Showing 75001 words to 78000 words out of 114314 words

Chapter 26 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

rufe gate din shima da mukulli snn ya koma mota ya fara driving, ƙarfe bakwai da minti sha biyar ya danna horn a ƙofar gidansu, mai gadi ya bude masa, ya shiga wawakeken compound din gida yayi parking ya kashe motar ya fito, ya danna door bell, babu jimawa Laure mai aiki ta buɗe masa, bai saurari gaisuwar da take masa ba ya wuce great room din Abba, Noor ta fito daga kitchen da Apron a jikinta tace "wane yake knocking?", Laura tace "Alhj ƙarami ne..", Noor ta zaro ido tace "Yaya na?", Laure tace "Eh hajiya..", Noor tabi palourn da kallo tace "ina ya shiga?..", Laure tace "ɓangaren Alhj", Noor ba tace komai ba ta koma kitchen ta cigaba da suyar plantain da take. Nurain na shiga great room din Abba ya ciro wayarsa daga pocket ya fara kiran Abban, tana daf da katsewa Abba ya ɗaga yayi sallama yace "Uthman..", Nurain yace "na'am, am so sorry for disturbing you, barka da safiya Abba..", Abba yace "lfy lou..", Nurain yace "dan Allah i need to talk to you Abba, gani nan a palourn ka..", Abba yace "Alright" da haka ya katse kiran, bayan minti biyu ya bayyana a great room din da coffee color jallabiya a jikinsa, Nurain ya sauka kan carpet ya sake gaishesa, Abba yace "me ya faru Son?, what's the matter?", Nurain yayi gathering courage yace "am sorry Abba, wllh i can't accept this marriage, zan datse sa", Abba ya ringa kallonsa kafin yace "what happened all of a sudden Nurain?", Nurain ya shafa kansa yayi ajiyar zuciya yace "bazan iya zaman aure da yarinyar ba Abba", Abba exhale heavily yace "why?, musaka ce, ko akwai tawaya ajikinta ko wani abun?", Nurain ya kasa cewa komai, Abba yace "answer me..", ɗago kansa yayi yace "no one, kawai dai i will never accept her as my wife", Abba yayi shiru na some seconds kafin yace "toh ya kake so ayi Nurain, an riga an ɗaura auren?..", Nurain yace "plxx father ina neman yardar ka dan sakinta zanyi..", Abba yace "toh me yasa zaka nemi yarda ta Nurain, ai wuƙa da nama na hannunka, na gama role dina, ra'ayin ka ne ka zauna da ita snn kuma ra'ayin ka ne ka rabu da ita, kai ne mai saki a hannu...", Nurain yace "am very sorry to turn you down father..", Abba ya gyaɗa kai yace "ba komai, bazan tilasta maka ba Nurain, amma ka tabbatar bka son auren?", Nurain yace "yeah", Abba yace "i will find another way, ka rubuta takardar sakin ka kawomin...", buɗe ƙofa akay, suka juya suna kallon mai shigowa, Hajjaju Hajiya ta shigo tana dogara sandarta, ta kalli Abba ta cikin kantamemen glasses dinta tace "Muntari, ya naji kana cewa yaro ya kawo takardar saki, takardar saki kamar ya?, karfa ina ganin kayi abin arziƙi ka ɓige da tsiya Muntari...", Abba yace "sannu da zuwa Hajiya", ba ta amsa ba kawai dai ta kafesa da idanu ta cikin glasses tana lasar wawulon bakinta, Nurain ya miƙe yace "sannu da zuwa", ta ɗaga kai tana kallonsa tace "wai Usuman, ince dai kai ma garin ƙanƙara kaje don naga ka ƙara haske", yace "babu ƙanƙara a ƙasar da naje" ya riƙo hannunta ya ƙarasa shigowa da ita palourn, Nurain ya koma position dinsa ya zauna, saida ta zauna akan kujera ta kalli Abba da ke shirin gaisheta tace "tin jiya naso zuwa naje na rungumo matar Usuman na kai masa ɗaki, to ciwon