Showing 90001 words to 93000 words out of 114314 words
Chapter 31 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
sbd bana so ranta ya ɓaci, amma yanxu mu ɗora daga inda muka tsaya Uthman, ka amince zaka zauna da yarinyar ko kuma kana kan bakarka na sakinta...?", Nurain ya ɗago kansa yana kallon Abba ya kasa cewa komai, ya shafa kansa har yanzu baice komai ba, Abba ya ƙura masa ido yana jiran amsa, Nurain ya kalli fuskar Abba kafin ya runtse idonsa ya buɗesu, a lokaci ƙanƙani suka rune, da kyar ya motsa peach lips dinsa maganar ma bata fita sosai yace "Abba na amince zan zauna da ita..", Abba yayi ajiyar zuciya yace "Allah yayi maka albarka, zaka iya aurar wacca kake so a ko wani lokaci, zaka girbi iri mai kyau for your obedient", Nurain dai ya dena fahimta sakamako tsittsinkewar da zuciyarsa take, Abba yace "toh yaushe zaka ɗauki matarka ku koma gida...?", Nurain da throat dinsa ya bushe yace "i think on Saturday insha Allah...", Abba yace "jibi knn?", Nurain yace "Yeah", Abba ya gyaɗa kai ya cigaba da sipping tea, Nurain ya miƙe yana jan farar T-shirt dake jikinsa yace "can i excuse myself", Abba yace "sure", Nurain ya masa saida safe ya nufi ƙofa, room slippers dinsa ya zura zai fita Abba yace "gobe in Allah ya kaimu zamu fita bayan sallar Juma'a", Nurain yace "Ohk" da haka ya buɗe ƙofar ya fita Abba ya bisa da kallo, Mami ta fito daga bedroom din Abba ta zauna side dinsa ta dafa hannunsa tace "hakan ai yafi gwara musan road din da zamu bi kafin abu ya tabarbare...", yace "haka ne, All thanks to you Mami".
★Washe gari da ta kasance juma'a, ƙarfe sha biyu Nurain ya fito huge compound din gidansu ya isa parking spaces, ya buɗe motarsa da ya fita da ita jiya da yamma ya shiga, wayarsa dake kan dashboard ya ƙurawa ido, gaba ɗaya ya dena amfani da ita saidai yayi using Mac phone, haka yake baya son takura, ya kwantar da hand brake ya tada motar, after warming for few minutes yaja motar ya fita daga gidan, tunani iri iri ke kawowa brain dinsa amma sai ya kawar dasu ta hanyar bin karatun Alkur'ani dake tashi a motar, wayarsa ce ta fara ringing, da kamar bazai ɗauka ba sai kuma yabi gefen titi ya ɗauki wayar ya duba wake kiransa, Farooq ne, Nurain ya saka wayar a handsfree ya cigaba da driving slowly, complain Farooq ya fara masa akan baya ɗaga wayarsa, Nurain yace "Hey punk nafa gaya maka ka dena kira idan zaka ajiye mail da yafi maka", Farooq yace "i won't, kira naga dama", Nurain ya ɗaga kafaɗa yace "Alright..", Farooq yace "ni idan ba ma iron lady da ta takura na kiraka ba me zaisa na kira unavailable person", Nurain yayi murmushi yace "kai har kayi mgana anan punk..", Farooq yace "are you coming daman iron lady ce take son ganinka..?", a hankali Nurain yace "yeah, idan na dawo daga mosque zan shigo", Farooq yace "fine" da hka ya katse wayarsa, saida Nurain yaje masallacin da ya saba zuwa sallar Juma'a snn ya wuce gidansu Farooq, suka gaisa da Ummi kafin ya wuce part din Hajiya, bai jima da zama ba saiga drink da ruwa Aysha ta shigo masa dasu harda abinci, Aysha ta tashi zata fita Hajiya tace "tin ɗazu nake fama dake Shatu akan ki shafamin man zafi a saman makyangyama amma kinyi burus dani, jifa yadda ƙafafuwan suka sussuntuma sai kace an buga musu iska, da kyar na iya yin sallah fa", Aysha tayi fuskar mage tace "iron lady, ina zuwa yanzu zan dawo, kinga abinci nake kawowa yaya ai bai kamata na taɓa man zafi ba", Hajiya ta ɗaga kai sama tana kallon Nurain ta ƙasan glasses tace "ke da Allah rabu dashi kizo ki shafamin mai na, yo ina ruwanki