Showing 42001 words to 45000 words out of 114314 words
Chapter 15 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
tamkar madara tace "nagode". wayarta dake tsuwwa ta ɗauka ganin me kira tayi murmushi tace "ina jin ma ya iso", kara wayar tayi a kunne tace "okay, gani nan fitowa", mayafin da ta fitar ta ɗauka ta yafa, Hafsa tace "laa ya naga kinsa mayafi ba Hijab ba, ko ba ustaz bane?", Hajar ta zabga mata harara tace "chab wai dan yana malamin islamiyya shine zai zama ustaz, wllh ba ruwansa indai zaki saka abinda zai rufe miki jiki to shi bashi da damuwa", Hafsa ta kalleta sama da ƙasa taga dai ruf mayafin da ta saka ya rufe mata jiki kuma ba shara shara bane, Hafsa tace "Eh, kinsan mazan ma kowa da ra'ayinsa, wani yafi son Hijab wani kuma mayafi wani kuma duka, wani kuma babu ruwansa indai za kiyi decent dressing is okay", Hajar tace "that's my Man shima decent kawai yake so", Hafsa tace "yana fa jira", Hajar tayi wasa da kwayar idonta tace "ai ya saba" ta ɗauki turare ta fesa sama sama. slowly Hajar ta fito compound ta nufi gate, ta bude ƙofa ta fita, yana tsaye jikin fillelen sabon motorbike dinsa yana danna wayarsa, yana ganinta yayi murmushi ya mayar da wayar aljihu, kallonta ya ringa yi ba ƙiftawa har ta ƙaraso, sosai silent kwalliyar da tayi da kuma decent dressing ɗinta ya tafi da imaninsa, sunkuyar da kanta tayi tace "sannu da zuwa", baice komai ba kawai kallonta yake, shirun da taji ne yasa ta ɗago kanta ai kam sukay ido huɗu, tayi sauri ta sunkuyar da nata tace "Bismillah ka shigo", yace "A'a nidae bazan shiga gidan mutane ba", tace "toh nan fa kan hanya ne", ya dubi street ɗin yaga akwai mutane yace "toh amma dai ansan da zuwa na dai ko?", childishly ta hararesa tace "Bismillah" ta juya ta koma ciki ba tare da ta jira cewarsa ba. bayanta yabi har suka shiga gidan tayi leading ɗinsa har sitting room. a kujera one seater ya zauna ita kuma ta zauna a two seater dake gefensa, Calmly tace "ina yini", ya ringa kallonta, ɗago kanta tayi jin bai amsa ba sukay ido huɗu, tayi pouting lips ta rufe fuskarta da palms ɗinta tace "dan Allah ka barii", murmushi mai sauti yayi yace "me fa?", tace "why are you staring at me?", yace "because i missed you so much and you look beautiful", murmushi tayi tana wasa da yatsun ƙafarta, yace "ba ki rubuta Jamb ba ko?", ta gyaɗa masa kai tace "Eh neco kawai na zana", yace "Ohk, suma yanxu school of Nursing suna amfani da jamb, gashi baki rubuta ba amma ba damuwa saiki rubuta next year ko?", tace "Admission din bazai samu ba saida Jamb result knn?", yace "Eh, ai da nasan sun canja tsari da sai kin zana jamb, kamar yanxu ne zaki ji an fara registration, and you're still young kinada enough time", tace "Ahh I'm not young", yace "ohk sai ki gayawa wanda bai sanki ba to me you're a little girl kuma you know akwai certificate of birth ɗinki a wajena", sallama akai a bakin ƙofa Hajar ta amsa, Hafsa ce ta shigo tana sanye da hijab hannunta riƙe da tray mai dauke da bottle water da drinks sai kuma plate ɗin semosa, a hankali ta ajiye trayn akan Centre table ta zauna kusa da Hajar, Hafsa