Showing 48001 words to 51000 words out of 114314 words

Chapter 17 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

aure, tinda kin fi son ki zauna a gida nida ke muna haɗa kafaɗa toh shknn ai ga fili ga mai doki, waccan ɗakin dai kwalli ɗaya tak da shi kaɗai zaki tsira...", Ruqayyah ta sake rushewa da kuka tace "na shiga uku na lalace, Momy kun karanta lettern da na bari kuwa?", Momy tace "ai lettern taki ce tasa akay cancelling komai, ki ɗauki kayanki ki fita, mu dosa zama nida ke a gidan nan tinda haka kike so", da gudu Ruqayyah ta fice a ɗakin tana kuka sosai, Momy tace "Au kayan fa.", Ruqayyah na shiga ɗakinta ta zube a kan gado, kuka ta ringa yi kamar ranta zai fita, wai an mayar da kayan lefenta kuma anyi cancelling aurenta da dearest, sharce hawayen da ya jiƙa mata cheeks tayi ta janyo wayarta, dialing numbernsa ta sake yi, ai tasan dearest ɗinta bazai fasa aurenta ba, Momy da Daddy ne kawai suke zancensu, tinda tayi masa message tace ya jirata tana nan dawowa garesa ai end of discussion, kuma she's very sure ya yarda da ita, wasu twin tears ne suka zubo a cheeks ɗinta jin wanda take da hope a kansa har yanzu wayarsa switched off, sister ɗinta Kulsoom ta shiga kira, Kulsoom na ɗagawa Ruqayyah ta fashe mata da kuka tace "na mutu na lalace sister..", a rikice Kulsoom tace "Ruqayyah kina ina?", Ruqayyah tace "am home sister, ina gida, ina cikin lukutar masifa da bala'i", Kulsoom ta sauke ajiyar zuciya don ba ƙaramar firgita tayi ba tace "toh wace masifa kuma?, tinda kinga dama kin dawo gida ai shknn", da muryar kuka Ruqayyah tace "mayarmin fa da kayan lefena sukai kuma wai anyi cancelling aurena da dearest..", tsaki Kulsoom tayi tace "ke dalla malama kin cika min kunne, uban wa yace kice ba kya son auren, ai abinda kike so akai miki", Ruqayyah ta zaro ido tace "billahillazi la'ilaha illa huwa ni bance bana son auren ba, wllh bance haka ba..", katseta Kulsoom tayi tace "dakata malama, kinsan irin baƙin fenti da kikai mana kuwa?, kin san irin kunyar da kika bamu kuwa, har yanzu tabon abinda kika aikata bai goge ba, dan wulaƙanci kuma kika kashe wayarki, da farko ma dai ina kika je?", Ruqayyah ta haɗiyi wani ɗaci tace "Egypt naje", Kulsoom tace "au ƙasar ma kika bari, toh me ya kaiki Egypt?", Ruqayyah tace "later zan miki bayani sister, ni yanzu so nake ki tayani bawa Momy da Daddy haƙuri don Allah su bar maganar cancelling auren nan", ta rushe da matsanancin kuka tace "wllh i can't imagine me loosing Nurain, na shiga uku na lalace, help me sister..", Kulsoom tayi tsaki tace "lallai Ruqayyah surely you need a Psychiatrist don kwakwalwarki ta taɓu..", Ruqayyah tace "naji ko ma me zaki ce kice nidai ki temakamin", Kulsoom tace "ehmm toh ki kira ya Aysha wataqila ta taimaka miki nikam I can't face our parent da maganarki, sai anjima girki nakewa mijina..", ƙif ta kashe wayarta, Ruqayyah ta ringa kallon screen ɗin wayar baki buɗe. kamar wata marainiya haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saida akay Sallahr magrib snn ta tashi tayo alwala tayi sallah, zaune tayi kan prayer mat ta rasa abinda ke mata daɗi, ƙarfe tara da rabi na dare ta tashi ta fito palour, kitchen ta shiga sbd ta samu wani abun ta zuba a cikinta, tin abincin jirgi babu abinda ta sake ci ko ruwa ba ta sha ba, kwata kwata ma bata da wani appetite, fridge ta buɗe tana neman koda fruit ne, ai kam dai babu fruit, glass cup ta ɗauka ta bude fresh milk, rabin cup ta zuba snn ta mayar da bottle din madarar fridge, sai kace mai shan maganin haka ta ɗaga ta kwankwaɗe tana yamutsa fuska, har wani amai ne ke taho mata. room ɗinta ta koma ta kwanta tana jin kanta na juya mata, har dare ya raba babu alamar bacci a idonta, kawai tunanin moment ɗinta da Nurain take, idan ta tuna cewa wai an mayar da lefe kuma an fasa aure sai hankalinta ya ɗugunzuma. sai wajajen Asuba snn bacci ɓarawo ya figeta.