ƙafa ya hanani, ai dole tayi ciwo na azabtar da ita lokacin ƙuruciya, tinda aka idar da Sallar asuba nake neman wanda zai kai ni gidan Usuman, shi Umaru bacci yake kuma gsky bazan tashi mai gida ba, ita kuma Shatu ba a maganarta maƙiwaciya ce..", Abba yace "Allah sarki", ya russuna yace "Hajiya barka da safiya..", tace "A'a bar barka da safiyar nan tukunna, wace takardar saki za a kawo?, wa za a saki?, waye zai yi saki?, kasan na tsani kalmar saki Muntari...", Abba ya kalli Nurain yace "Nurain ne zai saki matarsa..", Hajiya ta buɗe bakinta mai wawulo tace "wai Usuman, wace matar zai saka kuma?", Abba ya dubi Nurain yace "talk my friend..", Nurain ya sha kunu baice komai ba, Hajiya tace "Usuman a sbd wani dalilin za ka saki matar da aka aura ma jiya?, notin kanka ya kunce", Nurain yace "ba dalili, kawai bazan zauna da ita ba", Hajiya ta buga sandarta a kan carpet tace "haka fa, wato sbd ka mayar da mu ƙananan mutane a idon duniya ko, sbd ka zubarwa da Muntari kima ko, sbd ka zubar mana da mutunci ko, zaɓin mahaifin naka ne bai maka ba ko me?, naga hakan ne ya dace da kai tinda zaɓin naka da ka kawo guduwa tayi ta barka, shine daga aura maka yarinya jiya jiyan nan kace zaka saketa, toh ai ba akuya ko tinkiyar turke bace da za a saketa sakaka, sam ban amince da hakan ba, ai wnn ƙaranta ce...", Abba yayi ajiyar zuciya yace "Hajiya ayi haƙuri, nima Uthman ya bani mamaki wllh ban taɓa tunanin hakan daga garesa ba, tinda dai yace baya so ina ganin kawai ya saketan..", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "Au Muntari isa zaka nuna min akan ɗanka, wato abinda yake so za muyi sbd gashi uban mu, toh wllh bai isa yayi sakin nan ba, wnn ai mugunta ce da cin zali an auro yarinya jiya jiyan nan sai a saketa yau sbd rashin imani..", Abba ya rage murya yace "an janye maganar sakin, dan Allah Hajiya kiyi haƙuri..", ta janyo lulluɓin da ke kanta na atamfa ta cire glasses ta goge hawayen tace "Muntari na tsani kalmar saki", Abba yace "na sani Hajiya", ta mayar da glasses din ta dubi Nurain tace "Usuman na tsani kalmar saki", Nurain da zuciyarsa ke ƙoƙarin bombing ya shafa fuskarsa snn ya miƙe ya fita.


★Maama ce a tsakar gida sai zance take mara kan gado, goshi a kumbure yayi lemon tsami, ta gyara haɓar zaninta tace "tin jiya nake magana a gidan nan amma anƙi saurara ta, kawai an ɗau yarinya an kaita gidan yankan kai sai kace mara galihu iyee, naga dai da gatanta a duniya..", Baba ya fito daga ɗakinsa da shirin fita wajen aiki, yana zura takalmi Maama ta matsa kusa dashi tace "mal kana ji ina magana fa, wllh abinda kayi bai dace ba, ya zaka ɗauki ƴarka ka miƙata ga halaka ka kaita gidan yankan kai..", Baba ya kalleta yace "Au haba, ashe kin san Hajara ƴata ce ko Rabi?", Maama tace "yo ai ana ganin Hajara an san kaika haifeta mal, ni dai ina baka shawara wllh kaje ka ɗakko ƴarka daga wnn gidan tin kafin ayi layya da ita, toh ni dae na faɗa gidan yankan kai aka kaita..", Baba yayi wani murmushi na manya yace "tinda dai ba Nabilah ko Sa'adatu ko Maimuna na siyar ba ai shknn, ki zuba ruwa a ƙasa ki sha", da haka ya kira Umma da ke ɗakinta, fitowa tayi tace "gani mal", yace "na fita", tace "Allah ya tsare mal", yace "Ameen" ya saka kai ya fita daga gidan, Umma ta juya zata shiga ɗaki Maama tace "faɗima..", Umma