Showing 36001 words to 39000 words out of 114314 words
Chapter 13 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
zuciya mal ɗin, Nasiru me kake cewa ne?". Nabilah ta zaburo ƙasa ashe ba bacci take ba tace "Baban ne ciwon zuciya ta kamasa" ta figi hijab tayi waje da sauri, Naseer da zuciyarsa duk ba daɗi ya dubi mahaifiyar tasa yace "Abinda Baba yake buƙata addu'a snn kuma kar a ringa ɓata masa rai, duk wani abu dai da zai daki zuciyarsa toh zai iya tayar masa da cutar, kuma daman ga hawan jini, ya kamata a kiyaye Maama". kallonsa Maama ta ringa yi kafin tace "A'a Nasiru ai ba ni zaka gayawa a kiyaye ba, waɗancan gayyar shegun zaka gayawa sbd nayi imani da Allah sune suka saka masa ciwon zuciya, ba kaga duk sunfi damuwa ba sbd sunsan abinda suka aikata, tsoro suke ji kar ya mutu ta sanadinsu, tin ranar da shegiyar yarinyar nan da uwarta suka yiwa Sa'adatu ƴar albarka rubdugu toh shknn mal ya kwanta rashin lfy, to Allah dai ya kyauta ai zama da shegu ba kanta sbd tsinannu ne....", Naseer ya katseta da cewa "ni zan shirya na koma wajen aiki, zan ringa zuwa duk bayan kwana uku tinda lodin Lagos zuwa kano nake yi", Maama ta gyaɗa kai tace "toh shknn, amma kuma gidan bamu da komai, mai fita ya kawo ya kwanta rashin lfy, kasan ba abincin ne a jibge ba kullum sai an auno wanda za a sa a bakin salati, ruwan amfani ma sai mun siya", yace "ba komai insha Allah zan ringa yo aike, snn kuma ga wnn" ya karkace ya ciro kuɗi masu ɗan kauri ya miƙa mata. wuff ta amshe snn ta shiga ɓaɓɓaka masa albarka da godiya, ya shafa kansa yace "ba komai Maama" snn ya miƙe ya fita. yana fita Nabilah ta shigo, Maama ta fara ƙoƙarin ɓoye kuɗin a ƙirjinta amma sbd suna da kauri sai suka fito, Nabila ta taɓe baki tace "A'a Maama dama kin dena ɓoyewa ai na gani kuma nasan ya Naseer ne ya baki", ta cire hijab ɗin jikinta snn ta zauna a ƙasa tana fifita dashi tace "Baba na shiga na duba kuma naga jikin da sauƙi, nawa yayan namu ya bayar ne?", Maama ta ciro kuɗin ta ƙulle a haɓar zaninta tace "na gida ne, ina Maimuna tazo ta kira Sa'adatu a waya", Nabilah tace "wanka take", Maama tace "wanka?, amma dai ba fita za tayi ba ko?", Nabilah tace "can ta matse mata, ni bansani ba". Bayan minti goma Maimuna ta shigo ɗakin da ɗaurin ƙirji, ta ajiye kwandon soso da sabulu akan window, wardrobe ta buɗe ta ɗakko kaya da jakar kayan kwalliya ta zauna ta fara shafa mai, tana gama shiryawa tass cikin wasu matsattsun kaya wanda rabin ƙirjinta a waje yake ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka. Maama tace "Amma dai ba fita za kiyi ba dai ko?", Maimuna ta dakata da ɗaukar wayarta dake gefen gado tace "bangane ba, nafa gaya miki tin jiya", Maama tace "ehh kin gayamin amma yanzu kinga an sallamo babanku, kin manta dokar da ya kafa muku ne, toh babu inda zaki kuma ki kira Sa'adatu ta dawo.." tana gama faɗin haka ta miƙe ta fita tana cewa "ja'ira idan ma kin samo kuɗin ba alheri kike ba".