tace "sannu da zuwa, ina yini", Nura yace "mun yini lfy?", tace "alhmdllh", yace "masha Allah, ya karatu?", Hafsa tace "alhmdllh", a hankali Hafsa ta miƙe ta basu waje tana fita ɗakin akay knocking gate, bakin gate ɗin ta wuce ta buɗe ƙofa, ita tasha ma Humaira ce ta dawo daga islamiyya amma me sai taga wani yaro, tace "ya akai?", yaron yace "wani mutum ne yace wai ana sallama da Hajar", tace "yana ina?", yaron yayi nuni da wata jugunanniyar mota dake gefen titi a parke, Hafsa ta kalli mutumin da ya fito daga cikin motar, zaro ido tayi sbd ta ganesa, shine mutumin da suka hadu jiya a supermarket, Ahmad ya ƙaraso bakin gate ɗin yana kallon Hafsa da itama take kallonsa cike da mamaki.......✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{ 22..}
Ahmad ya shafa kansa yana kallon Hafsa yace "Assalamu alaikum", har lokacin mamaki bai bar face dinta ba tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, kinyi mamakin gani na ko?", tace "dole, ince dai lfy bawan Allah?", numfashi ya sauke a sauƙaƙe yace "Ammm lfy", tace "Ohk" ta juya zata koma gida, da sauri yace "amm Hajar fa?" ya fada yana shafa kwantaccen beard ɗinsa, ta juyo tace "what about her?", yace "i came for her, help me by informing her", hannunta na riƙe da ƙofa tace "ohh, amma Hajar ba ta nan", mood ɗinsa ne ya canza lokaci guda yace "bata nan?", Hafsa ta gyaɗa masa kai cause that was the only way, yace "I'm sorry to invade her privacy, tana ina?", ta saukar da kanta ƙasa tana tunanin abinda za ta faɗa, few seconds passed amma ba tace komai ba, ya ringa kallon fuskarta with his cool voice yace "girl.., where is your sister?", ta ɗago ta kallesa sbd yadda yayi pronouncing girl ɗin tace "amm sunje unguwa da Babarmu", yace "Okay thank you, ai naga yamma ma tayi sosai, bari kawai na jirata...", ta katsesa tace "A'a karka jirata, ba yanxu zasu dawo ba", yace "toh sai yaushe?" yana kallon cikin idonta da rashin gaskiya ya bayyana ainun, hade gira tayi tace "A'a, nace fa ba yanxu zasu dawo ba, may be ma acan zasu kwana", Humaira ce ta ɓullo ta layin dake gefen gidan ta dawo daga islamiyya, sosai gaban Hafsa ya faɗi ganinta da tayi, Humaira ta tsaya tana kallonsu ko ƙiftawa babu sai kuma ta ƙaraso ta shiga gida, Hafsa ta sauke ajiyar zuciya tabi bayanta da kallo, rediyo me jini knn, tasan tabbas saita zayyanawa Anty abinda ta gani, Hafsa tace "sai dai ka dawo gobe", yace "No zan dawo anjima dai", tace "toh idan kuma basu dawo ba fa sun kwana acan", yace "No problem sai na dawo gobe, she worth it", tace "alright" ta juya zata shiga gida yace "wait", ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace "kinga kwa Cousin dinki tana bani wahala kema kina tayata ko?", tace "kamar ya?", yayi slight smirk yace "kin ƙi faɗamin whereabout ɗinta, and my heart keep saying that my Hajar is inside the house", Hafsa can't help it dole tayi slight smile ta juyo tace "really", ya gyaɗa kai yace "sure, young lady do you believe in fate?", sosai tambayarsa ta bata mamaki tace "Yess Noo", yace "hmmm, toh yess ne or No?", ta karyar da kai gefe tace "toh nidae a nawa view ɗin is