dashi shi da yake da aure, zukumin cikinsa na wajen matarsa, kai matar Usuman yar aljanna ce yarinyar nan, wllh ta iya shafa man zafi, tinda nake ba a taɓa shafamin wanda naji daɗinsa kamar nata ba, ni idan ma naga ina ƙoƙarin rasa ƙafafuwan babu abinda zai hanani tarewa gidan Usuman..", Nurain dai kawai latsa wayarsa yake like he was not existed there, sai a lokacin yace "toh taso mu tafi", Hajiya tace "mu tafi ina kuma, ai cewa nayi sai naga ina ƙoƙarin rasa ƙafafuwan...", Nurain ya miƙe tsaye yana kallon hajiya yace "na tafi, idan Farooq ya dawo masallaci kuce masa na tafi", Aysha tace "Yaya what about the food", ko amsa bai bata ba ya nufi door, Hajiya kam kasa magana tai sbd abinda ma ta kirasa ta gaya masa bata kai ga fada ba, da sauri Nurain ya shiga motarsa ya bar gidan, shaf ya manta cewa Abba yace zasu fita yau, hold off ne ya riƙesa a wani round about, almost 20mins hold off din bai ware ba, Nurain ya daki steering motar murya ƙasan throat yace "damn it", kiran Abba ne ya shigo wayarsa, yayi picking, Abba ya tambayesa whereabouts dinsa, yace hold off ne ya tsaresa bayan ya fito daga masallaci, Abba yace "Okay, ni na riga na wuca ma amma zan turo maka inda zaka sameni sai ka tafi can din", Nurain yace "Aha". Nurain ya buɗe google map a wayarsa yana bin direction din da zai kaisa unguwar da Abba ke jiransa bayan ya samu ya fito daga hold off din, ya ringa kallon screen ɗin wayar ganin inda arrorn map din ke masa pointing, ya ɗago kansa yana kallon street din a zahiri wanda ya karya kwanarsa yanxu, street din ba baƙonsa bane kuma zamm ya ganesa tinda ya ajiye memory a nan din, Slowly yake driving a street din sbd ruɓewar kwalta da kuma shagiɗaɗɗun jakin baban gida, opposite inda Incidence din memoryn sa ya faru yaga motar Abba, drivern Abba ya fito yana ɗaga masa hannu, Nurain ya samu gefe yayi parking motar ya buɗe ya fito, koda ya fito sai ya tsaya yana kallon daidai wajen da motarsa ta taɓa ruftawa, anan ne kuma first encounter dinsa da mara kunyar yarinyar nan wacca a yanxu ta amsa sunan matarsa.....✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{42..}
Tsallaka titin Nurain yayi ya isa wajen Motar Abba, driver ya buɗewa Abba motar ya fito, Abba ya ringa kallon Nurain da ya ƙurawa street din ido yace "wajen mahaifin Hajar na kawoka ka gaishesa, ya kamata ya sanka..", Nurain ya kare hasken rana da yake haske masa ido yana tunanin wace ce kuma Hajar, sunan ya ringa yawo a brain dinsa amma ya kasa gane wace, ganin bai fahimta ba Abba yace "your wife, ko baka san sunanta ba..?", Calmly Nurain yace "Ohk, amm nan ne unguwar...?", Abba yace "yess, ga layin gidan can" ya nuna kwarɓaɓɓen lungun gidansu Hajar, with disgusting look Nurain ya kalli layin, how mutane suka rayuwa a nan wajen, Abba ya ciro wayarsa daga pocket yayi making call na minti biyu, yana gama wayar yace "muje" da haka ya fara tafiya ya shiga layin, Nurain yabi bayansa, Nurain dai kawai bin Abba yake suna surƙumawa cikin lungun, wani irin nisa yaga tafiyar ta masa duk da cewa gidan bashi da nisa da titi, Abba ya tsaya a daidai ƙofar gidan, Baba da already yana soro ya fito waje sukay musabaha da Abba, Baba yace "Bismillah", Abba ya bisa suka shiga soron gidan ya zauna kan tabarma da ke shimfiɗe a soron, saida Nurain ya rage tsaho snn ya shiga, ya zauna daga gefe yana kallon Baba yace "barka da rana", da fara'a Baba ya amsa, Abba yayi murmushi yace "he is my second born Uthman, dashi aka ɗaura auren...", Baba yayi ajiyar zuciya yana kallon Nurain yace "masha Allah..", Nurain