Showing 69001 words to 72000 words out of 114314 words
Chapter 24 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
gyaran murya yace "Hajiya ai bakin alƙalami ya bushe sai dai ɗanki ya nemi wata, yanzu maganar da nake miki na aurar da Hajara", Maama na fifita da mafici tace "Atoh ai yafi dai ka gaya mata gaskiya", Hajiya ta zabga wani uban salati sai kuma ta ɗaga murya tace "Nuraddeen...", Nura ne ya shigo da sallama, daman yana soro a tsaye shine ma ya rako Hajiyar. wata iriyar zabura Hajar tayi ta miƙe tsaye jin muryarsa, ta tsaya a jikin window tana leƙen tsakar gida, wani shauƙin kuka ne taho mata da taga fuskarsa, Hajiya tace "Nuraddeen, basu haƙuri da kanka, ni kam sun ƙi amsar nawa", Nura da har fuskarsa ta faɗa na wuni ɗaya ya durƙusa, ya gaishe da Baba kana Umma da hankalinta ya fara tashi, fuska babu yabo ba fallasa Baba yace "ba ƙin haƙura mukay ba, ai haƙurin ne ma yasa na saurare ki, kuma haƙurin za kuyi Hajara matar wani ce", Nura ya zuba guiwoyinsa a ƙasa yace "Baba, dan Allah kar a rabani da Hajar, ku yafe min...", Umma ta tashi ta shiga ɗaki, Baba ya girgiza kai yace "kayi haƙuri Nura wllh an riga an ɗaurawa Hajara aure...", Hajiya ta ɓarke da kuka tace "wllh nice sila, Nuraddeen ka yafe min, ban kyauta maka ba, ban yi maka adalci ba, duk abinda nake so shi kake min, ni kuma na datse maka farin ciki, wllh ban san na aikata maka hakan ba, na ɗauka mafarki nake ashe a zahiri na aikata...", Nura kam ko fahimta me take cewa beyi ba sbd juyawar da kansa yake masa, ga wani raɗaɗi da zuciyarsa ke masa, Baba ya kawar da kai yana jujjuya wnn lamari a kwanyarsa, abu sai kace a film. Nura ya tashi yana layi ya taimaki mahaifiyarsa ta tashi itama yace "Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan nimha", shi wnn babbar musiba ce a wajensa, ya juya yay hanyar soro, Hajar ta sulale ƙasa ta cigaba da rusa kuka da dashasshiyar murya, a ƙofar gida Nura ya haɗu da Mu'azzam da yake shirin shiga gida, cike da mamaki Mu'azzam ya dubesa yace "ya sayyadi..", Nura ya kallesa da jan ido yace "Mu'azzam" da haka yayi gaba ya fara tafiya da sauri tamkar zai tashi sama, gida Mu'azzam ya shiga, yabi Hajiya da ido wacca take ƙoƙarin fita tana matsar kwalla. yayi sallama a bakin ƙofar ɗakin Umma ya bawa Anty saƙon yoghurt da ya siyo. da kyar Hajar ta sha quartern yoghurt din, ta sha panadol sbd kanta da yake mugun ciwo. wnn night shine worst night a rayuwarta, she couldn't sleep at all even a nap.
