Showing 66001 words to 69000 words out of 114314 words

Chapter 23 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

ɗaura mata aure da wani ba...", katseta yayi yace "karki ɗaga hankalinki Faɗima, kiyi mata addu'a Allah yasa hakan shine alkhairy a gareta", tace "amma mal...", yace "idan kika ɗaga hankalinki waye zai kwantarwa da Hajara nata, itace wacca ya kamata a duba, idan kika samu nutsuwa itama hankalinta ba zai tashi sosaii ba, ƙaddararta ce, ko wane dan Adam da irin tasa, Allah ya rubuta ba Nura ne mijinta ba, ni kuma na gaya miki mutumin da na bawa auren Hajara bashi da matsala", Umma ta ajiye deep breathe tace "Allah yasa hakan shine alkhairy, amma taya ya zan sanar da ita?", Baba yace "she's your daughter fa, ki kiramin ita", ta gyara daurin dankwalinta ta miƙe ta fita da wani facial expression a fuskarta. ɗakin Baba ta nufa inda Hajar da muƙarrabanta ke zauna, a bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, Umma ta dubi Hajar da tayi wani kyau wanda bata taɓa irinsa ba a rayuwa tace "kije inji Babanku yana ɗakinsu Mu'azzam", Hajar tace "tom", ta saka wayarta acikin handbag dinta, gyara yafen mayafinta da yake fitar da ainahin ƙamshin kabbasa tayi, ta saka takalminta flat mai kyau snn ta fita. Umma kam ɗakinta ta shige, ta matsar da kayan dake gefen gado ta zauna ta dafe kanta, a haka Anty ta shigo ta sameta tace "Adda, lfy kuwa?, ya da tagumi haka a lokacin farin ciki", Umma ta ajiye numfashi a hankali tace "Jamila", Anty ta samu guri ta zauna sbd yanayin ƴar uwarta ta, Umma tace "kin san kwa bada Nura aka ɗaurawa Hajara aure ba", Anty ta gwalo ido tace "ban fahimce ki ba Adda", Umma tace "uhmmm" ta labarta mata abinda Baba ya sanar da ita, shiru Anty tayi tana kallonta, kasa cewa komai tay kawai juya lamarin take a kwanyarta, can tace "kiyi haƙuri Adda amma sai naga kamar kun yiwa Hajar gaggawa, wai har nawa take har yanxu fa bata cike shekara 18 ba, dan ma tanada garun jiki amma wllh bata isa aure ba...", Umma tace "ba haka bane Jamila, muma ai bamu kaita ba aka kaimu gidan miji, kuma muka zauna", Anty tace "haka ne Adda, duk yadda zamani ya juya haka za a tafi dashi, a wnn zamanin aure yafi kyau idan yarinya ta kai shekaru 20, ta mallaki hankalinta...", Umma dai tayi shiru, Anty tace "Hajar ɗin ta sani?", Umma tace "Eh nasan yanzu ta sani, Mal ya sanar da ita". Hajar ta fito daga ɗakinsu Mu'azzam ƙafarta na harɗewa, da gudu ta shige ɗakin Umma ta zube a ƙasa snn ta fashe da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, runtse ido Umma tayi tana jin itama kamar tayi kukan, Anty ta taso ta ɗagota ta rufe mata baki tace "shhhh, kiyi haƙuri kinji", kuka take kamar ranta zai fita.