★Bayan sallar azahar Hajar ta shiga ɗakin Anty sbd kiranta da take, sallama tayi a hankali, Anty ta amsa mata snn ta shiga ɗakin. Hajar ta nemi guri zata zauna a kan carpet Anty ta nuni mata gefen gado tace "zauna anan", ba musu ta zauna a wajen da ta nuna mata, Anty ta ƙarasa abinda take jikin press ta zauna kan stool tana kallonta tace "kin cire kayanki daga Ghana most go dai ko?", Hajar tace "Eh Hafsa ta saka min a wardrobe", Anty ta gyaɗa kai tace "Okay, idan kina buƙatar wani abun saiki gaya min", Hajar tace "toh", Anty ta kalli fatar ƙafarta da dogon wuyanta tace "wane cream kike using?", Hajar tayi murmushi tace "duk wanda ya sawwaƙa ko petroleum jelly ko mai gurguwa ko kuma Habiba", Anty tace "Okay, kinci abinci?", Hajar ta girgiza kai tace "sai su Hafsa sun dawo", Anty ta kalli agogon da yake maƙale da bango tace "yanzu ma zaki gansu, ita Hafsan ce tace ki ringa jiranta?", Hajar ta girgiza kai tace "A'a Anty", Anty tace "toh shknn, je ki soyamin kajin dana sulala ɗazu", Hajar tace "tom" ta miƙe ta fita Anty ta bita da kallo. Anty dai tinda Hajar tazo gidan bata taɓa ganin wani aibunta ba or something bad akanta, kwata kwata ba ta da wata matsala, gata da tsafta kamar me, kafin ma ta tashi da safe ta gama gyara gidan tass, amma kuma ƴar uwarta na complain da ita. wai bata da haƙuri to gsky in rashin haƙurin ne ga dukkan alamu sai an taɓota. Hajar na fita ɗakin ta wuce kitchen ta ɗauki frying pan ta tuttuli vegetable oil ta ɗora akan gas, bayan oil ɗin yayi zafi ta fara soya naman. tana gama soyawa ta fita kitchen ɗin ta gayawa Anty snn ta wuce ɗakinsu Hafsa. wayarta ta ɗauka ta shiga kiran umma, Umma na ɗauka Hajar ta gaisheta tace "ya jikin Baba?", Umma tace "da sauƙi, mun dawo gida", Hajar tace "Allah ya ƙara afuwa", Umma tace "Ameen", Hajar tayi gathering courage tace "Umma yaushe to zan dawo gida?", Umma tace "wani abun ake miki anan ɗin ne?", Hajar ta girgiza kai tace "ni ba abinda ake min, nafi son gida wllh, dan Allah umma kiyi haƙuri", Umma tace "laifin me kika min da kike bani haƙuri, gwara ma ki saba da zama anan sbd gsky bazaki dawo gida yanzu ba", hawaye ya ciko idanun Hajar tace "dan Allah Ummana", Umma ta sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya tace "kiyi haƙuri kinji, sai anjima", ta katse kiran. Hajar ta ringa kallon screen ɗin wayar tace "na shiga ukuna". palour ta fita ta zauna, tana zama Anty ta fito daga room ɗinta ta shiga kitchen ta fito da plate din abinci da soyayyen naman kaza a kai ta zauna a palourn tana ci, Anty tace "kee tashi ki zuba abinci ki ci ba wani sai Hafsa ta dawo", Hajar tace "Allah Anty bana jin yunwa", Anty ta cigaba da cin abinta bata sake cewa komai ba, few minutes kam saiga su Hafsa nan sun dawo. Bayan Hajar da Hafsa sun gama cin abinci Anty ta kalli Hafsa dake gyara wajen da suka ɓata tace "da yamma zan aike ku supermarket, idan kin kai plate din kitchen sai ki kawomin jotter da biro nayi list din abinda zaku siyo", Hafsa tace "toh" ta shiga kitchen. tana fitowa ta wuce ɗakinsu ta ɗakko jottern da pen ta kaiwa Anty. Bayan Sallahr la'asar rana tayi sanyi Hafsa da Hajar suka shirya zuwa supermarket. dukkansu dogon hijab suka saka. a tare suka fito palour, Anty dake palourn tace "yawwa karku kai magrib and go to the nearest", Hafsa tace "tom" ta amshi list ɗin da kuma Atm card ɗin da