★Washe gari da safe, Nurain na zaune a balcony perceiving the morning blessings, wayarsa yake latsawa time to tima kuma yana sipping black coffee, last night da kira aka addabesa har saida yayi silencing wayar ya samu yay bacci, da safe kam missed calls da ya shallake expectation nasa ya gani, sai kuma ta ɗora da text message, a ƙalla daga asuba zuwa yanzu da ake maganar ƙarfe bakwai da rabi ta turo masa da messages sama da goma, kuma ko ɗaya bai karanta ba, daga message ɗinta ya shigo yake wipping notifications ɗin wayar, shifa indai ya bar abu to ya barshi kenan no going back, yanada zuciya sosai saidai kuma kafin yayi zuciyar sai ransa ya ɓaci. wayarsa tay vibrating, yana dubawa yaga Abba ke kiransa, picking yayi ya kara a kunne, Abba yace "ka sameni a great room now", Nurain yace "yeah", da haka Abba ya katse kiran, ya ɗaga coffeen sa ya shanye snn ya tashi ya shiga ciki da cup ɗin a hannunsa, kitchen ya wuce ya ajiye cup din snn ya fito ya nufi great room din Abban sa. ya cire soft slippers dake clean legs ɗinsa ya shiga great room din, yana shiga Abba yayi pointing kujera yace "sit", Nurain ya zauna looking at his Father. Abba yace "Uthman, tin jiya naso nayi informing ɗinka amma na bari sai yau", Nurain dai baice komai ba kawai kallon Abban nasa yake, Abba exhale heavily yace "na ɗaura maka aure da ƴar wajen abokina...", with a weird facial expression Nurain ya dubesa, peach lips dinsa ya motsa a hankali yace "marriage..", direct Abba yace "yess, jiya aka ɗaura auren, and insha Allah today za a kai maka matarka gidanka, get ready to settle down Son".....✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{34..}
Nurain was speechless at that moment, he was shocked and confused, marriage shine plan dinsa na ƙarshe a yanzu, Abba ya katse silence din da faɗin "don't you have anything to say?", Nurain ya shafa cikakkiyar sumarsa yace "Abba, kawai i don't expect this, beside ma i think am not ready..", Abba yace "wane ready kuma Nurain?, ai komai an gama, shirin da ya rage maka shine settling down, kanada gida, kanada Sana'ar da zaka riƙe even four wives, you're rigid enough, sai dai in auren da nayi maka ne baka so", Nurain yayi ajiyar zuciya yace "No Abba, i like it, sai dai akwai consequences..", Abba yace "no matter what the consequences might be you most settle down, kamar duk wani abu mai merit to definitely yanada demerit, abinda nake so da kai shine, ka amshi auren nan ka zauna da matarka lfy, Allah ya bka ladan biyyar da kay min...", Nurain yace "ba komai Abba, nagode sosai..", Abba yace "madallah, Allah yay albarka..", Nurain yace "Ameen, if you excuse me?", Abba yace "fine, you may leave", tashi Nurain yayi ya fita, shi dai bashi da wni feeling akan mattern, shi ba mai farin ciki ba kuma ba mai baƙin ciki ba, Mami ta fito kitchen hannunta rike da wani royal tea flask, ganin Nurain na fitowa daga great room din Abba ta tsaya kallon expression en fuskarsa, tasan Abba ya gaya masa maganar auren, ya zuba hannayensa a pocket walking towards her yace "i just talk with Abba", tace "ka sani knn?", yace "sure, are you happy with the marriage..", Mami tace "Eh mna, am very happy, Allah ya sanya alkhairy.." da hka ta wucesa ta shiga great room din Abba. ƙarfe sha ɗaya Sakeena ta iso gidan da kids dinta guda biyu, Aymana da kuma Ayman wanda take goyo, a part din Mami tayi branching, Mami ta dauki Ayman tana masa wasa, Sakeena ta cire veil dinta ta zauna tace "ina kwana Mami..", Mami tace "lfy