ya ɗaga kansa yana kallon roof din soron wanda spider web ta cikasa har tana zazzagowa, Abba da Baba sai taɗinsu suke, past dinsu suke tunawa suna mgana akai, after 5mins Nurain ya duba agogon wrist dinsa, Abba ya dubesa ta gefen ido kafin yace "Nurain you can go idan Kanada wani appointment din", cike da girmamawa Nurain ya yiwa Baba sallama kafin ya tashi ya bar soron, Nurain na fita daga lungun ya ciro handkerchief ya goge fuskarsa, titi ya tsallaka ya shiga motarsa, zaune yayi cikin motar bayan ya kunna ya ware Ac, So a nan Abba ya masa aure, Ghetto area, shi ba wnn ne damuwarsa ba ma, bayan ƴar Ghetto da aka aura masa kuma mara manners, da reverse ya fita daga street din, yana hawa main road ya take accelerator, hanyar gidansa ya ɗiba, few minutes ya isa unguwar duk da cewa akwai nisa cause ya take motar ba ƙarya, a ƙofar gida yayi parking ya fito, Garba dake tsaye bakin gate tare da wani mutumi ya taso yana yiwa Nurain barka da zuwa, Nurain ya amsa yana kallon mutumin dake tare da Garba, Garba ya dubi mutumin yace "ga uban gidan nawa fa..", da sauri mutumin ya russuna yace "barka da zuwa Alhj..", Nurain yace "an yini lfy...?", mutumin yace "lfy alhmdllh an gode Allah...", Nurain na kallon Garba yace "shine ko?", Garba ya shafa kai yana ɗan russunawa yace "Eh alhj ƙarami, shine wllh, ɗan uwa na ne na jini, da Babansa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya..", Nurain ya jinjina kai yace "Ohk, hakan yayi" da haka ya ƙarasa bakin gate din ya buɗe, ya koma cikin motar Garba ya zuge masa gate ya shigar da ita huge parking space dake gidan nasa, saida Garba ya bari mutumin da suke tare ya shigo snn ya mayar da gate din ya rufe, Nurain ya fito daga mota bayan ya gama parking, ya ringa kallon compound din, kiran Garba yayi wanda ya taho da sauri, Nurain yace "ka gaya masa aikinsa ko?", Garba yace "Eh na gaya masa komai, gadi da bar ruwan shuka sai share tsakar gida", Nurain yace "Yawwa, kira min shi", Garba ya tafi ya kira mutumin suka taho tare, Nurain yace "Garba ya maka bayani ai", mutumin kansa a ƙasa yace "Eh alhj..", Nurain yace "yawwa, bar ruwan shuka da share tsakar gida na wani lokacin ne kafin a samu me yi naka dai shine gadi", mutumin yace "insha Allah komai bazai gagara ba..", Nurain ya gyaɗa kai yace "suna fa..?", mutumin yace "Inuwa..", Nurain ya jinjina kai kafin ya wuce ya bar wajen ya nufi main entrance din shiga gidan. Garba ya dashe haƙora yace "Allah kuwa Inuwa ka kwashi dami a akala don wllh tllh kirki dai a wajen bawan Allahn nan har ya masa yawa, ni dai na gaya maka ka zama mai gsky da amana, idan ka riƙesa da kyau tabbas zaka samu alkhairy bana wasa ba, wllh don ma dai kai ne amma in ba haka ba wani huhulahun zan nemawa wnn gangariyar aiki...", Inuwa yayi murmushi har cikin ransa yaji daɗi yace "ai Allah ne zai biyaka Garbati da wnn taimako da ka min", Garba yace "wnn fa aikin nawa ne na sadaukar maka..", Inuwa yace "ai shiyasa nake ta gode maka...", bayan minti sha biyu Nurain ya fito bayan ya rufe ko ina, keys guda biyu ya bawa Inuwa yace "key din ɗakinka ne da kuma gate, gobe da safe saika zo kayi abinda za kai ka buɗe ɗakinka, amma yau dai ka tsaya tare da Garba", hannu biyu Inuwa yasa ya amshi keys din, Garba ne ya masa nuni da ɗakin nasa wanda ke kusa da gate, Nurain ya ciro kuɗi daga pocket ya bawa Garba yace "saiku koma can gidan..", godiya Garba yayi masa sosai. sai bayan Sallahr la'asar wajen ƙarfe biyar snn Nurain ya koma gida, don sai yau ne ya samu yaje wuraren da yake son zuwa tin dawowarsa 9ja.