★Mami ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗin Abba, da sallama ta shiga, Abba dake zaune kan kujera two sitter ya amsa mata, a gefensa ta zauna, ta ɗauke hularsa dake hannun kujerar ta ajiye bisa huge Centre table dake palourn, tace "gani yallabai, amma dai ba'a masallacin sarki kayi juma'a ba?", Abba ya sosa forehead dinsa yace "Eh, a can Masallacin Abubakar Siddiq nayi", tace "Ohk", yace "yau ce ranar da Uthman zai dawo ko?", tace "insha Allah, ɗazu na gama waya dashi sun ma taso, 9pm za suyi landing", ya gyaɗa kai yace "Alright, a yau da na fita ban dawo gida ba saida na ɗaurawa Nurain aure", cike da mamaki Mami ta dubesa har tana haɗe gira tace "aure kuma yallaɓai?", yace "yess, so start all the necessary preparations tommorow insha Allah za aje a ɗakko masa matarsa", Mami was speechless na kusan 1minute kafin tace "but without his consent aka ɗaura", yace "Do i need his consent, he is my son, he most respect my decision", Mami tace "this is a different case...", yace "i know, a da fa haka ake daura maka aure ba tare da kasan waye ka aura ba, iyaye ne kawai suke haɗinsu", Maami exhale heavily tace "wa ka aura masa?", yace "sunanta Hajar, ƴar wajen abokina ce", tace "Allah ya basu zaman lfy", yace "Ameen, key din gidansa na wajenki ko?", tace "Eh suna wajena", yace "ohk, sai a duba gidan nasa kafin Allah ya kaimu gobe", tace "sure, za ai komai". Mami na fitowa daga wajen Abba ta shiga kiran ƴar uwarta Zulaiha, tana picking Mami tace "idan ba damuwa ina son ganinki Zulaiha", Anty Zulaiha tace "ohk, when?", Mami tace "idan ma zaki taho yanxu to nafi son haka", Anty Zulaiha tace "is everything ok?", Mami tace "sure, komai lfy urgent abu ne ya taso", Anty Zulaiha tace "Shknn I'll be there right away", da haka Mami ta katse kiran thinking of another thing to do, After 40mins Anty Zulaiha ta iso tare da Khausar, direct palourn Mami suka wuce, Khausar ta sunkuya ta gaida Mami, amsawa Mami tayi tana tambayarta school, Noor ce ta fito daga bedroom din Mami sanye da english wears, gaisawa sukay da Anty Zulaiha snn taja hannun Khausar suka fita daga part din zuwa huge room ɗinta, Anty Zulaiha ta cire gyalenta ta gyara zama sosai bisa executive sofar palourn tace "wai mene ne abinda ya taso urgent?", Mami tace "ɗaxu Abba da ya dawo daga masallaci yake gayamin cewa wai ya ɗaurawa Nurain aure da ƴar abokinsa", Anty Zulaiha tace "ikon Allah, daman har yanzu ana irin wnn haɗin", Mami tace "nima dai haka nagani, saidai fatan alkhairy, wai sai gobe za a kawo amaryar, yanzu dai gidan Nurain din nake so aje a duba, an riga anyi furnishing dinsa amma kuma almost 8months ba shigesa ba, kinga za aje a dudduba abinda yayi damage, komai dai ya zama intact", Anty Zulaiha tace "toh ai wnn ba aikin mu bane, na dangin Amarya ne", Mami tace "yess nasu ne, Abba ne yace a buɗe gidan a gyara", Anty Zulaiha tace "toh shknn, ai sai a tura ma'aikata su gyara, su firfito da abinda yayi damage, mu kuma in Allah ya kaimu goben sai muje mu gani", Mami tace "nima haka nake tunani, kawai a tura masu aiki", Anty Zulaiha tace "toh kuma haka za a ajiye yarinyar a gidan babu mijinta", Mami tace "No, ai yau Nurain ɗin zai dawo", Anty Zulaiha tace "toh masha Allah abu yayi kyau kinga yana dawowa sai yayi Settling down, Allah yasa ta zame masa babban tukuici na abinda Ruqayyah tayi masa", Mami tace "Ameen". labourers aka tura katafaren gidan Nurain, tin daga sama har ƙasa aka shiga tsaftacesa, babu wani datti sai dust da dry falling leaves.