No, a view din wasu kuma zance yess", yace "toh a ajiye naki view din a gefe a dauki na wasun, kema nasan bazaki so ki zama silar datse fate ba", kallonsa tay tace "sure bazan so hakan ba, abu guda ɗaya i promise you ni da kaina zan fito maka da Hajar amma not today, zanyi hakan ne dan na nuna maka cewa bazan datse fate ba..", kallonta ya ringa yi kafin yace "then when?", tace "sooner or later", ya gyaɗa kai yace "amma taya zan san lokacin?", tace "where is your phone?", wayarsa ya ciro a aljihu, a hankali ta fara karanto masa number yana lodawa, tana gama gaya masa tace "sau ɗaya zaka kira, idan lokacin yayi zan kiraka..." da haka ta shige gida ta rufe ba ta jira cewarsa ba. Ahmad yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya ya shiga motarsa, saida ya kira layin Hajar wajen sau uku amma bata shiga, tin ɗazu abinda ake ce masa knn. ƙarfe shida da minti sha biyar Nura ya miƙe daga kan kujera, ya ciro bandir ɗin ƴan 200 ya ajiye a hannun kujera, Hajar na ganin haka tace "kaga ka ɗauki kuɗinka", yace "toh ai ba ke na bawa ba, na Hafsa ne", ya fita a ɗakin tabi bayansa, a bakin gate ya tsaya yana kallonta yace "toh sai munyi waya", ta gyaɗa kai tace "toh", yace "toh shiga gida", ta juya ta shiga gida a hankali ta rufe ƙofa, sitting room ta shiga ta ɗauki kuɗin da tray ta fita, kitchen ta fara shiga ta ajiye trayn ta ɗauki glass cup mai ɗauke da ragowar lemon da ya rage tana murmushi, a hankali ta kafa kai ta moɗe lemon snn ta fito ta shiga ɗakinsu Hafsa, rafar kuɗin ta ajiye akan cinyar Hafsa dake gefen gado tana operating wayarta, ga Humaira a gefenta sai zaro idanu take tamkar ɓera a buta, Hafsa ta dubi Hajar da mamaki tace "meye wnn?", Hajar na warware ɗaurin dankwali tace "cewa yayi na baki", Hafsa ta zaro ido tace "na shiga uku Hajar shine kuma kika amsa", Hajar tace "tinda yayi niyya wllh ba yadda na iya", Hafsa ta ɗauki kuɗin tana juyasu tace "amma sunyi yawa wllh, ni ya zanyi dasu?", Hajar tace "nima ban sani ba", Hafsa ta kalli Humaira ta galla mata harara tace "na dai gaya miki, wllh kika kuskura kikai wata magana a gaban Anty sai na kira miki IT, yadda ya cinye wnn yaron acikin kwata kema haka zai miki", a rikice Humaira tace "dan Allah kiyi haƙuri wllh bazan ce komai ba", Hafsa ta hade gira tace "yawwa kin temaki kanki yarinya, tashi ki tafi palour ki kunna cartoon", a hankali Humaira ta miƙe tana murza ido ta fita, Hajar tace "ji muguwa, me yasa kike threatening dinta?", Hafsa tace "guess what?", Hajar tace "what?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka hadu a supermarket ne yazo", Hajar tace "ban gane ba", Hafsa tace "ɗazu ne kina tare da Nura, bayan na fito daga wajenku naji ana knocking gate, ina buɗe gate na tarar dashi a ƙofar gida, ke ba kiga dagar da mukay dashi ba kafin ya tafi, toh shine Humaira ta ganni dashi a ƙofar gida, kinsan rediyo me jini ce yanxu saita rattaɓawa Anty a yimin wata fassarar ta daban", Hajar ta taɓe baki tace "toh taya ya san gidan nan?", Hafsa tace "ke zan tambaya", Hajar ba tace komai ba ta canza kayan jikinta ta fita ɗakin zuwa kitchen ta ɗora dinner.