Anty take miƙa mata. Hajar tace "sai mun dawo". suka fita Anty na jadda musu cewa kar su kai magrib. suna fita road kam suka samu Napep, Hafsa tace "wellcare", mai Napep yace "Haɗeja Road?", Hafsa tace "Eh". ya faɗa musu bill. Hafsa ta shiga snn Hajar. saida suka hau saman titi snn Hajar tace "Anty fa tace muje na kusa shine zamu tafi Haɗeja Road". Hafsa tace "kinga supermarket ɗin da suke kusa ba komai ake samu a nan ba, kinga gwara muje wanda zamu samu komai mu dawo da wuri". Hajar dai ta gyaɗa kai ba tace komai ba. 20minutes of a ride suka isa supermarket ɗin. bayan sun sauka daga Napep ɗin Hafsa ta basa kuɗinsa snn suka nufi entrance. suna shiga ciki Hafsa ta ɗauki shopping basket ta miƙawa Hajar. ta ciro list ɗin ta fara ɗaukan abinda ke rubuce tana sakawa a basket ɗin hannun Hajar. bayan Hafsa ta gama ɗaukan komai dake rubuce a list ɗin tace "yawwa, saura man ki", Hajar tace "mai na kuma?", Hafsa tace "yess Anty tace a siya miki mai da turare, na ɗaukar miki turaren man ne dai bansan wanda zai miki ba", Hajar tace "ɗaukar min mai gurguwa", Hafsa tace "wane irin mai gurguwa?, bari na ɗaukar miki irin wanda nake shafawa", Hajar tace "A'a nifa man nan naki be min ba sai kace ka shafa ruwa gashi kuma kayi ta gumi kamar kuturu", Hafsa tayi murmushi tace "toh shknn bari na duba miki wani amma banda mai gurguwa", Hafsa ta juya wajen creams ɗin, a tsanake take dubawa cause Hajar is fair in complexion, haskenta irin me pink ɗin nan ne bata so ta ɗaukar mata wanda zai ɓata mata complexion. Tinda suka shigo harabar supermarket ɗin yake kallonta ta cikin tinted glass ɗin motarsa dake parking space, da sauri ya buɗe motar ya fito yabi bayansu, wani yadi ne ajikinsa sky blue mai mugun kyau, kai kana ganinsa kasan kuɗi sunyi kuka, tinda ya shiga wajen shopping ɗin yake nemansu sbd sun ɓace masa. ya ƙanƙance ido yana tuna fuskarta da ya taɓa gani sau ɗaya. tabbas itace. Hafsa ta ɗauki wani cream mai kyau ta saka a basket tace "yawwa mun gama mu tafi". Hajar na juyawa shi kuma ya iso wajen. kallon aisle ɗin da suke yayi. kallonta ya ringa yi ba ƙiftawa. a hankali Hajar da Hafsa suka fito daga aisle ɗin suka nufi counter. suna zuwa aka lissafa kayan aka zuba a ledoji biyu. Hafsa ta ciro card ta miƙawa cashiern wajen. cashier tace "ai ya biya kuɗin" ta faɗa tana miƙawa wani gentleman dake gefensu card ɗinsa......✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{ 20..}
Idonsa akan Hajar ya karɓi card ɗin ya zura a aljihun gaban rigarsa yace "thanks", Hafsa ta kalli cashier tace "an biya kuma, waye ya biya?", cashier ta nuna mutumin da har lokacin yake tsaye a wajen tace "sir", a tare Hafsa da Hajar suka juyo suna dubansa, ido huɗu sukay da Hajar, Hafsah tace "but why?", baice komai ba ya ɗauki ledojin guda biyu yace "plxx let's talk outside" da haka ya nufi exit way. Hafsa ta dubi mutanen dake bayansu suna jiran su basu space suma a irga musu kayansu. hannun Hajar ta riƙe suka fita harabar supermarket ɗin. adaidai exist door ɗin suka gansa, Hafsa tace "bawan Allah bamu ledojin kayanmu", wani soft smile wanda ya sake feso da kyansa yayi yace "tom, gashi" ya miƙa mata ledojin. kin karɓa tayi ta miƙa masa Atm card tace "muje POS ka cire kuɗin ka", yace "No ba kyau mayar da hannun kyauta", Hafsa tace "toh sbd me zaka biya mana kuɗin shopping ba tare da sanin mu