★Hajar ta saka Hijab dinta tabi bayan Noor data isar mata da saƙon kiran da Mami ke mata, Mami na zaune palourn ta tare da Tailor wacca ta saba musu ɗinki, Noor ta koma inda ta tashi ta cigaba da latsa wayarta, Hajar ta zauna kan carpet tace "gani", Mami ta dubi Tailorn tace "ga mai kayan nan", Tailorn tace "Okay tom bari na aunata..", bai ɗauketa wani lokaci ba ta gama auna Hajar tass, Mami tace "gobe fa nake son kayan nan Salmah", Salmah tayi murmushi tace "Mami kar kiji komai insha Allah gobe sha biyu na rana a gidan nan zata yiwa kayan nan..", Mami tace "toh Allah yasa", Salmah ta yafa mayafin Abayarta, ta ɗauki wata Babban leda dake kusa da ita tace "toh Mami na wuce, Noor sai anjima..", Noor ta ɗago kanta daga kallon waya tace "da wuri haka...", Salmah tace "gwara na tafi yanzu na fara aiki, bana so naƙi cikawa Mami alƙawari", Mami tace "dan kwa faɗa zanyi wllh idan kayan nan basu samu gobe da wuri ba", Salmah tace "insha Allah baza aji kanmu ba Mami.." da haka ta musu sallama ta tafi, Hajar bata koma ɗaki ba tayi zamanta anan, buɗe ƙofa akay Nurain ya shigo, hannunsa riƙe da handle ya ƙarewa ɗakin kallo, har yayi wanka ya canza kayan jikinsa daga manya zuwa ƙanana da yke zaman gida dasu, wani irin zaro ido Noor tayi ganinsa unexpected, da sauri ta kara wayarta a kunne ta fara wayar ƙarya, ta tashi zata shige bedroom din Mami, ƙarasa shigowa palourn yayi yace "idan kika shiga har nan zan biyoki na zaneki", Noor ta yarfe hannunta tace "yaya ka tsaya kaji don Allah...", yatsansa ya ɗora a lips yace "shhhh na tambayeki ne...?" ya samu Sofa ya zauna, yana zama Hajar ta miƙe ta nufi hayar ɗakin da take, Mami ta kirata tace "ina zaki...?", Hajar ta juyo a hankali tace "ciki zan koma..", Mami tace "dawo ki zauna nifa na kiraki kuma bance ki tafi ba..", ba yadda Hajar ta iya haka ta dawo ta zauna, koda wasa bata dubi position din da Nurain yake ba, shima tinda ya kalli inda tke sau ɗaya bai sake kallon wajen ba, Nurain ya dubi Noor da tay tsaye sai wurwurga idanu take, murya ƙasan maƙoshi yace "je ki kawomin abinci, surely we will meet later..", a ɗarare Noor tace "tom", har ta kai bakin ƙofa Mami ta kirata, ta dawo da baya tana kallon Mami, Mami tace "je ki kunna burners ki zuba turaren wuta..", Noor ta dubi Nurain kafin tace "tom" ta dawo ta shiga bedroom din Mami, Mami ta kalli Hajar da ta zubawa Tv ido, kawai Tv take kallo duk da ba wani abun arziƙi ake haskawa ba amma ta gwammace ta kalli Tv sbd kar idonta yaje inda zuciyarta zata sosu, Mami tace "Hajar..", Hajar ta kalli Mami tace "Na'am", Mami tace "tashi kije kitchen za kiga wasu silver warmers guda uku akan cabinet ki ɗakko min su, idan kin kawo sai ki koma ki ɗakko min ruwa da drink a fridge", Hajar tace "tom" ta tashi ta fita daga palourn, Nurain yayi