★Washe gari da safe Umma ta hadawa Baba breakfast ɗinsa, tana zaune gefensa yana cin abincin a hankali tana masa fifita, ledar drugs ɗinsa ta janyo ta ɓalli wanda zai sha ta basa, Baba yace "Allah yayi albarka", tayi murmushi tace "Ameen", ya jinginar da kansa ga bango yace "wai ina Hajara ne?", Umma ta ajiye maficin hannunta tace "tana gidan Jamila", ya gyaɗa kai yace "toh ta dawo gida haka nan", Umma ta gyara zama tace "malam na fi son ta cigaba da zama a can, wllh yanxu gidan nan kunnenmu ƙanƙanra ba hatsaniya, Hajara ba hakuri gareta ba, kamar dage take indai aka taɓata saita rama, zamanta acan shine zaman lfy", Baba ya ajiye numfashi a hankali yace "a wnn marrar bazaka ɗauki nauyinka ka rataya a wuyan wani ba, ai a rayuwar nan zama inda Allah ya ajiyeka da kuma ƙarƙashin wnda Allah ya ɗaurawa nauyinka shine daidai, idan kana so ka zauna lfy da mutane to ka guji abin hannunsu. Hajar ta dawo gida yau ɗin nan", Umma tace "amma malam...", katseta yayi yace "kiyi abinda nace", a hankali tace "toh, insha Allah zata dawo", Maama ce ta bankaɗo labule da ƙarfi ba ko sallama ta antayo ɗakin, hannunta riƙe da wani kantamemen kofi da cokali, daga tsayen da take tace "malam ya kufan jiki?", ba tare da ya dubeta ba yace "alhmdllh", ta gallawa Umma harara tace "madara zan ɗiba zamu karya kumallo nida yara", Baba yace "toh ina kika ga madarar?", Maama ta geɓare baki tace "Auu malam jiya fa naga an kawo maka manya manyan gwangwanaye na madara da milo, kayan marmarin ma sai sun ruɓe ba za a kasafta ba, ya kamata a raba a bawa kowa rabonsa", Baba yace "anƙi a raba", hangame baki Maama tayi tace "toh ai shknn, toh a bamu madarar mu karya kumallo", yace "suma an hana, mai neman auren Hajara ne ya kawo, ita kuma da kike kira da shegiya toh wnn arziƙinta ne....", Maama ta gyara hular kanta da ta wani waskace gefe tace "toh shknn.." ta fita fuuu a ɗakin sai kace wata kububuwa. ɗakinta ta shiga tana hucii, Maimuna da take tsefe kitson attachment tace "Maama ina madarar?", Maama ta wurga mata ƙaton kofin hannunta a fusace tace "madarar gidanku, malama ki cire kuɗi a ƙugunki ki siya, uwar tsimilmila kawai", Maimuna ta taɓe baki ta cigaba da tsefe kitsonta, Nabilah dake haɗa kayanta masu datti da zata wanke tace "toh Maama ina kuɗin da yaya Naseer ya baki ne?, ki bayar a siyo mana ƙosai da gasara", Maama tace "baki da hankali, toh ƙosan ɗari biyar ma yayi mana kaɗan", Nabilah tace "toh wainar gero fa?", Maama tace "wllh an wulaƙanta ni, ina Sa'adatu na?", Maimuna tace "ta fita", Nabilah tace "wane ɗan abu kazan kasan ne ya wulaƙantaki Maama?", Maama ta sauke ajiyar zuciya tace "wai akan wata mushiyar madara ake min gori", Nabilah ta yamutsa fuska tace "daman ai saida nace miki kar kije amma kika biyewa Maimuna ƴar san banza, ai ga irinta nan", Maama tace "ke Maimuna wai ina Alhaj ɗin naki ne shi bazai kawowa mahaifin naki kayan dubiya ba?, ko baki gaya masa ba?", Maimuna tace "chab na gaya masa mana amma bana son yazo ruɓaɓɓen gidan nan gaskiya, da ace ma har yanxu Baban na asibiti da sai yazo, ko da yake baya nan ma ya tafi Abuja", Maama ta wangale baki tace "Allah, wato har Habuja yana zuwa?", Maimuna na taje figaggen gashinta wanda ya gama tsiyacewa tass sbd yawan saka attachment tace "uhmm ai yace idan ya aureni acan zamu zauna", Nabilah ta kwashi kayan wankinta tayi waje tana cewa "bamu gani a ƙasa ba". Maimuna ta ɗaga murya tace "oho miki dai, ƴar ciki baƙi kawai", Maama tace "muna fatan Allah ya mayar da ƙoƙo masaki". Maimuna ta miƙe ta tattara gashin attach ɗin da ta gama tsefewa tace "Ameen". Umma na fitowa ɗakin Baba ta shiga nata, wayarta ta ɗauka ta fara kiran ƴar uwarta, bayan sun gaisa Umma tace "ya yaran ya ɗawainiya?", Anty tace "alhmdllh Adda", Umma tace "Hajara ta shirya ta taho gida..", Anty tace "to sbd me Adda?", Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "wllh malam ne yace lallai lallai yau ta dawo gida, ba yadda banyi ba akan ya haƙura amma ya kasa fahimta, kuma wllh ni wani abun ma sbd shi nake, yanzu fa ba isasshiyar lfy garesa ba, idan Hajara ta dawo gidan nan sai anyi hatsaniya, ita fa ba a mata ta kyale, ga muƙarrabanta nan suma duk suna nan", Anty tace "toh shknn Adda, nida kaina zan dawo da ita, kuma zan ja mata kunne, amma dai nidae tinda tazo gidan da nake banga wata matsalar ba", Umma tace "uhmm ai hakuri ne yayi mata ƙaranci", Anty tace "ba damuwa zan mata nasiha, insha Allah da yamma zan kawota tinda mahaifinta yace ta dawo gida", Umma tace "toh sai kinzo Allah yayi albarka, a yiwa Kabiru godiya da ɗawainiya", Anty tace "laa ba komai Adda muma fa masu riƙe Hajar ne, sai anjima" ta katse kiran.