★Da misalin ƙarfe takwas da minti hamsin na dare ya parker luntsumemiyar motarsa a parking space da ke babban international airport na garin kano, waiting area ya nufa ya zauna yana kallon wajen da matafiya suke ɓullowa, yana jin announcement na saukar jirgin da ya iso daga India ya miƙe tsaye, few minutes kam suka fara fitowa, shine na biyar, sanye yake cikin ƙananan kaya da Pcap saman kansa kamar yadda ya bar 9ja, hannunsa daya na riƙe da trolley da yake ja yayinda ɗaya yake maƙale cikin sweet black pant nasa, Farooq na hango brother din nasa ya fara tafiya towards him, Nurain ya ciro hannunsa daga pocket ya dunƙulesa, shima Farooq dunƙule hannun nasa yayi, suna haɗewa suka haɗa hannayen nasu, Nurain yayi murmushi yace "hey dude", Farooq yayi masa side hug yace "barka da zuwa punk". saida aka gama checking luggage ɗin Nurain snn suka baro airport din, Farooq dake driving da mininum speed yace "ko dai wajen amaryata zamu wuce", Nurain yace "No, iron lady ban shirya facing dinta ba", slight smirk Farooq yayi yace "tsohuwa mai ran ƙarfe", Nurain yace "oh God look at how you're driving, ka take accelerator", Farooq yace "as in how na take accelerator, wai naga fa Doctors suna lallaɓa lafiyarsa amma look at you kana so ayi risking taka", Nurain yayi resting jikin kujera can ƙasan maƙoshi yace "hurry up". Farooq ya ƙara gudun motar kaɗan, slow down yayi kafin ya juya kan motar ya shiga street din gidan uncle ɗinsa, a bakin huge gate ɗin gidan ya danna horn, da sauri mai gadi ya zuge gate, ya danna motar ciki, parking lots ya isa yayi parking snn ya kashe motar, yana ciro key daga Ignition yace "did you just take a nap?", Nurain ya buɗe idonsa yana kallon environment ɗin ya yake ciki, buɗe motar yayi ya fita, yayi ajiyar zuciya yana stretching kansa yace "home sweet slum".......✍️


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{33..}
Farooq ya buɗe back seat ya ciro bag da trolley, ya kalli Nurain da ya gama stretching kansa yace "wai ka gaji ne?", Nurain yayi ƙass ƙass da fingers ɗinsa yace "yeah, am exhausted". da sauri Garba ya taho wajen, har ƙasa ya durƙusa yace "sannu da zuwa Alhj ƙarami, an dawo lfy", Nurain yace "yauwa Garba, ya ƙasa?", Garba yace "ƙasa tana nan yadda ka barta", tashi yayi ya gaida Farooq ma snn ya amshi bag da trolley. huge luxury main building ɗin gidan suka nufa, suna isa balcony Nurain ya danna bell, few seconds Noor ta buɗe, ta daka tsalle tace "oyoyo Yaya" sai kuma ta koma cikin palourn tana cewa "the groom is here Mami", sosai abinda ta faɗa yayi hitting eardrums dinsa, wai the groom, ya juya ya dubi Farooq yace "you", Farooq ya girgiza kai yace "nope", ai tini Noor ta shige part din Mami, Farooq ya zauna a daya daga cikin executive sofar dake babban palourn, Garba ya ajiye kayan da ya shigo dasu yayi waje, Nurain kam part din Mamin sa ya nufa, Mami ta fito daga bedroom ɗinta knn ya shigo, Pcap ɗin kansa ya cire ya zo ya rungumeta yace "i missed you Mami", Mami tace "Nurain...", Noor da ke murmushi all her white tooth out tace "Yaya sannu da zuwa", yace "lil iron lady, how are you doing", tace "am great alhmdllh", Mami tace "ina Umar ɗin?", yace "yana palour", tace "Ohk, muje can", main palourn suka fito, Mami ta zauna tace "mijin Hajiya", Farooq yayi murmushi yana shafa kansa ya zamo ƙasa