ta haɗe gira ta juyo ta kalleta tace "dani kike?", Maama da ta koma wata psycho tace "akwai wata faɗimar ne bayan ke, dake nake..", Umma tace "Au", Maama har dasu gyara tsayuwa tace "idan mal baiji ba ina fatan ke kiji, wllh shawara nake baki, karki bari ayi layya da ƴarki, marmaza ki rugungunta kije ki ɗakko ƴarki..", Umma tayi wani murmushi tana kallon Maama sama da ƙasa tace "kashh baiwar Allah aini bana ɗaukan shawara dama dai basir ne wataƙila na ɗauka.." da haka ta bankaɗa labule ta shige ɗakinta ta bar Maama da sakakken baki, Maama ta ɗaga murya tace "in Allah ya yarda sai kunyi nadama keda mal, tinda kunnen ƙashi ne daku, a kwali za a kawo muku gunduguilar kan Hajara anyi layya da ita..", Sa'adatu ta fito tace "haba Maama ya zaki tashi da safiyar Allah ki ringa mana ihu a gida", Maama tace "Sa'adatu wai Maimuna ba ta gaya miki cewa mal ya siyar da Hajara ba, ai ita taga gidan, wllh na ƴan yankan kai ne", Sa'adatu ta yamutsa fuska tace "toh wai ina ruwanki Maama, ko gidan yankan kai aka kaita meye naki aciki..", Maama tace "wllh kuwa ba nawa a ciki, kawai dai shawara nake bawa mal yaje ya ɗakko ƴarsa a raba auren..", Sa'adatu tayi tsaki ta koma ɗaki. Maama tabi bayanta tana cewa "kamo min Balaraba a wayarki", Sa'adatu tace "ni bani da lambarta, Nabilah ce mai ita..", Maama ta ɗauki wayar Nabilah ta lalubo lambar Balaraba, tayi dialing saidai kuma babu kuɗi a wayar, da kyar Sa'adatu ta kira mata ita a tata wayar, tsabar rashin nutsuwa a waskace Maama ta riƙe wayar ta kara a kunne, Balaraba na ɗauka Maama tace "an yanka ta tashi, sai an biyani kuɗina", Balaraba tace "lfy ƙawata?", Maama tace "ina fa lfy, ai ko ƙamshin lfy babu a tare dani, gani nan zuwa gidan ki..", ba ta ƙarasa magana ba Sa'adatu ta warce wayar ta kashe tace "daman minti ɗaya nace", Maama ta bita da kallo.


★Noor ta shiga part din Mami ta sanar da ita cewar ta gama haɗa breakfast da za a kai gidan Nurain, Mami tace "good, an shirya a basket ko?", Noor tace "na bar Laure na shiryawa", Mami tace "Ohk, to kiyi sauri ki shirya a kai musu", Noor tace "tom, ai Yaya ma yazo", Mami tace "Nurain din, tin yaushe?", Noor tace "almost 20minutes, Hajiya ma is here tana part din Abba", Mami tace "okay, je ki shirya". Noor ta fita zuwa room dinta, Mami kuma ta fita zuwa part din Abba, Mami na shiga Hajiya ta miƙe kenan tayi support da sandarta, Mami ta gaisheta cike da ladabi, Hajiya ta amsa tace "ina Usuman din yazo ya kaini gidansa", Abba yace "call him for her", Mami tace "yana nan ne", Yace "yanxu ya fita daga nan", Mami tace "tom" da haka ta juya ta fita, upstairs ta haura zuwa room ɗinsa, ta ringa knocking amma no respond, murɗa handle din ƙofar tayi don taji a rufe yake ko a buɗe, ai kam tana murɗawa ta buɗe, Mami ta shiga, yana kwance kan bed yayi rigingine, kallon 5sec Mami tayi masa trying to figure out me yake damunsa, ta kirasa bai amsa ba, ta sake kiransa nan ma bai amsa ba, da alama ya lume cikin tunanin da yake, gefen bed din tayi taping tace "Nurain are you Okay?", ya tashi yana goge fuskarsa da palm yace "Sure, am okay", ta ringa kallonsa kafin tace "Alright, ka taso ka kai Hajiya gidanka", shiru yayi baice komai ba, Mami tace "kaji me nace?", yace "yeah", tace "toh yi da jiki gata can tana jiranka a palour", ta fita