Showing 60001 words to 63000 words out of 114314 words

Chapter 21 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

zan bada fuska ya zane muku jiki, kai wllh har ziga mal zan ringa yi dan jikinku ya gaya muku, ni zaku mayar yarinya kucemin wai baku da kuɗi..", Sa'adatu tace "to ki faɗa mana ai nace miki banda su...", Maama tace "haka kika ce ko?", Maimuna tace "Maama ai gaskiyar knn", gyaɗa kai Maama tayi ta isa bakin ƙofa ta ɗaga murya tace "Malammm", da wani mugun zafin nama Sa'adatu ta rufe mata baki, Maimuna kuma ta kama zaninta sai muzurai take, habawa ai Nabilah kifowa tayi daga kan gado sbd dariya, Maama ta kwace bakinta tace "zaku bayar ko a'a?", haɗa baki sukay su kace "zamu bayar", Maama ta hura tukubar hanci tace "jikinku ya huta" ta fizge zaninta daga hannun Maimuna. daga waje Baba ke neman ba'asin kiransa da akay, Maama ta sake ɗaga murya tace "daman cewa nayi barka da hutawa". A take Maimuna ta buɗe jakarta ta lalo duba ashiri ta miƙa mata a wulaƙance, Sa'adatu kuma ta kira Zeenatu tana mata wata maganar ƙirsa tace ta turo mata mutsabbai, da kyar Sa'adatu ta lusar da Maama cewa gobe da safe zata fita Pos ta ciro mata kuɗin. Da sassafe kam Maama ta tayar mata da mandiran zuciya, haka ta fita tasha wahala harta nemo pos ta ciro kuɗin ta kawo mata, tinda Maama taga dubu hamsin dumuss a hannunta ta fara shirin zuwa gidan Balaraba, ƙarfe goma na safe ta fice don saida ta bari Baba ya fita, tana isa gidan abokiyar cin mushen nata ta azalzale ta, sharp sharp Balaraba ta shirya suka saɓi hanya, tin ƙarfe sha ɗaya suka fita amma basu dawo ba sai yamma liƙis, gidan Balaraba Maama ta tsaya ta huta snn kuma ta amsa mata tambayoyin da take ta riƙonsu tin bayan fitowarsu daga wajen malamin tsamiya, ruwa kawai tasha ta hau surfa mata tambaya, Balaraba tace "kai Jama'a tinda fa yace aiki ya kammala to mgana ta ƙare", Maama da idanunta sukay jajur tsabar wahala ta tafiyar mota da ƙafa tace "da farko fa cewa yayi tabbas yaga ana biki, kuma aure sai an ɗaurasa", Balaraba tace "ai kece kika ringa cewa ga abinda kike so ayi, kinga kin ce masa a sawa yaron tsanar yarinyar kuma da ya duba allon bokancinsa yace miki hakan bazai yiwu ba sbd yaron akwai addini, ba za a iya samun galaba dashi cikin sauƙi ba, idan kwa aka matsa to lokaci zai ƙure har ranar auren tazo ba a samu galabar ba, shine yace ya sami lagon yaron wanda dashi zaiyi amfani, kuma ma yace aiki ya kammala kawai ki jira lokaci", Maama ta sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tace "yanzu dai ba matsala knn?", Balaraba tace "kwarai kuwa, ki saki jikinki ki shiga bidirin biki, daga gefe kuma ki zubawa sarautar Allah ido kiga ta inda ɓaraka zata ɓullo", tin daga wnn moment Maama ta samu peace of mind, daga gefe guda kuma tana jiran ranar da faɗima da shegiyar ƴarta za suji kunya.