ya gaidata, Mami ta amsa tace "ka ɗakko brother ɗinka knn?", yayi murmushi yace "Eh", Nurain ya zauna bisa lallausar rug din palourn ya gaisheta shima, ta amsa tana saka masa albarka, Kitchen Noor ta shiga ta ɗakko ruwa da drinks with glass goblet ta fito, kusa da Farooq ta ajiye tace "ina yina ya Farooq", yace "lfy lou Noory", tace "yasu Ummi da Aysha?", yace "suna nan lfy". Nurain yace "Abba fa?", Mami tace "yana ciki", yace "ohk bari naje wajensa", ya dubi Farooq yace "muje dude", a tare suka shiga part din Abba, Mami ta dubi Noor dake operating waya tace "ohh kin fara jarabar danna wayar ko?", tace "No Mami, course mate ɗita ce ta turomin da question na assignment", Mami tace "toh tashi ki shirya musu dining kafin su fito", tace "tom", ta ajiye wayar ta gyara hular kanta ta shiga kitchen. Abba ya kawar da system da yake operating ya daga kai yana kallon zaratan samarinsa, da Farooq suka fara gaisawa kana Nurain, Abba yace "ya aiki Engineer?", Farooq ya shafa kansa yace "alhmdllh Abba", Abba yace "toh madallah Allah ya temaka", Farooq yace "Ameen", Abba yace "Uthman..", Nurain yace "na'am", Abba yace "ya karatun, an gama lfy?", Nurain yace "Eh alhmdllh, an samu abinda aka je nema", Abba yayi ajiyar zuciya yace "masha Allah, Allah yasa ya amfana", tare suka amsa da Ameen snn suka fito. already Noor ta gama setting table, Mami tace "ga abinci kan dining", Farooq ya dubi tsadadden agogon wrist dinsa yace "wllh Alhmdllh, am full, zan wuce yanxu", yayi musu sallama ya tafi, har compound Nurain ya rakasa snn ya dawo, Noor ya saka ta kawo masa abincin nan palour ya ci don shi he don't like it eating on table, ba laifi yaci abincin cause yaji taste en abincin na Mami ne, ya ture plate din daga gabansa ya buɗe bottle water ya zuba a cup ya sha, stretching kansa yayi yana lumshe ido, duk gajiya ce ajikinsa, duk lokacin da yayi tafiya a jirgi sai yaji kamar nerves ɗinsa sunyi freezing, shiyasa yake yawan yin miƙa, Mami tace "ka je ka huta Nurain", yayi ajiyar zuciya yace "yeah", ya tashi yana massaging neck dinsa, trolleynsa ya janyo yace "ga stuff na India", Noor tace "Yaya a New Delhi ka zauna?", yace "yap, that's where my school is", da haka ya ɗauki bag ɗinsa ya haye stairs still massaging his thick neck, ya tarar da room ɗinsa a gyare tsaf tsaf komai tide, ƙamshin freshner da traditional scent mai dadi ne yake tashi, ga sanyin Ac, huge Chinese comfortable bed ɗinsa malale da white bedding. wayarsa ya ɗakko daga bag yayi powering dinta, ya cire Sim card ɗin ciki ya musanya da ainahin nasa na Nigeria, ya ajiye wayar akan mirror ya shiga bathroom domin ya sakarwa kansa warm water, ko 1min beyi ba da shiga wayarsa ta fara tsuwwa, kiran na yankewa wani ya sake shigowa, shima yana katsewa wani ya biyo baya, haka kiran yayi ta shigowa ba ƙaƙƙautawa, da sauri ya gama abinda zai ya fito, yayi wrapping kansa da bathrobe, gefen kunnensa duk kumfa sbd saurin da yayi ya fito don yaga wane yake masa wnn mummunar kiran daga kunna waya, ɗaukar wayar yayi wacca take ringing har lokacin, ya tattare gira gami da tsuke piercing eyes ɗinsa yana kallon screen ɗin wayar, sunan da yake jiki da kuma numbern ba baƙinsa bane, tabbas beyi blocking numbern ta ba amma kuma bai sake kira ba, wani ɗaci yaji a throat ensa, ya dangwarar da wayar yace "Damn it.."