kamar baiji me Mami ta faɗa ba ya fara duba Mac phone, Mami dake kallonsa tace "misplacing phone dinka kayi ne..?", yace "A'a, a ɗaki na barta", Mami tace "alright then", Hajar ta shigo da tray a hannunta mai ɗauke da warmers, ta ajiye nan kan carpet kafin ta juya ta sake fita, babu jiwa ta dawo da wani tray din na ruwa da lemo da Cup da kuma plate with spoon, ta ajiye kusa da warmers din, a hankali tace "zan koma ciki", ba ta bari ta kalli Mami ba ta faɗi hakan, Mami tace "toh", Hajar ta tafi a hankali tana zuwa ƙofar ɗakin ta buɗe ta shige da sauri har dasu tuntuɓe, jingina tay da jikin ƙofar ta lumshe idanunta. Ganin har wajen minti talatin da ajiye masa abincin amma bai taɓa ba yasa Mami tace "Nurain ba Abincin zaka ci ba kasa aka kawo maka..?", ya ajiye Mac phone din a gefensa yace "A'a ni ba ci zanyi ba, i thought ke zaki ci ma", da mamaki Mami ta ringa kallonsa, after looking at him for few seconds tace "zuba abinci kaci malam", ya shafa kansa yace "nifa am full bance zanci ba", Mami ta haɗe gira tace "nace ka zuba abinci", bai sake mata musu ba ya ɗebi abincin kaɗan wanda bai wuce loma biyar ba, duk da irin yunwar da yake ji amma samm yaji baya sha'awar abincin, gaba ɗaya ya fitar masa a raii, ya ringa juya spoon ɗin hannunsa, Mami dai ta ringa kallonsa ta gefen ido har ya gama caccakar abincin wanda ko kusa da baki be kai ba ya ajiye, ruwa da lemon ma bai sha ba haka ya tashi ya fita, Mami ta bisa da kallo, girgiza kai tayi a ranta tana addu'ar Allah yasa dai wnn abu mai ɗorewa ne kar ya zama fitina. washe gari wani irin odd Hajar ta ringa jin kanta, tinda aka kawota gidan yau ne ta wayi gari taji hakan, ita ba mai rashin lfy ba kuma bazata kira kanta da mai lfy kai tsaye ba, breakfast da aka kawo mata ma kaɗan taci, Noor ma saida ta tambayeta lafiyar ta kuwa sbd sauyin nata, Hajar tace "bacci ne bai isheni ba inajin", Noor tace "toh ki koma ki kwanta kawai..", Kwanciyar da Hajar tayi sam bata samu bacci ko na 1sec ba, kawai juye juye ta ringa yi sai kace ƙadondoniya, wajen ɗaya saura ta tashi ta shiga bathroom ta ɗora alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya, kamar wasa sai bacci ya ɗauketa, ba ita ta farka ba sai daf da sallahr la'asar, Noor ce ta shigo ganin ta farka ta fita a ɗakin, babu jimawa sai gata ta dawo tare da Mami, Noor ta ajiye kayan da suke hannunta a gefen bed kafin ta juya ta fita, Mami tace "har kin tashi dear..?", Hajar ta gyaɗa, Mami tace "Sallah za kiyi ne..", Hajar tace "Eh", Mami tace "idan kinyi Sallahr sai kiyi wanka ki saka waɗan nan kayan kinji", Hajar tayi shiru tana kallon kayan dake gefen gado kafin ta gyaɗa kai tace "tom", saida tayi sallah taci Lunch da Noor ta kawo mata snn ta shiga wanka kamar yadda Mami tace tayi, ta fito ɗaure da towel ta zumbula hijab,