★Wani irin fresh Hajar tayi, fatarta tayi luwai luwai har wani sheƙi take sbd gyaran jikin da akai mata na sati biyar, ga wani sassanyar kamshi da yake tashi ajikinta, duk inda ta gifta sai ƙamshi, ko a waje ta zauna sai ya ɗauki lokaci ƙamshin bai baje ba, ilahirin jikinta kamshi yake, gashinta kam tamkar gonar furanni masu ƙamshi, babu inda take zuwa, ba ta shiga rana shiyasa gyaran yayi armashi, ko kitchen Anty ta hanata shiga, idan ma aikin za tayi iyakacinta palour da ɗakuna amma banda gaban wuta da rana, Nura kam kullum yana kan hanyar zuwa, ɗaiɗaikun ranaku ne kawai baya zuwa, ji yake tamkar ya janyo lokacin akay masa ita kawai, wata shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsu a wnn taƙin, Yau ma dai mai gyaran jiki tazo tayi mata ta gama ta tafi, toilet ta shiga tayi wanka, ta fito tana wani ƙamshi na daban wadan ya gauraya da wanda take zubawa kafin shigarta wankan, zama tayi kan stool ta janyo sabon man da take shafawa na gyara fata da saka glowing, a tsanake take tattale fatarta da tayi wani laushi da santsi, ita kanta yaba kyan da tayi take a zuciya, Hafsa ce ta shigo hannunta riƙe da cup, ajiye cup ɗin tayi kan mirror tace "ki shanye yanxu ki bani kofin na mayar mata", Hajar ta ɗauki kofin ta kwankwaɗe ta miƙa mata empty, ( Ehen ba fa maganin mata bane, it's not good a bawa budurwa, maganin infection ne da cire dattin golden organs of a woman). doguwar riga ta material ta saka snn ta fita palour, zama tayi kan kujera tana latsa wayarta, tanan suke magana da zainab akan bikin musamman ma walimar da zatay, Anty ta fito da shirin fita da jaka a hannunta tace "ina Hafsa?", Hajar tace "tana kitchen", kitchen ɗin Anty ta shiga, bayan few seconds ta fito tace "na tafi", Hajar tace "A dawo lfy", tace "Ameen", snn ta fita, su Anty an shiga ruruma don yanxu bikin saura 1week, sha'anin jera gidan amarya suka karkata. A hankali Hajar ta dafe kanta tace "subhanallah innalillah wa'inna ilayhirraji'un" sakamakon gabanta da ya yanke ya faɗi ba gaira ba dalili, sau huɗu yana mata haka bayan zamanta a palourn, wayar ta ajiye ta miƙe ta tafi kitchen wajen Hafsa, Hafsa tace "Abu zaki ɗauka ne?", girgiza kai Hajar tayi tace "nope nagaji da zama ni kaɗai", Hafsa tace "kinga ki fita ynxu zan fito bari na gama zuba seasoning a miyar", Hajar tace "kawo na ɓare miki maggin", Hafsa tace "A'a zanyi da kaina, Anty fa tace ki dena shiga kitchen", turo baki tayi ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa ta fita, tana ƙoƙarin zama gaban nata ya sake faɗuwa, nan ma dai Addu'ar tayi, har bayan Sallahr isha'i abinda take fama dashi knn, a hankali ta tashi daga kan dardumar da tayi sallah ta nannaɗe, wayar tace tayi ƙara wanda ya razanata tsabar rashin sukunin da ya risketa a bazata, ta ɗauki wayar tana kallon mai kiranta, ( ya sayyadi na) haka tayi saving, picking tayi ta kara wayar a kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke snn yace "Hajar", tace "Na'am", yace "dan Allah fito na ganki, gani nan a ƙofar gida".......✍️


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{30..}