★Washe gari Sa'adatu ta cakare kwalliya cikin matsattsun kayan da ta saba snn ta zumbula hijab har ƙasa, ta dubi Nabilah dake saka riga tace "wllh kin fiya nawa Nabilah, tin ɗazu baki shirya ba", Nabilah tace "ke Malama sauri fa nake yi", Maimuna tace "Sa'adatu nima na shirya mu tafi tare.." haɗe gira Sa'adatu tayi tace "A'a yi zamanki ban gayyace ki ba", Maimuna ta taɓe baki tace "ku kuka ga duhu da kunje dani da ni zan biya kuɗin Napep zuwa da dawowa", Sa'adatu ta yatsine fuska tana mata kallon hadarin kaji tace "ji faƙiriyar talaka, ni za kice zaki biyawa kuɗin Napep, mtsww dalla can riƙe tsiyarki, ke daman ba cin arziƙinki ake ba uwar mammaƙo kawai...", Maimuna tace "A'a kinga malama karki gayan ba daɗi mana, tinda kince dai ba zaki dani ba ai shknn magana ta ƙare". Sa'adatu tace "kin samawa kanki salama kuwa". Maama ce ta shigo da kwanon abinci tace "kai jama'a har sai rana tayi zafi baku tafi ba", Sa'adatu taja dogon tsaki tace "wllh Nabilah ce, sai kace ba ƙaruwarta ba, tayi abu da jiki sai wani salalo-salalo take kamar dodon koɗi", Nabilah tace "kai jaraba nagama mu tafi" ta zaro takalminta daga karkashin gado tana kwamawa, Maama tace "ke Nabilah dan Allah ki tsaya ki musu abinda suke so kema ai kya fito gari, ɗan kuɗin nan ki ringa samu muma ki tsammana, karki musu kauyanci da gidahumanci da sakarci", Nabilah tace "idan abin baifi ƙarfina ba zanyi", Maama tace "yawwa ku salallaɓa ku fita karku bari malam yaji motsinku". tamkar munafukai haka suka fita ɗakin suna tafiya a hankali. Hajar da ke tsakar gida tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kai ta cigaba da abinda take. bakin titi suka fita suka tsarar da Napep, Sa'adatu ta faɗi unguwar da zai kaisu, mai Napep yana cewa zashi ba wani ciniki Sa'adatu ta shiga, Nabilah tabi bayanta tace "ba kuyi ciniki ba", mai Napep yace "kuɗin ku dubu ɗaya ne", Nabilah ta zaro ido za tay magana Sa'adatu tace "Allah ya kaimu lfy", suna hawa saman titi Sa'adatu tace "sai munje zaki fahimci me nake nufi..", Nabilah dai tace "uhmm". tafiya mai nisa sukay suka isa unguwar da zasu, a bakin wani annakakken gida suka sauka, Sa'adatu ta fello duba ɗayar mai Napep ta basa. wani lafiyayyen gida suka shiga, Nabilah sai kalle kalle take, Sa'adatu ta riƙe hannunta har suka shiga cikin gidan. direct wata ƙofa Sa'adatu ta murɗa sai gasu a wani katafaren palour. Zeenatu da ke zaune kan sofa tana cin cake ta juyo jin ƙarar ƙofa, zaro ido tayi ganin Sa'adatu, ta taso da sauri ta rumgumeta tace "nayi masifar kewarki baby", Sa'adatu tace "nima haka, ina baby Mabruk?", Zeenatu tace "tana ɗaki tare da Teema", Sa'adatu tace "hegiyar kati yaushe tazo?", Zeenatu tace "jiya, wace wnn?" ta nuna Nabilah, Sa'adatu tace "mu shiga daga ciki nayi miki bayani". Zeenatu ta nunawa Nabilah kujera tace "zauna ga guri", Nabilah ta zauna tana kallon damfareriyar TVn dake palourn, kitchen Sa'adatu ta shiga ta jibgo kayan ciye ciye tray guda, a gaban Nabilah ta girke tana mata wani shegen murmushi. Nabilah ta ringa kallon kayan ciye ciye yawunta na tsinkewa. kusa da Zeenatu Sa'adatu ta zauna ta ɗauki cake ɗin da take ci ta kai baki, Zeenatu ta rage murya tace "itama ƴar hannu ce?", Sa'adatu tace "ke ƴar uwata ce fa, sabuwa