★Da misalin sha biyu da minti uku Anty na zaune palour Hajar ta fito daga ɗakinsu Hafsa ta shiga kitchen, fridge ta buɗe ta ɗauki ruwa ta sha snn ta fito, har zata koma ɗaki Anty ta kirata, dawowa tay ta zaune kan carpet tace "Anty gani", Anty ta ɗakko sababbin ƴan ɗari biyu dake gefenta ta miƙa mata tace "toh kema ga naki", Hajar ta ɗaga kai ta kalli kuɗin ta girgiza kai tace "A'a na Hafsa ne", Anty tace "ba zaki amsa ba", Hajar ta sunkuyar da kanta tace "ai Hafsa ya bawa", Anty tace "Eh naji Hafsa ya bawa, ita kuma Hafsa ta baki, ki amsa tin kafin rai na ya ɓaci", a hankali Hajar ta sa hannu ta amshi kuɗin ta ajiye kan cinyarta tana ganin aukinsu, kamar ma gida biyu aka raba su aka bata rabi, Anty ta gyara zama tana kallonta da kyau tace "Hajar", Hajar ta ɗago kai tace "Na'am", Anty tayi softening voice tace "Haƙuri shine babbar ribar zama da mutane, duk wani mai haƙuri yana tare da waraka da kuma wadata shiyasa hausawa suka ce mahaƙurci mawadaci, akwai laifin da za ai maka ka rama akwai kuma wanda za ai maka ka haƙura, ammafa wanda za kayi haƙurin ya fi riba, Hajar ki zama mai haƙuri daidai mitsali ba wai wanda zaki zauna a cutar dake ba, kinsan me yasa nace ki zama mai haƙuri", a hankali Hajar ta girgiza kai, Anty tace "yawwa, nasan kinada haƙuri daidai naki amma ina so ki ƙara akai, ɗazu mukay waya da Adda tace Babanki yace ki koma gida yau ɗin nan, toh anjima da yamma zan mayar dake, kinsan dalilin da yasa mahaifiyarki ta haƙura da zama dake ta kawo ki nan dai ko?, ki ringa jin duk abinda mahaifiyarki ta gaya miki, tin kina ƴar tatsitsiya take haƙuri da kishiyarta a haka dai rayuwa take gara mata cikin zaman doya da manja, babu abinda ya cita dan tayi haƙuri, amma ke kin ƙi haƙuri ki zauna lfy, kimin alƙawarin cewa bazaki shiga gonar ƴan uwanki ba, kuma bazaki biye musu ayi tashin hankali dake ba..", da kyar Hajar tace "toh Anty, wllh abinda suke min ne yayi yawa nida Umma...." nan ta shiga gayawa Anty irin abubuwan da siblings ɗinta suke mata. Anty ta sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya kyauta, haƙurin dai da nace shi zaki yi, ba abinda yake dawamamme wata rana sai labari, Wataqila ma ba zaki ƙara shekara ba a gidan zaki tafi naki tinda Allah ya baki manema sai dai fatan zaɓi na gari", Hajar tace "Toh Anty, nagode", Anty tace "yawwa, Allah ya yi miki albarka, tashi ki haɗa kayanki". Hajar ta kwashi kuɗin da suke kan cinyarta ta miƙe ta wuce ɗakinsu Hafsa, bata wani daɗe ba ta gama shirya