Shiru tayi na some seconds kafin tace "tom" ta katse kiran, da dogon hijab din da tayi sallah ta fita, Humaira da Hafsa ne zaune palour, Abdallah ya fita masallaci salla, Hajar tace "Hafsa zan fita ƙofar gida", Hafsa tace "okay zuwa yayi knn?", gyaɗa mata kai kawai tayi ta nufi ƙofa, ta ƙetare small compound ɗin gidan ta buɗe ƙofar gate ta fita, jingine ta gansa da jikin gate ɗin, street light ta haska masa fuskarta, yayi ajiyar zuciya yana kallonta sosai, jinginar da kanta tayi jikin gate ɗin itama tace "ina yini", tini hancinsa ya cika da scent ɗinta, da cool voice ɗinsa yace "lfy alhmdllh, ykk?", tace "am fine", ya juyo sosai yana kallon yace "Hajar", kanta a ƙasa tace "Na'am", yace "karki bari azkar ya fita a bakinki, kinga dai ynxu zaki shiga ruruma, ki dage da Addu'a kinji", gyaɗa masa kai tay tace "insha Allah", ta ɗago ta kallesa tace "amma dai lafiya ko?", yayi ajiyar zuciya yace "alhmdllh", tace "ni kuma sai naga kamar you're not okay", keenly yace "partially", tace "me yake damunka?", murmushi yayi yace "ai tinda na ganki komai ya wuce, na dawo normal", tace "da gaske?", yace "uhmm", shiru ne ya ɗauka na wasu ƴan sakanni, ya katse shirun da faɗin "toh me kika shirya a bikin?", ta girgiza kai tace "ba komai", yace "ba komai, babu abinda za kiyi?", ta gyaɗa kai, murmushi yayi ya zaro envelope daga pocket ɗinsa, miƙa mata yayi yace "take", tace "meye wnn ɗin?", hade gira yayi yace "i said take", tasa hannu ta amsa tace "nagode", yace "good girl, toh shiga gida saida safe", tace "Allah ya tashemu lfy", har ta juya zata shiga sai kuma ta fasa ta juyo ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, murmushi yay mata ta mayar masa snn ta shige. Ranar talata da yamma Hafsa ta rakata wajen salon, Anty tace tayi amfani da kuɗin da ya bata, wankin kai na musamman akay mata, natural aka bar mata gashin, steaming kawai aka ƙara mata bayan wash and set, sai kyalli gashin yake da sheƙi, daman baƙi ne siɗik shiyasa sheƙin yay yawa, Hafsa ma aka wanke mata nata, kafin magrib suka dawo gida, da wuri Hajar ta kwanta sbd ciwon kan da ya dameta uwa uba faɗuwar gaban da take fama da ita, washe gari da sassafe wacca za tay mata lalle tazo, saida tayi breakfast wanda kawai turawa take snn ta zauna aka fara shaɗana mata lallen, jan lalle kawai akay mata banda baƙi, inda za ai baƙin akay mata shi da ja, waoh lalle ya samu inda yake so wato farar fata ga kuma jiki yaji gyara, duk da yadda kanta ke ciwo haka ta jure aka rangaɗa mata kunshinta, mai lallen ce ta yarfa mata kitso sirara mai kyau two steps, sha biyu na rana angama mata komai, tayi kyau harta gaji kamar a sace ta, kaf suka shirya suka wuce ainahin gidan biki sbd a ranar akwai ƴar gaɗa da ƙawayenta suka shirya. lfy ƙalau aka gudanar da shagalin gaɗa a wani kango da aka gyara tsaf dake bayan gidansu, washe gari Alhamis saura kwana ɗaya ɗaurin aure wato ranar Juma'a, a ranar akay walima wacca ta ƙawatu matuƙa daidai gwargwado, Hajar tasha kyau har ta gaji. Maama kam bata tsoma hannunta akan komai ba haka ƴan ci ku bamunta, saidai fa zuciyar nan baƙi ƙirin tamkar ta iblus.