ce fil a leda", Zeenatu tace "Allah itama ta amince ta shiga ƙungiyar tamu?..", Sa'adatu ta dubi Nabilah tace "Eh, ta amince", Zeenatu tayi wani makirin murmushi tace "gaskiya ni zan buɗeta daga kwali, bari na jarabata", Sa'adatu tace "toh", Zeenatu ta miƙe tana gyara kwalar rigar da ta bayyana rabi da kwatan ƙirjinta tace "baiwar Allah ya sunanki?", Nabilah da ke yagar naman kaza tace "Nabilah", Zeenatu tace "wow sunanki yayi min daɗi, taso muje", Nabilah ta ajiye naman hannunta tace "ina?", Sa'adatu tace "wai me Maama ta gaya miki ne, bafa cinyeki za tayi ba aikinki zata nuna miki". Nabilah ta miƙe tabi bayan Zeenatu suka shiga wani ɗaki. ko minti goma ba suyi da shiga ba Nabilah ta fito a fusace hannunta riƙe da gyalenta, Sa'adatu ta saki cake ɗin da take ci ta miƙe tsaye ganin Zeenatu ta fito itama a fusace, a hasale Zeenatu tace "ki fita da wnn bagidajiyar daga gidan nan Sa'adat idan ba haka ba nasa karnuka na su yagalgala namanta", Sa'adatu ta dubi Nabilah da ke huci jikinta na kyarma a hankali tace "mene haka Nabilah?", a hasale Nabilah ta ɓarka mata ashar snn ta wuce fuu ta fita daga palourn. da sauri Sa'adatu tabi bayanta, wani uban sauri Nabilah take zabgawa har ta doshi gate, tana fita waje tabi layin tana tafiya zuwa bakin titi, Sa'adatu biye da ita har suka ƙarasa main road. babu wanda yace da wani uffan har aka saukesu a bakin lungunsu, Nabilah na fita ta shiga lungunsu da sauri, Sa'adatu ta biya kuɗi snn ta biyota, adaidai ƙofar gida Sa'adatu tace "kin san bazaki iya ba shine kika zubar min da mutunci da kima", a karo na farko Nabilah tace "mutuncinki da kimarki duk sunci abu ta kaza kazan su, da ke da ƙawayen naki duk mahaukata ne ƴan iska tsinannu, dabbobi kawai, jakai marasa ilimin addini bare na boko..", Sa'adatu ta mulmulo ashar tace "jar bala'i daga temako shine kike zagina", Nabilah tace "an zage kin kiyi abinda zaki.." ta wuce cikin gida a fusace. da gudu Sa'adatu ta bita ta cakumota a tsakar gida, Nabilah ta juyo ta wanka mata wani mari na bazata, habawa ai hannun Nabilah bai gama leveling ba Sa'adatu ta ɗaga nata itama ta wanke ta da mari, lokaci guda suka kaure da dambe, Umma da tin shigowarsu take kallonsu tana daga tsaye inda take kwashe kaya akan igiya tace "kai ku bari mana..", Maama ta fito da sauri tana tafa hannaye ta shiga raba su, dambe kawai suke ba ji ba gani, Hajar dai na tsaye daga bakin ƙofar ɗakin Umma tana kallon ikon Allah, saida zanin Maama ya kwance garin raba faɗa amma basu saduda ba, Maama faɗi take "ba zaku bari ba, ke Sa'adatu bari mana, Nabilah ba magana nake miki ba, ku bari nace, ku wuce ɗaki kuyi acan cikin sirri...", Maimuna ma dai ƴar kallon ta zama tana dariya ƙasa ƙasa, ba wai su ƴan uwa ba aka wareta aka ƙi tafiya da ita ai gashi ba aje ko ina ba ta jagwale musu. da kyar Maama ta ɓamɓaresu tace "hauka kuke, mene haka?", sai huci suke suna kallo juna sai kace wasu maƙiya ba waɗanda suka fito ciki ɗaya ba, Sa'adatu ta goge bakinta da ke fitar da jini tace "wllh saina rama", Nabilah tace "idan kin fasa baki haifu ba", bangaje Maama Sa'adatu tayi ta cakumo Nabilah, damben da yaci uwar na farko suka ɓarke dashi, har ƙasa Nabilah ta yaga zumbulelen hijab ɗin Sa'adatu, takaici yasa Sa'adatu ta