lou, ya kids", Sakeena tace "suna lfy, ai Abba ma ya kusa zuwa yaye..", Mami ta shafa kan Ayman dake cinyarta tace "A'a Sakeena, wnn ɗan ne ya isa yaye?..", Sakeena tace "laa ya isa, watansa 11 fa", Mami ta haɗe gira tace "A'a gsky bai isa ba..", Sakeena tayi ƴar dariya tace "kamar haka na yaye Aymana ma..", Mami tace "ai dan an gansu ƴan lukutaye shi yasa ake ɗaukar alhakinsu..", Sakeena ta gyara zama tace "kuma a yau za a ɗakko amaryar?", Mami tayi ajiyar zuciya tace "Eh, yau da yamma ba", Sakeena tace "ƴar Abokin Abba ce ko?", Mami tace "Eh, but I don't know which one...", Sakeena tace "Alright, Allah yasa dai mai kirki ce", Mami tace "Ameen". Anty Zulaiha ma ta hallara da misalin ƙarfe ɗaya da ƴan mintina, ba ta jima ba saiga Mama Mardiyya ƙanwar Abba da kuma Umminsu Farooq, Mami tasa aka firfito da lefen Nurain na bikinsa da Ruqayyah, tace "yawwa da cewa nayi kawai sai a basu lefen idan an kawo amaryar...", Mama Mardiyya tace "Shknn kam, kinga an wuce wajen", Mami tace "to ku duba ko akwai abinda za a ƙara...", Ummi tace "wai lefen Nurain ne, ai a yadda nasan lefen nan baya buƙatar ƙari..", ai kam dai boxes ɗin nan basu da masaka tsinke acike suke ɗam ɗam, Sakeena tace "Ai da aka kaiwa Ruqayyah sun taɓasa..", Mami tace "Atampa da lace kawai suka ɗauka, kuma nayi replacing da wasu..", Anty Zulaiha tace "A wnn abu yayi, kawai miƙa musu za ai", Mama Mardiyya tace "Nurain ya bani tausayi a lokacin da aka fasa aurensa na farko, Allah yasa wnn shine mafi alkhairy", kowa ya amsa da Ameen, Ummi tace "Hajiya ma da cewa tayi zata biyoni sai kuma ciwon ƙafa ya hanata, ba mamaki idan taji dama dama tazo anjima, dan cewa tay ita zata riƙo matar Nurain", Anty Zulaiha tace "Allah sarki, ai Hajiya na ji da jikokinta..", Sakeena tace "Iron Ladyn mu akwai rigima...", Mama Mardiyya tace "gidanku, bazaku dena ce mata iron lady ba ko?", Sakeena tace "Allah ba ruwana Mama, Noory da Aysha ne suke ce mata iron lady...", Anty Zulaiha tace "toh yanzu dai da kayan lefen zamu tafi ɗakko ta knn?", Mami tace "wai da cewa nayi akai lefen can gidan Nurain, idan aka kaita can ɗin sai a basu lefen a can..", Ummi tace "Eh, hakan yayi, ba nan za a kawota ba knn?", Mami tace "gwara ta fara shiga gidanta in yaso Nurain ya kawota mu gaisa daga baya..". Haka kuwa akay ana idar da Sallar la'asar Ummi Anty Zulaiha da Mama Mardiyya suka tafi ɗakko Amarya, mota uku sukay, drivern Abba da yasan gidan shine yake musu jagoranci. Abba ya kira Baba ya sanar dashi don daman sunyi exchanging phone number. Sakeena Noory Aysha da kuma Khausar aka haɗasu da kayan lefe suka wuce gidan Nurain.
★Taci kuka harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, tin ɗan yoghurt din da ta sha daren jiya bata sake cin komai ba sai bayan Sallahr azahar taci awara kaɗan, Baba yana dawowa daga masallaci sallar la'asar ya sami Umma ya sanar da ita cewa su shirya yanxu za a zo ɗaukar Hajara, wani yanayi Umma ta shiga amma haka ta jure ta sanar da Anty, Anty tasa Hajar tayi wanka, babu musu ta tashi tayi, ita ta riga da ta saddaƙar tana jiran sakamakonta, asalin kayan da aka tanadar mata na zuwa gidan miji ta saka, atampa black mai manyan flowers red, da mayafi red mai stone na shuwariski mai walwali, sai handbag da flat shoe black colour, Hajar tayi kyau sosai duk da dai babu walwala a fuskarta, aihanin ƙamshinta na gyaran jiki da kuma na kayan da akay musu kabbasa ga kuma perfume sai tashi yake daga jikinta, a gefen gado ta zauna tana wasa da slim fingera