★Baba ne zaune bisa bencin mai siyar da dankali da doya a bakin titi, mai dankali dake cin banɗashen gurasa yace "mal Adamu gobe ne ko?", Baba yace "insha Allah, bayan Sallahr Juma'a za'a ɗaura", mai dankali yace "anan ƙofar gidan naka?", Baba yace "Eh", mai dankali ya luƙa wata ƙatuwar yankan gurasa baki yace "so samu ayi a masallacin juma'a na unguwar nan, yafi sarari kuma ga albarkar mutane", Baba yace "Eh saidai nafi son a ɗaura a ƙofar gidana, ƙofar gidansu yarinya", mai dankali ya jinjina kai yace "hakan ma yafi wllh, Allah ya kaimu goben", Baba yace "Ameen". wata shimfiɗeɗiyar mota mai numfashi ce tazo ta wuce, har tayi nisa sai kuma ta dakata kafin ta dawo da reverse, adaidai saitin benci da Baba da mai dankali ke zaune ta tsaya, tsayuwar motar a wajen ya katse musu firarsu, mai dankali ya suɗe hannu ya miƙe ya isa gaban motar sbd a zatonsa siyar dankalinsa ko doya za ai, tsaye yayi bakin motar yana gwalo ido yana jiran a buɗe ayi masa ciniki, da yake glass din motar tint ne don haka ba'a ganin wnda ke cikinta, back seat aka buɗe a hankali, wani mutum ne ya fito wnda yake sanye cikin wata shegiyar shadda, kawai kallon Baba yake kamar yadda Baban shima ya ƙura masa ido, mutumin ya saɓa babbar rigar jikinsa yana micincina idanu, miƙewa Baba yayi daga kan bencin, mutumin ya tako har kusa da Baba yace "Adam", Baba da shima ya ganesa ainun yace "Muktar", Alhj Muktar ya miƙawa Baba hannu sukay musabaha yace "duniya mai yalwa, Adam daman kana garin nan?", Baba yayi murmushin manya yace "Muktar ai kai zan tambaya daman kana garin nan, tinda nidae a sanina ai kana Abuja", Alhj Muktar yace "shekara ta sha biyar da baro Abuja na dawo Kano", Baba yace "ba masaniya", Alhj Muktar ya gyara babbar rigarsa ya samu waje ya zauna kan benci, Baba ma ya koma ya zauna, Alhj Muktar da yake jin wani daɗi na ganin aminin nasa da ya jima yana nema yace "ya bayan saduwa, ya iyali?", Baba yace "bayan saduwa sai alkhairy, iyali lfy alhmdllh an gode Allah, ya naka iyalin Muktar?", Alhj Muktar yace "Alhmdllh, amma dai ba'a kano kake zaune ba?", Baba yace "kano nake zaune Muktar", Alhj Muktar yace "baka koma Yola ba knn?", Baba yace "Eh, nan nake rayuwa da iyalina saidai dangina na can Yola", Alhj Muktar yace "masha Allah" ya faɗi hakan yana duba tsadadden wrist watch ɗin hannunsa, Baba yace "shekara da yawa Muktar, ban taɓa tunanin zan sake ganinka ba", Alhj Muktar yace "ikon Allah....", bai ƙarasa maganar ba drivern sa ya fito hannunsa riƙe da waya dake tsuwwa, russuna yayi ya miƙa masa hannu bibbiyu cike da girmamawa yace "ranka shi daɗe ana kira", Alhj Muktar ya amshi wayar snn ya ɗaga kiran, maganar da bata wuce ta minti ɗaya ba yayi ya katse yana kallon Baba yace "Adam, zan sameka gobe a nan wajen", Baba yace "Eh to, ba damuwa zaka samen", Alhj Muktar yace "ko dai anan unguwar kake da zama?", Baba ya gyaɗa kai yace "a nan nake", Alhj Muktar ya jinjina kai yace "to ko bayan nan akwai wani wajen da zan iya samunka, insha Allah gobe fa zan dawo Adam", Baba yace "idan ma baka sameni anan ba, kana tambayar gidan gini shknn", Alhj Muktar yayi ajiyar zuciya ya miƙe, ya bawa Baba hannu sukay sallama snn ya doshi motarsa da driver ya buɗe masa ƙofa, mai dankali da ke daskare tin ɗaxu yaja baya gudun kar a markaɗe masa ƙafa, saida motar ta ɓace snn ya juyo ya kalli Baba, ya ƙaraso ya zauna yace "mal Adamu, wnn mutumin fa?", Baba yace "mutumin arziƙi wanda ya gaji ainihin arziƙi ba ƴan tashi firgigit ba, Muktar knn", mai dankali ya kasa kunne yace "yo Mal Adamu aini a duhu ka sake dulmiyani, ai ban gane me kake nufi ba", Baba ya dubesa yace "hmmmm, Idi knn" daga haka bai sake cewa komai ba.