kama doguwar rigar Nabilah ta dire mata ita har ƙasa, cikin bacci Baba ya jiyo hanyaniya, fitowa yayi ya tsaya yana kallonsu. ɗakinsa ya koma ya ɗakko carbi, yana fitowa ya nufesu ya shiga tsula musu a jiki, ai dole suka rabu sbd zafin carbin, da hannu Baba ya nuna su yana so yayi magana amma wani tari ya sarƙesa, tamkar zai fitar da ruhinsa haka yake tarii, Umma tazo ta janyesa ta shiga dashi ɗaki. Maama da takaicin ƴaƴan nata ya turnuƙeta tace "abinda ku ka tarka knn?, ciwon zuciya za ku samin iyee?, dambe sai kace karnuka, me ya haɗa ku?", Nabilah da ta cukuikuiyo rigarta da ta ɓarke tace "wai wnn mahaukaciyar yarinyar shine ta kaini wajen tumakan ƙawayenta har suna ƙoƙarin taɓamin jiki...", Sa'adatu tace "ƙarya take munafuka, mai kai a tukunya kawai, wai fa aikinta za a nuna mata shine ta fara hauka da ballagazanci", Maama ta riƙe haɓa tace "mu shiga ɗaki karku tonawa kanku asiri a bainan nasi a tambara min ku, ku wuce ɗaki", Maama ta haɗa kawunansu ta turasu ɗaki.


★A hankali Hajar take cin abincin da ke gabanta, yamutsa fuska take cike da rashin jin daɗi sbd lower abdominal cramp da ke damunta, tin safe ta tashi da ciwon gashi har dare bai dena ba saidai yana lafa mata time to time, abincin ta ture ta sha ruwa ta haye gado ta kwanta gefen Sabra, Umma ce ta shigo ɗakin, ganin Hajar ta kwanta ga ragowar abincinta nan bata cinye ba ta kira sunanta, Hajar ta miƙe zaune tinda ba bacci take ba tace "Na'am..", Umma tace "ya baki cinye abincin ba?", Hajar na yamutsa fuska tace "na ƙoshi", Umma tace "ya ciwon yayi sauƙi?", girgiza kai Hajar tayi tace "A'a", Umma tace "toh taso muje chemist tinda yaƙi lafawa gwara ayi miki allura kawai", zaro ido Hajar tayi tace "Allah bana son allura, magani zan sha", Umma ta ringa kallonta kafin tace "toh bari na kira Mu'azzam sai ya taho miki da magani" ta ɗauki wayarta ta kira Mu'azzam, yana ɗagawa tace "kafin ka shigo gida ka biya ta chemist ka siyowa Hajara magani", yace "wane iri?", Umma ta kalli Hajar snn ta mika mata wayar tace "fada masa sunan maganin da kike sha ɗin", Hajar ta amshi wayar ta gaya masa. bayan kamar minti sha bakwai sai gashi nan ya shigo da maganin, tinda Hajar tasha magani ta samu relief, daman duk month sai ta samu cramp though ba ta flowing heavily amma dai abin na wahalar da ita. washe gari kam sumul ta miƙe ta fara harkokinta, yau dai kam Baba ya fita aiki, Umma kuma ta shirya zuwa Wajen Iya don haka Hajar ta bari a gida, Hajar na zaune tsakar gida akan kujera tana cin gyaɗa, Sabra ta shigo tace "Adda zan ci abinci", Hajar ta tashi ta zuba mata taliyar hausa da manja da yaji tinda ita ta dafa, Sabra ta amshi abincin ta wanko hannunta ta zauna tana ci. Hajar tace "ki yi sauri lokacin islamiyya ya kusa", Sabra tace "toh" ta cigaba da zuƙar taliyarta cike da yarinta. Maimuna ce ta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji sai kace wata tsohuwar guzuma, kan Sabra da ke cin abinci ta tsaya tace "ke je ki wajen Iliya mai awo ki aunomin shinkafa ƴar hausa gwangwani huɗu" ta faɗa tana miƙa mata kuɗin hannunta, Sabra tace "toh bari na ƙarasa cin abinci", fatali Maimuna tayi da kwanon abincin tace "kee ni sa'ar kice ko sa'ar uwarki da zan aikeki kice sai kin gama cin abinci", Sabra ta sunkuyar da kai tana hawaye ta ƙi amsar kuɗin, damƙota Maimuna tayi ta miƙar da ita tsaye ta kifa mata mari tace "ba magana nake miki ba", ɗaure fuska Hajar tayi tamkar wacca bata taɓa murmushi ba tayi wurgi da gyaɗar da take ci. gam ta riƙe hannun Maimuna da ta ɗaga zata sake saukesa akan fuskar little sister ɗinta......✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{25..}
