fuska a haɗe, mutanen yanzu basu da kirki ace ka kusan aika yaro lahira amma ka zauna ko a jikinka sai kace wanda ya kusan bige akuya yo ko akuyar ce aika fito ka duba idan kasan darajar rai, Zainab ta dawo gefenta ta tsaya tace "Hajar yanzu me kika aikata haka, Allah ya isa fa kikai masa, dubi fa har yanzu bai tafi ba", Hajar ta kalli motar da har yanzu take tsakiyar titi ta yamutsa fuska tace "me kwa na aikata, ya shekara a wajen kar ya tashi". a hankali ya juya kan motar ya gyara parking a gefen titi, Zainab ta damƙi hannun Hajar ta fara janta ganin ya fito daga motar ya tunkarosu, Zainab tana janta tace "Hajar kizo mu gudu kar yayi mana wani abun", Hajar ta fuzge hannunta tace "wllh bazan gudu ba", Zainab tayi tsam ganin har ya iso gabansu yayinda wani ƙamshi mai daɗi ya fara busowa a hancinsu, yana kallon Zainab speaking calmly yace "Assalamu alaikum young lady", a ɗarare ta amsa kana tace "bawan Allah kayi haƙuri dan Allah", Hajar da ta juyar da fuskarta ta juyo ta ɓalla mata harara jin abinda tace, girgiza kai yayi yace "ba komai, tell your friend itama tasan darajar ɗan Adam cause ba tayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan mutum ba", da sauri Hajar ta juyo ta kallesa, and that look makes her brain to boot on, she saw this calm and charming face familiar, but where and when??, walking fast ya koma ya shiga motarsa ya kunna ya fita daga street ɗin da reverse. gida ya koma sbd wannan incidence ɗin da ya faru yasa yama manta da wani batun fruit salad, yana parking motar Garba ya taho wajensa, ko kashe motar baiyi ba ya fito cikin sauri ya shiga cikin gida, Garba ne ya shiga motar ya kashe sannan ya zare key ya fito. har lokacin Noor da Khausar suna zaune a palour, Noor tana kallonsa tace "yaya ina fruit din ko basu ka fita nema ba", shiru yayi mata ya haye stairs, Khausar ta taɓota tace "he is weird", Noor ta sauke ajiyar zuciya tace "ina jin an ɓata masa rai ne", she knows her brother in and out kuma she is very sure rai aka ɓata masa.
★Hajar ta shiga gida sai gunguni take, Mu'azzam da yake alwala a bakin rariya yace "toh jarababbiya", ta zumɓuri baki tayi ɗakin umma, Maama da take talgen tuwo Nabila na mata tankaɗe tace "kin ji ba ɗan uwanta ma yasan jarababbiya ce", Nabila ta doka tsaki ta cigaba da tankaɗenta, Umma ta kalli Hajar da take ƙoƙarin cire hijab tace "ke kuma lafiya kike wani cin mur..?", Hajar tace "wai a duniyar nan Umma mutane basa son gaskiya, wai wani mutum ne ya kusan kaɗe wani yaro a titi amma ko a jikinsa, wllh ko fitowa ya duba yaron ƙi yayi", Umma tace "Allah ya kyauta bai dai bigesa ba ko??", Hajar tace "saura ƙiris fa, amma wllh mutumin nan yadda kika san gunki haka ya zauna a mota yaƙi fitowa ya duba yaron", Umma tace "ke kuma shine kike kumbura akan hakan", Hajar tayi shiru kawai tuno abinda yacewa Zainab take wai batayi hali ko kama da mutanen da suka san darajan ɗan Adam ba. kiran sallar magrib ne ya fitar da ita tsakar gida tayo alwala ta dawo ɗaki tayi sallah, bayan ta idar da Sallahr isha'i tana zaune akan darduma Sabra ta ajiye littafi a gabanta tace "Adda ki koyamin", Hajar ta janyo littafin ta duba kana ta fara gaya mata abinda zata rubuta. Umma ta shigo da wata warmer ta abincin da tayi tazarce ta ajiye a gefe guda, Hajar na kallon Sabra tace "yanzu ke Sabra mosquito din ne baki iya spelling ba, ƙwaƙwalwar dusa ne dake ko me??" ta zuba mata rankwashi aka, Sabra ta riƙe kai tace "ashhh Adda fa na iya", Hajar tace "to rubuta mana", Umma tace "kiyi mata a hankali dan Allah". washe gari Hajar taje islamiyya tayi screening dinta na ƙarshe, kuma a yau ne aka fayyace musu kuɗin sauka da walima, kwanaki uku bayan haka ranar Alhamis da yamma, Baba bai jima da dawowa daga wajen aiki ba yana zaune a ƙofar ɗakinsa yana cin abinci, wani yaro ne ya shigo gidan yace "wai ana sallama da mal Adamu", Hajar