★Ranar ta yau itace fa Juma'a, ranar ɗaurin auren Hajar, tin bayan sallar asuba ƴan uwan Umma suka ɗora sanwa, tuwo suka mulluƙa aka ɗaɗɗaura shi a leda aka zuba a ƙatuwar warmer, dabgen miyar taushe da taji tantakwashi itama aka juye ta a warmer, bayan nan aka shiga tuyar wainar shinkafa da sinasir, ga kuma gurasa da Mu'azzam ya kawo buhu guda. kai Hajar dai mai ƙashin arziƙi ce, tinda aka fara shagalin bikinta ba ai abu na ƙaranta ba duba da cewa gidansu ba masu hannu da shuni bane, komai an yisa cikin wadata, wnn magana ake ta masu arziki da yalwar zuci bata masu kuɗin banza da basu ciyuwa ba saidai a fito daga gida ana ƙombo, yo wasu masu kudin ma ai gidan su living hell ne. da gyatsine Balaraba ta shigo tsakar gida, duk wanda ke tsakar gidan nan kallon hadarin kaji tayi masa kafin ta faɗa ɗakin Maama, a karo na farko da Maama ta washe haƙora tin wayewar gari, Balaraba tace "wai haka aka mayar miki da gida sai kace na mahaukata Rabii", Maama ta taɓe baki tace "uhmm, baƙin cikin da nake shaƙa yafi ƙarfin kwatance", Balaraba ta ƙarewa Sa'adatu da Maimuna dake bacci kallo tace "su kuma basu tashi ba", Maama tace "ai jiya ba a barmu munyi baccin kirki ba a gidan nan", Nabilah da ke malelewa ƙasan siminti tace "Anty Balaraba ina kwana", Balaraba tace "yawwa". Maama ta matso kusa da Balaraba ta rage murya can ƙasa tace "kinga dai babu wani cigaba, anya kwa aikin malamin nan yayi?", Balaraba tayi yadda Maama tayi tace "hmm ai zuwa nayi na tayaki farin ciki, snn nima nasha kallo, don tinda malamin tsamiya yace ba aure to magana ta ƙare, kedai kawai mu zuba ido", Maama tayi ajiyar zuciya ta gyaɗa kai tamkar tsohuwar ƙadangaruwa. Tin daga soro har zuwa ƙarshen lungun ƙunshi aciki yake taf da jama'a, maza wanda suka zo halartar ɗaurin aure, ƴan uwan Baba na Yola da abokan arziki, ga dangin umma. daga soro kuma waliyyin Amarya da sauransu ne zaune suna jiran dangin Ango, lokacin ɗaura aure harya gota amma har yanzu dangin Ango basu hallara ba. Naseer da ke zaune soron ya dubi agogon hannunsa, yayi kyau sosai cikin farar shaddar da ya saka ta ankon da sukay shi da Huzaifa da Mu'azzam da kuma mahaifinsu, Naseer yace "lfy kuwa, ya har yanxu basu iso ba", Bappa ƙanin Baba wanda shi ne waliyyi yace "Baka da lambar wani daga cikin dangin Angon?", Naseer yace "ba nida ita Bappa", Mu'azzam ya shafa aljihun wandonsa yace "bari ni na kira Bappa", Bappa yace "yawwa, marmaza kira su, jama'a na jira", Mu'azzam ya ciro wayarsa daga pocket ya shiga kiran Nura Ango tinda lambarsa yake da ita, sau uku ya kira tanata ringing amma ba'a ɗaga ba. tsayawa yayi yana kallon uncle din nasa, Bappa yace "ya akay?", Mu'azzam yace "ba'a ɗauka ba"..........✍️


💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{31..}
A tare Baba da Bappa suka dubi Mu'azzam, Naseer yace "ka sake kira", Mu'azzam yace "tom" snn ya sake dialing numbern Nura, respond din dai daya ne, Baba da hankalinsa ya fara tashi yace "A ɗan jinkirta zuwa nan da minti goma sha biyar, ko wani uzirin ne ya riƙesu..", Bappa ya gyaɗa kai yace "ai ba jiran bane damuwa, jama'ar da suka taru kuma ba a rasa masu wani appointment din bayan wnn ba", Naseer yace "insha Allah yanxu zasu ƙaraso". Bappa yace "toh Allah yasa kar abar mutane a tsaye", kai har minti sha biyar da Baba ya ambata babu alamar dangin ango, tuni mutane suka fara canza fuska harda masu cewa su sauri suke, a yanxu kam hankalin Baba ya kai maƙura wajen tashi, Mu'azzam kam tinda ya koma gefe yake kiran lambar Nura. Naseer yanata duba agogon wayarsa, Bappa ya sharce zufar da ta wanke masa fuska sbd zafi, soron a cike yake da mutane gashi kuma ba a aiwatar da abinda ya tara jama'ar ba. kai abu fa ya fara wuce jira domin har an fara sidetalks, Huzaifa ne ya fito daga cikin gida ya durƙusa gaban Bappa yace "ko muje gidan nasu a jiyo lfy tinda nan gangare ne bamu da nisa", Bappa ya karkaɗa ɗan yatsansa yace "samm, ba zamu zubarwa da kanmu mutunci ba, a cigaba da jiran nasu, ai idan matsala ce waya zasu bugo", Huzaifa ya tashi ya koma kusa da Mu'azzam yana tambayarsa ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login