Maimuna ta wancakalar da hannunta tace "dalla malama cikani", Hajar bata tanka mata ba ta fizge ƙanwarta da ke kuka sosai, hawaye ta share mata tace "je ki wanke fuskarki, zan zuba miki wata taliyar, yi sauri kinji yarinyar kirki kar ayi miki dukan makara a islamiyya", a hankali Sabra ta wuce bakin rariya, Hajar ta ɗauki ledar gyaɗarta ta zauna ta cigaba da ci, baki buɗe Maimuna ke kallonta kafin ta mulmulo ashar tace "kut melesi, ke shegiya Hajara ina ruwanki dani, ina yiwa ƙanwata hukunci za ki shiga, ke asu wa iyee?, shegiya da ke kawai ƴar gaba da fatiha..", Hajar da zuciyarta ke tafarfasa hundred degree celsius ta mike tana kallon Maimuna, ji take kamar ta fizge tsumman zanin da tayi ɗaurin ƙirji dashi saita nuna mata aikin shegantaka da hujja, da sauri ta shige ɗaki zuciyarta na zafi don tabbas in ta tsaya zata iya waskatarwa da Maimuna mummuƙe. Maimuna ta koma bakin ƙofar ɗakin tace "ashe dai tsoro ne, da ki tsaya mana ki ga yadda zan yagalgala ki, da saina waskace miki ƙugun nan mai zubin na ƴar duniya, shegiya nunar rana...", Hajar kam zama tayi kan leda ta dafe kanta, calming kanta kawai take cause tana so tayi keeping promise ɗin da tayi, wllh ba daban promise din ba da sai ta gayawa Maimuna maganar da har ta mutu bazata manta da ita ba. wai itace shegiya nunar rana mai ƙugun ƴan duniya duk ita kaɗai, shiyasa bahaushe yace muni tudu ne ka taka naka ka hango na wani, wai har Maimuna ce za tace mata nunar rana ita ba taga kanta bane ai tafi kama da nunar rana tinda itace me bleeching irin na ƴan tasha iya fuska, kuma ƙugu ta godewa Allah yafi nata da yake flat sai kace an ɗaurawa muciya zani, gsky ita fa an mata katsalandan a al'amura, itafa haƙurinta bai kai nan ba wllh, bai kai gejin da za ayi mata rashin mutunci ko a gaya mata magana ta haƙura ba, amma dai yau Maimuna taci darajar masu daraja, ita kaɗai ta ringa sauke ajiyar zuciya tana huci, har Sabra ta shigo tayi shirin islamiyya tace "Adda zan tafi", Hajar ta ciro 20naira a bayan wayarta ta miƙa mata tace "toh ga kuɗin makaranta", Sabra ta amsa tace "na tafi" ta ɗau jakarta ta fita. Hajar ba ta sake fita tsakar gida ba, wayarta ta janyo ta buɗe data ta shiga whatsapp, yaushe rabon da ta shiga ita chatting bai dameta ba, saida tayi upgrading Whatsapp ɗin sbd ya zama outdated, ai kam ga unread messages nan rututu daga friends ɗinta na islamiyya da boko, message ɗin Zainab ta gani a sama ƙasansa kuma na Hafsa, tana gama karanta message ɗin Zainab ta taɓe baki ta shiga mayar mata da reply tinda online take, Zainab tayi mata reply da "Hajar kiji tsoron Allah daga tambayarki mutum sai kice kin saita masa hanya", Hajar ta yamutsa fuska bayan ta karanta ta rubuta mata "uhmm ke nifa ban ma basa fuska ba, na gaya miki ya sayyadi ya maye ko ina".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login