a ɗakin, saida yayi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa ƙanana snn ya fito, a hankali yake sakkowa daga stairs, thick eyebrows dinsa a haɗe, tini Hajiya da ke zaune main palour ta dogara sandarta tayi hanyar fita, Mami tace "tare da Noor za ku tafi zata kai breakfast", yace "tom" yabi bayan Hajiya, Noor ta fito daga kitchen da basket a hannunta Laure biye da ita itama da wani basket din a hannunta, Hajiya ta hakimce a gaban mota rungume da sandarta, Noor ta saka basket din abincin a boot snn ta shiga back seat, shi dai Nurain baice komai ba kawai ya kunna qira'ar Sheikh Abdul Baseet yana sauraro, har suka je gidan ba wanda yayi magana, ya sauka ya buɗe gate snn ya dawo ya shigar da motar compound, yana parking ya fita yaje ya buɗe ƙofar shiga main building, Hajiya ta dashare tooth tana kallon flowers tace "kaii gida zakwai", Hajiya na zuwa balcony Nurain ya buɗe mata ƙofar ta shiga shi kuma ya bar wajen, Noor na gama sauke basket yaja motarsa ya bar gidan daman bai rufe gate ba da suka shigo, saida ya zuge gate din amma bai sa masa key ba snn ya bar unguwar, da ɗaɗɗaya Noor ta shiga da kayan Abincin, Hajiya na tsaye ƙiƙam a palour tana ƙarewa ko ina kallo, Hajiya tace "kinga sai sallama nake ba amsa", Noor ta dubi tulin ledojin dake yashe a palourn tace "tana sama Hajiya, bari na kirata", Hajiya tace "A'a ina ke ina hawa sama, mijinta yazo ya kirata", Noor tace "ai ya fita", Hajiya ta hangame baki tace "ban san me yasa Usuman ya zama mai baƙar zuciya ba, kina gani fa zaman kurame mukay dashi a mota", Noor tace "mood ne ironlady..", Hajiya tace "meye kuma mood?", Noor tace "ina zuwa", ta haye stairs, ta kwankwasa ɗakin da Hajar take, bayan kamar minti uku tana knocking kawai ta murɗa ta shiga, surveying ɗakin ta ringa yi da idonta, daga can gefen gado ƙasan tiles ta hangota a kwance, ta ƙarasa kusa da ita ta tsugunna tace "Hajar.. Hajar.. Hajar..", ko motsi Hajar ba tay ba, Noor tayi taping ɗinta nan ma dai bata motsa ba, saida Noor ta nutsu snn taga yadda take breathing a hankali kamar zai ɗauke, ta taɓa goshinta taji zafi ɗau tamkar tasa akan wuta......✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{37..}
Noor ta sake taping dinta a hankali gami da kiran sunanta, da kyar Hajar ta buɗe idonta da sukay mata nauyi, tana buɗewa ta mayar ta rufe, Noor ta taɓa wuyanta taji shima yayi zafi ɗau amma bai kai kanta ba, Noor tace "Hajar are you Okay?", Hajar ta sake buɗe idonta da kyar tana jin yadda kanta ke sarawa kamar zai tsage, dishi dishi take ganin Noor, tace "Umma.. Umma.." kafin ta kuma lumshe idon, Noor dai ta fara firgita cause Hajar was so weak, ta tashi da sauri ta fita a ɗakin, downstairs ta sauka ta nufi inda ta ajiye handbag dinta, Hajiya da ke zaune kan sofa tace "ina matar gidan take?", Noor na ƙoƙarin ciro wayarta daga jaka tace "ina jin ba tada lfy ne, bari na kira yaya", tayi dialing numbern Nurain, no respond, ta kuma kira nan ma same thing, Hajiya tace "kai jama'a, ƴar nan kiyi min magana yadda zan gane mana waye kuma ba lfy?", Noor tace "Amaryar ce, jikinta zafi, ko motsi bata yi", Hajiya tace "ba kanta, sbd Usuman ya zama mai baƙin hali daga nace kar ya saki yarinya shine ya ƙullaceni, ya kawoni gidansa ya yasar sai kace bola, da badan ni na haifi mahaifinsa