ba?", yace "plxx accept it, yanzu ai kun sani", Hafsa tace "malam kana ɓata mana lokaci, dan Allah ka bani account No ɗinka na dawo maka da kuɗin ka". murmushi yayi yace "A'a", Hajar da take jin duk abinda suke cewa ta yamutsa fuska tace "kinga bar masa kayan sai mu koma ciki mu ɗauki wasu" da haka ta riƙo hannun Hafsa suka nufi entrance, da sauri ya biyosu a baya with cool voice yace "Hajar". dakatawa Hajar tayi da tafiya a lokaci guda ta saki hannun Hafsa snn ta juyo ta zuba masa lulu eyes ɗinta. ya ciro ƴar ubansun wayarsa daga pocket ya danna kira. ƙarar waya ya fara fitowa daga jakar dake hannun Hafsa. Hafsa ta kalli Hajar snn ta ciro wayar ta miƙa mata. Hajar ta ringa kallon numbern dake kiranta wacca ɗazu da safe aka kirata da ita. a hankali ya katse kiran ya shafa kansa yana kallon fuskar Hajar yace "am Ahmad...", Hafsa ta kalli Hajar cike da mamaki tace "au daman kin san sa?", Hajar na kallon cikin idonsa tace "not at all, yanxu ma na fara ganinsa a rayuwa", jin zazzaƙar muryarta tayi beating eardrum ɗinsa ya lumshe ido, a zuciyarsa yace woww beautiful and tasty. Hajar ta juya ta cigaba da tafiya while her heart is palpitating rapidly. Hafsa ta juya zata bita, ya dakatar da ita da faɗin "alright muje a biya kudin kar na wahalar da ku, amma sure they will be next time". Hafsa ta dakatar da Hajar da take gaf da shiga wajen shopping ɗin tace "jirani anan bari ayi refunding kuɗinsa". Hajar ba tace komai ba ta cake a wajen ba tare da tayi kuskuren kallon inda take jin arwa akanta ba, tare dashi Hafsa ta koma ciki akai masa refunding kuɗinsa, ta amshi ledojin hannunsa tace "nagode". yace "is she your sister?", tace "sure, she's my maternal cousin", ya shafa kansa yace "ohk, amma dai ba baiko akanta ko?", Hafsa tayi shiru tana kallonsa kafin ta gyaɗa masa kai ta juya ta fita. bayanta yabi da kallo kafin shima ya fita, Hajar ta karɓi leda ɗaya a hannun Hafsa snn suka fita daga harabar supermarket ɗin. suna fita kam suka samu napep suka shiga. Ahmad ya shiga motarsa yana sauke ajiyar zuciya kafin ya zura key a ignition ya kunnata, bayan adaidaitan da ya ɗaukesu ya ringa bi har suka je inda zasu. a gaban idonsa suka sauka daga Napep, Hafsa ta biya kuɗin napep snn suka shiga gida. wani murmushi yayi ya daki steering motar snn ya lailayasa gami da juya kan motar. ya gammace ya haƙura da appointment ɗinsa da yayi loosing wnn babban opportunityn, he won't let go of this hot cake again. su Hajar suna shiga gida aka kira sallar magrib, Anty da take kitchen tana kwashe tuwo ta fito tace "saida dai ku kai magrib ko?", Hajar tace "abin hawa ne suke wahala Anty?", Hafsa ta ƙarasa cikin palour ta ajiye ledar hannunta. Hajar ma ta ajiye ledar hannunta snn ta shige ɗaki domin yin alwala. tana fitowa daga toilet ta shimfiɗa darduma ta kabbara sallah, Hafsa ce ta shigo itama ta shiga toilet tayo alwala ta fito. a gefen gado ta zauna tana kallon Hajar har ta idar da sallah. Hafsa tace "kin sansa ko?", Hajar ta cigaba da azkar ɗinta bata tanka ta ba, Hafsa tace "gashi nan yanada numbern ki". Hajar ta shafa addu'ar da ta gama snn ta kalli Hafsa tace "yaushe kika zama journalist ne?", Hafsa tace "dan Allah ki bani amsa". Hajar tace "alright, Eh na sansa amma ban taɓa ganinsa ba sai yau, Zainab ce ta bashi numbern ta, ɗazu da safe ya kirani ni kuma na saita masa hanya