dinta da suka sha zanen jan ƙunshi wanda a yanxu ya koma maroon, Hafsa ce a kusa da ita itama ta shirya abinda, Sabra na tsaye daga jikin wardrobe ta zubawa yayarta ido, Hajar ta dubi little sister ɗinta tace "zo Sabra", da sauri ta matsa kusa da ita, Hajar ta riƙo hannunta, Sabra tace "Adda me yasa ki kai ta kuka jiya?", Hajar tace "kuka nake yi sbd zan rabu da ku, ke da Umma da Baba da yaya..", Sabra ta zaro ido tace "tafiya zaki ki barmu", Hajar ta gyaɗa kai tace "Eh, zaki bini?", ta gyaɗa kai da sauri tace "Eh zan biki..", Sallama ce ta ratsa tsakar gida tare da ƴar ruruma, Hajar ta runtse idonta snn ta damƙe hannun Sabra dake cikin nata, tabbas tasan cewa masu ɗaukarta ne suka hallara. Hafsa ta miƙe ta janyo mayafin Hajar ta rufe mata fuska. Shimfiɗar fuska da ta tabarma su Anty sukay wa baƙinsu, su Mama Mardiyya suka zazzauna, aka fara exchanging greetings ga juna, bayan nan Wasila ta kawo drinks da snacks da aka tanadar ta ajiye musu. Maama ta fito daga ɗaki tana ƙarewa baƙin kallo, sosai gabanta ya faɗi sbd yanayinsu, sam ba suyi kama da ƴan wahala ko yaku bayi ba, hutu ne kawai yake haskawa a jikinsu, ta shiga muhawara da zuciyarta, shin wane ne wnn abokin na Baba da aka ɗaurawa Hajara aure da ɗansa, tin safe take jiran taga su waye zasu zo ɗaukar Hajar, ta yamutsa fuska ta koma ɗaki ta hau canza kayan jikinta zuwa masu ɗan dama dama, Nabilah tace "Maama fita za kiyi?", Maama tace "zuwa zanyi naga kangon da za a kai Hajara". Mama Mardiyya ta ɗaga kai tana kallon Maimuna da ta fito daga wanka, ɗaurin ƙirji ne ajikinta, ga fuskarta ɗaɗau tasha man bleeching jiki kuma baƙi ƙirin, ko kallon inda suke Maimuna ba tay ba ta tsugunna gaban rariya ta fara goge baki. Mama Mardiyya suka haɗa ido da Anty Zulaiha. Ummi tayi ajiyar zuciya don itama taga Maimuna tace "ba zama za muyi ba ina ƴar tamu?", Anty tace "tana ciki, wai yau zaku tafi da ƴar taku?, sai kuma naga ba a gyara mata ɗaki ba", Anty Zulaiha tace "ai ɗakinta a gyare yake, jiranta kawai yake", Anty tayi murmushi ta tashi ta shiga ɗakin Umma, ta tsaya tana kallon Hajar tace "to taso Hajar", hannunta riƙe da na Sabra ta tashi tana jin bugun zuciyarta a maƙoshi, kawai dagewa take amma jikinta duk yayi sanyi, Hafsa ma ta miƙe, Anty tace "toh cikata mana, kin riƙe yarinya", da cracking voice tace "da ita zan tafi..", baki buɗe Anty tace "Au da ita zaki tafi..", ta gyaɗa kai don da gaske take. Anty ta riƙe ɗayan hannunta wanda ta saƙalo small handbag dinta ta fito da ita tsakar gida, Mama Mardiyya tace "masha Allah" sai kuma ta miƙe tace "toh mu tashi ko", ta shatin veil dinta da ya rufe mata fuska take kallon Umma, ta saki hannun Sabra taje ta rumgumeta, sai alokacin ta saki kukan da take ta dannewa, idon Umma yayi rau rau don itama yaƙe kawai take, da kyar ta yaficeta daga jikinta ta shige ɗaki, Hajar ta kuma rushewa da kuka tamkar zata shiɗe, Ummi ta riƙota tace "yi haquri ko wace mace yar haka ce". Maama ta kirma wani uban hijab tana kallon Nabilah tace "ki taso muje muga kangon da za a kai Hajara", Nabilah tace "A'a nidae ba inda zani", Maimuna tace "ni bari na saka kaya mu tafi", Maama ta leƙa window tace "yi da jiki naga sun tashi..", shap shap Maimuna ta gama saka kaya, suna fita already anyi soro da Hajar dake gursheken kuka. da yake mota uku suka zo da ita akwai space sosai, Amarya Mama Mardiyya da Anty suka shiga mota guda, sai Hafsa a front seat, Ummi da Anty Zulaiha da wasila suka shiga mota daya, Maama da taga an barta a waje