ba da yau sai ya iya kwakkwalla min mari, don yadda ya fusata ɗin nan ƙiris ya rage ya zargeni ɗaxu a palourn Muntari..", Noor dai bata tanka ba kawai kiran layin yayan ta take, sau wajen goma tana kira, ta sauke wayar daga kunnenta tace "Hajiya kinga bai ɗauka ba yanxu ya zanyi?, ba fa ta motsi", Hajiya ta gwalo ido tace "mun shiga uku, tana numfashi?", Noor ta haura sama da sauri da wayarta a hannunta, Hajiya dai ta bita da ido don ba ƙafar hawa bene, yadda Noor ta barta haka ta sake tarar da ita, ta ajiye wayarta gefen gado ta durƙusa gabanta ta kira sunanta don taga dai is she concious, yess she is concious amma daf take da zama unconscious, Noor ta fara ƙoƙarin ɗagata daga kan tiles, Hajar ta saka last strength dinta tayi ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, ƙafarta ta lankwashe za tayi collapsing a ƙasa Noor tayi saurin tarota ta turata kan gado, sosai hankalin Noor ya tashi ta ɗauki waya ta kira Mami, Mami na ɗagawa Noor tace "Mami, Hajar ce ba tada lfy, I don't think she is concious..", Mami tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un mai ya sameta?", Noor tace "i don't know wllh a haka na sameta", Mami tace "ina Nurain din?", Noor tace "he is not around tinda ya sauke mu ya fita, na kira wayarsa beyi picking ba..", Mami tace "seak for help outside, gani nan zuwa.." da haka ta katse kiran, Noor ta ringa kallon fuskar Hajar da pity eyes sai kuma ta juya ta fita, compound ta fita tana jin Hajiya na watso mata tambaya, ta buɗe gate ta fita, ta ringa bin layin da kallo wai ko zata ga wani, tsit har bayan minti goma da fitowarta ba taga wani ba, tayi deciding ko ta shiga wajen neighbors, gidan dake very close to the house ta fara knocking da dutse, almost 5mins amma ba a buɗe ba, wani tunani ne yazo mata don haka ta koma gida, ta maƙale jamlock ta yadda ƙofar ba zata garƙame ba, tana shiga palourn taga Hajiya sai jinjina take tana ƙoƙarin hawa stairs, ta riƙe railer gam da hannun dama hannu hagu kuma sandarta, Noor tace "Hajiya ki koma ki zauna bafa zaki iya hawa ba", Hajiya ta koma gefe tana haki tace "hankalina yaƙi ya kwanta wllh, naji kince batada lfy kuma naga kin fita kin barta ita kaɗai shine nace bari naje na zauna da ita ba a barin mara lfy shi kaɗai", Noor tace "ga Mami nan zuwa ai", taimako gaggawa Noor ta bawa Hajar ta hanyar jiƙa towel ta ɗora mata a forehead sbd zazzaɓin ya sauka. Babu daɗewa Mami da iso gidan tare da driver, Hajiya tace "Dije, a tsakani ga Allah mai Usuman yake shirin zama ne, tinda ya kawomu ya yasar ya saka kai ya fita, ga yarinya can a ƙololuwar samaniya sai suma teke tana farfaɗowa, mijinta likita amma bashi da wani amfani..", Mami tace "Noor na sama da ita knn?", Hajiya ta gyaɗa kai tace "takwarata keta wahala wllh", Mami ta haura saman, ƙofar da ta gani a buɗe ta shiga, Noor ta miƙe daga gefen bed tace "Mami you're here already..", Mami tana kallon innocent face din Hajat tace "how is she?", Noor tayi ajiyar zuciya tace "A bit okay", Mami ta matsa kusa da gadon tana kallon kyakkyawar fuskar Hajar, indeed she is beautiful and young, Mami tace "Bacci take?", Noor tace "A'a ta zama very weak ne", Mami tace "gyara mata ɗankwali sai mu wuce hospital en Dr Mansoor", Noor

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login