sbd nasan bazai taɓa samun abinda yake so daga gareni ba", Hafsa ta gyara zama tace "toh sbd me?", Hajar tace "inada wanda nake so", Hafsa tayi tsaki tace "au sbd kinada wanda kike so shine kike ƙoƙarin rejecting dinsa, wllh kinada matsala Hajar, ai ni dai a shawarce ba a riƙon saurayi ɗaya sbd may be ba shine zai zama mijinka ba, kuma suma samarin ba sa zama da girlfriend ɗaya wllh", Hajar ta miƙe daga kan dardumar tace "i won't double date gsky", Hafsa ta buɗe baki za tay magana Hajar ta katseta da faɗin "ki tsaya zance lokacin sallah ya wuce ki". da misalin karfe tara da ƴar mintina na dare kowa na gidan na zaune a palour, wayar Hajar ta fara ringing. ignoring call ɗin ta ringa yi sbd ta sha Ahmad ne, Anty tace "wai wayar waye wnn?", sai a lokacin Hajar ta kalli wayarta ta, ganin mai kiran yasa tayi saurin ɗaukar wayar a hannunta amma kuma ba tay picking ba. kiran na yankewa ta miƙe daga palourn ta nufi ɗakinsu Hafsa, Anty da Hafsa suka bi bayanta da kallo. Hafsa ta kalli Abdallah da yake jujjuya abincin gabansa, wato yau maƙiyinsa akai wato tuwo, ga Anty ta hana a dafa wata indomie, a hankali Hafsa ta fara dariya, Abdallah ya juyo ya kalleta ya haɗe jira yace "kee, meye haka?", ai kam ta sake tuntsurewa da dariya tace "ba komai yaya gani nai miyar taji busasshen kifi", tsaki yayi snn ya miƙe ya ɗauki kwanon abincin da bai ci ba ya wuce kitchen, Anty tace "ina zaka da abinci Abdallah?", yace "na ƙoshi", Anty ta ɗaga kafaɗa tace "shknn, wllh ka fiya tsirfa, naga da kana cin tuwon ai, Hafsa dafa masa indomien, sai yayi ta tsaho kamar wani zalɓe tinda haka ya zaɓa, amma mutum zai kwanta ba zai ci abu mai nauyi ba sai wata shegiyar indomie", Hafsa tace "tom" ta tashi ta nufi hanyar kitchen, tana zuwa kusa da Abdallah ta rage murya tace "ka turo 2GB ko nai maka mai uban yaji kuma na dafe ta", harara ya galla mata ya miƙa mata plate ɗin tuwon yace "ƙarasa dashi, zan turo miki 500MB in yayi miki, idan kuma bakya so shknn", Hafsa tace "Eh, turo amma zan gumbuɗa yaji" ta shige kitchen. Hajar na shiga ɗaki da sauri ta amsa kiran Nura da ya sake shigowa. tace "Assalamu alaikum" fuskarta ƙunshe da murmushi, yace "wa'alaykissam salam gimbiyata", tayi murmushi tace "ina yini", yace "lfy alhmdllh, ykk?", tayi twinking lulu eyes ɗinta gami da sukuwa kan gado tana rungume pillow a ƙirjinta tace "ina lfy alhmdllh, kaima ykk, ya aiki?", yace "alhmdllh, mun gode Allah", shiru tay bata ce komai ba, yace "ya jikin Baba?", tace "da sauƙi", yace "to masha Allah, Allah ya ƙara afuwa, insha Allah gobe zan shigo na dubasa", tace "tom, Allah ya kaimu goben", yace "Ameen, snn bayan isha'i kema zanzo", tace "ai yanzu bana gida", yace "kamarya bakya gida?, to ina kika je?", tace "ina gidan Anty Jamilah zan zaune a wajenta for the mean time", yace "okay, dole kam na biyo ki nan". tayi murmushi ba tace komai ba.
★Sa'adatu ce rakuɓe a soro ta ɓuya a bayan ƙofa, a hankali ta cire takalmanta ta rungumesu a ƙirji ta leƙa cikin gida, zaro ido tay waje ganin Huzaifa a bakin tukwanen ruwa yana ɗiba, ƙirji ta dafe tace "na shiga duba daman ya Naseer bai tafi ba", ta sake leƙawa sukay ido huɗu, Huzaifa yace "waye a nan?", wani relief taji da ta fahimci ba dodonta bane, tayi sauri ta ajiye takalmanta snn ta saka ta shiga ciki, karo suka kusa yi da shi. ya kalleta sama da ƙasa yace "ke daga