ta shiga buga windown motar Amarya, Mama Mardiyya ta buɗe glass tace "lfy?", Maama tace "ban gane lfy ba, ai harda ni za a kai amaryar", Mama Mardiyya tace "Ohk, ga wani motar can ai saiki shiga.." da haka ta zuge glass dinta, wani takaici ne ya turnuƙe Anty, idon baƙi ne zai hana ta tatawa Maama rashin mutunci, ɗayar Motar da ta rage Maama ta shiga tana zare ido, jikinta har rawa yake tana fatan waɗan nan motocin duk na haya ne wato Opay, Maimuna tayi kwam a gaban Mota, tafiyar minti talatin ce ta kaisu unguwar da zasu, motarsu Maama ce a front don haka itace ta fara shan kwanar street din gida, Maimuna sai cizon lips take tana kallon tsala tsalan gidajen da ke layin, a bakin gate din gidan da yafi ko wanne gida ƙawatuwa a layin motar ta tsaya, Maama ta ɗaga murya tana kallon driver tace "kai malam ya zaka ajiyemu a ƙofar gidan ƴan yankan kai, ba wancan ne gidan ba?..." ta nuna wani gida da duk yafi ƙanƙanta da rashin kyau a layin, driver ya danna horn yace "A'a ba nan bane, wnn wanda zamu shiga shine gidan", wani irin sakin baki Maama tayi har yawu na zuba. lokacin da suka shiga harabar gidan kam suman zaune tayi, motar Amarya da tasu Ummi ma ta shigo, Hajar Amarya ta fito a hankali tamkar wacca kwai ya fashewa aciki, idonta sai zugi yake tana shessheƙa a hankali. Mama Mardiyya da Ummi sukay main building da ita, Ummi tace "toh shiga da ƙafar dama da Bismillah"......✍️
💛 HAJAR💛
by Feenerh_feeche
{35..}
A hankali Hajar ta saka ƙafarta ta dama ta shiga gidanta bayan tayi Bismillah a zuciya, wani irin sanyi ne ya tsarga mata a jijiyoyin jiki, su Sakeena dake zaune a katafaren palourn suka fara musu sannu da zuwa, upstairs aka wuce da Hajar domin kaita ainahin ɗakinta, the room was in woah ba a cewa komai, it's very huge and luxury, aka ajiyeta a makeken italian bed dake ɗakin wanda a halin yanxu ya zama nata. Anty dake biye dasu tanata zabga murmushi tace "masha Allah", Hafsa ta shigo tana jan box din kayan Hajar, ta zauna gefenta tana ƙarewa ɗakin kallo, wnn ai daula aka kawo ƴar uwarta, wani hanin ga Allah baiwa ne, Allah ya bata zaman lfy da mijinta shine fatanta agareta, Anty ta fita tana bin ɗakunan dake saman ɗaya bayan ɗaya, bedroom biyu ne extra bayan wanda aka kai Hajar, saidai basu kai nata girma ba, wata sliding glass door ta hango wacca ko ba a gaya mata ba tasan turakar mai gidan ce, don haka ba tay hanyar ba kuma daman ma a rufe yake. da kyar Maama ta iya fitowa daga mota sbd jin ƙafafuwanta take tamkar ba zasu ɗauketa ba, Maimuna kam tini ta shige tana kashe kwarkwatar idonta, tamkar an wurgota haka ta shiga palourn tana zazzare ido, duk da sanyin Ac amma zufa take, Noor ta yamutsa fuska tace "wnn kuma daga ina?..", Aysha tace "who knows..", babu inda Maama bata shiga ba a ɗakunan ƙasa, kuma duk wanda ta shiga sai numfashinta ya ɗauke, nadama kam tayi yafi cikin kwando, duk ɗakin da ta shiga saita fito a gigice, tuntuɓe kam tayi wajen sau ashirin sbd kallon fitilu na jikin roof, tin jama'a basu lura ba har suka fara fahimta, a sama suka haɗu da Maimuna wacca ta maƙale a bedroom ɗaya tana fatan dama nata ne, Maama tace "kinga abinda Babanku ya aikata ko, ya siyar da Hajara, wnn ai gidan yankan kai ne", "ki ga yankan kai a kanki, wnn gidan auren Hajar ne..", Anty ce ta furta hakan tana shigowa dakin, Maama tace "ke Jamila ki shiga taitayinki..", Anty ta taɓe baki tace "dalla malamai ku fita karka saka mata ƙazanta a ɗaki, sa'a ma ku ka ci da akazo da ku..", Maama ta buɗe baki za tay