★Kaf waɗanda suka zo biki sun ɗaɗe, mutanen Yola kam ana gama ɗaurin aure suka saɓi hanya, Anty Jamila sai Hafsa wacca aka bari domin ta ɗebeba Hajar kewa ne kawai suke rage a gidan, Wasila kuma ta tafi da zummar insha Allah gobe da sassafe zata dawo. da hijab ɗin da tayi sallar isha'i ta ƙudunduna ta takure waje ɗaya, a kwance take kan dardumar da ta idar da sallah, hawaye na zuba daga manyan lulu eyes ɗinta waɗanda suka ƙanƙance tsabar kukan da ta sha, ƙirjinta da maƙoranta har zafi suke sbd shessheƙar kuka, Anty ta tsaya a kanta tace "hasbunallah, Hajar ba zaki dena kukan nan ba ko?", da dasasshiyar murya tace "ba kuka nake ba", Anty tace "toh tashi zaune", a hankali Hajar ta miƙe zaune ta jingina da bango, sosai ta bawa Anty tausayi tace "za kici abinci?", ta girgiza kai tana goge kumatunta tace "na ƙoshi, bazan iya ci ba ƙirjina ciwo yake", Anty tace "sannu, ai baza ki kwanta da yunwa ba bari a siyo miki yoghurt" da haka ta fita daga ɗakin. Hafsa ta matsa kusa da Hajar tace "sannu sister", Hajar tace "wllh ji nake kamar zuciyata zata fashe, wai ba ya sayyadina na aura ba, na shiga uku Hafsa", ta rufe fuskarta da hijab ta sake rushewa da kuka, Hafsa tace "Allah ya ƙaddara ba shine mijinki ba, kiyi addu'a Allah yasa hakan alkhairy ne a gareki", Hajar na shessheƙar kuka tace "ban san fa wanda aka aura min ba, ban san wane irin mutum bane". Hafsa tace "koma waye insha Allah alkhairy ne", jinginar da kanta tayi a bango ta lumshe idonta, hawayen da suka taru suka fara zarya a kuncinta. Sallama aka rangaɗa daga soro, Anty dake tsakar gida tana waya da Mu'azzam da take basa saƙon siyo yoghurt, kashe wayar tayi ta amsa sallamar da akay, Umma ta fito daga ɗakin Baba tace "waye?", matar da tayi sallama ce ta shigo tace "Larai ce", Umma ta tsaya tana kallonta da taimakon hasken kwan lantarki sbd akwai nepa, Umma ta shimfiɗa tabarma tace "Bismillah" duk da dai bata shaida wace ce ba, dattijuwar da ta kira kanta da Larai ta zauna akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa, gaisawa sukay, Anty ma ta gaisheta, ta dubi Umma tace "baiwar Allah kece mahaifiyar Hajara", Umma tace "Eh nice", tace "Alhmdllh, wllh tllh nice nayi muku laifi, dan girman Allah kuyi haƙuri", Umma tace "Allah sarki, laifin me kika min baiwar Allah?, ai ni ban ma shaida ki ba", tace "mahaifiyar Nuraddeen ce wanda za a ɗaura masa aure da ƴarku", tini Umma ta canza fuska, Anty da ke zaune kan ƙaramar kujera ta ɗaure fuska, Umma tace "oho, to ince dai lfy?, ai an mayar muku da kayanku", Hajiya tace "ba wnn bace ta kawoni, dan girman Allah kuyi haƙuri akan abinda mu kayi muku, wllh laifina ne shiyasa na taso takanas nazo domin na baku haƙuri", Umma tayi murmushin yaƙe tace "ba komai mun haƙura, muma Allah ya yafe mana", Hajiya tayi ajiyar zuciya tace "Alhmdllh, Allah yayi albarka, auren da aka fasa ɗaurawa da rana sai a ɗaurasa yanxu da daddare", Umma ta ajiye numfashi tace "bari nayi miki magana da baban yarinyar" da haka ta miƙe ta shiga ɗakin Baba, kaf yaji abinda ya faru don haka bai bata damar magana ba ya fito tsakar gidan, Anty ta tashi ta shiga ɗaki. Baba ya gaisa da Hajiya wacca ta shiga basa haƙuri, yace "Allah sarki, ai komai muƙaddari ne..", Hajiya tace "haka ne, amma wllh nice nan silar wnn babbar ɓarna, dan girman Allah ku yafe min, a ɗaurawa ɗana Auren da yarinyar ku", Baba yayi ajiyar zuciya yana jujjuya wnn lamari, Maama ta fito da ɗauri ƙirji da mafici a hannunta tace "haba don Allah, wllh kun fiya gutsittsira zance, kawai ku gaya mata cewa an ɗaurawa Hajara aure da wani a maimakon ɗanta", da matuƙar mamaki Hajiya ta dubeta sai kuma ta kalli Baba tace "wai haka ne?", Maama tace "Yo ya faɗa miki da bakinsa kiji, shi ya aura mata wani da ɗanki yace ya fasa", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "wllh babu ruwan Nuraddeen, nice me laifi, ni nace a fasa auren, wllh lokacin da nake faɗa ma ban san inda kaina yake ba, dan Allah dan darajar alƙur'ani mai girma karku hana ɗana auren ƴarku", Baba yayi ajiyar zuciya gami da yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login